Yadda ake Hada Lemon Kankana da Lemon Tsami

 Yadda ake Hada Lemon Kankana da Lemon Tsami

 

Kayan hadi:

•  Kankana

•  Lemon tsami/ Lemonade

•  Sukari/sirof

•  Filebo

Yadda ake hadawa:

Uwargida za ki fara dafa sukarinki ya zama ruwa amma fa kada ki bar shi ya kone idan ya dahu shi ne abin da ake kira sirof sai ki ajiye a gefe guda. Shi wannan sirof din ya fi saukin amfani a kan ki yi amfani da sukari na ainihi.

Sai ki yanka kankanarki ki fitar da kwallayen sannan ki markade yadda za ta yi laushi sosai. Sa ki samu kofin da kike hada lemo ki zuba a ciki sannan ki kawo lemon ana sayar da shi a manyan shagunan kayan masarufi idan kuma ba ki da shi za ki iya yin amfani da lemon tsami.

Idan kika matse sai ki ki tace shi da kyau ki tabbatar babu komai a ciki sai ki juye a kan kankanar nan sai ki dauko sirof dinki ki zuba ki kuma kawo filebo mai kanshin kankana ki zuba, sai ki juya ki sa a firiji don yin sanyi.

 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top