Yadda ake hada ‘Meat Pie’
Kayan hadi
Fulawa
Butter
Gishiri (kadan)
Nama ko kaza
Dankalin Turawa
Attarugu da albasa
Magi
Curry da thyme
Bakar hoda (Baking powder)
Meat pie cutter
Man gyada (in soyawa za a yi)
Oben (in gasawa za a yi)
Meat mincer
Hadi
Bayan uwargida ta yanka nama ko kaza, sai ta silala da magi da curry da thyme da albasa har sai naman ya yi laushi. Sannan sai ta tsame ta zuba a meat mincer ta gauraya naman. In ba ta da meat mincer sai ta yayyanka naman kanana sannan ta jajjaga shi da attarugu.
Sai ta sa manta kadan a kan wuta kafin ta mayar da dakakken naman ta yanyanka dankalin Turawa, sannan sai ta dafa shi, sai ta yanka shi kanana. Sai ta hada da dakakken naman a wuta tana gaurayawa. Idan sun nuna tare sai ta sauke daga wuta.
Sai uwargida ta dauko fulawarta ta zuba butter kamar karamin cokali biyu da bakar hoda da gishiri kadan.
Sai ta yi ta kwabawa da dan ruwa kadan. Sai ta yi masa kwabin cincin.
Sannan sai ta sa shi a tire filla-filla kamar za ta yanka cincin. Sai ta dauki meat pie cutter ta yanka. Sannan sai ta zuba kayan su naman da dankalin a tsakiyar meat pie cutter sannan sai ta kulle. Ta soya.
Ko kuma ta gasa shi a gas. Lallai sai kunnen maigida ya yi motsi.