Yadda Ake Kosan Dankali Mai Hade Da Nama

 

Yadda Ake Kosan Dankali Mai Hade Da Nama

KAYAN HADI : –

Dankali
Nama
Kwai
Attaruhu
Albasa
Maggi
Gishiri
Man gyaďa
Fulawa ko garin busashen buredi

*YADDA AKE HADA WA*

Da farko ki wanke nama ki zuba a tukunya sai ki zuba maggi da gishiri ki tafasa sai ki kwashe ki zuba a turmi ki jajjaga tare da albasa da attaruhu idan yayi laushi sai ki kwashe a kwano ko roba,sannan ki dawo kan dankalin turawa ki tafasa yayi laushi sai ki murmushe shi ko kuma ki jajjaga a turmi sai ki kwashe shi a cikin kwanon da kika kwashe naman da kika jajjaga sai ki ďauko kwai ďanye ki fasa a kai, ki zuba fulawa ko garin busashen buredi a ciki ki sa gishiri da maggi ki juya sosai, ki ďauki farantin suya ki zuba man gyada ki ďora a kan wuta ki dinga ďiba kina zuba wa a cikin man gyada mai zafi idan ya soyu zaki ga yayi brown sai ki kwashe kiyi wa Oga yayi breakfast DA SHI

WANI IRIN SALON HADIN

KAYAN BUKATA*

Dankalin turawa
Nama
Fulawa
Kwai
Albasa
Attarugu
Gishiri
Maggi
Man gyada

*YADDA AKE YI*

Ki jajjaga albasa da attaruhu ki kwashe a kwano ko roba sai ki ďauki dankali ki tafasa ki zuba a turmi ki daka shi amma kar ya yi laushi sai ki kwashe a cikin kwanon da kika zuba jajjagen attaruhu da albasa ki tafasa nama shi ma ki daka a turmi duk ki hada da sauran kayan hadin ki juya, sai ki dinga mulmulawa kina tsomawa a ruwan kwai ki juya shi a cikin fulawa ki jefa a cikin man gyada mai zafi ki soya , akwai daďi matuka…

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top