Yadda ake Kunun gyada sabon Launy Kashi na 2

 Yadda ake Kunun gyada sabon Launy

Kashi na 2

#Kayan da ake bukata;

#Farar shinkafa 3 tins

#Danyar gyada 4 tins

$Sugar dai-dai misali.

Abu na farko da ake bukata uwar gida ta yi, shi ne ta gyara farar shinkafarta danya sai ta wanke ta ta tsane tsaf,

Bayan haka,dama kin soya gyadarki sama-sama kin murje bayan km kin bushe sai ki kai a markado miki bayan an markado ki tace.

Sai ki zuba tataccen ruwan gyadar a tukunya in ya tafasa, sai ki dakko wanna shinkafar da ki ka wanke kk km tsane sai ki zuba ta a ciki suyi ta dahuwa har sai ta dahu sosai in kina gudun kada ya tsinke zaki iya zuba ruwan lemon tsami kadan.

Idan kuma kin ga bai yi miki kauri ba sai ki dan dibi gasarar koko ki dama da ruwan sanyi sai ki zuba ki juya sosai zai yi kauri insha Allah

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top