Yadda ake Lemon Kwakwa da Madara kayan

 Yadda ake Lemon Kwakwa da Madara

kayan Hadi:

KwaKwa 

Madarar kwakwa ko Madarar ruwa

sukari

filebo

Yadda ake hadawa:

Da farko uwargida za ki gyara kwakwarki, ki cire bakin da ke jiki.

Sa’annan sai ki wanke ta tas ki goge. Sai ki zuba ruwa a kai, sa’annan ki tace. Sai ki dauki ruwan ki juye a cikin kofin da kike hada lemo a ciki.

Sa’annan sai ki dauko madarar kwakwa (Coconut milk ko kuma madarar ruwa) sannan sai ki zuba ruwan sukari na sirof, Sa’annan sai ki kawo filebo ki zuba akai. Sai ki bar shi ya yi sanyi.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top