Yadda ake salad din kayan lambu da Dankalin Turawa
Abubuwan da ake bukata
Dankalin Turawa
Koren wake (green beans)
Karas
Koren tasshi
Albasa
‘Broccoli’kayan kanshi
Kayan dandano
Man gyada
Hadi
A kankare karas a wanke shi, sannan a wanke koren wake da ruwan gishiri da Broccoli da koren tasshi. A fere Dankalin Turawa sannan a tafasa da gishiri kadan sai a ajiye a gefe.
Bayan haka, sai a yayyanka karas manya-manya a wanke a zuba a cikin tukunya da koren wake da broccoli da gishiri kadan sannan a zuba ruwa shi ma kadan a rufe tukunya na tsawon minti daya sai a sauke.
A zuba man gyada kadan a tukunyar tuya sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken koren tasshi a yi ta juyawa sannan a tsamo hadin broccoli da karas da koren wake a zuba a ciki da kuma Dankalin Turawar a yi ta juyawa.
Sai a zuba kayan dandano da kayan kanshi domin kara wa girkin armashi.
Za a iya cin wannan girki da farar shinkafa ko da dafa- dukanta. A ci dadi lafiya!