Yadda ake Soyayyen Dankalin Hausa na musamman Da Miyan Kwai

 Yadda ake Soyayyen Dankalin Hausa na musamman Da Miyan Kwai

 

#Soyayyen dankalin hausa

Miyar kwai

#Yam ball

#Meat ball

#Fish ball

#Kunun gyada

#Kunun kwakwa with milk

#Farar shinkafa with coconut

#Farar shinkafa with bota

#Stew

#Kunun zaki na gyada

#Lemon aya

#Zobo with cocumber

#Zobo with pineapple

#Coconut drink

#Pineapple with orange

#Fruit salat

#Special taliya

#Tuwon shinkafa

#Miyar agushi da ogun

#Miyar zogale

#Miyar gyada

#Miyar ganye

Yanzu ne zamu dauki daya bayan daya domin yin bayani dalla-dalla uwar gida ki biyoni abaya don ki ga yadda abin zai kasance cikin yardan Allah.

Soyayyan dankalin hausa:

Kayan da ake bukata

Dankalin Hausa

Salt & maggi

Citta & kanunfari

Mai

Yadda ake yi

Da farko uwargida xa ki fere dankalin ki tsaf sai ki yayyanka shi dai-dai yadda ki ke son shape din sa amma idan ki ka yanka shi ta tsaye wato dogayen yanka ko kuma ki yi mishi round shape yana kyau sosai bayan haka sai ki zuba shi a ruwa in ya dau dan lokaci sai ki wanke ki tsame shi a mataci ki dan barbada gishiri ki jujjuya

Sai ki dora manki a wuta yai zafi ki yanka mishi albasa idan tayi ja sai ki zuba dankalin idan ya soyu zaki ga yy ja, in kuma farar suya ce xa ki sa cokali mai yatsu ki caka idan yayi baza kiji garas -garas ba toh ya soyu sai ki tsame shi a haka har ki gama.

In kina so zaki iya daka cittarki da kanunfari ki marmasa magi star sai ki barbada akan dankalin ki sa dan yaji da mai ki juya sai ci uwar gida in ki ka yi wasa kunnen oga sai ya kusa tsunkewa don dadi,

In kuma kina so zaki iya ci da wannan miyar mai zuwa;

Miyar kwai

Kayan da ake bukata

Kwai(egg)

Tomato

Pepe(attarugu)

Onion

Mggi & salt

Kanunfari & citta

Oil

 

Yadda Ake Yi

Ki yayyanka onion, peppe, tomato dan kadan saboda miyan kwai ba ta son tomato mai yawa domin mata da yawa suna son suyi miyar kwai sai dai suna cika tumatir wanda ke jawo labarin ya sha ban-ban, saboda ba ta dadi, domin mai house ya fi son yaji abu mai dadin gaske ta yadda za ki sace zuciyar shi idan ba abincinki ba bazai iya cin abinci ba ko a ina ne .

Uwar gida bayan kin kammal sai ki samo man gyadarki ki soya shi da albasa idan ya soyu ki zuba kayayyakin da kika yanka tomto, peppe, onion idan suka soyu xa ki sa dakakkun citta da kanunfari,sai ki kawo kwanki da kika fasa kk kada amma ya zama suna da yawa bayan ya kadu sosai sai ki kwara shi akan soyayyan kayan miyan da ke wuta zaki iya juyawa za km ki iya barin shi haka ba sai kin juyaba shi kenan miyan kwai ta kammala sai a zuba akan soyayyan dankalinnan, dadin ba’a magana, sai dai kun zo ci.

 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top