Yadda ake Tuwon Shinkafa miyar Ganyen Ugwu

 Yadda ake Tuwon Shinkafa miyar Ganyen Ugwu

Kayan hadi

Tuwon shinkafa

•   Shinkafar tuwo

•   Ruwa

Hadi

A jika shinkafar tuwo a ruwa ta jika kamar na awa daya. Sai a dora ruwa a wuta bayan ya tafasa sai a wanke jikakkiyar shinkafar a zuba sannan a rage wuta a rufe da marufin tukunya. Bayan minti 20 zuwa 25 sai a sauke a tuka. A kwashe a leda sannan a ajiye a kwano wa maigida.

 

Miyar ganyen Ugwu

Abubuwan da za a bukata

•         Ganyen Ugwu

•         Ganda

•         Kifi banda

•         Albasa

•         Tumatir

•         Attarugu

•         Magi

•         Kori

•         Manja

•         Garin tafarnuwa

Hadi

A wanke ganda da ruwan zafi sannan a sanya  a tukunyar dafa ganda a yanka albasa kadan da gishiri sai a rufe a dora a wuta. Bayan minti 40 sai a sauke a ajiye a gefe. A wanke ganyen Ugwun da gishiri da ruwa sannan a yayyanka a ajiye a gefe. A wanke kifi banda da ruwan zafi sannan a gutsura shi kanana a ajiye a gefe.

A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja bayan ya yi zafi, sai  a zuba yankakkiyar albasa da tumatir da jajjagen attarugu a yi ta soyawa har su soyu. Bayan sun soyu, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa da dafaffen gandar, bayan ya dan tafasa sai a zuba ganyen Ugwun a jira na tsawon minti uku zuwa hudu sannan a kwashe.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top