Yadda ake Yam ball (kwallon Doya)

 Yadda ake Yam ball (kwallon Doya)

 

Kayan da ake bukata;

Yam

Onion

Peppe

Spices

Egg

Maggi

Salt

Yadda ake yi:

Da farko dai uwar gida za ki fere yam ki yanka ta manya sai ki wanke ta tsaf kisa ta a pot da dan ruwa dai-dai misali ki zuba salt kadan sai ki barta ta dahu sosai yadda baza ta ba ki wahalar dakawa ba.

Idan ta dahu sai ki dakko tsaftattun turmin ki da rabaryar ki, ki rika tsamo doyar kina sa ta a turmi kina daka ta in ta daku sosai sai ki kwashe a mazubi mai tsafta amma fa wajen dakawan kada tayi lukwi kamar dakan sakwara kuma kada ki yi sama-sama don irin shi ne ke jawowa ta rushe a cikin mai sai a kula saboda ayi abin yadda zai kayatar sosai dama kin Riga kin daka tarugu da onion kin sa kayan kamshinki da maggi da gishiri, sai ki dan sa ruwa kadan don su narke sai ki zuba akan dakakkiyr yam din ki juya sosai in km kinga bai juyu ba sai ki mayar turmi ki bubbuga har y biyu sosai.

$Bayan kin kammala dakan kin kwashe sai ki rika dunkula shi kamar ball(kwallo),

Sai ki kada kwai ki sa mishi albasa wadda kk yanka kanana ki xuba salt sai ki juya ki yanka wa mai albasa ki Dora a wuta ta soyu sai ki dinga dakko wannan dunkulen yam din ki rika tsomawa a cikin wannan ruwa egg din sai ki sa su cikin soyayyan mannan in yayi zai yi brown shi kenan sai ki tsame

Aci lafia.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top