Yadda Akeyin Dambun Nama: Filin Girke-Girke
Da farko zaki tsaftace naman ki ki masa yanka manya manya bakya buqatar qana nan yanka saiki juye shi a babbar tukunya (kina buqatar babban tukunya saboda dambun ki ya sake a ciki yadda zaki kyakykyawan suya) saiki kawo albasa dakika yanka kika gyara ki juye, tafarnuwa ki daddaka ki juye, curry sai kisa rabin robar, ki bar rabi, zaki juye thyme, maggi, citta, kanimfari ki hade su da naman ki gauraya kibar naman ki zuwa awa biyu saiki dora shi a wuta ki kawo ruwa daidai yadda zai shanye.
1
Idan namanki yayi laushi zaiza kamar haka kina taba shi da muciya zai fashe, saiki tsaya ki sa muciya kina tuqashi
2
Haka zakiy ta tuqashi har sai ya hade gaba daya
3
Sai kisa mai da dan dama (man gyada ko na kanti)
4
Zaki dauko Rabin curry dakika bari acan ki juye shi
5
Saiki wanke taruhu ki jajjaga ki juye akai
6
To anan zaki rage wuta sosai saboda zakiy su yan dambu baya son wuta a hankali ake soya shi saiki na tuqawa akai kai
7
Kina tuqawa yana qara duhu shine alamar yana dauko soyuwa
8
Gashi nan yadda kike gani a hoto ya qara yin jaaa(shi dambu yana buqatar jajircewa saboda yana daukan lokaci musamman in yanada yawa kamar wannan)
9
Gashi nan kamar yadda kike gani man cikin dambun ya fara kumfa shine alamar dambun ki yakusa sauqa
10
Fitowar mai kamar haka shike nuna dambun ki ya soyu ba sauran ruwa a jiki
11
Gashinan
12
Saiki tsame shi ki juye a cikin abin tacewa
13
Zaki matsamin kina matse wa mai sai ya fita gaba daya
14
Saiki baza shi ya huce sannan ki Adana shi yadda ya dace
15
16
![]() |
Dambun Nama |
Done👍