Sakwara da Miyar Karfasa
Abubuwan da za a bukata
• Doya
• Kifi; karfasa
• Manja
• Barkwano
• Albasa
• Magi
• Kori
• Garin tafarnuwa
Hadi
Uwargida ta fere doya sannan ta wanke ta Dora a wuta har sai ta yi laushi. Sannan sai ta Dauko turminta tana jefa dafaffiyar doyar tana dakawa har sai ta yi laushi. Za ta iya zuba ruwan zafi domin samun sakwara mai laushi.
A yanka albasa sannan a daka barkono ya yi laushi sosai kuma a wanke kifi yadda ba za a ji karninsa ba. A Dora tukunya a wuta sai a zuba manja. Sannan a zuba albasa ta Dan soyu sannan a zuba jajjagen tumatir har sai ya soyu. Sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa da kuma dakakken barkono
A zuba kifin sannan ruwa kaDan. Sai a rufe bayan mintin talatin sai a sauke.
Agajahub publishers