YADDA ZA KI HADA NADADDEN KWAI DA NAMA

 YADDA ZA KI HADA NADADDEN KWAI DA NAMA

Kayan Hadi

Kwai

Nama

Mai

Maggi

Attaruhu

Albasa

Curry

Gishiri

Fulawa

Yadda Za Ki Hada

Dafarko dai zaki dafa kwanki yadda kikeso idan yadahu sai ki sauke, sai ki bare kwan ki rabashi gida bibbiyu ko hudu yadda dai kikeso, sai ki hada namanki ki dafashi ya dahu sosai idan yadahu sai ki dauko turmi ki zuba attaruhu, albasa, curry, maggi ki dakasu sai ki dinga diban naman shima kina zubawa kina dakawa haka dai kamar dambu amman sai dai shi bazaki soya shiba.

Idan yadaku sai ki sami karamar roba ki dibi fulawa kamar cokali 6 yadai danganta da yawan namanki sai ki kwaba da ruwa batai tsululu ba kamar kullin fanke da dan kaurinta dai zaki kwabata sai ki zuba akan wannan hadin naman naki ki hada ki kwaba sosai zakiga naman yana danko alamun ansa fulawa kenan, sai ki dauko kwanki yankakke sai ki dinga diban naman kina shafawa ajikin kwan harse kinrufeshi dukansa da naman yazama ba a ganin alamar kwan sai naman kawai ake gani duk haka zakiyi har ki gama.

Idan kin gama sai ki fasa wani kwan danye ki dora mai akan wuta in ya yi zafi sai ki dinga tsoma wannan kwan me nama cikin ruwan kwan kina soyawa in kin ga ya yi dan ja kalar brown sai ki sauke haka zaki tayi har ki gama duka, sai abawa honey ya ci zakiga yana santi kamar kunnesa zai cire

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top