[6/19, 7:26 AM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
By
*maryam gital*
1
_*labarine daga alqalamin marubuciyar prince naik, ba ahlulkitabibace, nibras, da nufin rabbine, labarine da zai zo muku cikin sauya salo daga zaren tunanin marubuciyar tare da kaifin bakin alqalaminta, marubuciyar tayi shawagi tare dogon nazari cikin tunaninta ta hakaito muku labari me kamar gaske, labari me sauya tunanin mai karatu, labari na ilimantarwa, nishaɗantar, da samun darasi cikin nishaɗi da halin rayuwa, akwai haske da yardar Allah cikin littafin zakkata, kar ki sake a baki labari*_
_*labarin zakkatah, labarine na wani shahararren jami’in tsaro me gaskiya da jajurcewa kan aikinsa duk da qalubalen da yake fuskanta, jami’ine da ya banbanta da sauran, ta fannoni daban daban, yayi nisa babu me kamoshi sai wanda ya ci ɗamara irin ta jaruman maza,saidai kash akwai wata cuta me raunatarwa da sanya zubar hawaye cikin zuciyar jarumin, sannan a gefe yana da wani irin kyauta daga ubangijinsa me ɗauke baqin cikinsa amma baya hana shi zubar hawaye duk da qarfin zuciyarsa da jarumtarsa*_🤔
_*kaɗan daga labarin zakkatah*_
Motocine waɗanda daga lokacin da me kallo ya kallesu zai fahimci motocine irin na jami’an sojin nigeria, tafe suke cikin tsarin da iya sarrafa qarfen nasara, sun sanya wata mota baqa wuluk a tsakiyarsu, motoci biyune masu ɗauke da tambarin sojin nigeria a gaban baqar motar cike da sojoji ma’abota ɗamara, yayin da motoci uku irinsu suke bayan baqar motar, kai da kaga waɗannan motoci ba ma sai an ɓata baki gurin cewa kauce ba, da kanka ya kamata ka kauce saboda ruwan bindigogin da hancinansu suke shirye tsab su ta da mutum murus har lahira, duk titin da motocin nan suka ratsa saidai kaga ana basu guri, sai jiniya suke zubawa kamar sa tafi da kunnuwan mutane, abin burgewar shine yadda mutane suke daga gefe suke nuna farincikinsu da ganin waɗannan motoci duk da an san halin ɗan adam da tsoron soja, wai suka ce in ji hausa people “soja birgimar hankaka”
***********
Cikin wani tangamemen gida naga moticin sun faka, sojojinne kawai suke ta tsalle suna dirowa daga motocinsu cikin qwarewa da gwanancewa da aikin nasau da sanin makamar aiki, ikon Allah kamar qiftawar ido sojojin nan suka qame qam, ni dai har yanzu burina naga uban da yake cikin motar nan har ake ta wannan waɗari ya qi ya qare haka, tsaida tunanina nayi sosai ganin wani cikakken jarumin soji ya durfafi motar nan cikin nuna jarumta ya kai hanu ya buɗe murfin baqar motar na baya sannan ya ja baya cikin sanin makamar aiki ya sara tare da qamewa, hmmm ikon Allah sai kallo, ban san ya zan ce ba amma ganin wannan jami’i me tsananin kwarjini ya sanyani tuna rayuwar zaki a cikin namun dawa, fitowarsa da daidaituwar qafafunsa a kan qasa yayi daidai da qamewar jami’an nan kaf, kai kace basa numfashi, cikin taku irin na mazajen fama masu isa da izza ya fara tafiya ya tunkari qofar shiga cikin gidan, ɗaya daga cikin sojin ne ya dafe masa baya ɗauke da wata qarmar jaka a hannunsa suko sauran sai waige waige suke kamar su cinye mutum da rai…..
*********
“Gee Fawwaz fa ranka ya daɗe har yanzu bai da niyyar bamu haɗin kai, wannan yaron shegen taurin kaine da shi, kuma don ubansa yana bamu matsala amma sai qara ɗaukaka yake yi, general fa, general fa ranka ya daɗe, duk iya shirya makircinka amma ka zuba wa yaron nan ido yake nema ya kai mu rami tun ba mu mutu ba”
Shirgegen mutumin da yake kishingiɗe kan kujerane ya furzar da iska me zafi ta hancinsa sannan ya karkaɗa kai yace
“ni kaina ina ganin gazawata akan wannan taqadarin yaron, yaron da ina da tabbacin ubansa ma na girma bare shi amma ya zame min qadangaren bakin tulu, ka duba duk tabo da giɓin da muka yi wa rayuwarsa amma yana nan yana neman ganin bayana, wallahi ni ban taɓa ganin jami’i me kwarjinin fawwaz a idona ba, wannan shegen da a lokacin sahabbai akayishi da ba qaramin kafaffe za a yi kuma tsayayye akan aqidar addinin ba, ka duba wai dan ma a zamaninmu yazo amma yaro komai sai ya nuna cewa shi musulmine me gaskiya, ka ji shege fa wai shi na Allah, amma wallahi na kusa na wa gee fawwaz dirar mikiyar da zata tafi da sauran farincikinsa, akwai lokaci”
*********
Almajirine futuk yake tafiya bakin titi cikin dare misalin qarfe tara ɗauke da ɗan buhunsa, abune me sauqi ka gane raunisa da babunsa, hanu yasa cikin gajiyawa yana tsare masu ababan hawa amma abin mamaki daga ya faɗi gurin da zai je da yawan kuɗin hanunsa zasu fece, ya daɗe yana roqon alfarma sannan wani bawan Allah yace ya shiga ya kaishi don Allahn da ya roqeshi da sunansa ya bar kuɗinsa, godiya yayi sosai sannan ya hau bayan mashin, bayan ya sauka sai ya miqa wa me mashin ɗin buhun hanunsa yana murmushi yace
“nima na baka don girman Allahn da ka gani ka kawoni”
Da mamaki ya kallesa sannan ya mayar masa da martanin murmushinsa yana kaɗa kai yace “ka bar kayanka na kawoka don Allahne”
Shima murmushin yayi yace “ka iya karatu”
Maganar taso ta bashi dariya amma sai yace yana me mamakin almajirin
“eh, nayi karatu kuma na iya karatu both”
Cikin er shararsa ya sanya hannu ya cire wata er qaramar card ya miqa wa me mashin, kusan sumewa me mashin ɗin yayi da ya karanta takardar, hakan yasa ya ɗago a firgice wanda yayi daidai da janye tsohon rawanin da yake kan almajirin…..
Ku biyo er mutanen gital ma’ana
*MARYAM A.I GITAL*
_UMMIN BEAUTY_
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/20, 9:21 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*🌼
*Gargaɗi*
Ban yarda a juya min littafi ba, duk wanda ya canza ko harafi ɗayane Allah ya bi min hakkina👌🏻👏🏼
*2*
Tsaye yake rataye da hannayensa a baya, idanuwansa na kan wani babban enlargement dake manne a bango ko qyaftawa bayayi tamkar mutum mutumi, matashi za a kirashi don bazai wuce shekara arba’in ba, cikakken na mijine me siffar qarfi da jarumta tare da tsayayyen zati da ubangijinsa ya qaga masa, yana da tsayi amma a tsaye yake car be tanqwara ba, abune me sauqi a haɗa ido da shi a diririce saboda kwarjininsa da tsananin dakewarsa, abin da yafi ɗaure min kai ga wannan matashi shine zubar hawaye da naga yanayi ɗaya bayan ɗaya kan kumatunsa duk da wannan tsumewa tasa, idanunsa kuwa sun rikiɗe sun burkice saboda damuwa da zubar hawayen da yake ciki, na daɗe ina kallon ikon Allah sannan naga ya sake matsawa gab da hoton sannan ya ɗaga hanu ya ɗauko shi daga majinginarsa ya rungume a qirjinsa, take kukansa ya qara tsananta cikin wani irin yanayi me ban tausayi, abin da ya sake kashe min jiki shine shessheqar kuka da na ji yana yi, magana naji ya fara yi cikin shessheqar kukan
“na miki alqawari kuma sai na cika shi da izinin Allah, ki yafe min bazan iya barin aikina ba har sai na ɗau fansa, ki yafe min, ki yafe min, nine silar komai…….”
Kasa cigaba yayi da maganar sai ma durqushewar da yayi a gurin yana cigaba da tsiyayar hawaye, bazan iya qiyasce tsawon lokacin da ya ɗauka a durqushe a gurin ba abin da na sani dai ya ɗau lokaci me tsawo durqushe a gurin sannan ya miqe tsaye cikin qyaftawar ido abin kamar sarafawar computer, take raunin fuskarsa ya narke zuwa tsananin jarumta da tsoratarwa, hoton ya mayar ma’adaninsa sannan ya wuce zuwa ga wata qofa da nafi tsammanin toilet ne,
******
Tsaye yake a jikin madubi yana gyara maɓallan rigarsa ya ji an turo qofa, ta cikin madubin ya hango su, take fuskar en mazan ta sake rikiɗewa zuwa zallar farinciki da annashuwa
Macece da alamomi suka nuna cewar mahaifiyar wannan matashin ne suka shigo ɗakin da wata kyakkyawar yarinya wacce baza ta fi 4yrs ba, farace qal yarinyar saɓanin matashin da yake baina-baina, shi ba fari qal ba kuma baya cikin baqaqe kamar dai siffar dattijuwar nan, da gudu yarinyar ta cilla tayi gurinshi, shima hanu ya buɗe mata da sauri ya cafeta yayi sama da ita yana juyawa da ita yana cewa
“my cwthrt and lovely amrat”
Dariya take yi cike da murna tana cewa
“my dady…”
Dakatawa yayi ya zauna akan kujera tare da ɗorata kan cinyarsa ya rungumeta kamar zai maidata ciki, fuskarsa ya mayar kan mahaifiyarsa hajiya hafsat yana murmushi yace
“Allah ya taimaki mahaifiyata, ya qara mata lafiya da imani”
Ameen tace tana murmushin da yake nuna zallar qaunarta ga ɗanta
“mun tashi lafiya hajiya”?
“lafiya lau fawwaz, ya gajiyar hanya”?
“alhamdulillah hajiyata, yanzu nake shirin zuwa duboku sai ga ku”
Nuna amrat tayi da take saqale da hanu da cikin dadynta tace
“ka ganta nan fitinanniya ita ta dameni da tambayar daddynta tun ba a shiryata ba, tun ina ce mata yanzu zaka zo tana yarda har dai ta fara min kukan rigima wai sai na kawota gurinka”
Murmushin farinciki yayi ya ɗago fuskar yarinyar yace
“cwthrt ɗin daddy na makarane nima ban je duboki da wuri ba, jiya bayan na dawo kuma na je dubaki kina bacci, kiyi hakuri kin ji”
Dariya tayi tace
“toh dady”
Kanta ya shafa yace “yawwa my amrat, me kika kawo wa dadyne”?
Sauka tayi daga jikinsa ta riqo hanunsa tana cewa
“abinci zaka zo ka ci daddy, hajiya tace min ba kyau zama da yunwa, ko hajiya”?
Ta qarashe maganarta tana kallon hajiyar, gyaɗa kai hajiyar tayi tace
“sosai ma kuwa qawalliyata”
Faɗawa tayi kan cinyar hajiyar ta rungumeta tana dariya, farincikinta take nuna wa sosai idan hajiya ta kirata da qawarta, shi ko fawwaz ido ya zuba wa yarinyar cikin wani irin yanayi na tunani da damuwa, idanunsa har sun fara rikiɗewa, hajiyace ta kalleshi da nufin masa magana sai ta ga halin da yake ciki, gaba ɗaya yanayinsa ya canza, juyawa tayi ta kalli amrat tace
“qawata je ki gurin usaina ki ce ta ɗora min ferfesun cowtail gani nan zuwa, ki ce ta koya miki yadda ake yi ke ma, idan na sake buqata sai ki min kin ji”
Tsallen murna tayi ta fice daga ɗakin tana ihun murna,
Kallon tsab hajiya ta masa wanda hakan yasa ya sunkuyar da kai, cikin muryar lallashi hajiya ta fara magana
“haba fawwaz, haba fawwaz ummmm, yanzu ace haka rayuwa zata yi ta juya maka cikin qunci, ashe baza kayi tawakkali ba, shin baka san duk abin da ya faru da bawa muqaddarine daga ƴbangijinsa ba, a waje ka zama kamar mayunwacin zaki a gida kuma mace ta fika dauriya, ko so kake raina ya ɓaci in ɗauke amrat daga gidan nan, wataqila idan ta nisanceka ka samu nutsuwa, kar ka bari na yanke wannan hukuncin fawwaz, kana jina ko?”
ɗago idanunsa yayi waɗanda suka rine yana kallon mahaifiyarsa ya fara magana cikin rauni
“kiyi hakuri hajiya, ba laifina bane, babu yadda zan yi da zuciyatace, duk lokacin da naga yadda amrat take gudanar da yarintarta sai ta tuno min da safiyyata, hajiya ni na raineta fa ko kin mantane?, na fi kowa tuna yarintar safiyya da quruciyarta ashee….., Allah sarki safiyya…..”
“ya isa haka, shikenan, amrat zata koma gidan hajiya bilki, ba sai ka ganta ba sannan hankalinka ya tashi, ai shikenan”
“ki yi hakuri hajiya, ba zan iya barin amrat a wani gidan ba”
Yana gama faɗin hakan ya jingina bayansa jikin kujerar ya rufe idanunsa, hannayensa kuwa harɗe suke a kan qirjinsa
Cike da tausayawa hajiya take kallon ɗan nata, ita kanta ta faɗane don ta shawo kansa amma baza ta iya ɗauke amrat daga cikin gidan ba, domin ita ce farincikin gidan gaba ɗaya, ita kanta hajiyar yarinyar tana tuna mata rayuwar safiyya a tsakaninsu, dauriya kawai ta fi fawwaz, ajiyar zuciya tayi sannan ta tashi ta bar ɗakin tana me masa fatan samun sauqi a ranta
*******
Cikin shigarsu ta sojoji yake yana tsaye a gaban mahaifiyarsa tana masa adduar Allah ya kiyaye yayin da amrat take riqe da hanunsa sai tsalle tsalle take yi abinta, wayarsa da take hanun sunday ce ta ɗau ruri, da sauri ya miqa masa cikin ladabi irin nasu na masu ɗamara, karɓa yayi ya kara a kunnensa yana sauraro, take fuskarsa ta rikiɗe zuwa ɓacin rai, bai gama sauraron abin da ake faɗa mishi a yawa ba ya kashe wayar, ya juyo ɓangaren da sunday yake yace cikin dakakkiyar murya
“sunday”
A ɗimauce sunday yace
“sir”
“ka dakatar da kowa, tare da kai kawai zamu fita”
“yes sir”
Cewar sunday tare da sarawa sannan ya juya ya fice
“hajiya zamu wuce”
“Allah ya kaika duk inda zaka je lafiya, ya tsareka, ya kareka, ya baka nasara”
Ameen yace sannan ya sumbaci goshin amrat ya juya ya fice cikin zafin nama amrat tana cewa
“Allah ya tsare dady”
Duk damuwar da yayi da amrat ko juyowa be yi ya kalleta ba balle yace ameen
*******
Duk da a haukace ya shigo falon amma hakan bai sa ya kasa sallama ba, tamkar wani matashin zaki ya tunkari tiqeqen mutumin da yake kwance kan kujera kamar kayan wanki, qafarsa ɗaya ya ɗaga ya ɗora a kan kujerar da tiqeqen yake babu shakka balle shayi a tattare da shi, da yatsarsa ya fara nunashi yana masa kallon qasqanci sannan ya fara magana
“kar ka sake ka yi wasa da tunaninka, kar ka yi marmarin ganin yadda zaki yake farautar abinci a halin yunwa, ni fawwaz habeeb ba sai ka nemoni ba, ni zan nemoka sai na zame maka tamkar guguwa me tsananin turnuqu da qura mai yaji, zaka jini a lokacin da baka yi tsammani ba tamkar saukar aradu, na rantse maka da ubangijina sai na zame maka tamkar wuta mai tartsatsi da tsananin quna, ka saurara, akwai lokaci zakine ni bana tsoron namun dawa”
Yana gama faɗin haka ya sauke qafarsa qasa sannan ya curo qaramar bindigarsa ya ɗaga kansa sama ya saita wata kafaffiyar na’urar CCTV ya tarwatsata sannan ya cilla bindigar tana dawowa ya mayar da ita aljihu ya juya cikin takun jarumta tamkar matashin zaki
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/21, 7:32 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*3*
Kusan sumewa yayi a kishingiɗen da yake saboda bindigar da yaga gee fawwaz ya ciro, a tunaninshi shi zai harba da bindigar, duk da yasan ba qaramin gamgancine ga fawwaz ba ya harbi mutum irinsa har cikin gidansa, amma ya yarda da jarumtar fawwaz zai iya kasheshi a cikin gidansa ko da yana nufin qarshensa kenan a duniya, musamman idan ya tuna abin da yake tsakaninsu wannan ba qaramin aiki bane da yake da tabbacin gee fawwaz zai iya sadaukar da rayuwarsa akansa, da qyar ya samu ya daidaita numfashinsa ya mirgina ya sauka daga kan kujeran, kai tsaye ya wuce toilet don gabaɗaya cikinsa ya hautsine
************
“na faɗa maka ka iya takunka, idan ba haka ba wannan shegen yaron tun da ya furta to tabbas sai ya aikata, babu abin da zai hana gee fawwa naɗemu matuqar ya samu hujja ko ya kashemu ma gaba ɗaya, matuqar muna buqatar tsira to dole mu yi duk yadda za muyi mu ɓoye duk wani hujja da yaron nan zai iya amfani da shi gurin garqamemu, ka sanar da yaranka su ɗaga qafa kwana biyu, ni ma na dakatar da nawa, zamu dinga yin abin cikin iya taku da birne baya, wannan shine mafita”
“haka ne alhaji bala, ni zam faɗa maka qwarin kan yaron nan, ni da naga mutuwa tsirara muraran, Allah ya bamu sa’a”
“ameen alhaji tukur, ai ina tausayawa gee fawwaz matuqar yafaɗa komata wlh sai na ga bayansa, ka barshi kawai duk motsinsa ina sane da shi akwai wani kukan a gabanshi”
“hhhhhhhahahahah, nima ina tuna ranar da zai sake rungumar wata gawar, saidai ina da tabbacin wannan gawar ko addua bazai samu damar mata ba zai bita”
“hhhahahaha kai tukur kai ma fa shegen kanka ne, wane mugu, na sanka faɗa da cikawa kake”
Hmmmm, wannan shi ake cewa shirmen shiriritar shirmemme
*********
Zaune yake kan wata luntsumemiyar kujera cikin office ɗinsa yayin da sojoji suke tsaye car cikin office ɗin cikin shirin ko ta kwana, signing yake yi kan wasu takardu tare da buga musu stamp, yana kammalawa ya ɗaga waya, maganar minti biyu yayi ya ajiye wayar, cikin qanqanin lokaci ya shigo office cikin girmamawa ya sara tare da qamewa a gaban gee fawwaz, takardun da yayi signing a kansu ya bashi yana me jaddada masa sabon aikin da za su tunkara, sake sara masa yayi sannan ya fice daga office ɗin,
********
Alhaji nasiru da ahlinsa gaba ɗayane zaune a falon gidansa da yake rukun gidajen masu tudun aljihu, labaran qasa yake kallo tare iyalensa bayan kammala dinner, kallon suke yi suna taɓa hira a tsakaninsu cikin farinciki da kwanciyar hankali, matarsa hajiya maimunace zaune a gefensa ta dama yayin da babbar ‘yarsa zainab zee baby take zaune a ɓangarensa ta hagu sai qaramar qanwarta basma da take kwance kan cinyar zee ɗin, qaninta hisham me binta kuma yana qasa zaune kan rug tsakanin qafar hajiya da alhaji, sake nutsuwa suka yi tare da dakatawa da hirar tasu lokacin da aka fara rawaito labaran da rundunar sojin qasar suka fitar ta bakin gee fawwaz, gangamine rundunar tasu za ta sake yi tare da baza komarsu kan ‘yan fashi da garkuwa da mutane da suke cikin dazuzzukan da suke tsakanin bauchi da jos da kuma tsakanin jos da kaduna, wannan wani gangamine na musamman tare da sa hanun gee fawwaz, cikin bayanin da gee fawwaz ya yi ya tabbatar wa manema labarai da cewar baza su bar wani ɗan ta’adda ya shaqi numfashi da kyau a waɗannan dazuzzukan ba, musamman dajin falgore da maqwabtansa, yayi alqawari sai ya tsabtace dajin da iznin Allah, fatansa da roqonshi ga jama’a su tayasu da adduoin samun nasara.
Abin burgewa cikin labaran na gee fawwaz shine yadda yake bayanin cikin dakewa da nuna rashin tsoro da zallar jarumta, sai wani murmushi ma da yayi irinta nasara a kan camera, murmushin da yayi nasarar sake jefa zuciyar zainab a tara dan ba na ce uku ba, har aka qare labaran idanuwanta na kan tv, dukkan alamomi sun nuna idanunta ne kawai a gurin amma hankalinta baya gurin ko kaɗan, sai tattauna lamarin iyayenta suke yi har da qaninta amma ita sai shiru wai mushriki ya ci shirwa
“keh ummee, lafiyarki kuwa”
Cewar hajiya maimuna
A firgice ta juyo sannan ta sauke ajiyar zuciya tare da qirqiro murmushi tace
“ba komai mummy”
“wani hausan ba komai gashi nan ana miki magana amma kin tafi wata uwa duniya”
Murmushi ta sake yi ta kwantar da kai tace
“ayya mummy, labaran gee fawwaz fa nake kallo”
“gee fawwaz”?
Hajiya maimuna tace cikin yanayin tambaya tana kallon alhaji
Murmushi alhajin yayi yana kallon zaina yace
“uwata duk labaran fawwaz ɗin ne ya sanya nai kiranki baki uku, mummynku kuwa sai da tayi biyu amma baki ji mu ba”?
Waro ido tayi cike da mamakin kanta tace
“haba dai dad, kira biyar fa kenan”
Kaɗa kai yayi cikin tabbatarwa yace
“sosai ma kuwa, a na shida kuma kika amsa ba”
“ohhh shett!!!, toh me ya sameni kenan, sorry dad, mummy am very sorry ban ji ku ba wallahi”
Murmushi dai hajiya da alhajin suke yi suna kallonta cike da mamaki, hisham da tun da aka fara maganar zee bai sa baki bane yace
“ke dai er rainin hankalice, tsabar iyayi wai me ya sameki, su hajiya zaki faɗa wa wannan amma bani ba, dan na san komai”
Harara ta banka masa cike da masifa tace
“wai kai wannan yaron ni sa’arkace, Allah dad kace hisham ya fita harqata ko in masa rashin mutunci wallahi”
Ta qarasa maganar bayan ta mai da hankalinta kan dady, tun kafin dadyn yace wani abu hisham yayi saurin cewa
“kin daɗe baki yi rashin mutuncin ba, bari ma in tona miki asiri sai ki ji daɗin rashin mutuncin”
Mai da kallonsa yayi kan dady yace
“wallahi dady son gee fawwaz takeyi, bata da aiki sai tura pics ɗinsa a wayarta da editing ɗinsu, idan qaryane a duba wayarta waɗansu hotunan ma ta haɗesu ne da nata, kuma ka duba ka gani dukkan hotunan za ka ga ta sanya gee my life a jiki tsabar rashin aikin yi”
Wayyo zee kamar ta cinye hisham ɗanye cikin fushi ta ɗauki remote ɗin da yake gefenta ta jefeshi da shi, da ta ga hakan be mata ba sai ta tashi ta ture basma daga jikinta a qufule zata bishi mazauninsa, ko me ta iya da wannan matashi oho
Dad ne ya riqota yana cewa
“yi hakuri uwata koma ki zauna, an ji kina son fawwaz ɗin sai aka yi yaya uban ‘yan gulma?”
Ya qarasa maganar yana kallon hisham,
Cikin dariya hisham yace
“me ruwana a ciki dad, na san dai iskace take wahalar da me kayan kara, wannan fawwaz ɗin ba sa’anta bane”
“kai ka faɗi haka ko?, to ni kuma bari in faɗi tawa maganar inshaa Allahu matuqar kina son fawwaz ba ki da miji sai shi, ki kwantar da hankalinki uwata”
Kunyace ko borin kunya oho, ɗaura hanunta tayi akan fuskarta tana jiniya ta bar falon tana buga qafa, duk falon babu wanda bai yi dariya ba saboda hatta iyayenta sun gano tana sonshi da gaske kukan da take yi ma borin kunyace
ISLAM IS MY IDENTITY
************
[6/23, 2:39 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*4*
Cikin qasaitacciyar takunsa irinta jarumta yake shiga cikin gidan, ɓangaren mahaifiyarshi yayi kai tsaye domin dubo lafiyarta da ta tilon gudan jininsa,
Zaune ya samu hajiyar kan rug tana duba kur’ani sanye da farin glass a idanunta, yadda bakinta yake motsi da er qaramar sautin da take fitowa daga bakinta zai tabbatar da karatun kur’anin take yi
Tsananin farin cikine ya lulluɓeshi sakamakon ganin mahaifiyarshi cikin wannan yanayi, shiyasa yake alfahari da samun iyaye masu tsananin riqo da addini, shiyasa kullum yake cikin kewar mahaifinshi tare da masa fatan samun rahamar ubangiji saboda kyakkyawar tarbiyar da ya ɗorashi a kai
Gefen hajiya hafsat ya je ya zauna yayi shiru yana sauraronta, saida ta kammala suratul waqi’ah sannan ta dakata tayi adduointa suka shafa tare sannan ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace
“fawwaz ka qaraso”?
“eh hajiyata, mun tashi lafiya”?
Yace yana murmushi
“lafiya lau, ka baro gurin aikin naka lafiya”?
“alhamdulillah hajiya, ya qawarki, na jita shiru”?
“bacci take yi, tun da aka mata wanka ta koma baccin wai sai babanta ya dawo a tasheta, sanyi take ji”
Cewar hajiya
Miqewa fawwaz yayi ya nufi hanyar ɗakin amrat da yake cikin ɗakin hajiya yana cewa
“hajiya ko dai bata jin daɗine tun da tace sanyi take ji”?
“to me ‘ya, jeka ka dubota da kanka, ko ba ta da lafiyar ne, wannan uwar iyayi da manyancen ai zata faɗi abin da ya fi haka ma”
Shidai fawwaz murmushi yake yi ba tare da yace komai ba ya tura qofar ɗakin ya shiga,
Idanunsa ya sauke a kanta, kwance take tana sheqar baccinta cikin kwanciyar hankali, tayi kyau sosai cikin barcin kamar a sace ta a gudu, domin ba qaramin kula yarinyar take samu daga mai rainonta ba, tsab tsab da ita gwanin sha’awa
Bakin gadon ya zauna yana murmushi ya ɗago da kanta ya ɗora a kan cinyarsa yana shafa kanta tare da faɗin
“cwthrt, cwthrt tashi ki ga dadynki”
Bai daɗe yana kiranta ba ta wata miqa ta rungumeshi tare da shigewa jikinsa sosai tace cikin muryar barci
“dadyna”
“na’am ‘yar dady, bacci ake yine”
Buɗe idanunta tayi a hankali ta ɗago kanta tace
“eh dady, yau ba school in ji nanie”
“haka ne amma kin ci abinci”
Cike da iyayi ta yi alamun mamaki tace
“dady…, yaushe hajiya za ta barni in yi bacci idan banci komai ba”?
Dariya yayi cike da qaunar yarinyar ya sake rungumeta yana cewa
“to tashi mu je gurin hajiyar, nima yau ina da lokacin wuni da ke my cwthrt”
“yehhh dady” tace sannan ta bashi kiss a goshi tace
“nice father”
Shima cikin qauna ya ɗagata sama ya sumbaceta a kumatu yana cewa
“nice daughter”
Qyalqyalewa take yi da dariya har suka wuce zuwa gurin hajiya.
Hajiya tana ganinsu ta fara dariyar ita ma tana cewa
“k’awalli an tashi kenan, an ga dady”?
“eh” amrat tace tana sak’ale da wuyan babanta
Da sauri ta sauka daga jikin baban ta nufi ɗan madaidaicin fridge a ɗakin hajiyar ta buɗe tana kallon abin da yake ciki, rufewa tayi ta ɗauko wani qaramin plate ta sake buɗe fridge ɗin ta ɗauko apple guda biyar ta ɗora a kai ta juyo ta nufi dadynta, duk abin da take yi idanu hajiya da fawwaz suka zuba mata suna kallon manyancen yarinyar
“dady gashi ka ci ka ji”
Murmushi yayi yace
“to my amrat zo mu ci tare”
To tace sannan ta ɗale kujera ta zauna kusa da shi ta sanya hanunta ta ɗauko ɗaya ta mik’a wa fawwaz sannan ta ɗauko wata zata kai bakinta ya rik’e hannun, kallonsa tayi da yanayin tambaya tace
“dady”?
“cwthrt kin manta daga bacci kika tashi, jeki ki wanke bakinki sai ki zo ki ci ko?”
Murmushi tayi tace
“toh dady”
Sannan ta sauka ta shige toilet ɗin hajiya ta wanko bakin sannan ta dawo ta ɗauki apple ɗin suka fara ci da baban, shi dai fawwaz duk abin da yarinyar takeyi idanunsa na kanta, ko maganar hajiya zai amsa baya ɗauke ido daga kan yarinyar, duk abin da yake yin hajiya tana lura da shi, sai da ta barsu suka cinye apples ɗin sannan tace
“ni ko fawwaz ya maganarmune”?
Sai da zuciyarshi ta harba amma cikin nuna rashin fahimta yace
“wacce maganar kenan hajiya”?
Gyara zama hajiyar tayi tace
“maganar aure mana fawwaz, ya kamata fa kayi auren nan, lokaci daɗa qurewa yakeyi ko baka la’akari da hakan ne”?
Take annurin fuskarshi ya ɗauke, sai ma alamomin damuwar da ta lulluɓe fuskar
“ya kamata zuwa yanzu a ce ka cire komai a ranka, kai ko kaɗan ne ya kamata ka rage ka auro wacce zata maye maka gurbin safiyya”
Hajiyace ta ci gaba da faɗin hakan cikin lallashi
Sai a lokacin fawwaz ya yi magana cikin tashin hankali da damuwa
“bazan samu madadin safiyyata ba hajiya, ta banbanta da sauran mata hajiya, na daɗe ina kallonsu hajiya amma babu wacce take da halin safiyyata, ko da wacce take koyi da ita ban gani ba”
“ba haka bane fawwaz, ba ka yi adalci wa sauran iyaye ba matuqar kace babu wacce ta samu halayen safiyyarka”
“hajiya baza ki gane bane”
Ya faɗa idanunsa cike da hawaye
“ni kuwa na gane fawwaz, idan tarbiyyace da safiyya da raudat duk tarbiyyarsu ɗayace domin ni da kaina na tarbiyantar da safiyya da yarka, ita kuma yartaka ita ta tarbiyantar da raudat ‘yar mijinta amma haka ka tubure kace baka sonta yanzu gashi raudat har da ɗa”
Cikin k’osawa da maganar yace
“hajiya safiyya ta babanta da raudat da duk wata ‘ya mace, ni dai ban ga kamarta ba”
Cikin ɓacin rai hajiya tace
“to kace kawai baza ka yi aure ba, amma ka daina faɗa min maganar banza, idan so kake yi ka dinga ɗaga min hankali da kiran sunan safiyya to ka ci gaba, amma ka sani babu wani da yake rayuwa a duniyar nan da ya fini k’aunar safiyya, tawakkali kawai nayi domin nasan baza ta dawo ba sai a darussalam”
Ta gama faɗin hakan ta fashe da kuka, hankalin fawwaz a tashe ya sauko daga kan kujerar yana tsiyayar hawaye shima ya durk’usa a gaban hajiyar ya fara magana
“hajiya don girman Allah kiyi hakuri ki yafe min, bana son kukan nan hajiya”
Amrat ma da take sauraronsu kukan ta fashe da shi ta rungume fawwaz ta baya
“zan yafe maka fawwaz amma dole sai ka nemo mata ka yi aure, hakan ne kawai zai sa in yafe maka in sanya maka albarka”
“na ji na yarda hajiya, ki taimakeni da addua, zan yi aure amma sai na samu wacce ta dace da ‘yata, wacce zata bata kulawa da kyakkyawar tarbiyya, ni dai na riga da na rasa wacce ta dace da ni”
Tausayinsa ne ya kama hajiya sosai, ita kanta da akwai yadda za tayi da bata tilasta masa yin auren nan ba, amma halin rayuwa take jiye masa
“addua kullum ina yi maka ita, inshaaAllahu matar farinciki zaka samu ta zama maka madadi, kar ka ɗebe tsammani daga rahamar ubangiji”
Hajiyace ta faɗi hakan bayan ta share hawayenta tare da jan hanci
“ki ban lokaci hajiya, zan nemota kwanan nan inshaa Allah”
Murmushin k’arfin hali tayi tace
“Allah ya maka albarka, ya haɗaka da zaɓin Allah wacce zata dace da zaɓin ranka sannan ta dace da amrat, safiyya kuma ubangiji ya k’ara lulluɓeta da rahamarsa ya karɓi shahadarta, duk lokacin da ka ji tunaninta ya addabeka to ka dage da nemar mata gafara a gurin Allah, ubangiji ya bamu guzirin taras da su, ka dinga dubawa ka rasa mahaifinka ma fawwaz, ka zama mai k’arfin zuciya don watarana nima rasa ni za ka yi komin daɗewa, Allah ya bamu ikon yin mai kyau domin samun dacewa”
Ameen fawwaz yace kansa na qasa, hawayen sun dakata da kwaranya amma idanunsa kamar garwashin wuta, mik’ewa yayi
ya ɗaga amrat ya ɗorata a kafaɗarsa zai fita daga ɗakin
“fawwaz”
Hajiya tace, juyowa yayi still idanunsa a qasa suke ba tare da ya kalli hajiyar ba
“ya maganar sadakar da ake musu, ina fatan ba a mantawa”?
Eh kawai yace ba tare da ya kalleta ba ya fice daga ɗakin
**********
Zaune suke kamar kullum hajiya da jikarta sai ga shi nan ya shigo cikin kakinsa
Da gudu amrat ta je ta ɗale shi tana ihun murna, shima cikin farincikin da baya iya ɓoyewa idan yaga yarinyar ya ɗagata sama yana shillata sai dariya kuwa gurin amrat kamar gonar auduga, guri ya nema ya zauna yana gaishe da hajiyar cikin fara’a, sun ɗan taɓa hira sannan hajiyar tace
“ni ko fawwaz ban ji kana maganar zakkah ba bana, ko hankalinka yayi wani gurin”?
Cire hular kansa yayi ya ɗora wa amrat a kanta sannan ya kalli hajiyar yace
“ina sane hajiya, ana kan aiki akan zakkar, idan aka cireta zan bayar amma sai na dawo daga tafiyar da zan yi jibi”
Cikin raha hajiyar tace
“dodon maza kenan, zakkarka ta mai raboce, ubangiji ya amsa maka, har kullum ina roqar maka kariya daga ubangijinka tare da aminci”
Murmushi yayi yace
“na gode hajiya”
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/25, 6:21 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*5*
“sir an samo irin kayan da ka buk’ata gaba ɗaya, bari in shigo da su ka gansu”
“a a, ba sai na gansu ba, na san za kayi yadda nace, ka shirya su kamar yadda aka saba”
“yes sir”
Yace tare da sara ya juya ya fice
*********
Yammaci ce mai cike da yanayi mai sanya nishaɗi da sururi, gab da lokacin kiran sallar magriba, saidai ga mai kallin yanayin zai iya tsammanin saukar ruwa cikin kowani lokaci daga wannan lokacin, lallaine manoman da suke cikin wannan qauye na feli zasu yi matuqar murna da sauqar ruwan domin lokacine da suke tsananin buk’atarsa.
tafe yake ɗauke da ɗan qunshin buhunsa cikin tafiyar da take nuna cewa yana cikin hali da yanayin neman taimako, almajirine sak ba sai an tambaya ba saboda yanayin shigar da take jikinsa, ko a almajiran ma wannan yana cikin sahun maqasqanta, jikin wani masallaci yaje ya zauna yana gyara zaman macacciyar hular kansa wacce tsufa yasa ta fara yagewa, tsohon buhun hanunsa ya ajiye a gefensa tare da ɗauko ɗaya daga cikin butocin da suke cike da ruwa ya fara alola, kasancewarsa baqo a idanun al’ummar wannan qauyen ya sanya mutane binsa da eyes, bai damu da kallonsa da akeyi ba ya mik’e da buhunsa a hannunsa ya shige cikin masallacin
Zaune yake cikin masallacin yana ta adduoinsa bayan idar da sallar, cikin ikon Allah a wannan lokacin hadirin da yake shawagi a sararin samaniya ya kaɗe ya narke zuwa wata sassanyar iska mai ni’mantarwa, wasu daga cikin masu sallan suna idarwa suka fice yayin da wasu suke zaman jiran sallar isha’i.
bai bar masallacin ba har sai da aka gabatar da sallar isha’i sannan ya ɗauki buhunsa ya fice, guri ya samu a kusa da masallacin ya zauna kan wani dutse yana kallon mutanen da suke fitowa daga cikin masallacin, yawancin waɗanda suka fara fitowa daga masallacin matasane sannan dattawan suka fara fitowa, ganin fitowarsu ne ya ja hankalinshi zuwa garesu ɗaya bayan ɗaya
“assalamu alaikum”
Kallon tsab mutum ya masa sannan cikin yanayin ban sanka ba ya amsa masa sallamar ba tare da ya miqa masa hannu ba
“don Allah bawan Allah taimako nake nema”?
Cikin saurin baki ya ce
“gaskiya duk da ban san taimakon da za ka nema ba amma ina ga ni dai bani da halin taimako, ni kaina da ka ganni in na samu taimakon bazan k’i karɓa ba, wallahi kuwa, ka san yanayin rayuwartamu a yau, taimakon nan wuya yake yi, toh ka ji, ni dai ka ga tafiyata”
Bawan Allah na sake kiransa amma ko ya saurareshi sai ma qara sauri da yayi.
Wucewa yayi zuwa ga mutum na gaba ya masa sallama tare da miqa masa hannu, shima dai kamar na farkon cikin tsumewa irin na ban sanka ba ya amsa masa sallamar ba tare da ya mik’a masa hannu kamar yadda shi ma ya mik’a masa ba
“don Allah taimako nake nema”
Cikin muzurai irin na nifa ban da halin taimako yace
“taimako wani iri cikin daren nan”?
Sassauta murya yayi sosai yace
“ni matafiyine, hanyace ta biyo da ni ta nan qauyen, to shine nake neman taimakon gurin kwana don Allah”
Gutsiren goro ya ciro daga aljihunsa ya jefa a bakinsa ya fara tauna kamar rago ya samu harawa, sai da ya tsotsi ruwan goron sannan yace
“ba ka san wani abu ba, ba wai gurin da zan ajiyekane bani da shi ba, yardace kawai banyi da kai ba, taimako irin wannan ai ba da ni ba ka je gaba ko za ka dace”
Cikin marairaicewa ya sake cewa
“don girman wanda ya baka muhallin a gurinka ka taimakeni, na maka alk’awarin zan kiyaye amanarka”
“ba zan iya ba fa bawan Allah, gida dai nawane, da kuɗina na sa naira na dukan naira na sayi abina, babu kwandalar wani a ciki, dan haka bazan iya ba ka je gaba”
Ganin da gaske tafiyar zai yi ya sanya ya kamo gefen rigarsa yace
“kar ka butulce wa ubangijinka, ka gode masa domin shi ya azurtaka da kuɗin da ka sai gidan, kar taimako ya sa ka rufe idanunka”
Fisge rigarsa yayi yana masifa yace
“kai nace bazan taimakeka ba, dole ne?, na ji Allah ne ya ban kuɗin sayen gidan, amma dai ba zaman mutuwar zuciya nayi irin naka ina yawon bara ba, nemowa nayi, kai ma ka nemi naka idan kayi zuciya, ha ah!!, ana dole ne”
“Allah ya baka hakuri, na gode da shawara”
Ameen yace tare da wucewa buya buya da babbar riga, shiko almajiri sai binsa da kallo yake yi.
Ya tare mutane uku bayan waɗannan amma duk amsar ɗayace, baza su iya taimaka masa ba, komawa yayi kan dutsen da ya taso har ya cire rai da samun mataimaki sai ya ga wani dattijo ya fito daga masallacin yana rufe k’ofofi da wundojin masallacin, cikin azama ya tashi ya je ya yi sallama wa dattijon, kallonsa dattijon yayi ba yabo ba fallasa ya mik’a masa hannu suka yi musabiha tare da amsa masa sallamarsa sannan ya tsaya yana sauraronsa
“don Allah taimako nake nema bawan Allah”
“wani irin taimako kake nema”
Sake rungume buhunsa yayi sannan cikin kwantar da murya yace
“ni matafiyine, hanyace ta biyo da ni wannan qauyen, shine nake neman gurin kwana kafin nan da kwana biyu zuwa uku in wuce inshaa Allah”
Sake fuskarsa yayi kaɗan sannan cikin nuna tausayawa yace
“inshaa Allah baza ka rasa gurin kwana ba matuqar baza ka raina ba”
Cike da farinciki yace
“wane ni malam?, na gode wa Allah sannan ina miqa maka godiyata gareka kan wannan alfarmar da zaka min, ubangiji ya biya maka buk’atunka na alheri, ya rufa maka asiri duniya da lahira”
Tunda suka fara maganar sai a lokacin dattijon ya yi murmushi, murmushin da ya qara fito da salihancinsa da kasancewarsa dattijo sannan yace
“ameen ameen ameen, na gode da addua ni ma, jirani a in zo mu wuce”
Sake gode masa yayi sannan ya matsa gefe yana jiransa, kammala rufe ko ina yayi sannan ya ce masa bismillah ya wuce gaba shi kuma ya biyoshi a baya
A kofar gida ya tsayar da shi sannan ya shiga gidan, ba a ɗau lokaci sosai ba ya fito wani matashi da ba zai fi shekara ashirin ba yana biye da shi, kai tsaye ya masa jagora zuwa cikin soron gidan bayan sun yi musabiha da matashin, wani ɗan qaramin ɗakine irin na matasa a soron gidan wanda daga waje zaka iya hango hasken fitilar dake cikinta, dattijon nan ne ya fara shiga sannan yayi bismillah wa bak’on shi ma ya shiga da sallama
“bawan Allah zance tunda ban san sunanka ba, nan shine masaukinka, ina fata ba wata matsala”
Murmushi yake yi yana bin ɗakin da kallo yace
“sunana ke nan bawan Allah baba, masauki yayi sosai, ina k’ara mik’a godiyata”
Cikin fara’a malam tanimu yace
“toh Abdullahi, ko?, bari su kawo maka abinci ka ci ka samu nutsuwa zuwa gobe sai mu yi hirar, kafin nan sunana tanimu ladan”
Wani murmushinne ya suɓuce masa sannan yace
“toh na gode”
Yawwa malam yace sannan ya juya zai fita, juyowa yayi da baya cikin rage murya yace
“na ce wa jama’ar gidan kai ɗan tsohon Abokinane, kai ma ka bari a haka, kasan mutane da tsoro, ka gane ko”?
Hatta turamensa sai da suka bayyana tsabar murmushi sannan ya ɗan dara kaɗan yace
“eh na gane”
Shi ma ladan juyawa yayi ya fita yana ɗan darawa
***********
Waige waige yake yi da alama wani abun yake dubawa, tsaye yake a jikin wata qatuwar bishiyar mangoro, a lokacin nan ba zai wuce shida zuwa da rabi na safe ba
Sai da ya tabbatar ba wanda yake kusa da gurin sannan ya sanya hanunsa cikin rigarsa er shara ya ciro wata er qaramar abu mai kama da waya, danna abun yayi take tayi wata sassanyar qara sannan ta hasko fuskar abun, take ta fito a siffarta ta waya
Kamar jira ake yi ya buɗeta kira ya shigo cikin wayar, ba tare da ya ɓata lokaci ba ya ɗau wayar ya kara a kunnensa tare da waigawa yana kallon bayansa
Daga ɗayan ɓangaren yaji an ce
“wannan itace kira ta hamsin da biyar da na yi maka cikin dukkan layukanka amma switch off nake ji duka layukan, ina fatan ba kayi hakan bane don qaurace wa kiraye kiraye daga gurinmu”
Baya buqatar tambayar mai maganar domin ya ɗau muryar, cikin dakewar murya yace
“ba ka da kima da darajar da zaka sanyani rufe layukana, ka faɗi dalilin kiran naka”
Dariya yayi a wancan ɓangaren sannan yace
“kana kasheni da jarumtarka jarumin maza, amma ka sani wannan shine kashedi na qarshe da za mu maka, ka janye rundunoninka akan jama’armu, idan ka qi ji kuma to wallahi da sauran kukan jini a gabanka ba na hawaye ba”
Bai san lokacin da ya daka masa tsawa mai firgitarwa ba har ya manta gurin da yake sannan yace
“qarya kukeyi alhaji bala, ina mai tabbatar maka wannan karon kai za ka yi kuka na zuciya da idaniya, sai na mayar da kai abin kwatance a cikin qasar nan, har da shi tsinannen abokin naka tukur”
Wata sheɗaniyar dariya alhaji bala yayi sannan yace
“toh shikenan jarumi, shege ka fasa, amma duk abin da za kayi kar ka manta da wata yarinya, wannan yarinyar ‘yar shekara huɗu da wata shida, takan fita zuwa makaranta misalin qarfe bakwai na safe ta dawo qarfe biyu, fara kyakkyawar nan abar alfahari abar qaunar mahaifinta, ta kasance farincikin mahaifinta mai maganin raɗaɗin zuciyarsa, na barka lafiya”
Ɓbai samu ikon cewa komai ba aka kashe kiran daga can ɓangaren
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/27, 4:04 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*6*
Hankalinsa idan yayi milion duk sun tashi, da gaggawa ya kira wata number, ba a ɓata lokaci ba aka ɗaga daga can ɓangaren,
“kana ina”?
Abin da ya fara faɗa kenan cikin tsananin buqatar jin amsa
“ina shirye tsab yanzu haka idan ta fito mu tafi kaita school”
Cikin maɗaukakiyar murya yace
“ku dakata da kaita school har sai na dawo”
“yes sir”
Wanda aka yi wa umurnine ya faɗi hakan cikin muryar da take nuna tsantsan ladabi
“ka haɗani da col. Mukhtar misalin qarfe takwas na dare, ni zan kiraka ka zama ready”
“ok sir”
“take care, ok”
Yana gama faɗin haka ya zare wayar daga kunnensa sannan ya kashe ya mayar cikin er shararsa yayi ɗan waige waigensa ya bar gurin.
************
“shegiya tsinanniyar yarinya mai gadon mugun halin tsoho da tsohuwa, ku da yake ba ku gaji arzik’i ba, to wallahi ko sata ko karuwanci duk wanda za ki yi ki je ki yi ni dai kuɗin kokona su fito”
Tsaye take tana ta sharɓar kuka hannunta cikin na tanimu ladan, bak’ar yarinyace kwata kwata baza ta wuce shekara sha bakwai ba, daga dukkan alamu yarinyar tana cikin haline na matsi da takura tare da tsananin rayuwa, abune mai sauki mai kallonta ya gane a firgice take saboda yanayinta da raunin da yake kan fuskarta, daga ganin yarinyar mai kallonta zai tabbatar da ta burne wani abu mai ciwo a cikin ranta, ba wata kyakkyawa bace sannan bata da tsayi amma baza a kirata wada ba, saidai duk da ramar da take jikin yarinyar hakan bai ɓoye kyan dirin da take da shi ba, k’aramar kulawama kawai idan ta samu makaman yak’inta zasu fara aiki, sai dai kash, hatta suturar da take jikin yarinyar zata iya yin dariya su qarasa yagewa a hakan ma duk sun sha faci da allurar hanu, takalman qafarta kuwa sun gaji da ɗaukar zare, sun suɗe sosai sun zama sufanu, abin dai sai godiyar mahalicci
“don Allah baba haule kiyi hakuri ki bar yarinyar nan, tsautsayine amma kin san tana iya bakin qoqarinta akan duk wani talle da za ki ɗora mata”
Cike da masifa baba haule ta fara yamutsa wawwaran bakinta tana faɗin
“kai ladan wallahi ina ganin mutuncinka, ba dan haka ba da sai na rufe ido kaima na ci maka mutunci, haka kawai, ku ma da kuka san Allahn ba yarda da tsautsayin kuke yi ba, sai ni kawai za ka zo ka tasani gaba dole sai na yarda”
Murmushin takaici malam tanimu yayi sannan ya gyara tsayuwarsa yace
“na gode da kike ganin mutuncina haule, ba zan gajiya ba ina sake rok’onki ki k’yale yarinyar nan, ki tausayawa rayuwarta domin ita abar tausayice don Allah”
“malam ka bar ɓata bakinka, idan ka ga na rabu da ita to ta biyani kuɗin kokona, shikenan sai in rabu da ita ba, amma wallahi idan ba haka ba yau sai na lahira ya fita jin daɗi, babu tausayinta da zan ji, uwace dai ba ni na kashe mata ita ba, na san a bin da zaka ce kenan, idan kuma ni na kasheta to ta zo ta ɗauko cebur da diga ta je ta cirota na fasa”
Wani irin ɓacin raine ya ziyarci zuciyar malam tanimu bai san lokacin da ya tura mata mairo gabanta ba cikin tsananin fusata yace
“idan ke ‘yar halak ce kar ki bar mairo da rai, ki kasheta ke kuma ki tabbata a duniya”
Ai kuwa shegiyar jahilar cike da hauka ta cafko mairo ta kai mata mahaukacin marin da yasa ta hantsila a kofar gidan, kwatsam ba zato ba tsammani ta ji an buga mata wata gigitacciyar tsawar da tayi nasarar mannanta da jikin katangar k’ofar gidannata
A kiɗime ta juya domin ganin gwarzon da ya ragargaza mata kaifin jinta da hargagin muryarsa,
Kusan a tare suka juya da malam tanimu da mairo dan su kansu tsawar ta matuk’ar razana su
A tsaye yake jikin k’ofar gidan malam tanimu, idanunsa gaba ɗaya sun rikiɗe zuwa launin ja saboda tsananin ɓacin rai har wasu irin k’wallace suka taru cikin idanunsa
Mamakin da yake kan fuskarsa ba abune da zai ɓoyu ga mai kallonsa ba, bak’on nashi ya zuba wa ido ganin yadda ya nufi baba haule a fusace kamar namijin zaki, wata iriyar tsayuwa yayi a gabanta wanda ya sanyata kusan sakin fitsari a jikinta, muryar ‘yan mazan yana fara dukan kunnenta ta sake burkicewa, da hannu ya nunata cikin zare idanu ya fara faɗin
“idan kika kuskura kika sake ɗaga waɗannan k’iraren hannayen naki kika daketa wallahi baza ki mayar dasu k’asa ba face wasu qasusuwan sun goce daga mazaunansu, azzalamu, muguwa, marar imani, zan nemo miki kuɗinki ko a ina suke zuwa dare inshaaAllah amma ina mai sake miki gargaɗi matuk’ar kina buk’atar sanya waɗannan hannayen ki karɓesu to ki kiyayi ko da zungurin yarinyar nan, wannan shine kashedina”
Ya k’arasa maganar yana mai nuna mairo da take zaune daɓas a qasa idanunta na kallonsa tana tsiyayar hawaye
Tunda baba haule take bata taɓa ganin tijarar da ta tsorata irin na yau ba, duk wata tijara da masifar da take ji da ita sai da ta neme su ta rasa saboda tsananin tsoron wannan matashi da ya shigeta, ba k’aramin kwarjini ya mata ba, ko mahaifin su mairon malam Ibarahim ba ta shakkarsa kamar wannan, shi kam ta riga ta gama dashi don ko wani irin uk’uba za ta yi wa mairon ba zai ce komai ba, idan yayi k’ok’arine ma ya ba ta hak’uri akan laifin da mairon ta mata ko k’anin mairon idris, sai yau gashi tsabar tsoron wannan matshin su baba haule har da sunkuyar da kai
Tsaki ya mata tare da mata kallon na tsaneki sannan ya juya ya bar gurin, ko bi takan malam tanimu bai yi ba ya shige cikin gida kai tsaye ya shige masaukinsa
Ganin yadda baba haule ta zama yasa malam tanimu murmusawa duk da maganar gaskiya ya ɗan tsorata da bak’on nasa saboda abin da ya hango cikin idanunsa
“ki daketa mana baba haule, ko kuɗinkin sun shiga hannune”
Kallon banza ta masa tare da yin tsaki amma fa babu magana tayi cikin gidanta bayan kamo hanu yarinyarta k’arama
Dariya ladan yayi ya kalli gurin da mairo take zaune yace
“mairo taso mu je cikin gida ki karya kumallo kin ji, ki yi hakuri, watarana za ki ga kamar hakan bai faru ba in Allah ya yarda”
Mik’ewa tayi tana goge hawayen da suke k’ara zubo mata sannan ta fara karkaɗe k’urar da take jikin mataccen zanin jikinta, har zanin ya ɗan yage ta wajen zama saboda faɗuwar da tayi a k’asa
Gaba ladan yayi tana bin shi a baya har suka shige cikin gidan ladan ɗin,
***********
Kansa a kife yake jikin bangon ɗakin tare da hannayensa, ji yayi an dafashi, da sauri ya ɗago da kansa yana kallon wanda ya dafa shi
“mu zauna Abdullahi, ina son mu yi wata magana da kai”
Neman guri yayi ya zauna cikin ladabi yace
“ina kwana malam, ka yi hakuri ba mu gaisa ba”
Murmushi malam ɗin yayi yace
“lafiya lau malam Abdullahi, ba komai, ni ma da na ga ban ganka ba na ce watak’ila ka biya wani gurin ne daga masallaci”
Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba
“Abdullahi jikina ya bani kai mutumin kirkine, ba za ka cutar da ni ba, amma ina da shakku a kanka musamman kan abun da ya faru tsakaninka da matar nan da kuma yanayin da na ganka yanzu a ciki, ka faɗa min gaskiya mai yake tafe da kai”?
Jimmm yayi kansa a k’asa, tsawon minti biyu sannan ya ɗago kan nasa ya tsai da idanunsa kan ladan ya fara magana a hankali
“ka yarda da abin da zan faɗa malam, ni ba mai cutarwa bane, abin da na aikata kuma wannan yanayinane, bana son zalunci, duk girman azzalumi da k’arfinsa baya firgitani, duk lokacin da naga ana zalunci a gabana nakan shiga irin wannan yanayin, malam don Allah ka min wata alfarma, ka ban labarinta, mai yasa take cikin sannan halin, ba ta da kowane??, ina mahaifinta, da gaske mahaifiyarta ta rasu, mai yasa take cikin tsummokara haka, menene alak’arta da wancan matar”???
*********
Motocin sojojine ma’abota jarumta da ɗamara suke shigowa gidan, sai dirowa suke yi, take filin gurin ya zama tamkar sansanin yak’i, sojojine ta ko’ina ciki da wajen gidan, gaba ɗaya gidan an masa zobe da jami’an soji
Cikin sassarfa ya kusanto mutumin da nake tunanin a sojojin nan yana da girman matsayi sai da ya k’araso inda yake yayi wani irin burki tare da sarawa sannan yace
“col. Gee fawwaz yace matakan tsaron sun isa haka, ba sai an sake turo wasu ba”
“ok, ku zama cikin shirin ko ta kwana a ko da yaushe”
“yes sir”
Ya faɗa cike da qarfin gwiwarsu irin ta masu ɗamara sannan ya sake sara wa ya juya cikin sassarfa
*******
“hhhhhhhhh, gee fawwaz lallaine kai mai taurin kaine, amma fa ka sani duk da mun ga hanya tayi duhu dole sai mun cimmaka domin babu abin da ya haɗo biri da gada, ba kukansa bane wannan, wai uwar kishiya ta mutu…., hhhhhhhh”
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/28, 5:16 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*7*
“mai yasa kake son sanin ita wacece”?
Kawar da kai yayi gefe kamar bazai yi magana ba, sai kuma ya juyo da ɗan hanzarinsa cike da fuskar tausayi yace
“tausayinta nake ji malam, ina da wani raunin kamar haka a zuciyata, ka taimakeni ka faɗa min wacece ita?, duk da ni ma ba kowa bane amma zan yi k’ok’ari akanta ko da yi mata addua da fatan samun sauk’i da nutsuwa”
Tsira masa idanu malam yayi yana nazarin bak’on da yake kira da Abdullah sannan ya numfasa yace
“Abdullah lallai wannan yarinyar da ka gani tana cikin wani irin hali da jinsa ba abune da kunne zai yi marmarin ji ba, rayuwar yarinyar da ɗan’uwanta abun tausayawace”
Shiru ladan yayi bayan ya sunkuyar da kansa a k’asa, wanda haka ya sanya bak’on cikin tsananin kwaɗaituwa da jin amsar da zai bashi, gabaɗaya ya buɗe kunnensa da zuciyarsa yana sauraronsa
Ganin malam tanimu ba shi da niyyar ɗagowa yasa bak’on cewa
“malam kai nake saurare, don Allah ka sanar da ni wani abu a kanta”
Ayyah malam, ɗagowar da zai yi sai hawaye ne ke kwaranya a idanunsa, sauk’ar hawayen wannan dattijo yayi gagarumin nasarar raba Abdullah da nutsuwarsa, bai sai mai yasa ya ji zuciyarsa tana bugawaba, naɗe k’afafunsa yayi da hannayensa yana bin malam ɗin da ido cikin rashin sanin wacce tambaya ce ta dace ya fara masa a kan halin da yake ciki
Sharɓe hawayen ladan yayi da gefen rigarsa sannan ya fara kamar haka
“mahaifin mairo mutumin kirkine, duk cikin mak’wabtana babu mai hak’uri da kawaicinsa, haka ita ma mahafiyar mairon take, abune mai wahalar gaske ka ji tana hayaniya da wata, ko da kuwa tsautsayi yasa ka ji hayaniyarta da wata cikin mata to tabbas ko baka gurin zaka iya rantsewa itace da gaskiya kuma baza ka yi kaffara ba, a hakan ma sai an kaita mak’ura.
Rayuwarsu suke yi da malam ibrahim cikin rufin asiri da mutunta juna bayan aurensu, ba a ɗau lokaci sosai ba Allah ya azurta malam ibrahim da matarsa ameena da yarinya mace, sun ɗauki son duniya sun ɗaura wa yarinyar, hakan yasa take samun kulawa sosai daga gurin iyayenta, ko da yaushe zaka ga mairo cikin tsaftar da ta zarta ta yaran mak’wabta, hakan yasa ta banbanta daga cikin yaranmu, idan ka ga mairo da dauɗa to rigimar nan ce irin ta yara da za su yi ta burgima da kayansu a k’asa idan suna kuka, nan ma kayan ba sa daɗewa a jikinta ake canza mata wasu
Shekarar ta huɗu mahaifiyarta ta sake haihuwa amma ɗan bai zo da rai ba, haka suka rungumi k’addara suka cigaba da rainon maironsu, daganan mahaifiyar mairo tayi ta haihuwa amma yaran basa zama, sai da ta haifi biyar a kusa kusa basu zauna ba, hakan yasa dangin ibrahim ɗaga hankalinsu kan cewa dole ya kara aure tunda wannan wabi take yi, ba yadda ba su yi da ibrahim ba amma fir ya k’i, hakan yasa wasu daga cikin ‘yan uwansa suka jonoshi da mahaifiyarsa inna habi, nan kuwa ta buɗe masa wuta kan san ya k’ara aure, da taga zai ɓata mata lokaci sai ta nemar masa auren ‘yar k’awarta wacce ta kasance bazawarace, ta taɓayin aure har uku, saidai duka auren rabuwar ɗiban albarka akeyi, tsiya tsiya, dole ba dan yaso ba ya amince da auren haule, anan yake zuwa ya kawo min k’orafinsa kan auren, ni kuma a matsayina na kusan uba a gareshi sai in bashi hakuri tare da nasiha, ba a ɗauki dogon lokaci ba aka ɗaura aurensa da haule, tun da haule ta zo gidan ta buɗe shafi shafin rashin arziqinta, tun ibrahim yana iya taka mata burki har abin ya fi qarfinsa, shi da kansa ya sha zama yayi kuka da hawayensa akan wannan shaiɗaniyar matar, haka al’amarin yake ga ameena, sai da ta kai ta kawo abincin da zata ci a gidan ya nemi ya gagareta ita da ɗiyarta, duk cikin abin da bai fi wata uku ba
Lokacin da haule ta samu ciki kuwa abin mamaki shi kanshi ibrahim tamkar ba a taɓa masa haihuwa ba ya zama, duk ya gigice akan cikin da ke jikin haule kamar zai yi hauka, wannan karon har da shi aka taru aka yi ta gana wa baiwar Allah ameena wahala, sai ta wuni bautar cikin gidan ba hutu, cikin dare ma wani lokacin bata isa ta runtsa ba, tana kwanciya haule zata tayar da makircin bata da lafiya, haka dole take fita ta je, musamman idan ibrahim ɗin yana ɗakin ita ameenar, sai da ta kai ta kawo ya tattara komai nashi ya koma ɗakin haulen da kwana wai saboda ya dinga kulawa da ita da kyau ba sai an zo an tashi ameenar ba, haka tayi ta jure duk cin kashin da ake mata ta mai da hankalinta kan ɗiyarta mairo, domin bata buqatar sauyin da ya zo musu ya shafi rayuwarta, saidai ita ameenar kana ganinta zaka san jiya ba yau ba, duk ta tsiyaye ta komaɗe ta fice a hayyacinta
Ana haka Allah ya sauki haule lafiya ta haifi ɗiyarta mace ita ma, ku zo ku ga rawar kai da na qafa gurin ibrahim, kai kana kallon lamarin kasan ba lau ba, ni dai a matsayina na makwabcinsa nayi ta bashi shawarwari musamman da na lura yana ganin mutuncina amma tsakanina da shi to za a gyarane kawai, a gurin yake bar min nasihata, hidimar suna akayi sosai yarinya ta tashi da sunan zainabu, sai suke ce mata Abula, haka rainon yarinya da wahalhalunta ya koma kan ameena da mairo, kullum cikin bauta suke kamar bayi
Allah ne kaɗai yasan rabon da ya rantse tsakanin ameena da ibrahim sai ciki ya ɓullo a jikin ameenar, tun da haule ta qyalla ido ta ga cikin jikin ameena ta ɗaga hankalinta wai ita lallai anci amanarta an munafurceta, nan fa tayi ta miyagun furucinta aka cikin ameenar, ni da kaina akwai randa rikicin yayi tsamari ta rufe ameenar da duka na shiga gidan, a gabana tace wallahi ameena baza ta haifi cikin jikinta lafiya ba matuqar tana raye, ba qaramin ɗauki ba daɗi akayi ba cikin gidan sannan ameenan ta haifi k’anin mairon idris, wayyo ina wuta haule ta jefa ameena wallahi uqubar da ameena ta gani a lokacin mutuwar da tayi hutuce a gareta
lokacin da ta haifi idris bata wani ɗora rai akan yaron ba, ashe ita kaɗai ta san abin da ke damunta, yawanci idan ‘yan barka suka je, kuka suke isketa tana yi, haka mata za su zauna suyi ta ba da labarin halin da take ciki, watarana na tambayi mairo mai yasa idan aka bata abu bata cinyewa komai qanqantarsa sai ta ajiyewa idris?, sai ta ce min wai kafin mamansu ta rasu kullum sai ta ce mata ta kula mata da idris, kar ta barshi da yunwa, ta kula da ɗan uwanta.
Ba a ɗauki tsawon lokaci ba domin ko wata uku me kyau bata ɗauka ba ta bar duniyar bayan aman jini da tayi ta sheqawa cikin dare, tun tanayi ita kaɗai har ta tashi mairo, lokacin da taga zata fita hayyacinta ta tura mairon ta kira mata mahaifinta ko da mairon ta je kiransa tsalle haule tayi ta dire tace babu in da zai je, wai ta san lafiyarta qalau munafurcin matane, haka mairo tafi tana kuka bayan mahaifin nata yace taje tace bacci na damunsa sai da safe, kai tsaye gidan nan yarinyar ta zo tana kuka tana bubbuga kofa, da kaina na zo na buɗe kofar dan matasan nan sun yi nisan barci, tana kuka take sanar da ni abin da yake faruwa, kasancewar ni namijine bai dace in shiga gidan alhalin mijin baya gurin ba yasa na kira matata uwandi nace su je da mairon su gano halin da uwar yarinyar take ciki
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/30, 12:06 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*8*
Lokacin da suka isa gidan sun sameta cikin mawuyacin hali, numfashinta sai kaiwa yake yana komowa, cikin tashin hankali uwandi ta zauna a kusa da kanta tana jan innalillahi cikin muryar kuka, ganinsu da tayi yasa ta ɗago hanunta ta riqo hanun uwandi gamgam tana ta qoqarin sanar da ita wani abun amma ina! harshe ya karye, da qyar uwandi ta ji kalma ɗaya a fisge wato sunan mairo, ganin haka yasa uwandin ta ce wa mairon ta fita, sannan ta fara maimaita mata kalmar shahada a kusa da kanta, cikin ikon Allah sai ita ma ta faɗeshi a fisgen kamar yadda ta kira sunan mairo, uwandi da take zaune gefenta sai gani kawai tayi idanunta sun qafe sunyi sama
Ladan yana zuwa nan sai yayi shiru ya sunkuyar da kai, zuwa lokacin kuwa bak’o zuciyarshi ban da harbawa da take yi da k’arfi babu abin da take yi, idanuwansa kuwa sun kaɗa sun yi jajur, zaune yake shiru kamar gunki a gaban tanimu ladan, baya ko qyafta ido, tsawon lokaci babu wanda yace komai sannan ladan ya ɗago bayan ya sharce hawaye da suka sake zubo masa da gefen rigarsa tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, cigaba yayi da cewa
“Abdullahi faɗin tashin hankalin da muka shiga lokacin da uwandi ta dawo a gigice take sanar mana da abin da ya faru ɓata bakine, gaba ɗaya iyalaina muka ɗunguma gidan cikin tashin hankali, amma ka san me ya faru?,
Shirun dai Abdullahi yayi amma idanuwansa na kan malam ɗin, hakan ya tabbatarwa malam yana sauraronsa
“wato Abdullahi har muka shiga gidan mata suna ta koke koke amma wallahi ibrahim da matarsa babu wanda ya fito, sai da na je ɗakin da kaina nayi ta bugawa sannan matarsa cikin tsawa tace
“wai wane ɗan iskanne zai zo ya dinga bugawa mutane qofa cikin daren nan, menene?”
Wani irin bak’in cikine ya dunk’ule min a qirjina, cikin takaici nace
“ɗan iska tanimune, idan da hali ibrahim ya fito Allah ya karɓi ran ameena”
Ka san wani iya shege gurin matar nan?, kukan munafurci ta fara yi ta zo ta buɗe k’ofar tana cewa
“innalillahi wa inna ilaihirraji’un, yanzu ameena haka zaki min, ki tafi ki barni ameena, wayyo Allah na shiga uku na lalace”
Sai kuma ta juya cikin ɗakin tana cewa
“baban abulah ka fito mana, wayyo duniya yau babu ameena a cikinki, duniya ina za ki da mu”
Sai a lokaci ibrahim ya fito, duk da ina cikin takaici abin da suka yi amma na tausaya wa ibrahim, domin abune mai saqi ka karanto kiɗima da gigicewar da yake ciki a kan fuskarshi, kamar wanda bashi da laka a jikinsa haka yayi ɗakinta ko kallon gurin da nake bai yi ba, lokacin da ya buɗe gawarta kuwa durk’ushewa yayi a gurin yana kuka kamar k’aramin yaro, duk wanda yake gurin dakatawa yayi yana sauraron kukan nashi cikin tausayawa, sunanta kawai yake kira sai yayi shiru, ya kasa cewa komai
“haba malam, mu mata muyi kuka kai ma namiji kayi, wani irin ragwantace wannan, yaushe ake son kuka irin haka akan mamaci, tashi ka koma ɗaki kawai idan kuka za kayi, mu ka barmu mu ji da abin da ya damemu”
Haule ce mai faɗin haka cikin masifa da ba da umurni kamar ba ita ce mai kukan nan ba
Abin takaici da baqin ciki Abdullahi sai gani nayi ibrahim ya tashi ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ban san lokacin da na buga masa tsawa na dakatar da shi ba sannan nace duka matan su fita daga ɗakin, dole babu yadda haule ta iya ta fice daga ɗakin tana cika tana batsewa, hanun ibrahim na kamo na dawo da shi kan gawar nace
“ibrahim ka gani ko?, ka ga abin da nake faɗa maka ka k’i ji ko?, yanzu ka yi wa kanka adalci?, yanzu a ce kana cikin gidan yarinyar nan tayi ta murk’ususu har ta bar duniyar amma ko neman gafararta ka zi ka yi ma abin ya gagara, shikenan ai yanzu ta bar maka duniyar sai ka zo ka yafe mata ita, ina nema mata alfarma”
Sake durk’ushewa baban mairo yayi ya kifa kansa a jikin ameena yana kuka wiwi
“ki yafe min ameena nima na yafe miki, na tuba, na tuba ameena”
Abin da yayi ta maimaitawa kenan har dai na gaji na ɗagoshi daga kan gawarta nace masa ya isa haka
Haka aka mata sutura da gari ya waye aka kaita makwancinta, ko da ‘yan uwanta suka zo sun samu har an dawo daga kai ta ana ta karɓar gaisuwa, tun daga lokacin ibrahim ya zama shiru shiru fiye da baya, bayan share zaman makoki ‘yan uwanta suka koma qauyensu nan sama da mu kaɗan, da yake lokacin da mahaifiyar ita ameenar hakan yasa ɗaya daga cikin ‘yan uwanta maza ya ɗauki idris akan cewar matarsa zata shayar da shi domin a lokacin matar ba ta yi ko arba’in da haihuwa ba, baban mairo bai yi jayayya ba ya amince aka tafi da shi, tun daga lokacin mairo take ganin uquba gurin matar ubanta, ita ce duk wani aikin cikin gidan ga duka da zagi, sannan ita za ta yi abincin amma rabonta bai wuce qanzo ba saidai idan yaranta ne suka ci suka rage, wata rana ma haka take zama da yunwarta matuqar abincin bai yi qanzo ba kuma yaran basu rage ba, idan kuwa taje talle ba ta sayar ba to ko da sauran abinci da qanzon baza a bata ba saidai ma a mata duka da zagin rashin mutunci, ga yarinyar da zurfin ciki idan ba daga cikin iyalainane suka ganta a takure suka zo suka faɗa ba duk wuyar da zata sha na yunwa ba za ta zo tace tana jin yunwar ba, ko kunun da ka ji ake rigimar a kanshi ita take damawa da kanta da safe ta kai tallensa amma wallahi naira ɗaya yayi ciwon kai cikin abin da take samu yarinyar ta shiga uku, wani lokacin iyalaina ke cika mata kuɗin ta kai mata ta amshe ba ko tsoron Allah, sannan takanyi tallen kayan miya da rana da dare kuma ta sunkuya tallen tasoyi da goro a ‘yar k’aramar kasuwar can ta bakin masallaci, komin sanyi kuwa idan ba ruwa ake yi ba gudun kayanta kar ya jiqe dole sai yarinyar ta je tallen nan, ba yadda bana yi da ibrahim akan hakkin yarinyar nan akansu amma kamar ce masa nake ku cigaba, sutura kuwa idan ka gani a jikin yarinyar nan to ba ta aka yi, nan ma fa ba barinta da kayan ake yi ba matuqar aka qyalla ido aka gansu sabbi, kasancewar ita haulen ta ɗauko yarinyarta da ta haifa a can gidan mai suna indo duk ta girme wa mairo amma haka ake kwashe mata kaya a ba wa indon har sai sun kuɗe sun kai a zubar sai ta ba wa mairon su tayi ta fama, cikin haka kakar mairon ta wajen uwa ta rasu, duk da mairon a lokacin yarinyace amma ta shiga tashin hankali sosai saidai kawai ka ganta ita kaɗai tana kuka, ba a ɗauki lokaci da rasuwarta ba aka dawo ta idris gidan bayan an yayeshi ba da jimawa ba kasancewar zumuncin yanzu anayinsa ne idan anga kana da wani idon da zai sa ayi zumuncin da kai
Dawowar idris gidan sai ya zama tamkar qarin tashin hankaline ga mairo, saboda ɗawainiyar ta ninku biyu, tayi fama da kanta tayi da idris, hmmm Abdullahi yarinyar nan ta sha yin surfe da daka a ɓoye idan ta samu lokaci domin ta saya musu omo da sabulu ita da qaninta, kai har wanki da gugan kayan matasan gidan nan takanyi ta nema musu abin buqata duk da ni da iyalaina muna iya bakin qoqarinmu akan yaran, saidai wani abin kana so ka basu idan ka tuna cewar ba su za suyi amfani da shi ba sai ka hana, saidai ko abinci da nake sawa ayi kiransu a basu a nan a ɓoye, duk abin nan da ake yi daga dangin uwa har na ubanta babu wanda bai sani ba amma kowanne ya ja ya noqe saboda basa son ɗaura wa kansu nauyi, musamman dangin ubanta ai yadda ka san ba ibrahim bane ya haifi yaran nan
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/1, 2:55 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*9*
Yanzu halin da ake ciki kuwa hatta yarana da na haifa a cikina na musu umurnin duk mai sonta ya nemo aurenta a rabata da qangin bautan da take ciki amma usman da usaini duk sun je gwada sa’arsu amma qiri-qiri matar nan ta cewa ibrahim ba za a aurar da yarinyar yanzu ba har sai yarinyarta tayi aure wai saboda ita indon itace gaba da ita, da na ji haka da kaina na samu ibrahim ɗin amma abin al’jabi buɗar bakinsa sai cewa yayi sai dai in nemi haule in ji abinda zata ce, don shi duk abin da tace haka za a yi, Abdullahi a wancan ranar sai da nayi kuka da idona na tausayin ibrahim da marayun yaranshi guda biyun nan, domin duk rashin fahimtar mutun dole zai gano ibrahim ba ya cikin hayyacinsa, kuma abin takaicin ita yarinyartar ko kare babu wanda yake zuwa gurinta saboda mugun halin uwarta, ka ga kenan yarinyar bata da ranar barin wannan uqubar
Dakatawar da malam yayi hakan yasa ya fahimci labarin ya zo qarshe don haka ya motsa qafarsa tare da sauke numfashi ya sunkuyar da kai qasa, ya ɗau lokaci a haka sannan ya ɗago da kansa yana kallon malam yace
“malam ya maganar karatu kuma?, tana zuwa makaranta kuwa?”
“ina ga rabon yarinyar nan da makaranta tun da mahaifiyarta ta rasu aka yanke mata saidai lokacin da su jamila sa’anninta yaran gurina suka zo zana jarabawar kammala primary na haɗa baki da headmastern su ya zo ya buɗe musu ido akan hukumace ta turoshi ya faɗa musu dole su bar yarinyar ta je tayi jarabawar idan ba haka ba hukuma za ta zo ta kamasu, to akan ba yadda haule za ta yi ta hakura yarinyar ta zana jarabawar”
Nan ma Abdullahin shiru ya sake yi na tsawon lokaci sannan ya ce
“na gode malam da ka bani lokacinka, ita kuma maryam ubangiji ya kawo mata kyakkyawar mafita”
Ameen ameen malam yace sannan ya juya ya nuna wa Abdullahi koko da kosai da aka kawo masa da ɗumamen tuwo yace
“ga kayan karin kumallo nan, watakil ma yayi sanyi, mun tsaya surutu”
Ya qarasa maganar yana murmushi, shi ko Abdullahi fuskar nan ba raha balle wargi, ciki ciki yace
“Allah ya biyaka malam, ina godiya sosai”
Miqewa malam yayi ya fita daga ɗakin yana cewa
“ameen Abdullahi’
Ba tare da ya ji qyanqyamin cin abincin ba ya janyo ya fara kaiwa, kaɗan yaci tuwon sannan ya sunkuya kan kunu da kosai
*************
A jikin masallacin suke tsaye bayan sun idar da sallar azahar, cikin neman alfarma yace
“malam ina roqon alfarmarka guda ɗaya, don Allah ka min alfarmar zama da kai na sati ɗaya mana, garin ya min daɗi, bana son barinshi a yau, duk aikin da kake so zan maka shi matuqar zaka amince min”
“to shikenan malam Abdullahi, ubangiji yasa hakan alherine”
“ameen ameen” yace da sauri yana murmushi shima malam murmushun yayi yace
“Abdullahi ina jinka kamar ɗan uwana”
Murmushin ya sake faɗaɗawa yace
“na gode malam”
Ladan ne ya fara gaba sannan Abdullahi ya bi bayanshi suka kama hanyar gida suna ta hira,
Hira suke yi sosai kamar waɗan da suka daɗe da sanin juna, Abdullahine da ɗan malam tanimu mai suna shafi’u, shi ma a ranar ya dawo daga qauyen babarshi can tafare, duk da ɗan gayune amma halin ubanshine da shi bai rainawa mutane, hakan yasa bai raina yanayin bakon nasu ba, suke ta hirar duniya abinsu, saidai shi kanshi baqon yakan lura da tsananta kallonshi da shafi’u yake yi, saidai da ya ga za su haɗa ido da bakon nasu sai yayi saurin ɗauke kai, duk da ya sha jinin jikinsa amma bai bari shafi’un ya fahimci ya san yana masa wannan kallon ba
A hankali take tafiya ɗauke da tiren ɗanyen kayan miya da bushasshe, kan ta a k’asa yake ta zo wuce gaban su Abdullahi
Bin ta da ido yayi sannan ya dawo da kallonsa kan shafi’u wanda shi kuma shi yake kallon, magana yayi wa shafiun qasa qasa, sai gani nayi shafiun ya mai da kallonsa kan mairo sannan ya ɗaga murya ya kwaɗa mata kira
A hankali ta juyo baya bayan ta amsa kiran, ita dai sai a lokacin ta lura da waɗanda suke gurin, gaban shafiu ta zo ta ɗan sunkuya tace
“ina wuni yaya”
“lafiya mairo, ya gidan”?
“lafiya qalau yaya, ka dawo qalau”?
“lafiya lau mairo, yaya idris”?
“lafiyanshi qalau”
Tace sannan ta mayar da hankalinta kan Abdullahi tace masa
“ina wuni”?
Haɗe rai yayi ya kawar da kansa gefe ya amsa ciki ciki kamar baya so, ba ta ji daɗin yadda ya amsa mata gaisuwan ba don haka ta juya tana kallon shafiu jiki a mace cike da rauni tace
“yaya zan tafi”
“toh mairo, amma kin ci abinci”?
Raurau tayi da idanunta kamar za ta yi kuka amma ta kasa cewa komai sai ma sunkuyar da kai da tayi
Kallon Abdullahin yayi ya na nuna masa ita da ido, cikin cin magani yace
“ka ce mata ta mayar da tallen har sai ta ci abinci”
Dariya shafiu yayi yana kallon Abdullahi yace
“kar ka fara, ka san wacece haule kuwa?, yanzu zata surfa maka rashin mutunci”
Wani kallo ya masa wanda ya sanya shakku cikin zuciyarsa sannan ya juyo da kallonsa kan mairo ya k’ura mata ido, take ta ji wani tsoro ya shigeta, cikin dakiya ta ji yace
“ki jirani a nan kin ji ko, idan na fito daga gida ba kya nan…..”
Sai yayi shiru yana wani girgiza kai sannan ya tashi ya wuce cikin gida, neman izini yasa aka masa gurin malam sannan ya shiga ya samu malam ɗin yana ta fifita da mafifici kasancewar yanayin akwai zafi, zama yayi yana fuskantar malam sannan ya fara magana
“malam don Allah ina so ka taimakeni akan yarinyar nan, duk abin da zaka ji nayi akan matar can kar ka ce komai, na yi maka alqawarin ba zan aikata abin da za ka yi danasanin karɓar baquntata ba, ka zuba min ido kawai har sai na dakatar da zaluncin da ake aikatawa ga waɗannan marayun, yin hakan wani nauyine a kaina”
Gyara zama malam yayi kansa a k’asa yana nazarin maganganun bak’on nasa sannan ya ɗago kai yace
“ban fahimci kalmar nauyine a kanka ba, akan me hakan ya zama nauyi a kanka, wa ya ɗaura maka?”
Murmushi yayi ya lanqwashe k’afafunsa yace
“Allah ne ya ɗaura min”
“kamar yaya Allah ne ya ɗaura maka”?
“hadisin annabi yace, duk wanda ya ga abin qi daga cikin ku to ya kawar da hanunsa, ko da harshensa, ko da zuciyarsa, ni kuwa malam ina da ikon aikata duka ukun, kana ganin idan na bari Allah ba zai tambayeni ba”?
Cikin jimamin lamarin malam yace
“kana ganin babu abin da zai faru, ina jiye maka tsoron abin da zai biyo baya, tun da ba ka da alaqa da su”
Murmushin girmamawa yayi wa malam yace
“kar ka damu da wannan malam, ina daidai da duk abin da zai faru, rauni na a zahirinane amma zuciyata cikakkiyar jarumtace cikinta”
Kalamansa sun sanya malam darawa cikin zolaya yace
“ka ce a zuciyarka kai jarumin mazane, qi gudu sa maza gudu”
Take yanayin fuskarsa ta canza, zuwa wani irin yanayi mai wuyan fassara, ba komai ya janyo hakan ba face kalmomin malam da suka tuno masa baya, cikin wannan yanayin ya tashi yayi sallama wa malam ya fice, shi ko malam bin shi yayi da kallo cikin ranshi yana sake jin wannan shakkun akan bak’on nashi yana sake kama mishi zuciya, wani sirri yayi da zuciyarshi ba tare da ya furta ba ya jinjina kai tare da amince wa abin da ya tsara
Gurin da ya barsu ita da shafiu nan ya taraddasu saidai yanzu kuka ya samu take yi shafiun yana ta bata hakuri
A kansu ya tsaya kusan minti uku bai ce komai ba sannan cikin tsumewa yace ta so mu je, shi ko shafiu da tun tsayuwarshi a gurin yake ta qare masa kallo a sace, so yake lallai sai ya tuna gurin da ya so ya san fuskar amma ya kasa
Miqewa tayi jiki a mace ta ɗau tiren kayan miye, kallon shafiu yayi yace ɗan uwa minti biyu, ina zuwa, ba damuwa yace sannan ya fara gaba tana binshi a baya
Sallama yayi a k’ofar gidan kamar sau uku sannan ta fito tana yatsina kasancewar baban mairo baya gidan, cikin raini ta kalleshi sama da qasa tace
“malam lafiya”?
“ki ce wa haule ana magana da ita”
yace cikin dakewa
Wani kallon rashin arziqin ta sake masa sannan tace
“kai wani irin haule ba ko ladabi, ina laifin baba haulen”
Tsawa ya buga mata wanda yayi qoqarin lalata mata netwrk sannan yace
“idan uwarkice, ni uwata ce”?
Tun ba a je kiran haule ba wannan tsawar ya gayyatota soron tana cewa
“lafiya indo?, me yake faru….”
bata qarasa ba maganar ta maqale saboda ido biyu da sukayi da dodonta, irin ta nuna taurin kan nan sai ta haɗe rai tace
“kai malam lafiya?, ce maka aka yi muna raba sadaka”?
bai damu da abin da tace ba balle ya bata amsa ya juya bayanshi yace wa mairo ta zo ta shiga gida, cike da tsoro biyu ta fara tafiya a hankali har ta shiga soron gidan idanunsa na kanta, kallon haule yayi cikin tsana yace
“idan kina son yarinyar nan ta je miki talle to dole ki bata abinci kafin ta fita tallen, idan kuma kina buqatar neman sabon jari to ki sake ɗaura mata talle da yunwa, idan kina neman zaman lafiya kuma kar ganganci yasa ki ɗora hanunki akan yarinyar nan, shawarace”
Yana faɗin haka ya juya zai tafi
“toh ban ji ka ce a matsayina na wane ba tsohona”
Haulece ta ke faɗin hakan bayan ta riqe qugu
Juyowa yayi yana murmushinsa na shu’umanci yace
“a matsayina na ɗan iskan gari, ina fata kin gane”?
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/2, 6:41 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*10*
“ai kuwa wallahi na ga alamar kai hukumace zata raba mu da kai, domin bazan zuba maka ido kana shige min iyaka ba”
Cewar haule cikin kuri da ɗaga jijiyar wuya
Cak ƴya tsaya a inda yake ya juyo yana kallon fuskar haule da take tsaye a bakin qofar gidan, wani irin kallon raini ya mata sannan yace
“hukumace kawai kike da ikon kira ina fata?, to ai da sauranki tun da ba mala’ikum mutuwa za ki kira su tafi da ni ba, amma ya kamata ki san bayan ɗan iska akwai ɗan guguwa”
Yana gama faɗin hakan ya juya ya cigaba da tafiyarsa
Nan kuwa haule ta hau zage zage kamar wata hauka new kamu🤣
Mairo da take tsaye cikin soron karkarwa ta fara don ta san yau sai yadda Allah yayi da ita wai ɓarawo a hannu mata
“ai wallahi baba haule ga shegiyar da ya dace ki kama ki naɗa mata duka, ki farfasa mata jiki, banza marar gata, mai baqin jini, tana yawo kamar mahaukaciya”
Indo ce take faɗin haka bayan ta kusanto mairo sosai kamar za ta dake ta
“bar ta kawai indo, ina da tabbacin wannan yaron zai yi janyo min asara idan na taɓa lafiyarta, ni ban taɓa jin shakkar wani namiji a duniyar nan ba kamar wannan shegen mutumin, mutum kamar ɗan wani a cikin qasar, ba ki ji yadda yake magana ba, cike da iko”
“burgace kawai, wannan mutumin da yake yawo cikin mutattun kaya mai yake tak’ama da shi da yake jin ya isa, ban da kuri da ɗacin hali irin na wanda talauci ya wa ɗaurin goro, toh ni ki barni in dake ta idan ke baza ki daketa ba”
“wane ni, wallahi ko da wasa, dan idan kika taɓa ta wannan matsiyacin ya talautani sai kin biyani kayana, abincine dai dan ubanta k’anzone ga shi can ta je ta kankare”
“shikenan ai, sai kiyi tayi, ni barin bar gurin ma kar takaici ya kasheni”
Cewar indo ta wuce cikin gidan tana mitocinta
“zaki wuce ne ke kuma munafuka ko sai na fasa miki idanun da kike zarewa”?
Sum sum mairo tayi cikin gidan, zaune ta hango idris a takure yana tsiyayar hawaye, tausayin ɗan uwan nata ne ya shigeta kasancewar ta san yana fama da zazzaɓi mai zafi amma tun maganin da ta saya masa jiya ya shaye bai sake shan wani ba kasancewar ba ta da wani kuɗin, babansu kuma da ta faɗa masa tun da yace ya ji, bai sake ce mata komai ba, ga shi ta san babu mai kula da shi idan ba ta gidan, abinci ma da yaya ake bashi, sai an tsine wa uwarshi tsaf har da uban ma wani lokacin kafin a ba shi kaɗan ya ci, wai shi bai k’i a bashi duka abincin gidan ba saboda cin tsiyarsa
Kusa da shi ta je ta ajiye tiren sannan ta zauna a gefensa ta janyoshi jikinta idonta cike taf da qwalla tace
“idris jikinne?”
Cikin rawar murya ya kaɗa kai tare da faɗin
“jikina sanyi yaya, yunwa nake ji”
Hawayen da ya zubo mata ta share sannan tace
“ka yi hakuri ka ji, idan na karɓo kuɗin wankin da na yi wa yusufa zan sayo maka maganin, bari na ɗauko qanzona mu ci tare ka ji”
Kai ya kaɗa mata yana duququne jikinsa, ba ta kai ga miqewa ba ta ji muryar haule a kanta tana cewa
“toh uwar kusasi me ɗan gyauto, za ki tashi ki kankaro qanzon ko kuwa sai na miki abin da kika saba da shi, ni za a kawo wa tsiyatakuna minajja’irina”
Cikin marairaicewa ta ce
“don Allah baba haule kiyi hakuri ki sammin koko in bai wa idris, ki taimakeni don Allah, ko na goma ki ɗibar min cikin naki zan nemo kuɗin in biya ki”
Abinka da rashin imani balle tausayi, ga tarin jahilci, cikin rashin hankali haule ta fara sababi
“ke dai akwai shashasha, ban da neman ɓata baki yaushe zaki tsaya roqon koko a gurina, ai da in baki kokona gwara in sheqar a kwata ya fi min alheri, don wallahi bana taɓa yin alheri komai qanqantarsa wa ɗan maqiyina domin shi ma maqiyinane, ni ai duk duniya bani da maqiyi kamar ta kushewa, ba dan kar in zo da sabon karatu ba sai in ce Allah ya qara nauyin qasa, munafuka har kike cewa zaki nemo kuɗin ki bani ko kunya babu da yake bariki ta buɗe miki ido, kina yawon bin maza kina nemo kuɗi ko?, to wa ya sani ma ko wannan matsiyacin mutumin shi ma yana son samu rabonshi ne tun da ke kin zama tandar gwamnati garar al’umma”
Tun ba ta dire a kalamanta ba mairo take kuka wiwi, wani irin zazzafan baqin cikine ya zo ya tokari qirjinta, ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu don har wani ɗaci take ji da maqaqi a wuyanta, cikin kukan take tuna ina ma da mutuwa ta zo ta ɗauketa ko zata huta da wannan rayuwar, ko yaushe za ta fita daga cikinta oho?
“har kike wani jan zuciya, sharri na miki ko qazafi, ina cewa ranan ilu na gani ya shafeki kamar tsohuwa ta samu maigurguwa”?
Cike da takaici ta ɗago ta kalli haule amma ta rasa me za ta faɗi ma tsabar baqin ciki
“kin wani tsareni da ido, zan daku ne?, yarinya ba yadda kika iya da abu ɗinɗimi, wai kishiya daga makka don kuwa dole ace mata hajiya, ko uwarki ma ba ta iya da ni ba”
Ganin abun ba arziqi yasa mairo ta miqe tana yin kuka mai cin rai ta je jikin tukunyar da akayi dahuwar a ciki, a buɗe ta sameta quda suna ta bi, amma haka ta sunkuya ta fara kankarar qanzon
Kwata kwata wanda ta kankaro ko idris ɗin bazai qoshi ba idan ya ci, loma biyu kawai tayi ta bai wa idris sauran, abinka da yaro, bai lura da cewar ita ɗin ba ta ci komai ba ya karɓe cikin qanqanin lokaci ya qaddamar wa qanzon nan sannan ta ɗebo masa ruwa a rijiya ta kawo masa ya sha sannan yace mata yana jin barci, ɗakin da suke kwana ta kamo hanunsa ta kaishi tace yayi barcinsa kafin ta dawo,
Haka ta sake ɗaukan tallen ta fita, maimakon Allah ba da sa’a haule sai bin ta tayi da cewa
“wallahi ko ɗaya kar ki kuskura ki dawo min da shi, ko zaki kai gobe dole sai kin sayar ki dawo gidan nan, na faɗa miki”
******
Waige waige yake yi kamar yadda ya saba, sai da ya tabbatar ba mai ganinshi sannan ya ciro abin maganarshi ya kunna, wata number ya dialing sannan ya kara a kunnensa
Daga can ɓangaren bayan an ɗau wayar sallama aka yi shi ma ya amsa cikin farinciki da annashuwa jin muryar farincikin tashi
“cwthrt kece?”
“eh dady ni ce, k’awallice tace in yi magana”
Hakoransa gaba ɗaya ya bayyanasu garin murmushi ba murmushi ba, dariya ba dariya ba sannan yace
“Allah cwthrt”?
“Allah my dady, kullum sai na yi kuka dady, ban ganka ba kuma baka kira ni ba”
“oh!! No no no my lovely amrat, kiyi hakuri kin ji, gurin da nake ne ba ko da yaushe ake samun daman kira ba, amma na kusa dawowa gurinki my cwthrt”
Cikin dariya tace
“toh my dady, ka kawo min jirgin sama, wannan irin nakun nan”?
“eh na ganeshi”
“yauwa to shi nake so, da irin bindigarka”
“an gama babyna, saura kuma me”?
ɗaga kai tayi sama cikin salon iyayinta tace
“ummm, shikenan kawai dady, uncle A ya kawo min abubuwa da yawa, kai ma na ce wa hajiya ta ajiye maka wasu, hmmm dady sai kunnenka ya tsinke saboda daɗi”
Bai san lokacin da ya qyaqyale da dariya ba yace
“Allah cwthrt”?
“Allah dady”
Ita ma ta faɗa tana ta dariya abinta
“to shikenan, ki ce wa hajiya ta cigaba da ajiye min kayana”
“toh dady, ga hajiyar ma kuyi magana ka tambayeta”
“toh my amrat, har an gama hirar da dadyn?”
“eh amma idan nayi barci na farka ka kirani”
“an gama ‘yar dady, gobe kenan ko”?
“eh gobe”
“toh bye my cwthrt, love you”
Har ta kai wayar kunnen hajiya ta sake dawowa da shi kunnenta ta ce
“me too dady”
Sannan ta sake manna wayar wa hajiya a kunnenta
Hajiya cikin farinciki suka gaisa da gudan jinin nata sannan suka nitsa hira, nan take tambayarsa cewar ta ga an qaro sojoji cikin gidan lafiya kuwa, lafiya lau yace mata sannan tace masa
“kun yi waya da honourable kuwa”?
“wanne kenan hajiya?”
“abokin alhaji nake nufi”
“oh abokinsa wanda suka haɗu sanadiyar aikin hajji”?
“shi fa”
“gaskiya ba mu yi waya ba”
“amma kuwa nayi mamaki da ka ce min ba kuyi waya ba, domin yace zai nemeka”
Cikin haɗe rai yace
“akan me”
Saboda kakkausan harshen da yayi amfani da shi yasa hajiya ta fahimci gurin da ya dosa, domin idan yana son mutuwarshi to yana so abokan babanshi suce za su auri hajiyarsa
“toh iyayen zafin kai, ba maganar da kake zato bane, tun da ma haka ne abin ba zan faɗa maka ba, ka jira shi ɗin ya kiraka da kanshi ya sanar da kai”
Dariya yayi yace
“a gafarceni hajiya”
Ita ma dariyar tayi tace
“taqadari, da ni kake zance, na kusa ɗaura aure ai, tunda kai baza ka yi auren ba”
ɗif taci ya katse kiran, nan hajiyar tayi ta tiqar dariya har amrat tana tayata
************
Zaune take ita kaɗai jikin bishiyar dirimi, gyaɗa qulli ukune akan tiren amma tana tsoron tafiya gida saboda gudun tijarar da za a mata, idan ba a yi sa’a ba har sai abin ya shafi uwarta
Sanyi ake yi saboda ruwan sama da aka tsula a yammacin ranar, sai takurewa take yi, wani shegen yaro da ake kira ɗan muguwa a qauyen ne ya tunkaro gurin da take sai warin wiwi yake yi
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/3, 6:33 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*11*
Toshe hancinta tayi lokacin da ya tsaya a gabanta tana binshi da kallon tsoro domin duk ranar da ya ma ta irin wannan zuwan sai ya zalunceta, domin cewa yake yi ta fanshi kanta da gyaɗar da take sayarwa ko kuma ya sa a ɗauko masa ita, kullum kuwa cikin faɗa mata yake masu gata ma ba su tsira a gurinshi ba balle yarinya wulaqantacciya irinta, ita ɗin ma yana tausaya matane a hakan, dole take bari ya ɗebi yadda yake so domin ta kare mutuncinta, idan ta tashi tafiya gida kuma sai ta bi gidan ladan su taimaketa da aron kuɗi idan ta yi wanki ko surfe sai ta biya su, wannan uquba ta ɗan muguwa ita ma qalubalece me zaman kanta a gurin mairo amma ba ta taɓa faɗa wa kowa ba, a ganinta tunda shi ɗan mai garine babu yadda aka iya da shi, a gefe guda kuma ga zurfin ciki.
Dariyar ya qyalqyale mata da shi ganin yadda ta firgita da ganinshi sannan ya fara magana cikin muryar waɗanda suka saba qwalewa
“mairoro yarinya mai gyaɗar dare, ga ta baqa ga ta mummuna, yarinya maras gata, ko ba haka bane”?
Ya qarasa maganar cikin tsawar da ko ni mace a qaramin gudu zan iya kwantsama ta
Da sauri ta fara kaɗa kai tana faɗin
“haka ne, haka ne, eh eh”
Sake qyalqyalewa yayi da wata dariyar sanna ya riqe qugu yana cewa
“yauwa yarinya, to yanzu ina labarin gyaɗata”?
Cikin rawar murya tace
“ɗan muguwa don Allah ka yi hakuri, wallahi yau bani da kuɗin da zan cika idan na baka gyaɗar nan, ko biyar ban da ita, ka taimakeni don Allah, idan na samu kuɗin ko ba ka zo ba zan tura maka da shi”
“ba ki da matsala da wannan ai daman zaɓi biyu ke gareki, ko gyaɗa ko mai gyaɗar, to in kin rasa kuɗi nasan ai mai gyaɗar kuma ba a rasa ta, ko kuwa”?
Shiru tayi ta sunkuyar da kai, take hawaye ya fara wanke mata fuska
“kai kai kai, ina miki magana ma kin yi banza da ni, to kin san wani abu?, da gyaɗar da mai gyaɗar yau duk sai na haɗa, zan ga wan da ya isa ya dakatar dani, ko da mutane a gurin nan, balle kin ga kowa sanyi ya kora shi, daga ke sai wancan mai shayin da wannan mai raken, to ke a ganinki cikinsu wa yake da damar tsayar da ni, mai shayi dai kafin ya qaraso har na saɓaki a kafaɗa mun wuce, shiko mai rake duka ɗaya zan masa ya kasa ganewa, to ya kika gani?, zaki taso mu wuce ba tare da hankalinsu ya dawo kanmu ba ki tona wa kanki asiri, ko kuwa kin fiso in ɗauke ki a kafaɗata ki gayyato hankalinsu kanki”?
Kallonshi take yi tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro sannan cikin kukan tace
“don Allah ka rufa min asiri, kar ka tozartani, ni ba kowa bace cikin mutane, kar ka qara min wani raunin akan wanda nake da shi”
“ke kina ɓata min lokaci fa, kafin na qirga uku ki tashi mu tafi, idan ba haka ba ki kuka da kanki don ni a nan gurin ma idan na so wulaqantaki zan yi babu abin da ya shafeni, ki za ki kasa fitowa”
Ya faɗa mata cikin tsawa har ya janyo hankalin mai rake ya dawo kansu
A firgice ta miqe tsaye tana kuka shaɓe shaɓe tana cigaba da ba shi hakuri amma kamar da dutse take yi, ganin tana ɓata masa lokaci yasa ya kai hanunsa ya damqo nata hanun tare da kwashe sauran qullin gyaɗar ya sanya a aljihun rigarsa sannan ya fara janta, turjewa ta fara yi tana ihu tana roqonshi amma ya qi ya sake ta, suna cikin haka kawai ba tare da ta ji zuwan mutum ba sai gani tayi ya ɗauke ɗan muguwa da mari, bai tsaya nan ba ya fara kai masa naushi da hannu da qafa, abunka da jikin da shaye shaye ya gama da shi, sau ɗaya yayi yunqurin ramawa sai ji yayi kawai an kai wa hanun dukan da ya rasa gane cewa hanun na jikinsa ko kuma ya tsinke, ɗagoshi yayi tsaye, ya sake gaggaureshi da wasu marukan da ba shiri haɓo ya fara wanke masa baki da hanci, sai ihu yake yi amma daga mai shayin har mai rake babu wanda ya zo balle ya kira masa gudumawar jama’a
“kai ɗan uban waye a garin nan, wa ya ɗaure maka gindin cutar da yarinyar mutane??, ka min magana mana”
Ya qarasa maganar cikin ihu tare da sake gaure shi da wata zazzafar marin da ta saka ɗan muguwa sakin jiki da baki
“ni ɗan mai garine kuma wallahi sai zaman qauyen nan ya gagareka, tun da ka taɓa ni”
Kamar abin qyama haka ya bishi da kallo sannan ya wancakalar da shi kan jiqaqqiyar qasar da ta dawo laka ya tsaya a kanshi yace
“lallaine, kai ɗan wanine a garin, toh bari in baka kyakkyawan sak’o zuwa ga tsohon naka”
Yana rufe baki ya fara qwallo da shi kamar ya samu tamola, abinka da dukan mutanenmu abin ba sauqi, sai da ya gama luguiguitashi yana ihu har mutanen da gidansu yake kusa da gurin suka fara fitowa sannan ya take mishi qirji da qafarsa ya fara faɗin
“idan ka je ka faɗa wa mai garin in jini na hukuntakane akan yunqurin fyaɗe da kayi kan yarinyar mutane, ka ji ko baka ji ba”
Shiru irin na an shiga ukun nan ɗan muguwa yayi, yana numfarfashi, cikin tsawa ya sake dukansa da qafa a qirji yace “nace ka ji ko baka ji ba”?
da dai yaji abun ba daɗi wai mahaukaci ya ci kashi, da sauri yace “wlh na ji”
Sauke qafarshi yayi wanda yayi daidai da qarasowar liman gurin, cikin ‘yan kallo wani ya ruga da gudu ya kirawo shi
Ai a miliyan ɗan muguwa ya taitaya ya kwashi gudu
“Abdullahi”
Cewar liman
Juyowa yayi ya kalleshi, duk da fuskarshi a murtuqe yake amma cikin ladabi ya amsa wa malam tare da qarasowa kusa da shi
“Abdullahi mai yake faruwa?, mai yasa kayi haka”
“malam qoqarin keta wa maryam haddi yayi, ni kuma na hukuntashi da irin hukuncin da ya dace da shi”
Kamo hanunshi yayi suka fara tafiya, suma mutane kowa sai ya fara jan sayyadarsa
“Abdullahi ka san ɗan waye ka daka kuwa, duk da kwananka biyar a cikin garin amma ina da tabbacin da ka sani da ba ka yi dukan nan ba”
“ɗan maigarine, kuma na rantse da ubangiji al’arshi, ko maigarin ne yayi yunqurin aikata abin da ɗansa yayi sai na hukuntashi da irin wannan hukuncin”
Da sauri ladan ya sake hannunshi cike da tsoronshi yace
“Abdullahi wallahi ban yarda da kai ba, ka faɗa min gaskiya kai waye?, mai ya kawoka qauyen nan, kai ba matafiyi bane, akwai wani sirri a baɗininka”
“tabbas ni ba Abdullahi bane, ina da wani sunan bayan wannan, ka jira martanin mai gari a gareni, a lokacin zaka san wanene baqonka”
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/11, 7:47 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*12*
Kallonsa sosai malam tanimu ladan yayi kamar ya samu TV sannan cikin rawar zuciya yace
“kamar yadda na sani, babu wata halitta cikin ruwa ko a iska, a sama ko a qasa da ta wuce baiwa ko bawan Allah, da mai cutarwa da maras cutarwa, don haka zan cigaba da kiranka da sunanka da ya bayyana a gareni har zuwa lokacin da zaka bayyana baɗininka a gareni, Abdullahi Allah ya sani, dominshi na karɓi bak’oncinka kamar yadda yayi umurni cikin ayoyinsa na alkur’ani, ka sani duk wani abin da ya ratso tsakaninmu na cutarwa daga ɓangarenka wannan ubangijin shine a tsakaninmu, domin shine mafi alherin masu ɗaukar fansa, Allah ya tashe mu lafiya”
Yana gama faɗin haka ya tunkari qofar shiga cikin gidan
Jikinsane yayi sanyi sosai, kalaman malam a gareshi yasa shi jin cewa bazai iya cigaba da ɓoye kanshi ga malam ɗin ba, zai bayyana masa ko zai samar wa tsohon nutsuwar zuciya,
Da sauri ya taka cikin qyaftawar ido ya sha gaban malam, hakan da yayi kuwa ba qaramin firgita ladan yayi ba, cikin ɗaukewar netwrk ya tsaya yana bin sa da kallo
Cikin muryar da take nuna tsantsar ladabi ya ce
“malam kayi hakuri da yanayin da ka sameni, ka cire tsoron da kake da shi daga ranka a kaina, ni ba mai cutarwa bane, ka fahimceni”
Cikin qosawa da surutunsa yace
“don Allah ka rabu dani da wannan dramar taka Abdullahi, kamar yaya kake cewa in fahimceka bayan ban san kai wanene ba, me kake tafe da shi, me ka zo nema cikin qauyen nan, ta yaya zan fahimci mutumin da ban san ko wanene shi ba”?
Cikin ɗaga murya ladan ya qarasa maganar yana nuna Abdullahi
“ni ba ɓoyayye bane malam, ka kalleni da kyau, zaka gane wanda yake gabanka, ka cire siffar rauni ka ɗauko ta jarimta ka ɗora akan fuskata, cikin sauqi zaka fahimci ni waye, ka yi sauri malam, ka gaggauta, bana so wani ya ji ko da kalma ɗaya cikin zantuttukanmu”
Hular da take kansa ya janye tare da macacciyar hiramin kan kafaɗarsa, sauya fuskarsa yayi daga ta dramar da yake yi zuwa fuskarsa ta ainihi mai cike da jarumta da tsoratarwa sannan ya ja da baya yayi wata iriyar tsayuwar da ya saba yinta a yawanci ɗaukar hoto ko videonsa da ake fitarwa, sai kuma ya taqware hannayensa ya juyasu tare da ratayesu a baya
Kallonsa malam yake yi cikin qoqarinsa na gano ainahin Abdullahi, bai kammala nazarinsa ba suka jiyo muryar a bayansu tana cewa
“tabbas kaine, hasashena gaskiyane, na ɗau lokaci ina son tuno inda na san wannan fuskar yallaɓai, ashe dai ina da tabbas cikin tunanina duk da sai yanzu na samu tabbas”
Gaba ɗaya suka juya suna kallonsa, shi dai bai so hakan ba saɓanin malam dayake neman mai taimaka wa tunaninsa gurin gano haqiqaninsa
“shafi’u a ina ka sanshi, waye shi ɗin”??
Gabansa ya tsaya ya kallesa da kyau sannan ya kalli mahaifinsa yace
“general fawwaz malam, wannan mutumin sunanshi na gaskiya kenan, na san ko a radio za ka taɓa jin labarin tsayayyen jami’in sojin nan wanda al’umma take kira da gee fawwaz, wanda ya samu matsayi da dama sanadiyyar jajurcewa kan aiki da sadaukarwarsa akan gaskiya, to shi ne wannan”
kamar gunki malam ya zama na waɗansu seconds sannan cikin firgici da tsoron abin da ya ji yace
“ka tabbatar da abin da kake faɗa kuwa shafi’u, idan shine mai zai kawo shi nan”?
“kai na zo nema malam, kuma na gode ubangiji da ya haɗa ni da kai”
Tsoronsa ne ya ninku akan wanda yake da shi, shi kanshi shafi’u ya tsorata da jin furucin gee fawwaz, bakinsa na rawa ya durqusa a gabansa yace
“yallaɓai don Allah ka ji qan mahaifina, wallahi mahaifina ba mutumin banza bane, mutumin kirkine, ba ya daga cikin mutanen banza”
Murmushi yayi ya ɗago shafi’u ya ɗora hannayensa akan kafaɗarsa cikin taushin murya yace
“na san abin da baka sani ba shafi’u daga mahaifinku, ina da tabbacin shi kanshi bai san na san wannan ɓoyayyan sirrin nashi ba”
Wannan karon malam ne yayi gaggawar amsawa cike da ya matso kusa da gee fawwaz yace
“na rantse da Allah yallaɓai ban san wani mummunan aiki da na sirrantashi nake yi a ɓoye ba, yadda zahirina yake haka ma baɗinina yake”
“ba daidai suke ba malam, kar mu yi jayayya da kai, ina bibiyar duk wani motsinka, musamman fitar da kake yi cikin dare”
Kallon tsoro malam ya bishi da shi, yayin da shafi’u kuma ya tsare ubansa da kallo domin iya rayuwarsa da mahaifinsa bai san yana wannan fitar cikin dare ba, neman tabbas kawai yake yi
“kar ka damu da wannan malam, kamar yadda ka sirranta kayanka nima zan cigaba da barinsa a sirrin babu wanda zai ji, wannan dalili yasa na qara sakankancewa da cewar kai na zo nema cikin qauyen nan, saboda gaskiyarka daamanarka, da halayenka na taimako, zan baka hakuri kan bibiyar rayuwarka da na yi tayi ba tare da amincewarka ba, duk da nima na san kayi ta qoqarin bibiyata domin sanin haqiqanina sadai tun ranar da ka fara tura wannan yaron a bayana na fahimceka, hakan yasa na sauya takun da nayi ta wahalar da ɗan leqen asirin naka, na tabbatar har yanzu da nake gabanka bai san komai a kaina ba”
Mamakine ya kusa sanqamar da ladan domin kwata kwata bai taɓa zargin baqon nashi yana bibiyarshi ba balle ya fahimci ya san abin da yake shiryawa a kanshi na bibiyar haqiqaninsa, ganin abin yake yi kamar a mafarki
“ba na so kowa ya fahimci haqiqanina shafi’u, idan wani ya san asalina kaine, domin malam ya rufa min asiri tun farko, da ya jinginani da ɗan abokinsa, ina fata ka fahimci hakan”
Cikin jaddada masa maganar da kai ya qarasa maganar,
“ban ma san komai ba ranka ya daɗe”
Shafi’u yace yana murmushi, martanin murmushin ya mayar masa tare da faɗi
“yawwa, ka kyauta”
Hankalinsa ya mayar kan malam da yake ta kallonsa kamar wanda ya warke daga makanta, cikin ladabi yace
“ko za mu bar maganar zuwa safe malam”
Gyaɗa kai ya fara yi yana cewa
“toh…toh…toh yallaɓai haka za a yi, Allah ya kai mu”
Ameen yace sannan ya miqa masa hanu suka yi musabiha, ya sake miqa wa shafi’u suka yi musabihar ya musu sai da safe tare da shigewa ciki, shi ma shafi’u da ya zo da niyar yin maganar noma da malam sallama ya masa ya juya ya wuce gidansa da ke jikin na malam ɗin
*********
Sallama ake ta kwaɗa wa a qofar gidan, kasancewar sanyin damina ta ratsa qasa ga kuma lokaci na safiya da yawa mutane sun koma barcin safe bayan sallar asuba
Kasancewa ɗakinsa ne a soron yasa shi fitowa bayan ya amsa sallamar da ake ta yi ba tare da jinkirtawa ba
Kallon kallo sukayi da mutumin sannan yace
“malam lafiya dai”?
cikin ɗaga murya yace
“lafiyar kenan saurayi, ina ladan?, ka shiga ka faɗa masa maigari yana neman baqon gurinsa, su taho da baqon yanzu yanzu”
“shi dai baqon ya zo dai ko?, amma menene laifin ladan”?
“kai yaro, yaya maigari zai yi aike ka tsaya kana tuhuma, ko dai so kake ka ja da hukuma”?
“wane ni, abi doka dai, saidai gani nayi mai laifi daban ai ba za a tuhumi wanda bai san me ya faru ba, ko kuwa”?
“kai ni yau Allah ya haɗani da jarida filin tambayoyi da amsoshi, wai dai ko kaine ka samu ɗan mai garin ka dinga casa kamar ka samu sabon wake, ka yi ta qwallo da shi cikin turɓaya”?
Ayi hakuri da wannan, da qyar na yi shi, hakan ma don na yi alqawarine amma mura irin me zazzaɓin nan yana damuna, ina buqatar adduoinku
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/13, 8:07 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*13*
Wani kallo gee fawwaz ya masa irin na dubekan nan sannan ya naɗe hannayensa a qirji ya fara magana cikin dakewa da rashin tsoro
“ni ne nan na jibgeshi son raina, nayi dama-dama da shi a cikin laka, duk da ba haka zuciyata ta so ba, na so a ce zuwa yanzu a asibiti yake ba da wannan labarin, so na yi a ce zuwa yanzu yana zuqar ruwa leda ta biyar ce, ban so ace yana hayyacinsa ba”
Tsab ya gama sauraron jawabin gee fawwaz cikin sanqamewar zuciya da tsoron zafin furucin nasa kan ɗan maigari, daidai ta tunaninsa yayi bayan ya sauke numfashin dole sannan ya fara kici kicin rataye babban rigarsa akan kafaɗarsa ya ɗago da kansa yana kallon gee fawwaz ya ce
“kai yaro, wallahi tallahi ka iya da bakinka, tsaro dai ɗan talakawa, ka san waye hakimi kuwa, ka san wutar da kake kunnawa wa kanka kuwa, ina kake bak’o, ka ganni nan ni kaina har jikina ya fara ɗanar raɗaɗin bulalun da zaka sha a fada, kai har gilmawar bulalun na fara gani a idanuna, iya baki baqo, kana jina ko baka ji?, yanzu tukunna kawo wani abu na ɗan lasa wanda zai zamo maka makarin lulluɓe wannan sirri naka abin ɓoyewa, idan ba haka ba ruwan wankan me jego sai ya fi naka sanyi wanda zaka gasa jikinka da shi bayan jibga da zaka sha a fada sanadiyar fitar waɗannan shuɗaɗa, baqaqe, munanan kalaman naka”
Wannan dogon surutu na garba rahoto ya matuqar qona ran fawwaz, ji yayi kamar shi ma yayi ta qwallo da shi har zuwa fadar, sai dai wata zuciyar ta dakatar da shi, a qufule yace
“ba zan bayar ba, idan mun je fadar zan ga wanda ya isa ya nuna ni da yatsa ma kawai”
“ai kuwa toh wallahi yau za k…….”
“kaiiii…………..”
Fawwaz ne ya buga masa tsawar da ta saka shi riqe kansa, sannan ya damqi gefen rigarsa ya jijjigashi cikin ihu yace
“kai ma azzalumine kawai, idan ka qara tari ba da izinina ba sai ka bar wasu qasusuwarka a gurin nan, mu je ka kaini fadar”
Ai kuwa daidai lokacin sai ga mairo ta fito da tallen kokonta na jaraba duk safiya, da yake ran ‘yan maza ya ɓaci ita kanta mairon tsawa ya buga mata yace
“keh! zo nan”
A tsorace ta matso kusa da su tana zare ido, shi ma ladan lokacin suka fito daga cikin gidan da ɗansa kabiru, har rige rigen fitowa sukeyi,
“kin ci abinci ko ba ki ci ba?”
Inda inda ta fara cikin kame kame
“keh! ki faɗa min gaskiya, idan kika min qarya ko?, hmm”
Sai kuma yayi qwafa
“ban ci ba amma wai…..wai…., wai… ya qare ne, za a bani idan na dawo”
Ai kuwa rufe bakinta yayi daidai da ɗauke robar da ke kanta na kokon ya saita qofar gidansu da shi ya maka a jikin dangar gidan, tuni koko ya watse ya tambaɗe a qasa robar kuma ta kifa abinta kamar an saka ta yin hakan
“wuce mu tafi”
yace wa mairon fuskarsa a haɗe
Ai wal fauru da gaggautawa, da sauri ta yi gaba duk da ba ta san gurin da za su je ɗin ba
“me ke faruwa kuma Abdullahi?”
Cewar ladan bayan ya zo gabanshi ya tsaya
“malam daga fada aka turo kiranmu ni da kai, ni kuma nace babu in da zaka je tun da baka da masaniya akan abin da ya faru”
Shiru malam yayi cikin rashin sanin amsar da zai bayar, don Allah na gani ya tsorata da fawwaz sosai, ko barcin kirki bai samu damar yi ba a daren jiya
“kwantar da hankalinka malam, idan duk garin nan fada ce babu wanda ya isa ya fitar da kai daga cikin gidanka zuwa fada ba tare da laifinka ba, ka je gida kawai, idan za ka tafi gona ma duk ka je abinka”
Yana gama faɗin haka ya cigaba da tafiya cakume da rigar garba rahoto, ko mai ya tuna kuma oho, sai ya sake masa rigarsa yace
“kai mu fadar”
Ko tarin kuwa garba rahoto ya kasa yi, gaba yayi fawwaz na bayanshi yayin da mairo take binsu a baya
“baba anya wannan baqon naka ba ɗan tauri bane?
Kabirune yake raɗa wa ladan haka a kusa da kunnensa, irin baya so a ji ɗin nan,
“Allah shine mafi sani kabiru, ban san komai ba”
“toh amma dai abokin naka shi ɗan taurine ko?”
Cikin gundura da tambayoyin yace
“ka bar waɗannan nan tambayoyin kabiru, ba na son surutu”
Juyawa yayi ya tafi cikin gida, yayin da kabiru kuma ya bi bayan su fawwaz bayan ya tabbatar da shigar mahaifinsa gida yana cewa
“wallahi ni ma ba za a yi bana gurin ba”
************
Zaune suke gaban maigari, ya ci rawani sai muzuran banza yake yi da wofi
“tabbas ni na dakeshi, saboda mummunan laifi da yake shirin aikatawa”
“wani irin laifi kenan?, ko zan iya sani”?
Kallon ɓangaren da mairo take yayi sannan yace
“ga wacce ya so keta wa haddi ni kuma na dakatar dashi da iyakata”
“wacce irin iya ka ke gareka da zaka fitar wa wani jini da ita, toh kamar yaya ma ban gane wani irin haddi kake magana akai ba yaro”
“za ka san irin iyakar tawa ba da jimawa ba, maganar haddi kuma waqa a bakin mai ita tafi daɗi, maryam ki buɗe baki ki faɗi abin da ke tsakaninku”
Ya qarasa maganar yana yi wa mairo kallon kin shiga uku idan ba kiyi yadda na ce ba
Ita kuwa da ta san halin baqon maqwabcin nasu ai a miliyan ta hau bayani, duk da tana jin nauyin wasu maganganun amma haka tsoro yasa tayi ta sakinsu a gurin, tsab suka gama sauraronta zuwa lokacin ran fawwaz ya sake ɓaci domin sai a lokacin ya ji wasu kalar zalincin da yaron yake yi wa mairo
Kasa magana maigari yayi, kunyace ta rufeshi sosai, musamman kasancewar yana tare da baqo amininsa kuma ɗan uwansa a gurin, cikin kame kame ya fara cewa
“amma albasa ba tayi halin ruwa ba, da ba ta yi yaji ba, yanzu iskancin da kake yi kenan, um uhm assha assha, ashe duk qoqarinmu na tsabtace yankunmu da muke yi kai kuma qoqarin rusata kake yi, ummm”?
” a tambayeshi dai a ji ta bakinsa shi ma ranka shi daɗe”
Cewar abokin maigari
“ba wani tambayarsa da za mu yi madu, ba ka ga munafuki ya sunkuyar da kai ba”
“gaskiyane a tambayeshin dai, wannan shine adalci”
Fawwaz ne yake faɗin haka yana kallon kai ka san sauran wa ɗan muguwa
“to shikenan, tunda kun nace muna sauraronsa”
Maimakon yayi magana sai ma sunkuyar da kai da yayi qasa, kwata kwata baya son haɗa ido da fawwaz
“ba da kai ake magana ba, an yi haka ko ba ayi ba”
Malam madune ya buga masa tsawa
Da sauri ya girgiza kai yace “anyi baba, kuyi hakuri”
“hakuri da uwaka, nace hakuri da uwaka za mu yi”?
“godiya yake ranka shi daɗe”
cewar kanzagi da yake zaune gefen garba rahoto a fadar
Sunkuyar da kai yayi irin na munafukan nan sannan ya cigaba da bayar da hakuri, duk da a zatonshi bai taɓa tsammanin mahaifinnashi zai masa haka ba, shi kanshi maigari ba don Allah yayi wannan fitittikewar ba, kunyar idanun ɗan uwanshine
“yallaɓai ya kamata a matsayinka na maigari ka ja wa yaronka kunne, kar ya kuskura ya sake kusantar yarinyar nan da wata cutarwa, idan ya qi kuma……, ba zance ga abin da zai biyo baya ba, saidai ka sani kowani sarki yana da nashi iyakar, zaman lafiya shine tsayuwa a daidai iyakar da take mallakinka ce”
Fawwaz ne yake faɗin hakan cikin yanayin da ba za ka iya kiranshi gatsali ko akasinsa ba
Shisshigi irin na ‘yan fada kanzagi yace
“murya qasa dai ɗan talakawa, a sassauta kalamai, gaban maigari kake”
Wani mugun kallo ya masa sannan ya tashi irin tashin jarumtar nan tasa ya nuna kanzagi da yatsa yana cewa
“ba ni da lokacin ɓata lokacina, zan yi biyayya wa shugabane kawai idan ya bi Allah, wannan shine salona, ka ji ko baka ji ba”?
Yadda yake furucin ne ya ɗauke hankali maigari da ɗan uwansa, tamkar sakarkaru haka suke binshi da kallo
Shiko ko a jikinsa ya dawo da kallonsa kan mairo yace
“ta shi mu tafi keh!”
Cikin yanayin ni dai wannan yana janyo min masifa ta tashi ta sanya matattun takalmanta ta yaɓi jiki, ko kallonsu bai sake yi ba ya wuce shi ma
“ran maigari ya daɗe yanzu haka za a zuba wa yaron nan ido ya ci mutuncin fada”
Ajiyar zuciya maigari yayi yace
“kanzagi wannan daban yake, a bar fada ta yi nazari kafin ta yanke hukunci”
daga um sai um fada ta zama, wai er me gulma tayi ciki sai kuma girgiza kai na al’ajabin abin da suka ji suka gani
************
Sun tunkaro kwanar da za ta kawosu qofar gidajen suka jiyo muryarta tana ta bala’i, sanqamewa mairo tayi a gurin ta kasa gaba ta kasa baya saboda miyagun furucin da ke fitowa daga bakin matar akanta, take hawaye ya fara ambaliya kan kumatunta, bata san lokacin da ta durqushe a gurin ba tana cewa
“Allah ka karɓi raina in huta da wannan rayuwar”
Tsawa ya daka mata yace
“kar ki sake in sake jin bakinki ya furta waɗannan kalmomin, kin ji ko ba ki ji ba?”
Gudun kukanta ta qara ba tare da ta ce masa komai ba
Zuciyarshice ta fara tafarfasa, ba tare da ya iya control ɗin kanshi ba ya sanya hannu ya fincikota ya riqo hanunta ya cigaba da tunkarar gidan, ba ta yi tsammani ba sai kawai ganinsa tayi a gabanta yana huci kamar zaki,
“me kika ce?, kika ce ko za ta bi uwarta sai ta biyaki kokonki”?
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/15, 8:34 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*14*
Shiru haule tayi cikin bugawar zuciya sai rarraba ido takeyi kamar mai muzurai, idan tana qaunar mutuwarta to tabbas tana son ganin wannan mutumin da ta tsana domin yana neman zame mata qarfen qafa, domin ko hargagin da take yi a tunaninta maironce ta ɓarar da kokon ta ji tsoro ta gudu, bata ɗauka shi ya kifar ba saboda duk masifar da take yi ɗin babu wanda ya ce mata kanzil cikin iyalan maqwabtan nata, duk waɗanda suka fito daga gidan ladan wuceta sukeyi ba tare da sunce mata ci kanki ba, shi ma baban mairon tun gari da sauran duhu ya fice zuwa lanbunsa dake can kwari balle yayi ta bata hakurin tana masa tijara
“kin yi shiru?, ki maimaita abin da kika faɗa mana”
Cikin qarfin hali ta fara ja da baya tana cewa
“na faɗa wallahi yau ko sama da qasa za ta haɗe sai ta biyani kuɗin kokona, idan ba haka ba zina uwata tayi ta haifeni, ehe babu wanda ya ban jari balle ya rusa min, ko sata sai tayi ta biyani”
Kau da kansa yayi gefe kamar mai nazari sannan ya dawo da kallonsa kanta cikin wani irin kallon qasqanci yace
“yanzu dai kin fasa kasheta kenan ko?, kuɗin kika fi so”
“ah wai malam ya haka ne?, ya zaka dinga titsiye min uwa haka kawai, akan wannan banzan”
Indo ce take faɗin haka cikin nuna izzarta da gadararta, ta wani ci uwar jambaki tamkar kilaki, sai cuna baki take yi kamar kare ya ɗau tukunyar qasa wai ita a hakan ta haɗe
Takawa yayi gabanta yana mata kallon sama da qasa sannan yace
“idan ina magana da mutane bana buqatar muryar dabbobi, musamman haushin karnuka, ina fata kin fahimta”
Waigo wa yayi ga haule ya cigaba da cewa
“ke kuma ba kuɗi, ba abun kuɗi kuma ba magana mai daɗi, saidai kina da damar ɗaukan duk wani mataki a kaina domin nine nan na kifar da kokon, damarkice ki taɓa maryam ko akasin haka, saidai ki sani ba kowani hadiri bane yake zuwa da ruwa, zan so ace kin san da hakan”
Mairo ya sake kallo yace
“mu je gidan ladan ki ci abinci”
Tsayawa tayi tana rarraba idanu tana kallon baba haule cikin tsoro da fargaba, dan ta san yau ita da idris sai ta Allah
“keh!! kin ji abin da na ce ko baki ji ba”
Yanayin yadda yayi maganarne yasa ta yi saurin juyawa zuwa gidan malam, shi ma bayanta ya bi ba tare da ya sake cewa komai ba
“gaskiya kema haule kina ban haushi, duk masifarki ki tsaya kina tsoron wannan matsiyacin?, mtsss”
“ke dan ubanki indo ni ce haule?, ko baban ma babu”?
“yooo meye sunanki idan ba haulen ba, ai haushi kika bani, idan kin ji ance baba ai maganar daɗin rai kenan”
Tafa hannu tayi sannan ta kai mata duka tace
“ka ji sheɗaniyar yarinya, to ki kasheni tunda na baki haushi, ke me yasa ba ki rufeshi da duka ba, kuma wannan asarar ma duk ke kika ja min ita, sai da nace ki bata ɗumamen tuwon nan ko kaɗan ne amma kika qi tsabar taurin kai kika zuba wa agwagi”
“kin ji ki fa, zaki ɗaura min laifi, ke ma ba haka naga kike yi ba?, a gurinki na koya fa”
Da duka ta bita tana cewa
“to fitsararriya maras kunya, to dan ubanki sai kin biyani kuɗina tunda ba ubanki baduku bane ya ban jari, dan ni dai wallahi ban san asara ba, ko ta qwandalace bazan yarda ba”
Da gudu ta je ta shige ɗaki tana cewa
“wallahi ni dai a bar zagin ubana ehee”
Da yake ciki ciki ta faɗa hakan yasa haule cewa
“ni kike zagi indo?, toh idan kin isa ki ɗaga murya ki faɗi abin da kike faɗa”
Banza indon tayi mata, haka tayi ta zage zagenta, tayi da mairo da fawwaz ta kuma sake komawa kan indon duk ita kaɗai, shi dai idris yana ta fakon idanunta, yana ganin ta shige bayan gida ya arta da gudu zuwa gidan ladan, ita daman haka ɗabi’arta take, asara komin kashinta yanzu zata fara gudawa🤣, wayyo duniya
*******
A tsorace malam tanimu yake kallonsa, cikin rawar baki yace
“Yallaɓai ni ….ni…ni tanimu ka ba zakkar waɗannan maqudan kuɗaɗen,? yallaɓai kar ka yaudareni, wallahi ban taɓa ganin kuɗi irin haka ba, kuma….”
“Don Allah malam mu bar maganar nan, kamar yadda na faɗa maka haka nake cire zakkatah, mutum ɗaya nake nema na kirki wanda babunsa bai hana shi taimako ba, wanda zai taimaki al’umma shi ma da abin da Allah ya azurtashi na zakkata, wanda nake fata shima ya cire zakkar a nan gaba domin ciyar da addininmu gaba, kar ka damu da girman dukiyar da na baka, ka damu da girman wanda yayi min umurni da na bayar sannan ya zaɓeka a matsayin wanda zan ba zakkatah, ayyukanka na ɓoye sun saka na raina aikina malam, a wancan ranar da ruwa ya maka duka gurin qoqarinka na gyara wa makauniyar tsohuwar nan hanyar ruwan da yake bi ta cikin gidanta sai da nayi kuka malam, ban taɓa cin nasarar haɗuwa da irinka ba, mutane suna bacci kai kuma kana qoqarin kare gidajensu daga ambaliyar ruwa, kuma hatta ‘ya’yan cikinka ba su san da hakan ba, ni ya kamata in yi mamakin cewar akwai irinka a duniyar nan?, ba kai ya kamata kayi mamakin kuɗin da suke hakkin Allah ne a cikin dukiyata ba”
“ban so ka gani ba yallaɓai, wallahi ban so ka ganni ba domin duk aikin da aka cika bayyanashi yana kawo rauni ga mai aikin, bana so Allah ya jarrabeni akan hakan”
Cewar ladan kenan yana share qwalla, dukkan alamomi sun nuna daga zuciyarshi maganar take fitowa
“haka ne malam, amma na ji daga gurin mahaifina cewa Allah yafi bayyana aikin da aka sirranta dominsa”
“hmmm yallaɓai kenan, Allah ya sa mu dace kawai”
“ameen malam”
shiru suka yi na wani lokaci sannan fawwaz yace
“gobe nake shirin tafiya malam amma ina tunanin halin da rayuwar maryam da ɗan uwanta zata shiga, ina tunanin tsananin da zai sake shigowa rayuwarta, ban san yadda zanyi na ba ta wata gudumawa a rayuwarta ba, abin da ake yi wa maryam ya isa a kirashi da maqurar zalunci”
Daga yadda ya qarasa maganar zaki fahimci ɗacin da maganar take masa akan zuciyarsa da harshensa
Cikin jimami ladan yace
“ba kai kaɗai ba, ni kaina damuwar yarinyar nan ce a raina, saidai duk taimakon da za ka mata na banzane matuqar tana cikin wannan gidan bazai amfaneta ba, shiyasa nake mata adduar ubangiji ya kawo mata qarshen zamanta a gidan nan”
Shiru sosai fawwaz yayi kamar bazai ce komai ba sannan yace
“malam ka cigaba da ɓoyeni ga mutanen garin nan, su cigaba da ɗaukata a Abdullahi ɗan abokinka, zan dawo nan kusa domin kawo canji wa rayuwarta inshaaAllah, hakan kuma yana nufin rufe maganar *zakkatah* kenan ga kowa malam har sai na cimma burina, saidai ban hanaka amfanar dukiyarka ba, ni dai burina kar sunana ya je kunnensu a matsayin wanda ya baka zakkah”
“inshaa Allah babu wanda zai ji asalinka daga gurina sai da izininka, ina roqon ubangijin da yayi umurni da zakka ya tsarkake maka zuciyarka da dukiyarka, ya baka aminci duniya da lahira, ya haifar da farinciki mai ɗorewa a gaba ɗayar rayuwarka”
Ameen yace sannan suka cigaba da tattaunawar sirrinsu cikin ɗakin da aka saukeshi
**************
Kansa a sunkuye yake lokacin da take ta kumfar baki kamar uwarsa, saidai ga dukkan alamu maganar tana dukan zuciyarsa
“ni dai wallahi saidai ka zaɓa ko mairo ko ni, amma ba zan zauna da wannan tsinanniyar yarinyar ba ta dinga janyo min asara ba, ina dalili ina ɗan mafari?, haka kawai yarinya ta dinga turo min garaden maza har gidan suna neman halakani, yarinya kamar kishiyata, yooo da wannan baqar jakar yarinyar ba gwara kishiyar ba, ni da gidan mijina yarinya ta hanani saqat, sam baza ta yuwu ba, ka sawwaqe min ni ko kuma ka san yadda za ka yi da mairo, dan ni dai wallahi ba zan zauna ba”
Hankalinsa a matuqar tashe ya fara ba ta haquri
“don Allah haule ki rufa min asiri, ba zan iya rabuwa da ke ba, ita kuma mairo idan ta bar nan ba ta da gurin zuwa, ina kika ga zata shiga”?
Cikin bala’i da masifa ta daka masa tsawa tana cewa
“to wallahi ni zan bar maka gidanka, idan ya so sai ka auri mairo ka sata a ɗaki, ai daman bariki qawar dandice, har kake kallona kake ce min ina zata je yarinyar da take kai kanta da kanta wa maza a titi, sau nawa ake kawo min gulmar sheɗanar da take yi a garin nan, ko rannan sai da yusufa fagal ya faɗa wa indo ya sha ganinta a ɗakin abokinsa manu suna sheqe ayarsu, ko ba haka ba indo”?
Ta qarasa maganar tana kallon indo da take wurwurga loman tuwo tamkar dai dabba
Da abincin a bakinta tace
“yooo kema haule sau nawa nace miki na ganta sun fito da ɗan liti daga ɗakinsa”
Kamar gaske ta nuna gigicewar qarya tace
“to ka gani ko?, wallahi ba zan zauna gida ɗaya da wannan yarinyar watarana ta kawo min ɗan dakar kuka ba ko ribar tire, dole ne cikin ‘yan iskanta ka nemo wani ka aurar da ita, tunda abin na ta yayi yawa har wannan matsiyacin baqon gidan ladan ɗin bashi kanta take yi, shiyasa tsohon gardi jikinsa na rawa yake zuwa ya shirga min asara yayi gaba, to ka san na yi tun yanzu, ka je ka nemo ‘yan iskan nata su zo a rufa wa juna asiri, domin idan ba haka ba gobe goben nan zan bar gidan nan”
Hankalinsa a tashe ya kallo gurin da mairo take takure take rusar kuka ita da idris yace
“yanzu mairo ashe abin da kike yi kenan, ashe ke matsiyaciyar yarinyace, to wallahi dole ki bar min gida tun baki jawo min abin kunya ba”
Cikin matsanancin kuka tace
“baba ka tausaya min, kai ne mahaifina baba, idan baka tausaya min ba wa zai ji tausayina, wallahi ban san komai akan wannan maganar ba, ka yi bincike don Allah”
“keh baqar makira, indonce zata miki qarya ko me kike nufi, faɗi in ji”?
Haulece ta faɗi hakan bayan ta kai mata duka da takalmi
“bar ta kawai haule, ni ina daidai da duk tsiyar da take ji da shi, yanzu zan tashi mu tafi gidansu yaran, duk wanda zai kwasa to na yarje masa ya kawo ko nawa ne”
“ai an bar kari tun ran tubani malam, ita da bakinta ta musanta balle su yaran da suka samu na banza, abu mafi sauqi ka ɗauketa ku je gurin baqon gidan ladan, ka kafe masa kace shi ya lalata maka yarinya don haka dole ya aureta, duk tsiya kar ka yarda ya qi amincewa, ko sadakane ba sai ka bashi ita ba idan ya amince, ai rufin asiri yafi komai, ko kuwa?”
“kuma fa kina da gaskiya haule, hakan kuwa za a yi”
“qwarai kuwa, gwara ka tashi tun cikin daren nan domin da zafi zafi akan daki qarfe”
Gurin da mairo take ya sake kallo yace
“tashi mu tafi munafuka, kin tsaya kina kukan munafurci bayan ki gama dawowa gantalalliya, matsiyaciya kawai”
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/17, 6:42 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*15*
Wani irin abu ne me ɗacin gaske ya taso ya tokare wa mairo qirji, numfashinta kuwa sai sassarfa yake yi cikin huhunta, hakan ya jawo ɗaukewar yawun bakinta, kasa tashi tayi kamar yadda mahaifinta ya umurceta, tozarcin da ake shirin aikata wa gareta ne ya fi komai ɗaga mata hankali, gaba ɗaya an birkita mata lissafin qwaqwalwa,
“zaki tashi ne ko kuwa kin raina mahaifin naki kamar yadda kika rainani, fitsararriya,? ni wallahi ba dan kar ace na yi cin fuska ba sai in ce da haihuwarki dai mairo gwara ɓarin cikinki domin ni ban ga amfanin haihuwar taki ba”
Haulece dai mai mummunan fata ta sake faɗin hakan ga mairo baiwar Allah, shiko ibrahim da yake son ya zauna lafiya da matarshi sai cewa yayi
“faɗi ki qara haule, wannan batu naki haka yake, ban ga amfanin da mairo ta min a duniyar nan ba ban da baqin ciki, ace wai wannan yarinyar yaushe aka haifeta amma ta san bin ɗakin maza, qalu innalillahi wa inna ilaihirraji’un”
Kukan qarya haule ta fashe da shi tana cewa
“ni takaicina Allah yasa babu ciki malam, to gwara cikin ma da irin wannan muguwar cuta mai karya garkuwar jiki, ba za ma a rasa cikin a jikin mairo ba domin alamomin da take nuna wa kwanan nan kenan, aikin kenan zubar da yawu da lasar qasa duk ina lura da ita, ayya mairo ayya mairo baki yi wa mahaifinki adalci ba”
Tana gama faɗin hakan ta sake gigicewa da kukan munafurci
Ai kuwa kamar wanda aka masa allurar doki ya ɗaga hanu ya gaure mairo da mari tare da haurinta cikin fushi yana cewa
“don uwarki zaki tashi mu tafi ko sai na kusan kasheki a nan gurin, mu je gurin ɗan iskan naki wallahi saidai ya san yadda zai yi da ke amma ba za a raini cikin shege a gidana ba”
Hausawa suka ce kuka samun dama dariya samun dama, neman hawaye mairo tayi ta rasa sai miqewa tayi ta fara gaba cikin zuciyarta kuwa ban da roqon mutuwa babu abin da take yi, so take kawai ta mutu a tunaninta ko za ta huta da quncin da take ciki, ta manta ko in ce bata san cewa manzon Allah s.a.w yace duk tsanani kar ɗayanku ya roqi mutuwa
Shi kuwa mahaifinta yana biye da ita sai haki yake yi irin dai na wanda yayi masifa a rashin sabo
Qofar gidan malam tanimu suka je suka tsaya, a daidai lokacin suna cikin ɗakin da aka sauki fawwaz suna ta hirarsu, hakan yasa tun a sallamar ibrahim na farko ladan ya ji amma sai da yayi ta kwaɗawa har sau uku
Hakan yasa ladan saurin fitowa yana sake amsawa domin a tunaninshi ba lafiyane saboda tun da suke da baban mairon bai taɓa jin muryarshi tayi sama irin haka ba, kwata kwata babu nutsuwa a muryar tasa
“lafiya ibrahim, me yake faruwa”?
A harzuqe yace
“ina baqon gidanka malam?, wallahi duk inda yake ya fito muyi wacce za mu yi da shi domin ba zai lalata min yarinya in zuba masa ido ba, azzalumi yana nan kaman mutumin kirki ashe baqin mugune, to ya zo idan ma da ciki ya san yadda zai yi da shi amma ba za a raini shege a gidana ba”
Tun da ya fara bala’in malam yake kallonsa, mamakine ya daskarar da shi, tambayar kansa ya fara yi anya kuwa yau ibrahim yana cikin hankalinsa, sai da ya ji ya dasa aya sannan ya numfasa yace
“ibrahim akan me kake magana ne?, ni ban fahimceka ba, wani irin magana ce wannan marar fasali”?
Janyo mairo yayi wacce take jingine jikin katanga a gefensa ya wurgata gaban malam yace
“gata nan mairo, baqon gurinka shi ya dinga yaudararta har ya lalata min ita, to wallahi tallahi ba zan yarda ba, ba zan taɓa amince wa ɗan gaba da fatiha a gidana ba”
“subhanallah, wani irin zancen banzane wannan ibrahim?, menene alaqar Abdullahi da mairo da har zaka zo min da zancen ya lalata maka yarinya?, ita maironce ta ce maka ya mata wani abin”?
“ko mairo ta faɗa ko kar ta faɗa malam duk abin da yake faruwa tsakaninsu ya dawo kunnena, ba fa zan yarda ba, na tabbata haule ba za ta mata qarya ba, toh ga maciji malam ai ba a maganar ja, idan bai lalatata ba ta ina shi kuma cikin da yake jikinta ya zo?, ko kuma tsabar ni kaɗai Allah yake so sai ya haɗa min ɗa da jika a tare, iyeeh?”
Cikin takaici ladan yace
“eh lallai ibrahim, ban taɓa sanin haukace ta kama ka ba sai yau, idan ba mahaukaci ba yaya za a yi mutumin da yake da kwana shida yau a garin nan ace yayi wa yarinya ciki har ya bayyana?, kai mahaukacin inane ibrahim, to na fahimci abin naka haukane da raini, to bari ka ji in faɗa maka ka tattara ‘yarka ka bar min qofar gida tun ban sa yara sun maka korar kare ba, ka je can da tsinanniyar matarka ku nemo wanda ya lalata maka yarinya, balle inshaa Allah saidai ta ga lalacewa akan ‘yarta ba dai mairo ba, mahaukacin banza mahaukacin wofi”
Abinka da halin lafiya dan bana ce na hauka ba, cikin masifa da qaiqayin gubar da haule ta saba banka masa yace
“ka dai nemi tsinanne can ba haule ba, yarinyace dai gata nan ku san inda zaku yi da ita wallahi tana tako min gida zan doketa da taɓarya, idan yaso ta shiga duniya wannan ba abin da ya shafeni bane, garin banza ai na farau-farau ɗin wofine”
“to kuwa saidai ka kasheta nima indai mairo jininka ce ba dai gidana ba, keh tashi min daga qofar gida ki bi ubanki”
Sai jin muryarshi kawai sukayi yana cewa
“malam kayi hakuri, na yarda da abin da yake tuhumata akai, ya faɗi yadda yake so a yi yanzu”
A kiɗime mairo ta taso daga tsugunen da take jin za a tabbatar mata da wani babban laifin da take guje masa, shi kanshi malam a ɗimauce yake kallon fawwaz irin kallon nan na ban gane ma hauka cikin hankali ba, murmushin takaici yayi yana mai jaddada abin da ya faɗa wa malam da kai tare da faɗin
“kar ka yi shakka malam, amsa laifi ga mai laifi shine kaɗai mafita”
“ka tabbata”?
Cewar malam yana nuna shi da yatsa, murmushin takaicin ya sake yi yace
“na tabbata”
Kuka ta fashe da shi wanda sautinshi kaɗai zai tabbatar da qunci da baqin cikin da me yinshi yake ciki sannan cikin kukan tace
“wallahi malam ni babu abin da ya haɗa ni da shi, ni bani da komai sharri ake min, ni ko hanuna bai taɓa riqewa ba walla….”
Sai kuma ta kasa qarasawa, abin da ya faru tsakaninsu da safe ta tuna ya hana ta cika rantsuwarta, shi kuma jin tayi shiru ta kasa qarasawarne ya bashi damar takowa kusa da ita ya tsaya ya qura mata idanu cikin hasken farin wata, kasancewar an ci sa’a yau sararin samaniyar ta washe babu hadiri sosai, da sauri ta sunkuyar da kanta tana cigaba da kukanta
“me ya hana ki qarasa rantsuwar?, ki qarasa mana, ummm”?
Jin tayi shiru yasa fawwaz kallon mahaifin mairo yace
“kayi hakuri, ka faɗi abin da kake so a yi yanzu”?
Tuno huɗubar haule yayi don haka da sauri yace
“matuqar zaman lafiya kake so toh dole ka aureta, hakan ne kaɗai zai sa in rufa maka asiri, amma idan ba haka ba gobe warhaka duk qauyen nan an ji abin da kayi wa mairo, ka je can Allah ya saka min zaluncin da ka yi min akan naka, za ka haifa kai ma”
“shikenan ka yanke mata sadaki, zan aureta amma………”
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/22, 4:03 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*16*
“ina so ka min wata alfarma”
Da sauri ya tareshi da cewa
“wacce alfarma?, ni babu wata alfarma da zan maka bayan wacce na maka”
Kallonsa kawai fawwaz yake yi ransa a ɓace, irin kallon nan ne na ba dan wani abu ba da na yi wani abu
Malam tanimu ne cikin fushi da tsananin haushin da yake ji na baban mairo yace
“Ibrahim ka saurareshi mana ka ji irin alfarmar da za ka masa, me yasa ka zama haka ne kai?, idan yace ba zai aureta ba kana da yadda za ka yi da shi ne?, ko ka kama shi ne lokacin da yake lalata maka yarinyar?, haba wannan wani irin shashancine?”
“toh ya faɗi alfarmarsa ina jinsa amma wallahi matukar alfalmar zai shafi auren ba zan yarda ba, ko ban kama shi ba ai Allah ya kama shi tunda da bakinsa ya amsa laifinsa”
Har malam ya buɗe baki zai cigaba da faɗa fawwaz yayi saurin katsewa da cewa
“alfarmar da nake nema ba za ta hana aurenmu da maryam ba, ina so ka ba ni dama in je in sanar da iyayena domin su samu daman halartar ɗaurin auren sannan ina so ka san cewa mijin dakake shirin aurar da ‘yarka gareshi ba kowa bane, ba shi da komai, bai ajiye ba kuma bai ba wa wani ajiya ba, ina so idan za ka yanke min sadakin ka rangwanta min domin in samu ikon biya”
“ahaff, ni wannan ai bata shafeni ba, ko a jikina, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa yakan doka, idan ɓeran masallacine kai tsabar babu ita ta sani, ba ta da miji sai kai, ni ko kyauta zan iya aurar maka da ita ba dan iyakan addini ba, ita ta jawo wa kanta, da ta riqe mutuncinta me za ta yi da aurenka haɗuwar tasha rabuwar bakin gate”
Murmushin takaici fawwaz yayi sannan ya kalli malam da yake bin baban mairo da kallon takaici yace
“malam ka karɓa min ranar auren da kuɗin sadakin ni kuma na yi alqawarin duk inda kuɗin yake zan nemosu mu zo tare da iyayena kafin ranar da za a ɗaura auren”
Tun malam bai ce komai ba Ibrahim yayi sauri cewa
“ai ba ɓata lokaci za a yi ba, iya qoqarin da zan maka shine sati ɗaya, sadaki kuwa ko nawane ka kawo domin ba zan ɓata baki gurin faɗin abin da ba za a samesshi ba”
Numfasawa ladan yayi yace
“toh ubangiji ya kyauta, ya kaimu nan da satin, sadakin ni zan biya da kaina zai je dai ya taho da iyayensa in Allah ya yarda”
Girgiza kai fawwaz yake yi amma bai ce komai ba
“toƴ da kyau, hakan ma ya fi tabbas”
Cewar baban mairo,
Ladan bai bi ta kan maganarsa ba ya mai da hankalinsa kan fawwaz yace
“mu shiga ciki Abdullahi ka kwanta ka huta dare yayi”
“zan shigo malam amma ina son yin magana da maryam kafin in shigo”
“toh ba laifi, a shigo lafiya”
Wucewa yayi cikin gidan ya barsu a tsaye a gurin har da baban mairo, shi ma baban mairon shigewarsa yayi gida yana ta masifa abun da ba halinsa ba, wayyo duniya ina za ki da mu😭
Kusan sama da minti goma suna tsaye a gurin ba tare da sun yi magana da junansu ba, ita mairo kanta a sunkuye yake zuciyarta na ta dukan miliyan miliyan, dukan ya mata yawa, ga tsoronshi da take ji ga kuma sharrin da aka mata, aka mata baqin fenti sannan kuma wai aure ake shirin mata a wulaqance a tozarce, ita kanta ba za ta iya qiyasce quncin da yake cikin ranta ba, kuka ne ya kufce mata ba tare da ya nemi izininta ba, ban da sautin kukan baka jin motsin komai sai haushin karnuka daga nesa
Shi dai fawwaz tun bayan tafiyar su malam ya ke kallon jikin wata bishiyar gwaiba da take saitin gurin da suke tsaye, wanda yake kallonsa zai gane wani irin yanayi da yake ciki maras daɗi a qwayar idanunsa, zuciyarsa kuwa ban da zafi babu abin da take masa, baqin cikin abin da ya faru yake ji, yana so ya taimaki yarinyar amma ba shi da niyyar aure kwata kwata, amma babu yadda ya iya da ransa auren mairo a gareshi shine kawai taimako mafi muhimmacin da zai ba ta a daidai wannan lokacin saboda gudun lalacewar rayuwarta.
Sautin kukanta ne ya addabi kunnuwanshi hakan yasa ya juyo gaba ɗaya ya fuskanceta, kusan minti uku yayi yana kallonta duk da yana da tabbas cewa yarinya ba ta bin maza kamar yadda aka ce balle maganar ciki amma sai yace
“ki faɗa min gaskiya, bana son qarya, me ya jawo waɗannan maganganun?, da gaske ne kina da ciki”?
Kamar abin tsoro haka take kallonsa, ta rasa me za ta ce
Cikin muryar tasa mai dagula lissafi yace
“kin ji abin da nace ko ba ki ji ba”?
Murya na rawa tace
“ni ban san komai akan wannan maganar ba”
“wa yace wa mahaifinki ina nemanki”?
Cikin muryar kuka tace
“ni fa wallahi ban san komai ba, baba haule ce ta faɗa masa, amma Allah ne shaidata bani da alaqa da wani cikin qauyen nan”
“har ɗan maigari”?
Ba ta san lokacin da ta watsa idanunta cikin nasa ba, abinka da rashin sabo, da sauri ta sunkuyar da kai ta cigaba da shessheqar kuka
“ban ce ki min kuka ba, tambayarki na yi har da ɗan maigari”?
Girgiza kai tayi ba tare da ta ce komai ba alamar eh amma ba ta bar shessheqan kukan ba
“toh menene na kuka idan har kin tabbatar da gaskiyar abin da kika faɗa?, ko kina kukan auran maqasqancin mutum irina ne wanda ba shi da komai?”
Nan ma da sauri ta girgiza kai domin ita ko wanda bai kaishi bane a ganinta gwara tayi auren da wannan uquba ta gidansu
“ban fahimci abin da kike nufi da girgiza kai ba,? ki buɗe baki ki min magana”
“ko da ka fi kowa talauci ba zan yi kuka saboda zan aureka ba”
“sabo da me?
Yayi saurin taran numfashinta
Shiru tayi sannan ta ɗago ta kalleshi tace
“saboda za ka kare min mutuncina kamar yadda kake yi a yanzu”
“Ba kya tunanin zaki sake shiga wani quncin saboda zaki auri miji me qaramin qarfi, kin ga ba lallai ki wadatu cikin gidan aurenki ba kamar yadda maiyuwuwa kike fata”
“um um, bani da sauran buri a rayuwata bayan samin aminci daga tsananin da nake ciki”
“aminci”?
Kai ta kaɗa masa tare da sake cewa
“um”
Duk maganganun nan da take yi muryarta a raunace take yi
Wani irin kallon ya mata da ya sanyata sunkuyar da kai
“kin tabbatar da abin da kika faɗa”?
Kaɗa kanta tayi ba tare da ta ce komai ba
Hannayensa ya rungume a qirjinsa yace
“maryam”
ɗago da kanta tayi a hankali ta kalleshi tace
“na’am”
“inshaa Allahu zan aureki nan da sati guda, na miki alqawari kuma za ki sameni kamar yadda kika yi tsammani, canji zai shigo rayuwarki da izinin Allah, ki je gida zan nemeki gobe inshaa Allah kafin in wuce”
“toh na gode, Allah ya tashe mu lafiya”
Ameen yace sannan ta juya zata tafi gida
“maryam”
Ya sake cewa, juyowa tayi tare da amsawa tana kallonshi ta sanya hannayenta tana share hawayen fuskarta,
“ki kula da kanki kiyi hakuri da duk abinda zaki ji kuma ki gani zai wuce nan gaba kaɗan kin ji”
Toh tace masa sannan ta juya ta cigaba da tafiya a ɗaɗɗaure
Sai da ya ga ta shige gida sannan ya juya shima ya shiga gida
*******
Dariyar mugunta suke ta qyalqyalawa ita da indo suna maimata abin da ya faru a daren jiya kasancewar baban mairon baya nan ya tafi lambu,
Mairo kuwa a lokacin take shirye shiryen fita da kokon haule, abin da suke ta faɗi a kanta duk da yana qona mata rai amma bata jinsa a ranta kamar kullum, yadda ta nuna ma tamkar ba da ita suke yi ba
“gaskiya baba haule duk da wannan mutumin talauci ta addabeshi amma fa ba laifi yana da kyau”
Cewar indo
“keh ina amfanin wannan kyau nashi, ai shi namiji kyanshi aljihunshi, idan ya kai ruwa kyau mummunane wallahi tunda bashi da qwadala, ni ai na fi kowa murnar auren nan duk da gaskiyar magana zan rasa ‘yar nemo kuɗi, saidai har na fara hango shegiyar yarinyar nan tana surfe da daka tana ciyar da qaton banza hanu duk kanta”
kwashewa suka yi da dariya don asara irin na uwar banza har da tafawa
“da sauqi ma baba ko ba komai zata dinga kallon fuskarshi tana jin daɗi saboda kyawunsa, ba za ta ga wahalar da zata sha ɗin ba”
“ke dai akwai qaramin qwaqwalwa Abula, har baba haule ta fiki ganewa”
“ni dai ba mai qaramin qwaqwalwa bace saidai indo mai baqin jini”
Cewar Abula cikin jin haushin abin da indo tace mata
“ke dan ubanki ni ce me baqin jinin”?
“ni dai ba ubana ba, na faɗa mai baqin jini, qarya aka miki? ko kare yana zuwa gurinki ne?, ba gwara mairo ba akanki”
Ai kuwa nan suka tashi kamar zakaru sai zagin juna suke yi suna tsine wa iyayensu, duk da haule tana ta musu magana amma babu wanda ya saurareta sai ma ɗaukan ita ce da indo tayi ta jefa wa Abula, ita ma Abular dutse ta ɗauka ta jefa wa indon, ai kuwa sai goshinta fas, take jini ya fara wanke mata goshi, ganin jininne yasa tayi kukan kura ta cafki Abula suka fara zuba kokawa, kafin haule ta taso cikin tsautsayi indo ta wawuri qafar Abula ta zuba ta kan robar koko, tuni koko ya watse amma duk da haka da yake abin ya samu masu ɗacin hali haka sukayi dama dama cikin kunun, hannu baba haule ta saka a ka ta kurma kururuwa
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/23, 6:51 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*17*
Kururuwa take yi iya qarfinta kamar taɓaɓɓiya tana faɗin
“wayyo ni haule na shiga uku, waɗannan wasu irin tsinannun ‘ya’yane, da kashe kanku kuka yi ya fiye min da wannan asara da kika ja min, me za ayi da haihuwarku, kai innanillahi wa anna alaihirraji’un”
Shashashar ko innalillahin ba ta iya faɗa ba sai tsabar jahilci da zalunci
Da taga dai surutun ba zai mata ba itace ta sura tayi kansu har da hawayenta kamar ta rasa miliyan ta rufesu da duka tana cewa
“wallahi dukkanku sai kun haɗa min kuɗina domin bazan yadda da asara ba, azzaluman yara, so kuke ku ga bayana iyeh”
Ai da gudu suka bar dambe suka wuce ɗaki suna haki, ita kuwa bata fasa ba ta bisu ɗakin da itacen, ganin haka suka dakata da zage-zagen da suke yi Abula tayi saurin rufo qofar ɗakin tana ihu dan tasan halin uwarsu sai ta shemar da su akan kuɗi
Tsayawa tayi a kofar tana dokawa sai zage-zage takeyi tamkar ba yaran cikinta ba, ta zagi uban ɗaya ta koma kan na ɗayar, ita dai mairo tunda ta ga abin da ya faru ta ja ta tsaya kallon ikon Allah domin har ta ɗauko gammo za ta zo ta ɗaura robar kunun a kanta hakan ta faru
A cikin ranta kuwa godiya take yi wa Allah da ya ɗauke mata qaddarar zubewar kokon a hanunta, a hakan ma tsoro duk ya rufeta domin gani take yi idan ta gama da su manyan qwari za a dawo kanta
Sallamar jamila qawarta ‘yar malam tanimuce ta katse mata tuntuntunin da take yi a cikin ranta, waigawa tayi tare da amsa sallamar bayan ta sake fuska kaɗan
Ita ma jamilar murmushi ta mata ta qaraso kusa da ita tana cewa
“wai ki zo in ji yaya Abdullahi, yana qofar gida yana jiranki”
Yanayin fuskarta ce ta canza zuwa damuwa cikin yanayin ta ɗan kallo gefen da haule take tsaye take sauraronsu domin ganin jamilah ta shigo gidan ta ɗan sarara da masifar da take yi
Kallonta ta mayar kan jamilah tare da yin kalar tausayi, fahimtar damuwarta yasa jamilah ɗan taɓe baki tare da jan guntun tsaki ta kalli girin da baba haule take babu yabo babu tonon silili tace
“ina kwana baba haule”?
Fuska a ɗaure tace
“fitsararriya sai yanzu kika ga daman gaisheni?, to idan ban kwana ba za ki gani?, eyeh?
Turo baki jamila tayi cikin tsiwa tace
“wai mairo ta je yayanmu yana kiranta”
“idan nace baza ta je ba fa, ko zaki iya janta”
Ai kuwa cikin ɗaurewar fuska haule tana rufe baki jamilah ta fisgo hanun mairo tana cewa
“dallah zo mu tafi, ta kashe ki idan kin dawo”
Qwace hanun mairo tayi tana girgiza wa jamilah kai yayin da haule ta fara cewa
“wallahi idan turoki aka yi ki min rashin kunya sai in naɗa miki duka, maras kunya tacacciya”
A zuciye jamilah tayi hanyar fita tana cewa
“ni dai ba mairo bace da zan tsaya ki dakeni ehee, ki hana ta zuwan mana kin san sauran ai, ga tacaccu nan kina fama da su har zaki kira wani tacacce”
Haka jamilah ta fita tana ta kalar nata rashin kunyar, toh shi haka al’amarin ubangiji yake, idan ka qi kimanta shi, ka qi masa biyayya toh ɗan cikinka ma sai ya rainaka, kukan kurciya dai jawabine, mai hankali ke ganewa
Idan rai na tafasa toh ran haule ya tafasa da maganganun da jamilah ta faɗa mata, inda take shiga ba nan take fita ba bakinta har yana kumfa, sai da ta gama tijarar sannan ta dawo kan mairo tace
“ke kuma munafuka me kike jira uwar kusasi, amaryar da babu kwarjini amaryar asara, ko so kike mahaukacin naki ya shigo min gida garjejen qato da shi, gardi ba sisi”
Yadda haule take maganar cikin zare ido da hargagine yasa mairo karkaɗa mata kai kamar akwalar keke tare da faɗin a a
“to ki wuce maza aje a fara darasin kwaɗina da tunanin me gobe zata ci, mai kuɗi ma yayi tsare tsare balle talaka liqis gayyar wagairahum gayya tsiya gayyar arna a idi”
Da sauri mairo ta wuce waje har tana tuntuɓe na tsoro
******
“maryam zan tafi amma zan dawo inshaa Allah, duk rintsi duk wuya ina so ki kula da kanki, kar ki bari wani baqin ciki ya sa ki manta da Allah domin shi ma zai manta dake, ki sani tsanani tare suke daf da sauki, babu wani abu a tsakaninsu, kiyi hakuri domin shine mabuɗin cin nasara, ki mai da lamarinki ga Allah inshaa zaki samu ubangijinki a inda kika zace shi”
Fawwaz ne ke faɗin haka wa mairo bayan fitowarta da kuma gaisuwar da ta wanzu a tsakaninsu
Jin yayi shirune yasa ta ɗago ta kalleshi sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta saboda idanunsa da ta gani a kan fuskarta, cikin jin kunya tace
“na gode, inshaa Allah zan kula”
Shirune ya ratsa na wani lokaci sannan ya sake cewa
“maryam”
Na’am tace tana mammatsa yatsun hanunta ba tare da ta ɗago ta kalleshi ba, wata iriyar kunyarsa take ji tana dabaibayeta
“ina jin qyamar tallen da kike yi na daren nan, duk tallen da kike yi kiyi da rana, na faɗa wa mahaifinki a masallaci shi da malam cewar na soke tallen dare, ta qirga ribar da take samu a daren na sati duk zan nemo kuɗin in biyata idan na dawo, ko wani abin nawa zan sayar in zo mata da ribarta kin ji, ko da wasa kar ki sake kula ɗan maigari, balle shima ina da tabbacin bazai kulaki ba”
Qwallace ta taru a idanunta na farinciki domin idan akwai abin da mairo ta fi tsana bai wuce wannan tsinannen tallen daren ba, ba ta qaunarshi domin a ganinta sam bai dace da macen qwarai ba, cikin sanyin murya tace
“Allah ya saka da alheri, na gode”
Hannunsa ya sanya a aljihu ya ciro wasu koɗaɗɗun ɗari ɗari guda uku, sai wata ɗari biyun da ta sha gam yace
“ga wannan kiyi hakuri da shi, ki sai muku ɗan abin buqata da idris kafin na dawo”
Girgiza kai tayi tace
“um um ka barshi kawai, mun gode”
Sunanta ya kira cikin muryarsa na tsaro yace
“ki karɓa nace bana son jayayya”
Kasancewar tasan halinsa sarai, ban da jiya zuwa yau da taji sassauci a muryarsa kullum ta ji muryarsa sai ta diririce yasa tayi saurin miqa hanu ta karɓa tana sake godiya, gida ya mata umurni ta shiga kafin ya juya shima ya samu shafi’u a gindin bishiyar durumin da suka saba zama suka wuce bakin hanya gurin taran mota, su shafi’u sai ladabi ake yi domin dai har lokacin bai san dalilin zuwan fawwaz qauyen ba, aurensa da mairo da ya ji gurin malam kuwa ba qaramin kaɗuwa yayi ba domin ko ‘yar aikin gee fawwaz mairo bata kai wannan matsayin ba, hakan ne ya sake toshe masa lissafinsa game da lamarin fawwaz
******
Kamar yadda suka saba zaune suke da jikartata suna ta hirarsu har da nanie ɗin amrat ɗin sai kwasar dariyar iyayi da manyencen da yarinyar take yi suke
Qarar da suka ji na shigowar motocin da suke shigowa gidan da fawwaz shi yasa amrat wani ihun murna da tsalle tana cewa “ga dady ga day”
Ita kanta hajiyar murnar dawowar gudan jinin nata take yi sai washe baki take itama tana cewa
“ga auta ga auta”
“kai hajiya, ke sai kullum kullum ki dinga ce wa dady na auta, ina ce yarane ake cewa auta”
Cewar amrat kenan
“toh ni babanki a gurina ai yarone amratu”
Ta buɗe baki zata yi magana kenan ta ji sallamar dadynta ai a miliyan ta ruga da gudu gurinsa shima cike da farinciki ya buɗe hannayensa ya ɗagata sama yana cewa
“oyoyo cwthrt, oyoyo my luvly amrat”
Ita ma sai cewa take yi
“oyoyo dady, oyoyo dady”
Rungumeta yayi a qirijinsa qamqam yana jin son yarinyar sosai na ratsashi sannan ya nemi guri ya zauna yana gaishe da hajiyarsa cikin girmamawa, ita ma haka take amsa masa cikin kulawa da nuna qauna tare da tambayarsa gurin aikin domin ita a tsammaninta tafiyar aiki yayi, kasancewar duk zakkarshi sai ya aikata yake sanar da ita
Sun daɗe suna hira sannan ya tashi ya wuce ɗakinsa da amrat tana ta zabga masa surutu kamar parrot
hmmm su amrat an ga dady
********
Hajiyace ta lura da tunanin da yake ta yi cikin hirar tasu, sama sama yake amsa wa hajiya na’eemat yarsa zantuttukan da take masa,
“lafiya kuwa fawwaz?, ko kana da wata matsalarce, me yake faruwa”?
Jijjiga qafarsa yayi tare da murmushi yace
“ba komai hajiya, me kika gani”?
“ni zaka tambaya me na gani fawwaz?, ni fa mahaifiyarkace, ka faɗa min damuwar da ta saka kake ta tunani tun ɗazu kawai”
“hajiya ban da abinki idan ya matsu zai faɗa mikine ba ma sai kin takura ba, ki yadda kawai yadda ya faɗa miki babun babƴne”
Cewar hajiya na’eemat kenan tana dariya
“ina kuwa zan yi shiru, na san halin fawwaz ai, ba ni na haifi kayana ba, akwai damuwa ni na sani, faɗa min kawai autan hajiya”
Murmushi yayi tare da shafa kai sannan ya cigaba da jijjiga qafarsa a hankali suko su hajiya sun baza na zomonsu gurin sauraronsa
kallon hajiya yayi cikin jin nauyi yace
“aure zan yi hajiya amma abun ya zo a qurarren lokaci ban san yaya za a yi ba”
Cikin farinciki hajiya tayi hamdala tace
“aure fawwaz?, yau da bakinka kake cewa za ka yi aure?, wannan shine ikon Allah wai na kwance ya faɗi, ai kuwa ko gobene inshaa Allahu kamar anyi auren nan an gama, ‘yar waye?, a ina take”?
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/26, 3:27 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*18*
“ai ni hajiya har na wangale baki ina sauraronsa, yau baban amrat ne da maganar aure”?
Hajiya na’eemat ce take faɗin haka ɗauke da mamaki a fuskarta
Binsu yayi da idanu sannan yayi murmushi yace
“hajiya taimako da tausayine zai sa ni yin wannan auren, yarinyar abar tausayice ba ta da tudun dafawa a rayuwarta, tana cikin tsananin da take buqatar taimakon gaggawa, ina tsoron kar rashin tallafi da gata ya sa rayuwarta ta lalace”
Jinjina kai hajiya tayi sannan tace
“wacece wannan yarinyar fawwaz?, a ina ka samota?”
Gyara zama yayi ya kwashe labarin mairo tas ya faɗa musu tare da ɗorawa da cewa
“hajiya kina ganin idan ban taimaketa ba Allah bazai tambayeni ba, a tunanina ubangijina yana son ya damqa min amanartane a hannuna shi yasa ya ɗaukeni daga nan zuwa qauyensu akan *zakkatah* ya nuna min irin halin da rayuwar yarinyar take ciki, ina tunanin Allah yana so ya min wata jarabawarce domin ya ga mai zan aikata, ni kaina ina jujjuya cewa aure ya zo min a lokacin da ban shirya ba, lallaine babu ran da ta san me zai faru da ita gobe”
Qarashe maganar yayi cikin wani irin yanayi da za a kirashi da rauni, wataqila hakan ya farune sakamakon fami da yayi wa cutar da ke ransa, amma ko ma dai menene nima kamar yadda hajiya tace haka nima zan ce, fawwaz kana nuna rashin jarumtarka sosai a gaban hajiyar taka
Tun kafin hajiya tace komai hajiya na’eemat ta fara cewa
“gaskiya ni dai baban amrat bana son wannan yarinyar, ka san so dayawa sharrin wanda ka taimakawa yafi na wanda baka taimaka masa ba, kar ka je ka ɗauko mana furen juji, yarinya ta zo ta samu guri ta tarwatsa mana farincikin gida, ko a addini fa cewa aka yi ka ji tsoron sharrin wanda ka kyautata masa, sai ka ja mutun inuwa shi kuma ya tunkuɗaka rana, ni a ganina ka mata wani taimakon dai amma ban da aure, gaskiya”
Girgiza kai yayi yana bin fuskarta da kallo, cikin muryar mamaki yace
“amma antyn raudat ban taɓa tunanin waɗannan maganganun za su fito daga bakinki ba, anya ke kike faɗin waɗannan maganganun?, na ɗauka ko ni nace bazan aureta ba ke mai qarfafa min gwiwace akan taimako, ki tuna wasiyyar mahaifinmu a ranar da zai bar duniya, idan kin manta bari in tuna miki, cewa yayi
“ina muku nasiha da irin nasihar annabi yakub ga ‘ya’yansa, ina muku nasiha da cewa ku zama masu bayarwa kar ku zama masu karɓa, ku taimaki wanda ya tambayeku da wanda bai tambayeku ba, kar kuyi taimako domin samun wani abu daga hanun kowa domin babu mai isar muku sai Allah, ka da kuyi tunanin cutuwar da za ta biyo bayan taimakonku ga kowa domin wasiyyar sheɗan ce, ku nemi tsari daga cutarwar ita ta fi muhimmanci sannan ina muku wasiyya da riqon wannan marainiyar da amana, musamman kai fawwaz ina so ka auri safiyya ka riqeta da amana, ka sani tausaya wa maraya koda da shafa kansa ne yana qara imani da tausayi, ina roqon Allah kar ya baku dukiya da rufin asirin da ba za ku rufa asirin wani da shi ba, ban yafe wa ɗayanku ba matuqar taimako yazo kan idanunsa bai taimaka ba, ina muku fatan alheri da zuriyarku, ina muku fatan alheri….”
Dukkansu babu wanda idanunsa baya kwaranyar hawaye lokacin da fawwaz ya zo nan a maganarsa, musamman hajiya hafsat domin a daidai gurin da ya tsaya ɗin a nan maganar mijinta ya tuqe, tun daga nan bai sake magana ba har ya bar duniya
Cikin shessheqar kuka hajiya na’eemat tace
“ka tuna min abin da na manta fawwaz, tabbas waɗannan sune kalmomin mahaifina na qarshe a rayuwarsa, amma ina so ka fahimci wani abu, kasancewar rayuwar yarinyar abar tausayice hakan ba yana nufin ta samu ingantacciyar tarbiya bane, kar ka aurota tarbiyar ‘ya’yanka ya lalace, har tallen dare fa kace tana yi”?
“ki bar wannan maganar antyn raudat, ko maryam ba ta da tarbiya ina da tabbacin idan ta shiga cikin zuri’arki tarbiyarta za ta inganta, to yaya kike gani idan gyaran tarbiyyarta ya dawo hanun hajiya, kina kokonto akan canza war ɗabi’unta?, to bari ki ji, na rantse da Allah tunda na je feli ban taɓa ganin wani abu da yayi kama da rashin tarbiya daga yarinyar ba, kullum mai kallonta zai dinga samun quncin zuciya saboda raunin da zaka dinga kallo kullum cikin qwayar idanunta”
Kaɗa kai tayi tana cewa
“haka ne toh amma…”
“ya isa haka ke kuma, haba don Allah, yaya qanin bayanki zai fiki fahimtar abin da ya dace, ki kwantar da hankalinki inshaa Allahu matar farinciki zai aure, kullum adduar da nake masa kenan, tarbiya da wasu maganganu duk na Allah ne shi zai ingantata fiye da yadda kike zato, fawwaz na maka umurni ba amincewa kaɗai ba, ka je ka auro yarinyar nan, Allah ya kaimu ranar da rai da lafiya”
Ameen suka amsa da shi sannan fawwaz ya kalli antyn raudat cikin zolaya yace
“ku fa matan ‘yan siyasa haka kuke, ba kwa son talaka ya raɓeku ko”?
Murmushi tayi tace
“kayya baban amrat kaidai a je sha’ani amma matar ɗan siyasa ai ba ita ce ‘yar siyasar ba, mu a suwa ma”?
dariya yayi sosai yace
“ku a matan komishinoni, ai ke ma komishinace”
“hmmm zancen kake so wai ance wa gauro yaya iyali”?
Hajiyace ta katse hirar da cewa
“saidai kuma nayi mantuwa fa”
Dawo da hankalinsu sukayi kanta suna sauraronta
“maganar da nace maka zakuyi da honourable”?
“eh” cewar fawwaz
“shi kanshi maganar da ya min wai yana son haɗa aurenka da ‘yar gurinsane zainab ko?, to amma ni na nuna masa amincewata matuqar kun yarda da junanku, toh shi dai yace min ba shi da matsala da yarinyarsa, toh nima kuwa ka ga ba zan nuna cewa ban isa da ɗan da na haifa ba ko kuwa?, ina ga abin da zai faru kayi hakuri ka haɗasu duka kawai wannan alfarmatace”
Mutuwar zaune fawwaz yayi yayin da hajiya na’eemat tace
“haba hajiya, ba dai yarinyar honourable abokin alhaji na aikin hajji ba”?
“ita fa, ita ɗin dai”
“amma gaskiya hajiya suyi hakuri kawai, ina waɗannan yaran suka ga tarbiya, yara suna yawo tsaraici a waje wai wayewa, babbar matsalar ma uwarsu, matar da aka ce sai yadda tayi da honourable, wacce tarbiyya kika ga za ta ba wa yaranta”?
“keh ki fita idona kin ji ko?, wai ke yau lafiyarki kuwa, kamar wacce bata san addini ba, ki zauna kina kama waiwai, toh Allah yasa matsafiyace uwarsu ba juya miji kaɗai ba sai ya aureta, haba don Allah, kina so mu saka qafar wando ɗaya da ke kenan”
“kiyi hakuri hajiya, ba za a sake ba”
Cewar hajiya na’eemat, amma duk wanda yake kallon fuskarta zai fahimci rashin jin daɗinta ga wannan hukunci na hajiya
Qarar wayar fawwaz ce ta kaɗa musu kunnuwa, jikinsa a mace ya ɗaga wayar, saidai wata zabura da yayi ya tsaya ba qaramin tsorata su hajiya tayi ba, murya sama yace
“what?, a wacce hanyar”?
Ko me aka ce masa a ɗayan ɓangaren oho sai cewa yayi
“lahaula wala quwwata illa billahil aliyul azim, yanzu ina sundayn, kun kaishi asibitine?
Saurarawa yayi sannan ya sake cewa
“ok ok, gani nan zuwa, ku kai sunday asibiti a bashi kulawa, kar a bar kowa ya ganshi sannan kar kuyi gangancin sanar da wata kafa ta yaɗa labarai balle wata hukuma, ni zan ji da komai, komai ya zama cikin sirri”
Sake saurarawa yayi sannan yace
“ok ok”
hankalinsa ya dawo da shi kan su hajiya da suka baza na zomo da na mujiyarsu suna sauraron shi
“matar sunday da jinjirinta aka yi kidnapping ɗinsu a hanyarsu ta komawa gida daga kasuwa, lallaine duk yadda akayi wannan abin akwai hanun alh. Bala da alh. Tukur, lallai kuwa idan hakan ya tabbata sai na nuna musu yadda zaki yake farautar sauran namu dawa, sai na gigita musu tunaninsu, sai na hana su tabbatar da mafarkinsu”
salati su hajiyar suka rafka tare da faɗin “toh me ya samu sundayn da za a kaishi asibiti”
“sumewa yayi bayan an kirashi an sanar masa da cewar ko ɗansa da matarsa ko miliyan hamsin, hmmm wannan yawan kuɗin shiyasa na tabbatar su alhji balane masu wannan aikin”
“toh wai ni waye alhaji balan nan ne,? me yasa nake yawan jin sunanshi a bakinka”??
Hajiyace ta faɗi hakan cike da tashin hankali
“zaki sanshi wata rana hajiya, a lokacin da kafafen yaɗa labaran qasar nan za su yi ta maimaita fuskarshi a kodayaushe a matsayinsa na azzalumi mai ha’intar qasa”
Kafin hajiya tace wani abu wayar tashi ta sake bazamo wani qaran
Cikin zafin nama ya ɗaga kiran tare da ɗora wayar a kunnensa
“hhhhh, ranka ya daɗe jarumi, yaya muka ji da abin da ya faru”?
“kai waye”?
Cewar fawwaz
“ba lallai ka san ko ni waye ba, jaje ne kawai, amma kafin nan ina so ka rage kafiya da taurin kai domin abokaine na hannun daman talauci a wani qaulin”
“haka ne amma ina so ka sani matsiyacin karene kawai baya marmarin sauraron busa irin ta farauta, tabbas wajen qoqarin a sanka sai a manta da kai, a wani qaulin”
“ummm to da kyau, amma ka sani kare fa da ya ga rawar kura cewa yayi da kyau, amma a wani qaulin”
“gurnanin zaki kawai yakan girgiza namun dawa kaf ya hana su samun kwanciyar hankali ba kura kawai ba, cikinsu kuwa har da maciji wanda ake wa kirari da ba ka ramin kanka wannan ma qauline”
“dama, damammaki, rana ranaku, lokaci da lokuta duk a lissafe suke kuma tafiya suke cikin tsarin gidaje, mafi haɗari daga cikin gidajen kuma shine gidan tara, wannan shine ake kira qarangiya kar ka sake ka rufta, wannan haka yake qauline”
“cikin jerin ranakun mako, rana ɗai ɗai ne tak basa taɓa maimaitawa, kamar haka ne a yau da gobe a kwana a tashi idan kere na yawo zabo na yawo sai anyi kiciɓus, ka sani rana ɗayace tak take zuwa kafin juma’a da sunan yau, ita kuwa tamkar maturice da take turo juma’ar har su gauraya, amma ita kuwa juma’a nasarace da take zuwa da kanta, toh tun a waccar ranar ake nemo nasarar, domin gano inda nasarar take kuwa sai an yarda da cewa ita juma’ar me kyau tun daga laraba ake ganeta, wannan ma qauline, tare da haka ina me farincikin sanar maka da cewa bani da lokacin ɓata lokacina, ka zaɓi abinda zaka baza, ido ko kunne amma dole sai ka riski ɗayan cikin abu biyu, you most!,”
Yana zuwa nan ya katse kiran tare da sake kallon hajiya da antyn raudat yace
“a kullum ina takaicin lalacewar qasata, yaushe za ta gyaru?, yaushe canji zai zo mana, kowa ya juya bayansa yana tafiya a kife, oh yah Allah”
Qarasa maganar yayi yana mai shafa kanshi
“imani da niyyar gyara ita ce manufa, irinku nigeria take nema ɗan uwa, ka sani shi marar jin magana sai an masa hukuncin jaki, domin kawo gyara cikin al’umma dole sai wasu sun sha duka, dole wasu sai sun jijjiga kafin wasu su raurawa, kayi amfani da damar da Allah ya baka ka kawo gyara gwargwadon iko domin guje wa shiga tarnaqi da tashin hankali a ranar kiyama”
Hannayensa ya rataye a qirjinsa ya zuba wa antyn raudat ido sannan yace
“wannan haka yake amma ki sani, domin sauqaqawa wasu dole sai an takura wa wasunsu, sai kuma an sadaukar da wani abin ake samun wani”?
“kamar yaya?”
“misali a ce kece na kama da laifi, domin kawo gyara fa dole sai kin fuskanci hukunci daidai da laifinki daga gurina, toh yanzu keh a gurinki mai za ki ɗau hakan”?
Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin
“adalci”
Murmushi yayi tare da jijjiga kai yace
“ummm, kin tabbata”?
“tabbas”
Hanunsa ya sa a aljihu yace
“ok, ok, hajiya ni zan wuce, antyn raudat sai mun yi waya”
fatan Allah ya tsare suka masa sannan ya juya ya fice yana murmushi, ni dai meroro nace kaidai ka sani 👌🏻
*************
Tsaye suke qam a gabanshi yana kwararo musu umurni cikin wannan yanayinsan na ba wasa, amintattun yaransa kenan bayan sunday
“kai mustapha ka tabbatar kayi yadda nace, domin waɗannan ba qananan shaiɗanu bane, kuskure kaɗan za ka yi su harbo jirginka, ka san wannan, kamar yadda suka umurta ga miliyan hamsin ɗin cif cif cikin wannan jakar, ka kai gurin da suka umurta ka ajiye, kada ka je a motarka sannan kar ka je a kan abun hawa sannan ka dawo a kai, ka nemi ‘yan mashin zai fi, sannan kada ka je da waya kuma kada ka sanya takalmi sau ciki, kada kuma ka je da wata shaida da za ta nuna cewa daga rundunarmu kake, ka bi komai cikin tsari, ajiyewa kawai za kayi ka juya, ka sani duk abin da za kayi tun daga fitarka daga nan zuwa can akan idona yake, ka kula”
Yes sir yace tare da wata iriyar sarawa irin ta jarumai, hankalinsa ya mayar kan ɗayan yace
“Garba kai kuma ka bi diddigin duka nambobin da suka yi ta kira da shi daga ranar da abin ya faru zuwa yau, a ina layukan suka fara aiki har zuwa yau ɗinnan, guri ɗaya suke ko kuma suna mabanbantan gurare, ni kuma zan kasance a nan domin karɓar saqo daga gurinka, duka ku biyun ina bibiyar aikin kowa tamkar muna tare, ku je ina muku fatan nasara”
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/28, 9:23 AM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*19*
Sara masa sukayi sannan suka fice ɗaya na bin bayan ɗaya cike da zummar cika umurni
“ka shigo yanzu”
Abin da fawwaz yace kenan bayan ya kara wayarsa a kunne, ok ya sake cewa sannan ya nemi guri ya zauna cikin shirin gudanar da aikin da yake gabanshi da zarar baqon nashi ya shigo
Da sallama ya shigo sannan ya mai da qofar ya rufe ya tako zuwa kusa da fawwaz ya nemi guri ya zauna akan kujerar da fawwaz ɗin yake ya miqa masa hanu yana murmushi sukayi musabiha
“Adams ina fatan ka qaraso lafiya”
“lafiya lau ɗan uwa, mutumiyarka tana gaisheka”
ɗan tsaki yayi tare da harararsa yace
“wannan shi ma yana daga cikin aikin da ka zo yi anan”?
Dariya yayi yace
“tuba nake qi gudu baban amrat, za mu iya fara wa”
Ba tare da ya sake cewa komai ba ya miqe tsaye, ganin haka shima adams ya miqe tsaye suka nufi gaban girkakkun na’urarorin da suke ɗakin, kayan aikine na musamman da fawwaz ya haɗa na mamaki cikin gurin waɗanda suke taimaka masa gurin gudanar da ayyukansa cikin sauqi
“zamu karɓi saqonni kan bin diddigin kira da ake yi a yanzu, maqala wannan a kunnenka, kai ɗaya za mu yi aikin da mai wannan aikin, aikinka kai kuma shine bincikar fuskoki da hotunan waɗanda suka yi amfani da layukan, ni kuma aikina shine bibiyar jakkata da ma ɗaukinta har zuwa gurin da jakkar za ta dire, ina fatan ka gane?”
Cike da tsokana adams ya sara masa yana cewa
“yes sir, amma na koka musu, da sun san abin da zai biyo baya da a gurin suka bar jakkar suka sako matar nan kyauta”
Nan ma bai kulashi ba ya fara gudanar da aikinsa, ganin haka yasa adams yin azama gurin cicciɓar nashi aikin
Abin al’ajabi ga baqon abun (wanda bai san irin aikin ba) shine cikin qanqanin lokaci fawwaz ya zuqo hoton maɗaukin jakkar tasa yana zaune bayan okada sai tsula gudu ake yi dashi, jijjiga kai yayi sannan ya sanya hanu ya tare haɓarsa tare da yin amfani da yatsarsa manuniya yana goga kan kuncinsa
A ɗaya ɓangaren kuma adams yana ta qoqarin fara aiki kan sakamakon da garba yake turo musu
Daidai gurin da aka masa umurni ya sauka ya biya mai mashin sannan ba tare da ya yi wani waige waige ba ya gangara cikin ɗan kwarin da yake bakin titin ya je daidai jikin wata qaramar bishiya mai duhuwa sosai saboda ganyenta da ya kwanto qasa gashi kore shar, jakkar ya ajiye sannan ya juya nan ma ba tare da ya sake kallon ko ina ba ya fice a gurin ya juya cikin gari, tafiyar minti goma sha biyar yayi a qafa kafin ya sake samun wani okadan ya ɗaukoshi ya yi cikin gari da shi
Kamar yadda aka ce mai son abinka ya fika dabara wannan haka yake, saidai fa wani mai abin ma a ankare yake, cikin duhuwar nan kusan gurare shida ne masu fakon wanda zai kawo kuɗin suke ɓoye domin gano da mai yazo, idan akwai ta ɓaci to su sanar da junansu ta hanyar haɗaka da suke da shi ta wayoyin sadarwarsu, tun farkon yankowarsa kwanar shi da mai mashin ɗin suke ankare da shi har zuwa ajiye jakkarsa da juyawarsa duk akan idanunsu
Na kwanar farkon ne ya fara cewa
“kai guys mu jirge kawai, ba wata matsala soloɓiyon har ya juya”
Na kusa da inda jakkar take ne yace
“ka tabbatar babu wani hadiri, karfa mu je jirgewa mu jiqe”
Kusan duk irin kalamansu kenan domin gudun ruftawa, na farkon ne ya sake cewa
“babu ko gajimare balle hadiri, mu zame kawai”
Na tsakiya ko ince na uku a jerinsu ne yace wa na kusa da bishiyar
“toh makaru dafe kawai mu kauce”
Dariyar mugunta yayi yace “aikinku na kyau maza, amma kafin nan bari in sanar wa cali”
Zaro wata wayarshi yayi ya kunnata, sai da ya jira ta gama kawowa sannan ya kira lambar da yake son kira ya fara cewa
“oga komai haske fa, mu ɗaga ne”?
Daga ɗayan ɓangaren aka ce
“idan ka tabbatar da abin da ka faɗa to ku ɗaga ku juyo”
Cikin rashin sani wanda aka ce ya fi dare duhu ya kashe wayar tare da yin umurni wa sauran su fito, jakar ya ɗauka yana fito, har da wani juyi na nishaɗi
tafiya suka yi sosai a gefen qwarin nan sannan suka riski gurin da suka ɓoye motarsu cikin ganyayyaki, yayeta suka yi sannan suka shiga ciki tare da rurrufo qofofin suna ta tiqar dariyar iskanci,
Shi kanshi fawwaz da yake kallon duk abin da suke yi ta hanyar jakkarshi murmushi yayi mai sauti tare da jijjiga kai, kusan aikin adams na tafiya daidaine da nashi domin hotunan da yake fitowa dasu ta hanyar bin diddigin kira suna daidaita da waɗanda suke cikin motar nan sai qalilan
Tafiyarsu sukayi ta tsulawa har suka shigo cikin gari, nan ma kurɗawa suka tayi suna shiga suna fita har suka wuce can gidan sauqan baqin ogan nasu, ba tare da ɓata lokaci ba aka buɗe musu suka shige kasancewarsu sanannu gurin mai gadi
Zubewa sukayi kan kujeru suna ta hayaniya irin na ‘yan iskan gari, kai kace sabbin kamun haukane, taimaka wa kansu suka yi ta hanyar samar wa kansu ɗan abin korawa a cikin gidan sannan suka kira ogannasu kowa na sanar masa da irin nasarar da suka samu cikin zaqewa tare da tabbatar masa da ga kuɗi nan a qasa, zuwanshi kawai suke jira
“ku tabbatar da cikar kuɗin, ni kuma yanzu kafin in qaraso zan yi umurni wa jagus ya yi umurni wa yaransa su kai matar nan daidai gurin da aka ɗaukota su ajiyeta
Kamar qyaftawar ido gwanayen abin suka qaddamar da komai, wannan karon makarune ya kira shi ya sanar masa da tabbacin cikar kuɗin
A can ɗayan ɓangaren ya kira jagus ya masa umurni da ya faɗa wa yaransa su kai matar gurin da suka ɗauko ta
“an zo gurin yanzu za a fara”
Cewar fawwaz sannan ya ɗaga waya ya kira
“ku zam cikin shiri, ku tabbatar kuna gurin da na muku umurni, kar kuyi abin da zai ɓata shirinmu, ina da tabbaci ba mutum ɗaya ke directing ɗinsu ba, kuyi harbi idan za su baku matsala amma duk runtsi mutun ɗaya ya tsira”
Ba tare da na ji me aka ce masa a ɗayan ɓangaren ba ya katse kiran ya sake kiran wata lamba yace
“get ready, bayan gidan gwamna, hannun hagu sannan ku riske kwana ta uku, ku shiga gurin ku ɗau doguwar hanyar nan, amma kafin isarku filin jirgi ku dakata a gurin, ban da jiniyar motoci, ku shiga gurin a qaramin gudu, zan sake sanar da ku mataki na gaba idan lokaci yayi”
Motoci biyune cike da zafafan sojoji, kai da kayi ido biyu da su kasan abun da zai kasance a gaba babu daɗi wai mahaukaci ya ci kashi
Gudun da sukeyi ma kawai zai tsinka wa mai kallonsu hanji, hancin bindigoginsu kuwa a sama
A sukwane suka iso anguwar wanda shigarsu cikinta ya sanyasu rage gudu, tafiya suke shuuuu, kasancewar gurine da babu ruwan wani da wani kowa na cikin gidansa yasa ba su ɗauki hankalin people a kansu ba, daidai gurin da aka umurcesu suka dakata suka kashe motocin suna jiran wani umurnin
Halinka da ɗan daba, hankali kwance suka faka motarsu sannan suka buɗe murfin motar suka mata umurni da ta fita
A tsorace take da su dan haka jiki na ɓari ta fito daga motar tana rungume da goyonta, tafiya ta fara yi sai taga taxi ta tsaya a gabanta, tana kallon na cikin taxi ɗin ta wangale baki, hana ta magana yayi tare da mata umurni da ta shiga su bar gurin, ai a miliyan ta shige ciki tana ta kiran jesus, sannan tace thank god
Hhhhhh, hmmmmm to ki kira wanda kika zaɓa mana kawai
ɗaga motarsu sukayi da zummar wucewa sai kawai suka ga mota ta tare musu gaba, gane abin da yake shirin faruwa ne yasa suka yi azamar juyawa, ai nan ma ba zato ba tsammani suka ji wata motar ta dakesu ta baya, a gigice suka rarumo bindigoginsu da nufin kai harbi, ruwan bindigogin da suka jine ya tsoratasu ya ɗimautasu, hakan yasa suka miqa wuya domin sun tabbatar da ba sa’a, duk da harbin tsoratarwa aka musu ba na kashewa ba, hhhhh mai kashewa shi ma baya son ya mutu, toh Allah ba kuyi kashi ko fitsari a wondo ba
Yana kan hanyarsa ta zuwa gidan sauqar baqin nasa yaji wayarsa tana qara
Kamar ba zai ɗaga ba saboda nishaɗin da yake ciki sai kuma yayi tsaki ya ɗaga yana qorafin wai baya son matsala sam
Ganin mai kiran ne yasa yayi saurin kara wa a kunnensa yana cewa
“hello soja birgiman hankaka yaya akayi”?
A ɗayan ɓangaren kuma abokin aikin fawwaz ne daga cikin jami’ansu yace
“kana ina ne”?
“ina kan hanyata ta zuwa gidan saukan baqina, wani abu ne?
“mummuna ma kuwa, kada ka kuskura ka qarasa gidan nan, tsab kana isa zaka faɗa haɗaɗɗiyar tarkon fawwaz, ka sanar da yaranku su bar gurin”
“what?, wannan wani irin shaiɗani ne wai”?
“tambayata za ka tsaya yi kenan?, kayi yadda nace idan ba haka ba kasan me?, daga ni har ku kashinmu ya bushe”
“toh toh toh”
Abin da yake cewa kenan yana gyaɗa kai, cikin sauri irin na tashin hankalin nan ya katse wayar, har wayar tana shirin faɗuwa ya tarota tare da fara qoqarin kiransu makaru, saidai bai samu nasara kiran ba kiran jagus ya shigo wayarsa, muryarsa na rawar tsoro ya ɗaga wayar yana cewa
“me..me…me ya faru jaguss?
“ta ɓaci muku oga, an kama yarana, ni kuma yanzu zan kama kaina domin ba zan iya ji da gee fawwaz ba, sai wani jiqon”
Hello hello yake ta cewa amma ina, ya riga da ya katse wayar
Ai a miliyan ya juya da motarsa baya sai da ya tabbatar ya saita hanya sannan ya kira nambarsu makaru, dukkansu babu wanda ya ɗaga kiran da aka masa cikinsu har ya gaji da kiran, kamar mahaukaci haka ya zama
Su kuwa a lokacin sunyi ɓarin ruwa wa cikinsu sai shirme sukeyi ga uban kiɗa da suka cika gidan da shi, babu wanda ya ji qarar wayar
Miqewa tsaye gee fawwaz yayi yana dariya abin da bai cika yi ba ganin irin haukan da mashayan sukeyi, wayarsa ya ɗaga ya kira mutanensa
“ku qarasa kwanar gaba, ku shiga ta dama, gida na qarshe mai baqin gate wanda daga shi sai bishiyoyi, kuna da damar harbi idan sun baku matsala”
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/29, 10:22 AM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*20*
Kamar yadda ya faɗa haka suka yi, ba su ɗauki lokaci ba sai gasu a qofar gate ɗin gidan, mai gadine ya leqo da kanshi domin ganin waɗansu motocine suka tsaya a qofar gidan, ai tsabar tsorata da yayi sai ga bitsari yana tsiyaya a jikin maigadi saboda hancin bindiga da aka saita masa akan goshinsa
Qafafuwansa ne suka kasa ɗaukansa ganin mazajen suna dirowa daga cikin motocinsu, tafiya yayi zai faɗi ɗaya daga cikinsu irin ‘yan zafin kai ɗin nan ya kai masa wani wawan naushi da yayi sanadiyar hantsilawarsa cikin gidan da baya, kuma da wannan dukan hanya ta wangale saboda qarfinta, wani irin bajewa yayi a qasa kamar shemamme sai harbawa qirjinsa yakeyi
Magana yake sonyi amma ya kasa sai motsa baki yake kamar tsohuwar tunkiya tana tuqa
Wanda nake tunanin babbansune ya basu umurni shiga cikin gida, aikuwa cikin qwarewa da sanin makamar aiki suka fara kakkasuwa cikin kowani lungu da saqo na gidan
Cikin qanqanin lokaci suka haɗo kansu kaf sai gasu amfito dasu suna ta tanɓele irin na ‘yan maye, abinka da soja kafi qarfin raini, nan aka zubesu a tsakar guri sai naushi da duka akeyi, yadda ake tattaka qafafuwarsu da buge gwiwowinsu da qasa bindiga kuwa ko ce musu akayi ku gudu saidai a kashesu amma ko motsawa baza su iya ba daga gurin
Mai gadi kuwa ganin irin casa da ake wa manyansa tuni ya sake gigicewa cikin ɗimuwa yace
“ni dai don Allah kar ku dake ni, ban san komai, bana so na mutu wallahi, ku tausaya min ina da iyali”
Tsawa wani bayerabe ya buga masa a cikin sojojin yace
“zaki si ubanki, baki so ki mutu ammon kina kase wani ko, se ki mutu walle yansu yansu”
Wage baki yayi cikin tsoro don ya fahimci abin da bayeraben yake faɗi yace
“wallahi ban san komai ba oga, ban kashe kowa ba, wayyo oga a taimakeni in je yi kashi, gudawa oga gudawa”
A zuciye ya buga masa gigitacciyar tsawa tare da saitashi da bindiga sai ga maigadi kwance a sume
Tattarasu sukayi suka watsa su a bayan mota suka bar gurin cikin gudun da aka san mutanen namu da su
👍👍👍, jinjina ga dukkan runduna ta sojin nigeria, kuna qoqari ubangijinku ya dafa muku, ya amintar da ku, ya baku tsaro, ni dai cikin ɗamara babu kamar soja, gaisheku mazajeeee👍🌸🌼
********
Ba qaramin sambaɗa fawwaz ya sa aka musu ba, gaba ɗayansu abune mai wuya a tambayesu sunayensu su amsa da gaggawa saboda tijarar da suka gani cil da cil wai ganin annabin tsohuwa
“wa ya turoku aikata wannan mummunan aikin?”
Tsawar da wani qaqqarfa daga cikin madakan ya buga musu kenan a ɗakin caskalewar
Shuru sukayi saboda mayuwacin abune daman su iya magana
Cike da wani irin zafi na fitina wani daga cikin madakan ya ɗauki qasar bindiga ya dinga doka muku a qafafuwansu, ni dai a ganina waɗannan nan ‘yan ta’adda sun kakkarye saboda gaba ɗayansu ba wanda yake zaune daidai cikinsu sai jini da yake fita ta hanci ta baki
Wani tsawa aka buga musu tare da faɗin
“kuna ɓata mana lokaci, idan baza su faɗa ba kawai mu aikasu gurin da sauran ‘yan uwansu suka tafi domin wannan shine sakamakon mai taurin kai”
Kasancewar tun zuwa da su da akayi aka gaurayasu da waɗanda aka kamasu da sauran ‘yan ta’addan da aka kama su a gurin da suka ajiye matar sunday, kowannensu tsoratar da shi ake yi da cewa an kashe ɗayan ɓangaren ko za su tsorata su furta abin da ake nema
Cikin gajiya da haki ɗaya yace
“ko za a kashee…..ni…bazan faɗi komai ba”
Duk abin da suke fawwaz yana zaune gaban na’urorinsa yana kallo, maqale da abu a kunnensa da yake sadar da shi ga madakan, jin maganar ɗan daban ne yasa shi fusata cikin maɗaukakiyar ƴmurya yace
“kill him”
Ai kuwa cikin cika umurni wani mai kama da basamude ya zuba masa ruwan alburusai a qirjinsa, take ya zube a gurin ko shurawa bai yi ba
Ganin haka yasa sauran firgita kamar ba sune suka gagara motsin arziqi ba, sai gasu har da tashi zaune daram hannayensu a kai
Hhhh mutuwa dole
Sauran ma haka ake ta fama da su, saidai babu wanda yayi wani mugun furuci a cikinsu, amma taurin kai suke nuna wa suma na mamaki, hakan yasan gee fawwaz ba da umurnin a musu azaba da ruwan sanyi da tiyagas
Wannan azaba kuwa ba qaramin gigitasu yayi ba, tsananin sanyin ruwan ma kawai saida ya sumar da ɗaya daga cikin kidnappers ɗin, gee fawwaz da ganshi ya tashi ya shiga ɗakin ya ba wa sumammen taimakon gaggawa, yana farfaɗowa yayi umurni da a cigaba da azabtar da shi sannan yayi fitowarshi daga gurin
Zamanshi kenan a kan kujera bayan komawarshi ɗakin da na’urorinsa suke ya ji kira ya shigo wayarsa, ba tare da ya duba wa ya kira ba ya ɗaga tare da ɗorawa a kunnensa
“general fawwazne, wake kira”?
Maganar da ya ji an fara masa ne ya gano mai maganar don haka sai ya qara nutsuwa sosai tare da janye abin da ya maqala a kunnensa
“ka rabu da yaran nan gee fawwaz, ina ga hakan shi zai fi maka alheri kai da iyalenka, amma idan…..”
Da qarfi yace
“amma tir da halinka, wai kai ministan tsarone ko ministan tsoro?, amma baka yi sa’ar zuwa duniya ba, ina mai tabbatar maka ni fawwaz ba ɗan asara bane, ɗan halak ne, na saudaukar da rayuwata gaba ɗaya wa qasatace, ba zan bar wani ɗan ta’adda ya shaqi numfashi da kyau ba matuqar na samu iko, don haka iyalina da duk wani abin da ya shafeni ba damuwarka bace”
Dariyar mugunta ya masa domin bilhaqqi maganganun fawwaz sun ɓata masa rai, cikin gadara yace
“toh sannu mai gaskiya, ni dai ina baka shawara kayi abin da ya dace da kai tun kafin a yi maka abin da ya dace”
Tsawa fawwaz yayi yace
“ba ni da lokacin ɓatawa akan surutun banza, ina sauraron abin da ya dace daga gurinku, sai an jima”
Har zai kashe wayar yaji yana cewa
“lallai ka manta da abin da ya sameka shekaru uku da suka wuce, saidai ka sani rashin dangi, uwa da ‘ya sun fi rasa mata ciwo, ummm”
Wata iriyar tsawa da fawwaz ya buga sai da ɗakin kaf ya ɗauka, hakan yasa daga ɗayan ɓangaren aka kashe kiran
cikin zafin nama ya fice cikin takunsa na zarra ya shiga ɗakin da ake bugun shegun, yana zuwa ba tare da yayi magana ba ya karɓi bindigar da take hanun ɗaya daga cikin madakan ya harbe mutum uku a cikinsu har lahira, har ya ɗaga bindigar zai ɗauke na huɗu mai qiran basamuden nan ya riqe bindigar yana kaɗa masa kai, wani kallo fawwaz ya masa, a miliyan ya sara masa tare da faɗin
“sir evidence, idan ka kashesu duka ina zaka samu, calm down plss”
Ba tare da yace komai ba ya sake bindigar ya fice daga ɗakin
*********
Kwance yake yayi shiru, nazari yake yi kan irin kafiya da taurin kan yaran, duk uqubar da suke sha amma babu wanda ko da wasa ya faɗi wani abu da zai iya riqewa a matsayin shaida wanda zai taimaka masa akan cafke waɗanda yake shirin cafkewa, wannan abu yana hana shi kyakkyawan bacci, gefe guda kuma sauran hotunan da sukayi amfani da layukan wayar da aka yi ta kiran sunday da suka rasa gano fuskokin
A zabure ya tashi ya je kan girkakkun na’urorin ya fara buɗe kan hotunan sannan ɗaya bayan ɗaya ya fara binciken da yake gani ta nan zai gano mamallakan hotunan
Karon farko ya zuqo wani hoto tare da canza masa zubi, gashin fuska da kai ya fara saisayewa a hankali, sai da ya rage daidai yadda yake so sannan ya fara qirqiran furfura wa fuskar, gashin baki ya koma ya qara wa fuskar, wata iriyar faɗuwar gaba ce ta riskeshi da bai taɓa ji ba, hankalinshi a tashe ya miqe tsaye yana nuna hoton da yatsa tare da faɗin
“what?”
Dadai nan wayarsa da yake amfani da ita gurin kiran family ta ɗau qara, tsabar kiɗima ma ya rasa gurin da ya ajiye wayar, can ya ganta kan kujerar da ya taso, nambar da ya ganice ya sa shi kallon agogo tare da faɗin ya salam sannan yayi gaggawar ɗaga wayar
“fawwaz wai mai ya samekane?, tun jiya nake saka ran ganinka a gida amma shiru babu kai babu labarinka balle wayarka”
“wayyo Allah na hajiya, wallahi wani aikine ya ɗauke min hankali”
“ba dai kana so kace min ka manta da marainiyar Allah a feli ba, ka duba a gogo da kyau ka gani yanzu qarfe sha ɗaya da minti arba’in fa”
“innalillahi wa inna ilaihirrajiun, na mance hajiya, kiyi hakuri gani nan zuwa”
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/30, 2:44 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*21*
Carko carko suke tsaye tsakar gidan yayin da haule take ta sheqa rashin mutuncinta, idan hankalin mairo yayi dubu a wannan lokacin to duk sun tashi, har wani irin jiri ne taji yake ɗebanta, haka mahaifinta shima a wannan lokacin yana cikin wani irin ruɗani ne da fargaban abin da yake shirin faruwa, musamman kalaman da haule take ta furtawa tun jiya akan lamarin
“yarinya dai anyi asarar haihuwa, daman nasan wannan matsiyacin ba dawowa zai yi ba tun da ya gama samun rabonsa, wa zai auri karuwar gida? ai sai dai mahaukaci da bai san inda kanshi yake ba, toh ga shi nan dai qarya ta qare, jiya ina cewa ya gudu ne kawai abinsa wannan tsohon najadun yace a jira yau, toh ga yau ɗin tayi ina yake?, yanzu gashi har ana kiran sallar azahar shiru, yanzu kuma wani qaryar zai mana?, kai ni fa bari ka ji malam, wallahi har yanzu ina kan bakata, dole ayi ɗaya cikin biyu, ko dai yarinyar nan ta bar gidan nan ko kuma ni in barshi domin ni bazan zauna da yarinyar da zata ɓata min tarbiyar yara ba, ka ji na faɗa maka”
“haba haule, don Allah kiyi hakuri, babu wanda ya isa ya min wannan cin kashin, tunda yace ɗan abokinsa ne dole ya nemo sa duk inda ya shiga, ba zan taɓa lamunta……”
Da gudu ta shigo tana haki kamar wacce zaki ya biyo ta, gaba ɗayansu suka firgice da shigowar na ta, hakan yayi matuqar tasiri gurin sanqame maganar da baban mairon yake yi, idanunsu duka suka zuba mata suna sauraron abin da za ta faɗi
Cikin haki tace
“ba…ba…haule!.. motocin sujojine da yawa suka shigo garin nan, kuma…kuma…kuma”
“ke dan ubanki ki yi mana magana mai kyau, duk kin firgita mu, kuma me?”
Tana qoqarin daidaita numfashinta tace
“tambaya suke yi wai ina ne gidan ladan”
Dafe qirji tayi tare da zaro ido tace
“la me?, wani ladan ɗin?”
Wani irin bugawa qirjin mairo yayi wanda ya janyo mata ɗaukewar netwrk, yawun bakinta ma qamewa taji yayi, haka kawai taji ta tsargi kanta da shigowar sojojin cikin qauyen, take ta fashe da kuka wanda sautinsa ya doki kunnen kowa a gurin
Jiyowa sukayi da hankalinsu kanta kowa da irin kallon da yake mata
“munafuka ko dai kin san wani abu akan zuwan nasu ne?, in ba haka ba daga cewa sojoji sun zo gidan ladan sai ki tasa mu a gaba ki fashe mana da kuka”
Indo cikin rashin mutuncin nata da ta saba tace
“yoh wa ya sani ko ɗan iskan nata ɗan fashine ko wani mai laifin ya ɓuya a nan jami’an tsaro suka samu labari suka biyoshi, ke kin manta ta’addancinshi”
Cikin yarda da maganarta haule tace
“zancenki dutse indo, tabbas wannan ɗan fashine ko dan saboda yadda yake nuna wa mutane dabanci, kin manta da bakinsa yace min shi ɗan iskan gari ne”?
“ina kuwa zan manta baba haule”
“caɓ lallai kuwa tsohon ɗan iska, wata qila ya ji labarin suna nemansa shine ya raina mana wayo ya gudu, lallai baban abula da ka zama sirikin ɗan fashi hhhhh”
Ta qarasa maganar da dariyar mugunta, ni ko nace ɗamsil basirati
Rasa bakin magana baban mairo yayi, sai zazzare ido yake yi, duk mai kallonsa sai ya tausaya masa don ba za ka gane haqiqanin halin da zuciyarshi take ciki ba sai ka kalli cikin qwayar idanunsa
“toh kai malam ka tsaya kana zare ido, ai zuwa za ka yi ka jiyo mana labari”
Nan ma haka ta sake tuntsirewa da dariyar mugunta har da tafa hanu
Haka kuwa zungwi zungwi ya yi hanyar fita daga gidan, sai dai tun bai qarasa ficewa ba haniyar mutane daga waje ya sashi qarasawa da gudu, firgicewa yayi sakamakon yawan sojojin da ya hango wasu cikin mota wasu da qafa suna qarasowa gidan malam, ita kanta haule da yaranta haniyar ne ya ɗauko hankalinsu zuwa waje ko lulluɓi babu, ita dai burinta idanunta su gane mata abin da yake faruwa
Shi ko malam da ya fito ganin sojojin bai saka shi firgicewa ba sai ma farinciki da godiyar Allah da yayi, take ya fara faɗin Allahu akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar sannan ya ɗora da cewa
“kowa yace yaya zanyi ya manta da Allah”
Buɗe qofar mota wani daga cikin sojojin yayi, sai ga wani hamshaqi daga cikin sojojin ya sako qafa domin ni a tunanina gee fawwaz ɗin ne zai fito sai kuma na ga banbancin fuska amma hatta khakheen jikinsa irin na fawwaz ne.
Rufa masa baya waɗansu cikin sojin sukayi yayin da yake takawa zuwa gurin malam, abinka da qauye har guri ya fara ɗinkewa da jama’a, wai don hausa people ma sun ce soja marmari daga nesa
Hhhh yoooh ko a birni ne ai sai an kalla balle irin mu da ba mu saba ba, hhh qauye daɗi
Da gudu yaran malam mazan suka ratso cikin mutane a firgice domin rahotonni ya riske kowanne akan sojoji sun zo tafiya da babansu, saidai fa kowannensu cin burki yayi domin ba halin tambaya wai tsohuwa ta shiga turakar ɗanta 😂
Shafi’u kuwa ya qaraso gurinne daidai lokacin da malam yake gaisawa da abokin general fawwaz, shidai daman ba a firgice ya zo ba domin ya san komai,
duk da bana jin me suke faɗa amma ganin yadda bakin malam yake washewa na san zancen yaji zuma
Su haule sai Allah2 ake yi aga an cacumi ladan an yi gaba da shi amma sai shiru take ji, shi kanshi baban mairon kansa ya kulle, ya rasa me yake shirin faruwa da maqwabcin nasa
Ana haka sai qarar jiniya ta sake doso qauyen, gaba ɗaya hankalin sojojin da ma sauran jama’ar gurin komawa gurin yayi, take sojojin suka qame cikin jeri tamkar daman can a jere suke, wasu daga cikinsu kuma sai kore jama’a sukeyi, cikin qanqanin lokaci suka samar da wadatacciyar hanya a tsakiya
Kamar yadda ya saba fita haka ne yau ma, motocin sojin ne guda biyu a gaba, sai motar da yake ciki da hajiya bilki da antyn raudat sai wata dattijuwa, yayin da wasu motocin biyu tam da sojojin suke bayansu, kai tsaye suka nufo qofar gidan ladan, sai da aka sake buɗa wa fa sannan motocin ayarin fawwaz suka samu gurin fakin
Ni kaina tun da aka buɗe qofar motar gaban qirjina yake dukan tara tara saboda kokawa baba haule kyakkyawan gamon da za ta yi a yanzu
Qafafuwansa ya fara fitarwa kafin ya sako kai gaba ɗaya, cikin takunsa na jarumta yake takawa har zuwa qofar gidan malam, kasancewarsa cikin uniform ya ɗauke masa wancan kamar tasa ta talauci musamman rashin fara’ar fuskarsa, wannan dalili yasa har lokacin da ya qarasa gaban malam babu wanda ya ganoshi cikin jama’ar qauyen
Antyn amrat da hajiya bilkin suma fitowa suka yi yayi da hajiya bilkin take riqe da hannun dattijuwar
Malam da kanshi ya musu jagora cikin gidan yana ta washe baki kamar gonar auduga
Karramawa ta musamman da tarɓa me kyau suka samu gurin malam, ji yake kamar ya haɗiye fawwaz, hajiya bilki da ta fara nuna qyanqyaminta wa qauyen ma saida ta sauko ta ɗan dara saboda barkwancin ladan da iyalansa
Wai fa don hauka har lokacin haule bata fahimci komai ba, saidai zuwa lokacin ta samu daman komawa cikin gida ita da zugarta sai zuba zance suke wai a ina ladan ya samu sojoji haka, wai meye alaqarsu da shi??, nan dai aka saki labarin mairo aka kama na ladan, saidai daga mairo har babanta babu wanda yace uffan, kowa da abin da ya dameshi, ita dai mairo a lokacin ta bar kuka amma jinta take yi a sanyaye kamar ba ta da lafiya kamar irin ana zuba mata qanqarar nan
Sallama akayi a qofar gidan, kasancewar ba a cikin nutsuwarsa yake ba hakan yasa yayi saurin amsawa tun daga cikin gidan tare da miqewa yayi waje
Har bakinsa na rawa yake gaishe da malam da wannan sojan mai irin kayan fawwaz, a mutunce suka amsa sannan suka fara gabatar da abin da ya kawosu ta bakin malam
Sumewane Allah bai ba wa baban mairo damar yi ba amma ya matuqar gigicewa da kalaman bakin malam, a tsorace yake kallon ladan yace
“malam idan dai na maka wani laifine toh don Allah kayi hakuri, na tuba ba zan sake ba, ka min rai, amma ta yaya wancan mutumin zai zama general fawwaz bayan shi sunanshi Abdullahi”?
“eh wannan ma abin da ya kamata ka jimanta ne amma kai kira yallaɓai ɗin ya zo don Allah”
maganar ya qarashe da yi wa abokin gee fawwaz umurni
Murmushi yayi ya ciro waya ya kira fawwaz a ranshi yana mamaki da al’ajabin abin, shi ko a mafarki bai taɓa tsammanin fawwaz zai nemi aure yanzu ba balle a qauye ma irin wannan
“muna jiranka”
Abinda yace kenan sannan ya jinkirta sai kuma ya sake cewa ok
Ayya fawwaz me masoya, cikin sauri ya fito daga gidan malam, ai kuwa sojoji suka qame, ba tare da ya sauraresu ba ya qarasa gurin da su malam suke ya musu sallama, tunda baban mairo ya ɗora idanunsa akan fawwaz ya kasa motsi kuma bai bar kallonsa ba
A ladabce fawwaz ya gaishe sa, muryar fawwaz ɗin ce ta dawo da shi daga doguwar sumar zaunen da yayi
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/1, 2:03 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*22*
_zan yi amfani da wannan damar wajen taya ‘yan uwana, yayyena, kuma qawaye ta wani fuskar murnar kammala littafansu, marubuciyar *taura biyu* mamue gee, ina roqon ubangiji ya amintar da rubutunki, ina alfahari da kaifin bakin alqalaminki, ubangiji ya dafa miki, sai kuma luvly aunty Ruky mom Abdjjll, kina rawa irin ta kallo da dubawa cikin rubutunki, ke tamkar haske kike a gareni mai kore duhu, ina alfahari da kasancewarki tare da ni, Allah ya qara zaqaqa alqalaminki ba dan ba shi da zaqi ba, ya kuma amintar da shi ki cigaba daga in da kika tsaya domin ke amintacciyace cikin writers, qamshi anty, ki ci gaba da qamshi ni kuma in cigaba da feshin turare ɗan indiya a gareki, love you guys jibgi jibgi💓_
Muryarsa na rawa ya amsa gaisuwar ya ɗaura da cewa
“yanzu bawan Allah daman kai general fawwaz ne? yaya akayi haka?, me ka….”
Kaɗa kai malam yayi tare da cewa
“a a Ibrahim, ba wannan maganar ya kamata muyi yanzu ba, maganar aure suka zo yi, ina ga abin da ya dace muyi yanzu shine muje muyi sallah idan aka idar sai a ɗaura auren kawai”
Cikin sanyi jiki ya fara girgiza kai yana hawaye
“malam bana tunanin auren nan zai yuwu, shi ɗin ba mijin mairo bane, akwai tazara mai girman gaske a tsakaninsu, ni dai ina mai bashi hakuri akan abin da ya faru, kuskurene, ya gafar…..”
Baqin cikin wannan maganar malam ya ji amma kafin yace wani abu fawwaz ya tare numfashin baban mairo cikin ɓoyayyen ɓacin rai da cewa
“ni nace zan auri mairo, babu abin da zai canza hakan sai ikon Allah, matsayina ba abune da zai shafi aurena ba, matsayina ba komai bane idan aka haɗa da na manzon Allah, toh shi ma ba matsayinsa ya duba ba cikin dukkan aurensa, don Allah ake aure ba don duniya ba, idan maryam ba ta san matsayina ba, ni na san da shi amma a hakan na amince da zan aureta”
Dafa shi abokinsa yayi domin ya dakatar da shi, yasan halin gee fawwaz sarai cikin ɓacin rai yake faɗin hakan, yana tsoron kar ya faɗi wata maganar da ba ta dace ba wa surukin nasa
“eh gaskiyarka gee, ina ga abin da za ayi baba ka kwantar da hankalinka, ka bamu aurenta, babu wanda ya fi wani matsayi a gurin Allah sai wanda ya fi tsoronsa, ayi hakuri dai a duba lamarin”
“toh shikenan, ni dai bani da wata matsala yanzu, amma ina so ku min uzuri in je in sanar wa babarta halin da ake ciki”
“babu inda zaka je Ibrahim, kai ne mahaifin mairo ba haule ba, da kai za mu yi magana, tun da ka amince shikenan hakan kawai ya wadatar da mu”
Yadda fawwaz yake ci ba dan baban mairo bane sai ya gigitashi da tsawa, domin shi a ganinsa son zuciyace kawai irin ta wasu mazan baban mairon yake nuna wa ba wai mallakeshi akayi ba, fuskar nan a tamke yace
“malam kaine waliyina, shi kuma waliyin ‘yarsa, ka bashi sadakin a ɗaura auren yanzu a nan kafin mu wuce masallacin, munir kai da ɗan malam kune shaidu”
Tsit wai ɗaukewar ruwa😂, haka baban mairo yayi domin qarara ya hango ɓacin rai fal a fuskar fawwaz, shi a tunaninsa zai iya sa yaransa su harbeshi
Sadakin da fawwaz ya bashi malam ya fito da shi yana murmushi yace
“ga sadakin mairo Ibrahim, kamar yadda yace ina ga hakan za a yi, ka san su masu ɗamara ba sa son dogon surutu irin haka, sai a tunzurasu, bari kawai a kira shafi’u a ɗaura auren”
malam ya ci nasara domin ya faɗi hakan ne saboda ya tsoratar da baban mairon, ban da toh toh haka za a yi babu abin da yake cewa,
🤣🤣🤣
Barikin ladi sunan wani gari a plateau
********
Cikin qanqanin lokaci aka ɗaura auren general fawwaz habeeb da maryam Ibrahim akan sadaki dubu ɗari cif cif
Take guri ya kaure da haniyar da ta fi ta farko, sojoji sai wasanni sukeyi a guri, hmmm wani rawan ya fi gaban takawa, masu sallah dai tuni suka wuce masallaci yayin da waɗancan suka cigaba da tsaron gurin
****
Ko ina cikin qauyen nan maganar auren mairo ake yi cikin al’ajabin mijin da ta aura, wasu suna mamakin zaman da yayi a qauyen ne a matsayinsa na talaka liqis marar qwandala, cikin zugan da ake yi gurin kallon general fawwaz sai ga maigari ya taho bankaɗai bankaɗai ya kawo gaisuwa gurin gee fawwaz bayan sun dawo gida daga masallaci, har qasa ya durqusa yana gaishe da fawwaz, yana wani irin washe baki da ya fi kama da na tsoro da firgici, musamman da ya ga fawwaz ɗin fuskarsa a ɗaure tam, gashi yana amsa masa gaisuwar ciki, hakan yasa maigari faɗin
“ayi hakuri dai ranka ya daɗe, Allah ya huci zuciy….”
“je ka, ya isa haka”
Cewar fawwaz yana mai wucewa gaba abinshi
****
Har yana tuntuɓe yake shiga gidan yana cewa
“haule haule haule, ina kike ne”?
Fitowa tayi daga bayan gida tare da ajiye butar ta rugo gurin baban mairo da gudu tana cewa
“baban Abula me nake ji ne wai?, yanzu matar shitu ta shigo min da wani zance, da har na qaryatata sai ga yara suna leqowa suna cewa mairo amaryar soja, wallahi ka ganni nan daga masai nake don gaba ɗaya ban san lokacin da gudawa ta taho min ba”
“gudawa kuma haule, me ya ɓata miki ciki”?
Tsabar jakanci babu kunya ba tsoron Allah tace
“auren mairo da aka ɗaura da soja, bani tabbaci in ji, ita da za a ɗaura aurenta da wancan matsiyacin yaya kuma za a ce an ɗaura auren da soja, sojan ma na ji an ce babba”
Sai da qirjinsa ya buga, wannan tijara ta haule yake gudu shiyasa ya tun farko yaso a barshi ya nemo izninta, zuciyarsa na cigaba da rawa yace
“shi dai wannan Abdullahi da ya zauna a gidan malam shi ne general fawwaz, kuma da shi aka ɗaura auren, ni kaina abin ya ban mamaki”
“general fa ka ce malam?, ta yaya wannan matsiyacin matashin zai zama general fawwaz, ka kuwa ji da kyau malam”
“wallahi haule shi ne, domin har gabana gani ga shi muka yi magana, yana ma sanyene da uniform a jikinsa, duk waɗannan sojojin da kika gani ‘yan rakiyarsa ne, yace ma yau zai wuce da matarsa, shi ba ya buqatar ayi wani biki”
Hannu haule ta ɗaura aka tace cikin muryar kuka
“wayyo Allah na ni haule na shiga uku, wacce irin masiface wannan?, wanne irin bala’ine wannan, wayyo Allah, waih waih waih Allahna na shiga uku ni haulatu”
Su kansu indo da Abula wannan labari ya daki zuciyarsu balle kuma haule, mairo kuwa bata san wani irin yanayi wannan labari ya haifar mata ba, zuciyarta kanta tana tsakanin gaskatawane da qaryatawa, ta yaya Abdullahi zai zama general?, ta yaya? wani abu ta tuna da sauri ta tashi tayi cikin ɗakinsu
Da mamaki yake binta da kallo sannan yace
“haule auren da kike son tayi ɗinne ya zama masifa da bala’i”?
Cike da masifa tace
“kai dalla ja can, sakarai kawai azzalumi macuci, da saninka aka haɗa munafurci zaka zo kana tambayata, don munfurci da qiyayya irin wacce malam yake min, arziqin yazo har gida maimakon a ba wa babba a gida sai a ba wa qarama, ba ga indo ba?, iyeh?, wayyo ni Allah haule na ga ta kaina, na mutu”
Haka ta qarashe maganar tana mai sulalewa a qasa tana burburwa a guri, tana zunduma ihu kamar wacce ta kuɓuto daga dawanau
Kai tsaye ta wuce gaban wata calender da ɗan haule me bin Abula ya taɓa zuwa da ita ya manna a ɗakin da koko, shi a burinsa wai soja yake so ya zama idan ya girma, kusan duk ɗakunan gidan har da na uwarsa irin hotunan da suke manne kenan har da waɗanda ba na qasar nan ba
Da iya ilimin da ta samu a primary ta fara bin hotunan general da muke da su
Bata yi nisa ba tayi kiciɓus da hotonsa cikin unifoam ɗinsu na sojoji yayi wani irin tsayuwa yanayin fuskarsa a sake amma ba murmushi yayi ba
Zuciyarta ce ta harba da qarfi, ba ta taɓa tunanin ko a mafarki wannan al’amari zai faru da ita ba, auren shahararre kuma fitaccen mutum, tana fatan canji da burin samunsa amma mijin da kullum take hararo wa kanta shine kamar Abdullahi, ba ta taɓa kawowa a ranta Abdullahi yana da alaqa da fawwaz ba balle kuma shi fawwaz ɗin da kansa
Kukane ya taho mata, a gurin ta sulale tayi qasa tana sharɓar kuka, idris da yake tsaye a bakin qofar yana kallonta qarasawa yayi gurinta da sauri yace
“yaya mairo me yasa kike kuka”?
Kasa magana tayi sai ta rungumoshi jikinta ta cigaba da kukanta
A tsakar gidan kuwa mai borice iskokin suke daɗa yawa a kanta sai faɗe faɗe take yi kamar ta zauce,
“wallahi yau ba zan yarda ba, dole sai an raba auren nan, ko kuma ni da kaina in raba auren, abune mai sauqin gaske ni a gurina, tsinannu azzalumai macuta masu qashin tsiya, ina mairon take ma, fito ki zo nan baqar azzaluma munafuka”
Shi dai baban mairo a tsayen ya buga tagumi saboda damuwa, yayin da mairo ta ture idris da yake kan cinyarta ta fito jikinta na ɓari
Cafkota tayi tare da dalleta da mari tana cewa
“dan ubanki tsinanniya ashe kin san yaron nan general ne kika munafurceni, toh yau sai na kashe ki da duka kin bi tsinanniyar uwarki can kushewa”
Abu dai kamar hauka haka ta fara dukan mairo, babanta na tsaye amma ko tari ya kasa yi sai sunkuyar da kai da yayi hankalinshi a tashe,
Dukanta takeyi tana cewa
“Allah ya tsine miki albarka mairo, yau sai na kashe ki mairo”
Ba tare da anji shigowarsu da sallamarsu ba sai ganinta sukayi a tsakaninsu hannu ta ɗaga cikin zafin rai ta ɗauke haule da gigitaccen mari tare da hankaɗeta, idanunta cike da qwanla ta fara nuna ta da yatsa tana cewa
“wallahi kin yi kaɗan kin kasa, idan a baya kin daketa saboda tana qarqashin ikonku yanzu baki isa ki sake ɗaga hannu ki daketa ba saboda a qarqashin ikon ɗan uwana take, azzaluma muguwa, macuciya, sai kin ga irin mummunan qarshen da za ki yi, idan kin isa ki ce fit ki gani, wallahi yanzu in saka a tattakaki kema a nan gurin”
Hhhhhhh, wuta dai,
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/2, 7:12 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*23*
*Zan yi amfani da wannan dama gurin miqa saqon ta’aziyyata ga ‘yar uwata a muslunci Safiyya Abdullahi huguma bisa jarabawar da Allah ya mata na rasuwar ‘yar da ta haifa, ina me baki hakuri safiyya, kamar yadda na sanki da mai da al’amarinki ga Allah toh yanzu ma ki jure duk da akwai ciwo amma ki mayar da al’amarinki gurin Allah, zai sake baki wacce ta fi wancen alheri, ubangiji yasa sanadiyyar tsirarki kenan a gurin Allah, Allah yasa ta zamo zakka wa zunubanki, kiyi hakuri friend amma haqiqanin gaskiya munyi rashi, amma fa sabrun jamil haka annabi ya’kub yace*
Hajiya bilki ce ta ruqota tana cewa
“na’eematu qyaleta don Allah, muyi abin da ya kawo mu, bai kamata mu tsaya muna ɓata lokacinmu kan mutumin da bai san ciwon kansa ba”
Ranta a ɓace tace
“haba hajiya, wani irin zaluncine ki kama yarinyar tayi ta duka fiye da dukan da ake wa dabba, wallahi da kin barni ma na kira yanzun nan aka naɗeta, baqar jahila kawai”
“ya isa nace ko, kar in sake jin bakinki”
Qwafa tayi ta wullah wa haule kallon na tsaneki sannan ta sunkuya ta ɗago mairo da ta kifa kanta akan gwiwarta tana rusa kuka
Ganin yadda aka kumbura mata fuska ne ga kuma gefen kumatunta da yake fitar da jini kaɗan kaɗan yasa hajiya na’eemat runtse ido, zuciyarta na wani irin suya, hankalinta idan yayi miliyan duk sun tashi
Buɗe idanun tayi ta saukesu akan mairo, ba tare da control ba ta ji hawaye na bin fuskarta, mai da hankalinta tayi kan baban mairon da yake tsaye a gefe kansa a sunkuye, alamomi sun nuna hawaye ne ke kwaranya daga idanunsa, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗauke kanta
Hannu ta saka cikin jakkarta ta ciro wani tattausan hanky zai zabga qamshi yake irin nasu na manya ta fara goge wa mairo hawaye sannan ta ɗora shi kan gurin da yake fitar da jinin
Ganin wasu hawayen suna qara zubowane yasa hajiya na’eemat cewa cikin sassanyar murya
“mairo”
Bata amsa ba sai sanya idanunta da tayi cikin nata, girgiza kai ta fara yi mata ta ɗora da faɗin
“ki bar kukan kin ji”
Kaɗa mata kai tayi alamar ta ji, sannan hajiya na’eemata ɗin ta kalli uwandi da ma’u tace
“baba uwandi muyi abinda ya kawomu, za mu wuce”
Uwandi da mutuwar jiki da kunya duk ya daskarar da su sai a lokacin ta samu ta numfasa tace
“toh hajiya”
Kallon gurin da baban mairon yake tayi tace
“baban mairo sun zo tafiya da amaryarsune”
Shi ma sai a lokacin ya motsa, ya sanya hanu yana share sauran qwallar idanunsa sannan yace
“toh baba uwandi bari a ba su gurin zama”
Da sauri yayi cikin ɗaki ya fito da tabirma babba da qarami ya shimfiɗa su Abula suna zaune ko a jikinsu balle su karɓa su shimfiɗa masa
Ita kuwa haule tana tsaye gefe tsuru tsuru tun da ta ɗebi mari tare da gargaɗin ‘yan uwan ‘yan gayu bata sake ko tari ba, ba qaramin tsorata tayi ba musamman da ta ji za a mata dukan ita ma, amma baqin cikin marin nan ta ji kamar ta rasu, a ranta ta sake ɗamarar tozarcin da za ta saka a yi wa yarinyar, domin ba za ta taɓa bari ta rayu cikin kwanciyar hankali ba
Nan dai suka tattauna gajeruwar zance a tsakaninsu sannan suka nemi a faɗi abubuwan da za su bayar a al’adan garin su ba da kuɗin komai, qirga musu komai uwandi da ma’u suka yi, take suka fito da kuɗin suka biya, saidai gurin maganar tafiyane aka samu targanɗa domim baban mairo bai gayyato kowa ba cikin danginsa da na mahaifiyar mairon, neman alfarma yake a ɗaga tafiyar da ita ko nan da kwana biyune ya je ya gayyato waɗanda za su kaita gidan mijinta, ba yadda bai yi ba antyn raudat ta fitittike tace qafarsu qafar amaryarsu, sai da hajiya bilki ta sa baki akan cewar nan da kwana biyun sun yi alqawarin za a zo a ɗaukosu su je ganin matsuguninta, akan wannan yarjejeniyar suka tsaya, ciro waya hajiya na’eemat tayi ta kira lambar fawwaz
“baban amrat mun gama komai, a shigo da kayan mu samu mu wuce”
Jinkirtawa tayi alamar tana sauraro sannan tace
“eh babu wata matsala inshaa Allah”
nan ma shirun tayi sannan ta sake cewa
“a a ka bari sai lokacin da za mu tafi”
Umhm tace bayan ta sake saurarawa sannan ta kashe wayar
Akwatuna aka shigo da su aka jerasu a gurin, abun har da na tura haushi ni dai a ganina domin ko ‘yar birni wata ba ta kai mairo samun akwatuna masu girgiza hankali ba, faɗa ɓata baki, hira qauyanci abin dai sai wanda ya gani, amma fa babune babu, ganin akwatunan ne ma ya taimaka yasa haule zaman ‘yan bori a qasa, babu wanda ya bi ta kanta balle yace ta zo ta kalli kaya, baban mairo kaɗai su uwandi suke nuna wa, shi kuwa ba qaramin girgizar zuciya kayan suka saka masa ba, ya dai yi shirune saboda zuciyarshi ta kasu kashi biyu, yana matuqar tunanin irin tijarar da haule za ta masa bayan tafiyarsu
“toh ana ta tuya fa an manta da albasa”
Cewar antyn raudat kenan tana murmushi, ma’u ma murmushin tayi tace
“me ya faru hajiya”
“amaryarmu, ba ku wanke mana ita ba, ko dai haka za mu tafi da ita”
Karɓe maganar uwandi tayi da cewa
“ai kuwa lallai an yi tuya an manta da albasa, bari na je gida na zo da ruwan zafi sai tayi wankan”
Tashi tayi ta fice yayin da hajiya bilki take cewa
“toh uwar baki sai ki zaɓo wa amaryar taku kayan da za ta saka”
Dariya tayi tace
“yanzu ma kuwa, har da soson wanka da sabulu da kayan qamshi”
ita ma hajiyar dariya tayi tare da girgiza kai
Haɗaɗɗiyar doguwar riga ta ciro mata da mayafi kalarsu ɗaya pink sai takalmi da jaka baqaqe, duk wani kayan ado da kwalya da za tayi amfani da shi a lokacin sai da ciro mata, uwandi tana dawowa ta haɗa mata ruwan wanka ta kai mata, soso da sabulun da antyn raudat ta ciro mata su aka bata aka mata umurnin yin wanka
Cikin qanqanin lokaci antyn raudat ta zage cikin gidan mutane ta sheqa wa amaryarsu kwalya sannan da taimakon ma’u suka shiryata cikin kayan, sai qamshi kawai take fitarwa kuma ba laifi sosai ta canza
Daga haule har yaranta sai rarraba ido kawai suke yi suna kallon ikon Allah wai na kwance ya faɗi
Gurin baban mairo aka kaita da yake zaune cikin ɗakin baba haule ya buga tagumi, duk abin duniyar sun masa zafi, uwandi ce tace masa an kawota ne ya mata nasiha ya kuma yafe mata, da farko shiru yayi kamar ba zai yi magana ba sannan daga baya yace a kaita gurin malam kawai ya mata nasihar sannan yace ya yafe mata duniya da lahira, sai kuma fatan alheri da na Allah ya kiyaye hanya ya mata tare da miqa mata sadakinta a hannunta, qin karɓa tayi saida uwandi tayi mata magana sannan ta sanya hannu ta karɓa tana shessheqar kuka da hawaye sannan suka tashi suka fito tsakar gidan
Kiran waya antyn raudat tayi aka zo aka fice da kayan sannan suka bar gidan ko kallon haule babu wanda yayi a cikinsu balle suce tayi wa mairo nasiha, toh me ma za ta ce readers???
Nasiha sosai malam ya mata wanda ya sanyata kuka sosai, ayoyi da hadisai duk ta shasu a gurin malam sannan ya mata adduoi da fatan alheri a zaman aurenta kafin ya sallamesu yana me musu fatan zuwa gida lafiya
uwandi ma da sauran matan gidan abokan zamanta nasihar dai suka mata tare da fatan zaman lafiya banda kuka da sharar hawaye babu abin da suke yi, har suka sa ‘yar dattijuwar hajiya matsar qwallah, yaran gidan malam ma kukan suke musamman jamila da salma, kuka suke yi sosai kasancewarsu qawayenta na kusa, malam kuma ya kafe yace sai dai jibin idan za a je su bi ayari kuma su dawo cikinta amma baza su bita yanzu ba
Har wajen mutan gidan suka biyota ɗuuu amma kasancewar gurin da tsaro ba su matsa kusa da motocin ba, saidai fatan alheri da kowa yake mata da bankwana da kalmomin yafiya daga nesa yayin da ita mairo qeyarta yayi nisa
Kai tsaye motar da za a tafi da ita a ciki uwandi ta je ta sakata bayan an buɗe musu murfin motar sannan ta matsa aka mayar aka rufe
Fawwaz da shafi’u da munir ne suka fito daga gidan baban mairo, gaisuwa suka je masa da godiya, har qofar gidan shima ya rakosu yana musu godiya
Gurin mala suka nufa suka masa sallama sannan suka qaraso gurin motocin
Motar da aka saka mairo a ciki aka buɗe ma fawwaz tare da sara masa ya shige ya zauna a gefenta sannan aka rufe masa motar yayin da abokinsa ya shige gidan gaba
Motocin ne suka tashi a jere sai baza jiniya sukeyi suka hau titi, wayyo Allah idris, wato wani irin kururuwa da birgiman da ya farayi a gurin dole ne ma ya saka mutane kuka, shafiu ne ya cicciɓeshi yayi cikin gida da shi yana ta harba qafafu
A hankali ya juyo da kansa yana kallonta, ita kuwa kanta na qasa sai shassheqan kuka takeyi
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/5, 12:28 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*24*
Tsawon lokaci ya ɗauka yana kallonta yana nazarin me ya kamata yayi a ransa domin dai har ga Allah shi ya tsani sauraron kuka, musamman kukan mace, macen ma mai rauni irin maryam
Murya qasa qasa yace
“maryam”
Ta ji shi amma bata ɗago ba kuma ba ta amsa ba, sai ma cigaba da tayi da shessheqar kukanta
Sautin muryarshi ya qara ya sake cewa
“maryam”
Yanayin kiran ne yasa ta ɗago kai da sauri ta kalleshi hawaye na cigaba da kwaranya a idanunta
Waro idanunsa yayi tare da ɗaga hanunshi da sauri ya tallaɓo haɓarta,
Kumburin fuskarta musamman gefen kumatunta da ya ɗau lafiyayyun maruka gurin haule da ciwon da ta ji mata su suka ɗau hankalinsa har ya tallaɓo haɓarta bai shirya ba
“maryam me ya sameki?, me ya ji miki ciwo, me ya kumbura miki fuska haka”??
Rufe idanunta tayi kirif tana cigaba da tsiyayar hawaye, baza ta iya cigaba da kallonsa ba saboda kallon cikin ido da yake mata, ga kuma tsoronsa da take ji, idan a baya ta haɗa idanu da shi a matsayinsa na Abdullahi yanzu ba za ta iya ba saboda rikiɗewar bazata da ya mata daga Abdullahi ɗan uwanta talaka zuwa general Fawwaz mai tarin dukiya da muqami cikin nigeria baki ɗaya
Muryarsa ta asalin mazan ya ɗauko yace
“keh ina miki magana kin yi shiru, me ya sameki nace?”
Nan ma dai shirun tayi bata buɗe idanun ba kuma bata ce komai ba
Qaramin tsaki yayi ya ciro wayarsa ya kira antyn raudat, wayar bata daɗe tana kaɗawa ba ta ɗaga
“me ya samu fuskar yarinyar nan”?
Abin da ya fara cewa kenan, sai da antyn raudat tayi jim alamar tana nazari kan abin da yake magana akai sannan tace
“oh mairo kake nufi”
“eh maryam dai antyn raudat”
Dariya maganar sunan ta bata amma sai ta murmusa kawai saboda abin da za ta faɗa ɗin bai dace da dariya ba sai tace
“hmm bari kawai general, Allah ne ma ya taqaita, da ba a san me zai faru ba”
Cikin zaquwa yace
“kamar yaya Allah ya taqaita?, ki min bayani”
Duk abin da suka je suka taras a gidan su mairon ta sanar masa sannan ta ɗaura da cewa
“wallahi kayi tunani sosai baban amrat, Allah ya tayaka riqo kawai”
Sake haɓar mairon yayi tare da faɗin
“what?, da aurena”
“wallahi, ni ma abin da ya fi ban haushi da takaici kenan”
Cikin ɓacin rai yace
“amma mai yasa tun muna can baki faɗa min ba”?
“toh idan na faɗa maka me za ka yi,? kar ka manta fa yanzu sun dawo surukanka, duk zafin ranka bai dace ko da yatsa ka nuna musu ba, ko ni da nayi iqirarin saka wa a naɗeta duk burgace, domin ita kanta yarinyar ba za ta so haka ba”
Rasa bakin magana yayi sai kawai yayi qwafa ya kashe wayar, ya jingina bayanshi jikin kujerar motar ya rufe idanu
A sace ta ɗago da kanta ta kalleshi, ganin idanunshi suna rufe hakan ya bata damar qare masa kallo cikin uniform, kyau taga ya mata sosai cikin kayan kamar ba shi ne ya zo musu qauyen a matsayin Abdullahi ba, komai na shi ya canza, ga wata zarra da izza da mai kallon fuskarsa zai hango a wannan lokacin, muryarsa ce kawai ba ta ɓace ba, domin ko a yanzu da ya mata magana yayi amfani da duka murya biyun da ya taɓa mata magana da su a lokacin da yake amsa Abdullah
Bata san me ya janyo ba, sai tsintar kanta tayi da jin mummunar faɗuwar gaba, da sauri ta janye idanunta daga kallonshi da take yi ta kifa kai tsakanin cinyoyinta tana istirja’i a hankali
Lokacin da suka iso gari fawwaz ya fara wartsakewa daga ɓacin ran da ya samu sakamakon abin da haule tayi wa mairo, wayarsa ya ɗaga ya kira nambar hajiya bilki
“Assalamu alaikum ɗan gidan hajiyarsa”
“wa alaikumussalam, hajiyan Arfat ku wuce gida ni zan wuce can gidan gona, yarinyar nan ba za ta so hayaniya ba saboda ba ta jin daɗi, zan kira likita ya dubata may be zuwa gobe zan kai ta can”
“yaya za a yi haka fawwaz, ka san ‘yan uwa suna ta zaman jiran tarɓar amaryarka sannan a ce kuma ba za ta je gidan ba”
“ki rabu da waɗannan hajiya, tunda keh da hajiyarku kun ganta ai shikenan, ga antyn raudat ma, su ma duk gulmarsu idan suka yi hakuri watarana sai sun gaji da ganinta”
Dariya hajiyar tayi ta ce
“kai fawwaz, wato ma gulmane ya kawosu ko?, hmmm me hali dai baya canzawa, toh ita yaya fa”?
Kawar da zancen yayi da cewa
“yawwa ki ce wa feenat ta shirya, zan turo a ɗaukota”
“na ji nace yaya fa, ita ma kana ganin ya dace ka wuce da ita ba tare da ka kawota ta ganta ba”??
“zan yi mata bayani”
Yana faɗin haka ya kashe kiran, abokinsa da yake zaune a gaban motar ya kira kasancewar basa ji tare da ganin juna saboda kariyar da ke tsakaninsu
“munir mu wuce gidan gona”
Shiru yayi kafin ya sake cewa
“eh can”
*****
Fakawa motar tayi cikin gidan gonar daidai qofar wani sheqaqqen gida, duk da kasancewarsa qarami amma dole ya ɗauke hankalin duk mai kallonsa, ba za a taɓa tsammanin gida irin haka cikin wannan danqareren duhun itatuwa da ganyayyaki ba
Sojan da ya ja motar da kanshi ya fito ya buɗe wa gee fawwaz murfin motar sannan ya ja da baya ya sara masa
Umurni ya bashi na kaucewa daga saitin qofar sannan ya juya ya ruqo hannun mairo tare da faɗin
“fito mu je”
A baya take binshi yana riqe da hannunta ya tunkari qofar shiga cikin gidan da aka buɗe kofarsa tun shigowarsu gidan gonar, kasancewar masu gadin gurin ma sojojin ne amma ba su da yawa, ba kamar gidansu fawwaz ɗin ba
Wani irin sassanya tsabtataccen qamshine ya doki hancinansu duka biyu, sakamakon gyara da gurin yake samu na musamman a kullum, sai ɗauke ido komai na cikin gidan yake yi saboda walwali,
Kan kujera ya zaunar da ita fuskar nan kamar hadari saboda tsaro sannan ya juya da sauri cikin tafiyarsa ta jarumta ya fice waje
“munir na gode sosai fa da ɗawainiyya, ka miqa min gaisuwata gurin madam”
Yana murmushi yace
“za ta ji, ai na san ma za ta kiraka ta yi tsokanar nata na fama”
“ai shukrah ba dama ce, shiya….”
Wayar munirce ta katsesu, kallon screen ɗin yayi sannan ya qyalqyale da dariya yace
” ‘yar halak, ga ta nan ta kira”
“subhanallahi, don Allah ka ce bama tare, ni ba zan iya da surutun shukrah ba”
Katse kiran yayi yana dariya ya kira wayar yana cewa
“toh ba ka nemi sulhu ba tunda kake kiran matata surutacciya a gabana”
Tsaki yayi tare da faɗin
“dallah malam kauce, kai ma ai surutaccen ne idan ka samu guri”
Ba tare da ya bashi amsa ba ya ji ya fara magana a waya
“Allah ya taimaki hajjaju kina lafiya”
Can ɓangaren shukrah tace
“ameen sojana, lafiyata qlau ya hanya”?
“hanya alhamdulillahi tayi kyau, yanzu haka mutumin naki igiyoyi uku rus ne akansa, har ma mun dawo”
Dariyar shaqiyanci ta yi cike da son yin tsokana tace
“don Allah sojana ba shi wayar”
“kash ai kin makara, yanzu muka saukeshi, nima ina kan hanyata ta zuwa gidan”
“wayyo amma ban ji daɗi ba, da ya ji martanin maganganunsa yau”
Dariya ya qyalqyale da shi yace
“toh ta Allah ba taki ba, ya riga da ya sauka sai ki riqe martaninki”
“zai zo ne ai ya sameni”
“toh shikenan sai na qaraso kawai”
“Allah ya kawoka lafiya”
Ameen yace ya kashe wayar yana murmushi sannan ya kalli gee fawwaz
“toh ni zan wuce ango, a sha angwanci lafiya”
ba sar da maganar yayi da cewa
“ka tura a ɗauko min dr. Ngozi zan kira ta a waya in mata bayani”
“ok toh sai wani jiqon”
wai kare ya zubar da tsamiyar kura
“yawwa sai mun yi waya”
Cewar fawwaz sannan suka yi musabiha ya juya ya shige motar suka ja suka fice daga gidan
Sai da ya ga ficewarsu sannan ya juya ya shige cikin gidan
A takure ya sameta ta qudundune jikinta da gyalen da aka yafa mata
Tsayawa yayi yana kallonta yana nazarin yanayinta, kallonsa ya mayar kan na’urar sanyaya ɗaki ya taka zuwa gurin da yake ya kashe tare da rage gudun fankokin da suke sama suke ɗauke hankalin mai kallonsu
Hajiyarsa ya kira bayan ya zauna a kujerar da ke nesa da ita
“Assalamu alaikum”
“wa alaikassalam fawwaz kun dawo lafiya”?
“lafiya lau hajiya, na ce kar ki ga ba mu zo da ita gidan ba ba ta da lafiyane, sai ki ga haniyar ya takurata, idan likita ta dubata ko zuwa gobe zamu zo gidan”
“ba damuwa, Allah ya kyauta, ai hajiya bilki tayi min bayani”
“yawwa hajiyata, ki ce wa feenat ta shirya yanzun nan za a zo ɗaukanta, duk kayan da yarinyar zata buqata don Allah antyn raudat ta bata ta taho da su”
“toh shikenan har da abinci ma zata zo muku da shi, Allah ya tsare”
“ameen hajiyata, ina qawalliyarkice ‘yar rigima”
” ‘yar rigima fa, ai ni kun tafi feli kun barni da rigima, wai sai ta biki, da qyar raudat ta lallaɓata tayi barci, yanzu dai ga ta nan ta tashi fuskar nan a haɗe”
Yanayin fuskarsa ne ya canza yace
“hajiya to ko a shiryata kawai su zo da feenat goben sai mu zo tare”
“rabani da shirme ka ji, da yau da gobe duk ɗayane”
“toh hajiya a shafa min kanta, sai goben”
Yawwa tace tare da katse wayar, nan dai ta sanar da antyn raudat da feenat abin da za suyi suka tashi kowa ya fara qoqarin cika umurni
Hajiya bilki da kanta ta haɗa musu abin da za su ci, yayin da feenat take ta tsula kwalyar zuwan kallon amarya, tsabtar feenat da gayunta yana daga cikin abin da ya sa fawwaz yake ji da ita, ga kuma iya magana, ita ma wani abin idan tayi tana masa ɗibin safiyyarsa
“don Allah mu je tare feenat”
cewar kubrah ‘yar kawunsu fawwaz
“toh shirya mu tafi”
“babu in da za ki kubrah, ki yi zamanki kawai feenat ɗin ta dawo ta sameki”
“ni ma dai haka na gani anty, kin san halin fawwaz tunda bai nemeki ba sai ya koroki”
Cewar raudat
Ayi hakuri da wannan, yau muna da walimar saukar kur’ani da ɗan antyna yayi AUWAL HUDU, ku saka masa albarka, sai mun sake jonewa
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/7, 6:18 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*25*
“don Allah antyn raudat ki barta mu tafi tare, yah fawwaz ba zai ce komai ba plss”
Cewar feenat tana marairaicewa
“ita ta sani idan ya korota babu ruwana, kun san halinshi ai, kar in ji kun zo kuna qorafi”
Cike da murna feenat tace
“eh antyn raudat mun yarda, ba zai korota ba ma inshaa Allah”
“um um feenat, gaskiya na fasa zuwa, kin manta yah fawwaz lokacin marigayiya safiyya da muka shigar musu falo ba tare da neman izini ba..”
Tuno horon da ya musu ne yasa tun kubrah bata qarasa ba feenat ta kwashe da dariya tace
“ki bari kawai kubrah har kin tuna min, soja ba daɗi kin ji, mun ci wuya”
Raudat ma dariyar tayi tace
“har kema feenat ‘yar gaban goshi kin shaida”?
“hmmm mom akram ki bari kawai, gaskiyar hausawa da suke cewa soja marmari daga nesa”
“toh da ke ya aura kuma yaya za kiyi”?
Ita kanta bata san me ya qwarar da ita ba sai ji tayi kawai tana zabga tari
Sannu sannu sukayi ta mata suna haɗa wa da dariya don sun san qwarewar yana da alaqa tambayar da raudat ta mata
Ba ta bari ta kammala tarin ba ta fara magana tana mai da numfashi idanunta qulu qulu
“har kin sa zan mutu lokacina bai yi ba mom akram, wallahi kin ɗau alhakina”
Dariyar mugunta suka sake fashewa da shi su kubrah har da kwanciya a qasa ganin yadda feenat ta birkice lokaci guda
Antyn raudat ce ta ce
“kun ga ku rabu min da ‘yar uwa, haba kun saka min ita a gaba, waye kuma fawwaz da har kuke tsoratata da aurenshi, sai me idan ta aureshin?, ka ji min yara fa”
Wayarta ce ta ɗau sauti da sauri ta ɗaga tana cewa
“kace me?, ina jinka”
“ta shirya”?
“owoo feenat?, ta shirya tuntuni”
“toh ta fito su taho, ki ce mata saura ta min gayya sai ta koma akan qafarta”
“toh za ta ji”
Ta faɗa tana dariya, sannan ta ajiye wayar ta juyo ta kalli feenat tace
“a faɗi mutum a sameshi haka sai baban amrat, yace ki fita ku tafi, kuma idan kika masa gayya ko numfashi baza ki ja a gidan ba za ki dawo”
Haɗa ido sukayi da kubrah suna murmushi kubrah tace
“toh nafasati ni kam daman, Allah ya tsare sisi, ki ɗauko mana hoton amarya”
“ameen ‘yar uwa, sai kin ji ni, toh tashi ki rakani wajen mana”
Tashi tayi suka ɗebi kayan sukayi gaba raudat tana biye da su da basket ɗin abinci wanda aka zuba tsala tsalan warmers, ko warmers ɗin kawai sun isa qosar da mai qaramin yunwa, amma a wani qaulin🤣🤣😂
***********
Zaman shiru sukeyi babu me magana cikinsu ko qwaqqwaran motsi, tsawon lokacin nan suna cikin wannan yanayin, saidai gee fawwaz ya ɗan kishingiɗa kaɗan a kujerar da yake, sabar mulki qafarsa ɗaya tana kan taya sai girgizawa yake yi ga dukkan alamu yayi matuqar nisa gurin tunani, yayin da ita kuma mairo take duqunqune kan kujerar da ya ajiyeta
Qarar doorbell ne ya ankarar da fawwaz akwai wani a bakin qofar amma ko motsi bai yi ba balle ya tashi ya je ya buɗe qofar
Wayarsa ya ɗaga bayan ya daina jin qarar doorbell ɗin domin yin kira da ita, missed call ya gani da yawa, musamman na Dr. Ngozi da munir sai kuma shukrah da ta masa 2missed call
Mamakine ya kamashi na yadda akayi bai ji kiran ba ko sau ɗaya, da sauri ya kira Dr. Ngozi yana me wani irin tashi daga kujerar mai ɗaukar hankali
“Dr kin qarasone”
Daga can Dr. Ta fara cewa
“wani irin barcine wannan? kiran waya yayi ɗari amma ba ka ɗauki ko ɗaya ba”
Jin muryarta da ɓacin rai yasa shi murmusawa da sigar lallashi da kuma tsokana yace
“ayi hakuri likita, kin san amarya ba wasa ba, bana jin kiran kwata kwata”
Da mamaki a muryarta tace
“wuh general?, toh in koma ko?
Tafiya yayi da sauri ya buɗe qofar yana cewa
“zaki kwaɓani kenan Dr, kar ayi haka gani”
Har gurin motar ya tako ya buɗe mata qofa yana murmushi sosai irin na tsokana again
Fitowa tayi ta tsaya tana fuskantarshi ta ce tana murmushi
“wai ango na gaske ko na wasan yaran geee”?
“na gaske mana Dr., mu je ciki amaryar ma zaki duba min, ki caje min ita da kyau, duk abin da yake akwai sai mu san matakin ɗauka Dr.”
Cike da mamaki Dr. Tace “mu je”
Gaba yayi ta fara binsa a baya har cikin falon
Mamakine ya kusan kashe Dr. Ganin mairo da tayi a matsayin amaryar gee fawwaz, ba ta taɓa tunanin ko a matsayin ‘yar aikin gida gee zai so wannan abar ba, sai gashi ta ga abin da ya fi wannan wai aure
Danne maganganun da suke ta kai kawo cikin zuciyarta tayi ta fara duba mairo,
Karon farko da ta tambayi kumburi da ciwon fuskarta yace ta zame ne a toilet, a ran Dr. Kuwa cewa tayi “kin yi qoqari da baki karye ba”
A fili kuma murmushi tayi tace
“gee kana son qananan mata, duka matanka under 18 ne”
Hmmm kawai yace yayi shiru ya tamke fuska kamar ba shi yake murmushi yanzu ba domin ya fahimci matar tana so ta damu tunaninshi
Ita ma ganin haka yasa ta ja bakinta ta tsuke domin ta san halin gee sarai, idan ba ta iya da bakinta ba akwai matsala
Aikinta kawai take yi tana jinjina kai tare da ɗan tambayoyi wa maryam, abubuwa da dama sun kulle mata kai daga yarinyar amma ta san ba fuskar bin diddigi
ɗago da kanta tayi tana mai kallon fawwaz tace
“general akwai matsaloli fa”
Kallon mairon yayi sannan ya dawo da kallonsa kan Dr. tare da zuba hannunsa cikin aljihun wandon unifoam ɗinsa yace
“um hm, ina jinki”?
Gyara tsayuwarta tayi tace
“da farko dai tana fama da zazzaɓi a jikinta har da ma ciwon kai, akwai qarancin jini da ruwa a jikin yarinyar, me yuwuwa zazzaɓin ya daɗe sosai a jikinta hakan ya kawo qonewar jini da ruwa a jikinta, don sun yi baya gaskiya, ga bayanan da ta min da nazarina zai zama akwai typoid da maleria amma ba tabbas zan dai tafi da jininta domin gwaji saboda a tabbatar, ammm…. sannan a qarshe sorry to say yarinyar tana fama da rashin hutu da ishasshen barci and……”
Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa
“ya isa haka Dr., na ji, duk abin da bincikenki ya nuna miki ki ɗora aikinki a kai, baki da matsala da ni, ni dai fatana yau ki fara ba ta kulawa don Allah Dr.”
Agogon hanunta ta duba sanan ta ɗago ta kalleshi tace
“lokaci be qure ba general”?
“a a Dr., da sauran lokaci, har za ki je lab ki dawo ki mata komai “
“kai ma fa Dr ne, mu je tare ka karɓo result ɗin daga nan kai ka san me ya dace da iyalinka”
“kin taɓa ganin angon da yake barin amaryarshi?, yau a kawo min amaryar in je wani wajen in barta”?
Kamar ba shi yayi maganar ba still fuskarshi da tsaro,
Kallonshi tayi sannan ta kalli mairo tace
“idan hidimar amaryar za ka yi kuma fa”?
“No Dr., ki je ki dawo, za ki sameni a nan”
Yana faɗin haka ya yi shigewarsa cikin wani ɗaki domin baya so ta sake masa wani dogon turancin
Sai da taga ya turo qofar sannan ta dawo da kallonta kan mairo, wani irin kallo ta mata wanda ita mairo ba ta san fassararshi ba sannan ta fara ɗaukan jinin,
Ko da ta kammala sai kiranshi tayi a waya tace ta tafi domin ta san ba fitowa zai yi ba, haka ta karanta daga lamarin gee fawwaz, wani lokacin sai ta rasa da me za ta fassarashi
Tattara komatsanta tayi ta fice, tana fita motar da aka ɗauko feenat ta faka,
Kai tsaye feenat tayi gurin Dr Ngozi cikin washe baki tace
“Dr. Barka da yamma”
“madam ya gida”?
Cewar Dr. tana murmushin ita ma
Nan dai suka ɗan taɓa hira duk da Dr Ngozi ta haifi feenat ma amma sabon da sukayi da ita ya wuce haka, tun a zamanin safiyya, ita ma kuma soja ce amma tana gwada musu sauqin kai, hannu ta bata suka tafa kamar yadda suka saba sannanta shige ciki lokacin har an shige da kayayyakin da ta zo da su
Da sallama ta tura qofar ta shiga, ba ta taras da kowa a falon ba, neman guri tayi ta zauna tana rarraba ido tana kallon sauyawar da gurin yayi, ta ɗan jima a haka sannan ta tashi ta fara jera abincin akan dining table, komai sai da ta tabbatar ta kintsa ya zama ready sannan ta koma ta zauna, ba ta jima da zama ba sai ga gee fawwaz ya fito
Tsaye ta mik’e sai kace ita ma sojar ce tana gaisheshi
“yawwa feenat, kin qaraso”?
Eh tace kanta a qasa tana jan yatsu
Neman guri yayi ya zauna ya ɗan kalleta a fisge sannan yace
“kin zo da kayan maryam ɗin”?
Nan ma eh tace tana gyaɗa kai, ummmm yace tare da mik’ewa tsaye
“ki zauna mana, ina kayan?”
Da baya ta koma ta zauna tana nuna masa k’aramar akwati da hannunta
Ba tare da yayi magana ba ya ɗauki akwatin ya tafi da shi cikin ɗakin
daga toilet ɗin ta fito alamar wanka tayi amma kayan da ta cire ta mayar a jikinta ta fito
Kallonta yayi cikin ido wanda hakan ya sanyata sauke nata idanun qasa
Ba tare da ya mata magana ba ya zuge zip ɗin akwatin ya ciro waɗansu riga da sikat ɗan kanti na zamani, rigar orange sikat ɗin blue, duk abin da ya san za ta yi amfani da shi a matsayinshi na gwani a harqar a baya shekarun da suka wuce ya ciro mata ya ajiye a bakin gadon sannan yace
“idan an yi wanka ba a maimaita kaya, ki saka waɗannan yanzu kin ji”
Be jira amsarta ba ya fice daga ɗakin
Ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta cire kayan jikinta ta sauya da waɗanda ya ciro mata, daidai misali kayan sun ɗauketa amma ba su ba da kala ba gaskiyar magana,
Waɗanda ta ciren ta ninke ta ajiye a kan gadon sannan ta ɗebi inners ɗin tayi cikin toilet ɗin, ita dai yadda fawwaz ya nuna mata amfanin komai ta bi ta wanke su tas ta shanya ta fito, a bakin gadon ta sameshi zaune yayi tagumi alamar akwai matsala
fakon idanunsa tayi ta janyo gyalenta ta sake nannaɗe kanta, tana dai tsaye kuma ta sunkuyar da kai
Da kallo ya bita sannan ya sake tashi ya buɗe akwatin ya curo wani gyale yace
“yafa wannan”
Ta mik’o hanu za ta karɓa hanunta ya taɓa nashi, ji yayi jikinta ya fi na ɗazu da ya ruqota zafi
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/8, 8:09 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*26*
Bai ce komai ba sai bin ta da ido da yayi yana jin wani irin abu a ransa na rashin jin daɗi
“ya akayi zazzaɓi yake qaruwa a jikin yarinyar nan kamar haka?
Abin da yake faɗa a ranshi kenan yana cigaba da nazarinta, tashi yayi tsaye ya zo kusa da ita ya tsaya, rasa mai zai faɗa mata yayi ko maganarne ba zai yi ba oho, sai da ya ɗau minti biyu a tsaye a gurin yayin da ita kuma mairo kanta yake qasa sannan yace
“maryam”
ɗago da kanta tayi a hankali yanayin fuskarta kuma a tsorace ta kalleshi, ita da zai taimaka mata ya canza kayan jikinsa da ta fi samun kwanciyar hankali domin kayan suna qara mata tsoronsa musamman idan ya matso kusa da ita
Idanunsa cikin nata yace
“yaushe kika fara wannan zazzaɓin”?
Taf idanuwanta suka cika da hawaye amma ba ta da niyar cewa komai
“keh malama ni ban ce ki min kuka ba, kuma bana buqatar shirun nan”
Hawayen ne suka gangaro kan kumatunta cikin sanyin murya tace
“ya fi sati biyu”
Wani irin kallo ya watsa mata tare da faɗin
“sati biyu”?
Kai ta kaɗa masa tana share hawayen da bakin gyalen jikinta
“tsawon sati biyu kina zazzaɓin kike yawon talle har cikin dare maryam”?
“ya fi damuna cikin dare, da rana kuma yana sakeni”
“kin taɓa shan magani”?
Shiru tayi nan ma
Nazarin yawan ramarta yayi sannan yace
“hmm, me take miki”?
Da idanu ta bishi sai kuma tayi saurin ɗauke idanun a kanshi ta cigaba da yin shiru
“na ce meh take miki”?
Ya faɗa murya sama tare da sake kusantarta
“ni…ni… fa ban san wa kake nufi ba”?
Kai tsaye yace
“Haule nake nufi”
Kamar baza ta ce komai ba saboda tsoro sai kuma ta ce
“babu”
“umm, babu ko?, saidai tana hanaki abincin dare, kikan kwana da yunwa, hakan yana saka ki zafin jiki da ciwon ciki har ya haifar miki da ulcer ko?”
Kallonshin dai da bata son yin tayi idanunta a waje irin ban gane ulcer ba kuma bayan ance typiod da maleria?, ya akayi kasan ina kwana da yunwa?
“um na san abin da ya fi haka game da ke, kar kiyi mamaki”
Zuba hannunsa yayi a aljihunsa sannan ya juya mata baya ya hura iska da bakinsa yace
“ta dakeki da aurena ni kuma zan ɗaureta shikenan ba bashi tsakaninmu”
Sake juyowa yayi ya ce
“mu je ki ci abinci ko?”
Wai irin nauyin nan na amare wanda yake sakasu haɗa qarya da yunwa yasa tace
“na qoshi”
Ai kuwa ta haɗu da makaman aiki irin na fawwaz, domin wani irin kallo da ya harba mata a miliyan murya na rawa tace
“zanci” sannan ta sunkuyar da kai
Shi kanshi sai da ya ji tausayinta yadda ta amsa ɗin, yana so ya ɗan sake mata fuska amma wani abu ya addabeshi a zuciyarshi, ya hanashi saqat, banda cunkushe zuciyar ba ya aikin komai, abin da ya sani kawai yana tausayinta har cikin jininsa zai kuma yi duk yadda zai yi ya samar mata da amincin da ta nema da kuma nutsuwa
Hannunta ya kamo ya fice daga ɗakin zuwa falo
A zaune suka samu feenat tana kallon kartoons domin zaman kaɗaici ya dameta, jin an buɗe qofa yasa ta yi saurin ajiye remote ɗin hanunta tare da miqewa ta fuskantar da fuskarta saitin qofar
Sai da zuciyarta ta harba sakamakon ganin mairo hanunta sanye cikin hanun gee fawwaz, cikin wani irin sauri sauri ta fara jerawa zuciyarta tambayoyi
“me nake gani?, wacece wannan ɗin?, menene alaqarta da yah fawwaz”
Dam ta ji zuciyarta ta sake harbawa da ta tuno cewar amaryarsa ta zo gani da sauri ta sake tambayar zuciyarta
“ba dai wannan ce amaryar yah fawwaz ba”?😳
Shi ko sarkin bonsy fahimtar abin da take nufi ne yasa shi haɗe rai ya kalleta da gefen ido yace
“ke kuma aikin zama da tashi ne ya sameki yau”?
A a tace idanun nan wuqi wuqi kamar tayi sata a ɗakin suruka
Ummmm yace sannan ya tunkari dining table ɗin ya janyo kujera yace wa mairo ta zauna shima ya ja kujera ya zauna
Mai da kallonsa yayi kan feenat yace
“keh zo ki zuba mata abinci”
Da sauri feenat ta taso tana cewa toh,
“ina wuni”?
Cewar mairo
Feenat da ta mance da wata gaisuwa tace
“yi hakuri antynmu ina wuni”?
“lafiya lau, yaya gida”?
Qirqiran murmushi tayi domin ta tabbatar yanzu dai ita ce amaryar tace “lafiya lau”
Abincin ta zuba ta tura gaban mairo tare da haɗa mata komai na cimar da ta zo da shi a gabanta sannan ta fara zuba wa fawwaz
“barshi feenat, damuwata maryam ta ci tukunna, sai na tabbatar ta qoshi sannan zan samu nutsuwa, kin san amarya”
Maganar yake yana murmushi kamar ba shi ba, ita dai feenat wannan hali na fawwaz yana tsoratata, tamkar hawainiya yake, akwai saurin canza kala, abune mai wuya gane inda ya dosa
Murmushi me kama da yaqe tayi tace
“haka ne yaya”
Sannan ta juya ta je ta zauna a inda ta taso
Kaɗan ta tsakuri abin da taga yayi kama da cimarta ta ci sai ta sunkuyar da kai
“kin qoshi ko me”?
Ba tare da ta kalleshi ba tace
“na qoshi”
Buɗe murfin ɗaya daga cikin drinks ɗin da suke gurin yayi wanda feenat bata buɗe ba tsabar ra’ayi ya tsiyaya a cup ya miqa mata yace
“shanye wannan”
Bata yi musu ba duk da ba ta so ta karɓa ta shanye tana yamutsa fuska saboda kwata kwata bai mata daɗi ba sai hamami da yake mata
Cup ɗin ya karɓa ya ajiye sannan ya tashi tsaye yace
“mu je”
Tashi tayi tana binsa a baya, guri ya nuna mata kan ɗaya daga cikin kujerun falon yace ta zauna shima kuma ya nemi guri ya zauna a gefenta
“canza tashar feenat, mayar sunna TV”
Cewar fawwaz yana kallonta
Toh tace tare da saurin fara nemo sunna TV,
Kamar kurame haka suka zauna banda sauraron muryar malamin da yake wa’azi babu mai ko qwaqqwaran motsi cikinsu, ni dai nace feenat kin banu
Sai da aka fara kiran sallar magriba a sunna TV sannan fawwaz yace
“feenat mu je sallah, ki shiga can ɗakin”
ɗakin da ya nuna mata ta bi da kallo tare da faɗin toh sannan ta tashi tayi ɗakin ɗauke da jakarta a hannu
Shi ma tashi yayi tare da umurtar mairo ita ma ta tashi suka shige ɗakin da suka fito, sai da ya umurceta da shiga toilet sannan ya janye wani labule a bangon ɗakin, ni dai nace me za kayi a jikin bango fawwaz? sadai tambayata ta koma cikine tare da dubun mamaki lokacin da naga ya danna wani abu a jikin bango wanda sai a lokacin na lura da shi, sai ga bangon daidai gurin da ya janye labulen yana yin qasa, cikin qanqanin lokaci gurin ya samar da qofa ‘yar madaidaiciya, bai tsaya ɓata lokaci ba ya shige cikin qofar
Wow wato idan aka ce haɗewa qauyenci kenan, wani irin haɗaɗɗen ɗakine me abubuwan mamaki, komai na gurin ya fita daban da sauran guraren da na rawaito labarin fawwaz a gurin, duk abin da yake gurin green ne da pink, kama daga furnitures da duk wani abin qawata ɗaki har shimfiɗu da carpet, sai walwali gurin yake yi ga sassanyan qamshi da yake dukan hanci
Na’urori kuwa ba a magana, sai wani guri kuma a gefe cikin falon kuma ɗaki an zuba kayan motsa jiki, daga gani gurine da aka wareshi domin motsa jikin saboda irin girkakkun kayan motsa jikin da suke gurin
Can gefe kuma lilone da aka kafa shi a falon kuma ɗaki ɗan daidai kuma qasa qasa da kuma ɗan qaramin table a gaban lilon na glass
Rigar khakheensa ya cire ya jefa a kan gadon da ke gurin, ya ɗago vez ɗinsa zai cire kenan ya ji wayarsa tayi qara
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/10, 8:23 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*27*
Qarasa cire vez ɗin yayi ya jefa a kan gadon ya nemi guri a bakin gadon ya zauna tare da ɗaukar wayar
“hello gee gani nan a qofar gida”
Abin da aka faɗa masa kenan bayan ya ɗaga wayar, batare da yayi magana ba ya ajiye wayar a gefensa ya sanyata a handsfree yace
“sannu Dr., ki shigo ki jarani a falo, zan fito yanzu”
Daga can ɓangaren tace toh tare da katse wayar
Takalmansa ya fara cirewa sannan ya cire safarsa ya tashi da sauri ya zare belt ɗinsa tare da zame wandon khakheensa ya wurga a kan gadon ya wuce toilet daga shi sai boxer da vez
A gurguje yayi wanka ya fito ɗaure da towel, ba tare da ya shafa mai ba ya sanya wata jallabiya baqa da wando iya gwiwa ya fesa turare ya ɗauko abin sallah ya shimfiɗa ya tayar da sallah, adduoi sosai yayi har na ɗauka ya manta da Dr Ngozi sannan ya sauke hannun tare da share siraran hawayen da ya gangaro masa ya tashi daga gurin sallar ya zo ya sake danna irin abun da ya dannan qofa ta buɗe lokacin zai shigo sai ga bango ya sake yin qasa, ni dai da yake ni ɗin ‘yar qauyece nace MAGIC😳
*******
Ita ma mairo bayan fitowarta daga alola bata tsaya ɓata lokaci ba ta fara gabatar da nata farillar saidai fa sallar mairo fa daga gani sai a hankali, domin addinin ake yi kawai da ka ba tare da sanin qa’idodin addinin ba, tun qashin baya bai daidaita ba take saurin ɗagowa daga ruku’i, tsayuwar ma cikin qanqanin lokacin da bai kai a kammala fatiha ba ake haɗa fatihar da surar a kammala, sujjada ma ɗosana goshine kawai akeyi ba tare da hanci ya taɓa qasa ba, qafafuwa kuma sai ta wani ɗage su sama ta haɗesu guri guda abinta, ba ta baza yatsunta na qafa akan qasa, idan ta zo tahiya shi ma cikin gaggawa takeyi tayi ta sallame, wannan ya samo asaline sanadiyyar azalzalar da haule take mata, ba damuwarta bace ita ko sallah mairo take yi za ta je tayi ta hura mata wuta akan tayi sauri ta gama ta mata wani abin ko ta tafi mata talle, hakan ya matuqar tasiri a jikinta, ya bi jikinta ta yadda sai anyi da gaske kawo gyara
Tana kammala sallar ta nemi guri jikin gadon ta takure saboda azababben sanyin da take ji har cikin qashinta
Ɗda yake kanta a sunkuye yake a nannaɗe da gyale bata san yaya akayi ba sai jin muryarsa tayi yana cewa
“maryam”
Muryarta na rawa ta ɗago kai tace
“na’am”
Yanayinta da ya ganine yasa shi saurin ficewa daga ɗakin yayi falo
A zaune ya sameta tana waya, bai katseta ba ya fara dudduba result ɗin maryam da ta dawo da shi domin shine abin da ya fi komai mahimmanci a gurinsa a lokacin, sai da ya gama karancewa tas sannan ya fara duba allurai da magunguna da ruwan da ta zo dashi, sai a lokacin ta kammala wayar ta kalleshi tace
“general ga result ɗin nan da abubuwan da ya dace ta ɗoru akai, ka duba ka gani ko”?
Kai ya kaɗa mata sannan yace
“na gode da qoqari Dr, kar dare yayi mu je a mayar da ke zan gudanar da sauran ayyukan da kaina, amma in Allah ya kaimu gobe zan tura a ɗaukoki”
Tashi tayi tana cewa
“washh wash wash, na gaji daman sosai, bacci kawai nake buqatar yi yanzu”
Gaba ya wuce tana biyoshi a baya yace
“ayyah sorry Dr”
Daga nan bai sake cewa komai ba, har suka fice daga falon, gurin motar ya rakata ya sake mata godiya sannan ya juyo cikin gida
Kai tsaye ɗakin ya tura ya shiga, gurin da ya barta a nan ya sameta sai rawar ɗari takeyi
A gabanta ya durqusa cikin tausayawa yace
“sannu maryam”
Umhm tace bakinta na haɗa haqoranta danbe
“da me kike shan magani?”
“da ruwa”
“za ki iya sha da abu me ruwa ruwa, ko ba ruwan ba”?
“a…a…”
“ok toh bari in ɓalla miki maguguna ki sha ko”?
“toh”
Buɗe fridge yayi ya ɗauko goran ruwa da ɗan qaramin cup ya dawo ya tsuguna a gabanta ya ɓaɓɓalle mata magungunan da za ta sha ya miqa mata yana cewa
“toh ungo sha”
Hannunta na rawa ta miqa ta karɓi cup ɗin ta riqe ta fara karɓar maganin bibbiyu tana sha bayan ta kawar da fuskarta gefe har ta kammala da magungunan, kifa kanta tayi a kan gwiwarta tana sake duqunqunewa
“tashi ki kwanta a kan gadon mana”
Bata yi magana ba kuma ba ta motsa ba,
“maryam tashi ki kwanta a gadon kin ji”
Sai a lokacin ta motsa domin gaba ɗaya zazzaɓin da gaske ya taso mata kamar jira yake yi dare yayi
A hankali ta miqe tsaye ta zauna a bakin gadon saidai yadda tayin kamar wacce take ɗosane akan wuta
“kwanciya za kiyi, zan ɗaura miki ruwa yanzu, inshaa Allah zuwa lokacin da zaki farka zazzaɓin zai sakeki”
naɗe qafafunta tayi ta haura da su kan gadon ta ɗora kanta a kan filon
Ganin irin abin da take yi ne yasa shi miqewa tsaye ya zauna a bakin gadon ya sanya hannu ya fara zare gyalen da take ta duqunqune jikinta da shi, gefenta ya ajiye gyalen, ba tare da ya kalli fuskarta ba ya riqo hanunta ya fara nemo jijiyar da zai ɗora mata ruwa, kusa da babbar yatsarta ya sameta, hakan yasa shi ɗauko allura ya huda
cikin qanqanin lokaci ya kammala komai sannan ya zuba wasu allurai cikin ruwan tare da sake daidaita gudun ruwan
Sai a lokacin ya kalli fuskarta, karaf idanunsu ya haɗu domin tun a lokacin da yake nemo jijiya take satar kallonsa, duk da tana yawan lumshe ido saboda yanayin da take ciki
Kasa ɗauke idanunta tayi daga kansa duk da ba ta so ya kamata tana kallonsa ba, hawayene da bata shirya zubarsu ba suka fara bin kumatunta, sauke idanunta tayi daga nashi ta rufe idanun kirif tana cigaba da tsiyayar hawaye
Takowa yayi zuwa kusa da ita ya zauna a bakin gadon yana bin fuskarta da kallo
“maryam me yake faruwa?, jikin ne”?
Yace cikin sanyin murya
Jin tayi shirune yasa shi cewa
“toh ban yarda ki cigaba da zubar da hawayenki ba, ko so kike jikinki ya qara zafi ummm”?
Kaɗa masa kai tayi ba tare da ta buɗe idanun ba alamar a a
“yawwa toh yah isa haka kin ji”
Buɗe idanun tayi sai dai ba ta kalleshi ba tace um
Tsaye ya tashi ya fice daga ɗakin yana cewa “ina zuwa, bari na dubo feenat”
********
Jikinta duk yayi sanyi saboda labarin mairo da gee fawwaz ya bata, abu ɗaya ya qara mata cikin labarin shine son mairo da yace yana matuqar yi,
“gudumawarki da nake nema feenat shine ki ja maryam a jikinki, ta zama qawarki, ki zama idanunta a cikin dangi, kar ki bari ta ji cewa ba ta tare da ‘yar uwa ta jini game dake, kin san rayuwar da tayi a baya ta sha baban da irin wacce za tayi da mu ta fuskoki daban daban, toh abin da nake so dake feenat shine maryam ta zama kamarki, ina so ta mance da tsarin rayuwarta ta baya kwata kwata, so nake ta zama kamar ba ta taɓa wancan rayuwar ba, kama daga suturu, magana, tafiya, hira, zamantakewa, tsabta, ado da kwalya, ni kuma na miki alqawari ko nawa zaki buqata wajen gudanar da aikin ba ki da matsala, burina dai ki zama so close da ita, amma ban da raini domin matatace, na zaɓekine saboda na san zaki fi yin abin da nake buqata don kin fi sauran yaran hankali ba za ki qyamaceta ba”
“toh ya fawwaz amma wani abin dole sai a hankali kasan ba gida ɗaya muke da ita ba, sai lokacin da na zo”
“me kike yi yanzu”?
“a ina?”
“a gida”
“babu komai, sai zaman jiran result kafin mu ɗora”
murmushi yayi cikin zolaya yace
“wa ya ga feenat a jami’a, rawar kai kuma sai abin da zai qaru”
Ganin fara’ar fuskarsa yasa ta yi ‘yar dariya cike da kunya irin ta ‘yammata tace
“a a yah fawwaz”
ɗaga qafarsa yayi ya ɗora akan ɗaya yana girgizawa yace
“toh shikenan yanzu dai idan amaryata tana gidan gona kina gidan gona, haka idan tana gidan hajiya kema kina can, idan kin min haka na san feenat tana tare da yah fawwaz”
“ba ka da matsala da ni yah fawwaz, saidai ita antyn tamu ka nemi izininta kar ta ga kamar an mata shisshigi”
Murmushi yayi yana me jinjina wa fahimtarta
“kar ki damu da wannan, amaryata duk da tsadarta amma ta fi sauqi sauqi”
Ayi hakuri da wannan, kusan abinka da matafiyi
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/12, 9:00 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*28*
Murmushi tayi tare da cewa
“na ɗauka yayana, inshaa Allahu zan yi iya qowarina gurin canza ta”
Murmushin shima yayi tare da jinjina kai
“mu je sallah”
***********
Zaune yake a kan rest chair daidai saitin fuskarta, duk wani motsinta da take yi cikin baccin da tayi sakamakon ruwan alluran da ya ratsa jikinta yana lura da shi
Wayarsa da take kan gadon kusa da mairo ce ta fara vibrating, sau uku tana yi tana katsewa amma bai ɗaga ba, jin vibrating ɗin zai takura masa a karo na huɗune ya miqa hanu ya ɗauko wayar tare da danna ok ya ɗora a kunnensa
“happy marriage life gee fawwaz, ina matuqar tayaka murnar aurenka, a sha angwanci lafiya matashin zaki, tare da haka nake farincikin sanar maka da cewa lissafinmu ya qara yawa, mu kwana lafiya”
Ba tare da yace komai ba aka kashe kiran, sauke wayar yayi daga kunnensa ya qura mata ido kamar zai hango hoton mai kiran a fuskarta, rest chair da yake kai ya matsar daf da gadon
ɗaga idanunsa yayi ya kalli ruwan da yake tafiya saura kaɗan ya qare, sai ya dawo da kallonshi kanta, kusan minti biyu yana kallonta sannan ya sauke ajiyar zuciya,
Hannayensa ya ɗaga sama kasancewar lokacin biyu saura, addua ya fara a hankali muryarsa na rawa
“Ya Allah, ya ubangijin halittu, ya mai tausayin bayi, ka amintar da ni da iyalaina, ya Allah kar ka ba wa wani azzalumi nasara a kaina, ya Allah na gode da jarabawar da ka min akan safiyya, Allah na gode, Allah na gode, ya Allah ina roqonka da ka tseratar min da maryam, ya Allah maryam baiwarkace me rauni ya Allah, ka jiyar da ita daɗi duniya da lahira, ka sanyata cikin bayinka masu gode wa ni’imarka ya ubangijina”
Kafin ya sauke hannu hawaye sun fara bin fuskarsa, hawayen ya fara sharewa da yatsunsa biyu yana cigaba da kallon maryam, wani irin zafi yake ji a zuciyarsa game da su alhaji bala, saidai wannan karon yana shirye tsab da izinin Allah yana gab da tarwatsa rayuwarsu
Ranqwafowa yayi ya fara mata adduoin neman tsari ya hura mata iskar a jikinta
Cikin magagin barcin da ya fara saketa taji kamar abu na bin jikinta, a hankali ta fara buɗe idanunta, tun suna mata dishi dishi har dai ta wartsake,
Idanun ta sauke a kanshi daidai lokacin da yake ɗaga kansa daga ranqwafawar da yayi
Wai aka ce bacci qanin mutuwa, sai a lokacin ta tuna gurin da take, hannunta mai qarin ruwan ta motsa wanda yayi daidai akan idanunsa
“maryam kin farka”?
Yace
Maimakon tayi magana sai ta gyaɗa masa kai kawai abinta sannan ta ɗauke idanunta a kanshi
“yaya kike jin jikin yanzu”?
Nauyi ta ji bakinta ya mata kasancewar ta daɗe tana barcin, sai da tayi da gaske ta buɗe bakin tace da sauki
“mashaa Allah, bari ruwan ya qarasa in cire miki ki samu wani abu ki ci ko”?
Toh tace sannan ta kalli ledar ruwan da yake tafiyar sai ta sauke idanun tare da lumshesu ta sake mannewa a jikin katifar da tun hawarta kai take ji kamar ana zare mata duk wata gajiya ce a jikinta saboda daɗin kwanciyar da ta ji a kanta
Hhh, su mairo wai don ma ba lafiya
Bayan ya cire mata ruwan sai da ya taɓa gefen wuyarta ya ji zafin jikin da sauqi sannan yace
“za ki iya wanka yanzu”?
Da sauri ta kalleshi tare da kallon agogo sannan ta sunkuyar da kai
Murmushi yayi yace
“dare yayi ko?, to ai idan kika yi wankan za ki fi jin daɗi, sai ki sanya kayan barci kiyi baccinki, toh ma meye maraban dambe da faɗa, kin san dole tunda kinyi barcin nan sai kin yi brush kafin ki ci abinci ko?, kin ga don kin yi wanka ma ai ba wani dogon zance bane”
Kai ta kaɗa masa alamar eh, amma a ranta cewa take sabuwar tijara, wanka cikin dare da goge baki kafin cin abinci
“yawwa toh bari in haɗa miki ruwan wankan ko”
Nan ma toh tace sannan ya juya ya shige toilet ɗin ya haɗa mata ruwan wankan ya fito yana cewa
“ki je kiyi, kafin ki fito kiyi alolar bacci, idan kin zo zaki samu kayan da zaki saka a kan gadon, zan shigo miki da abinci, idan kuma kin ji bakinki ba zai iya ɗaukar abincin ba ki buɗe fridge ɗin nan ki zaɓi abin da ya miki ki ci ki kwanta kin ji”?
Na gode tace tare da shigewa toilet ɗin tana mamakinsa a ranta domin salon nasa gani take yi yayi yawa, idan ba haka ba a ina aka taɓa yin alolar barci😳😂 wayyo Meroro
Sai da ya ga ta rufo qofar sannan ya fice ya dawo da abinci ya ajiye, kayan barcin da za ta saka ya ciro mata farare tas ya zuba su a kan gadon sannan ya juya ya yaye labulen da yake saitin bangon nan ya sauke bango ya shige ɗakin tare da rufowa ta hanyar sarrafawar nasara
Alola yayi ya ɗauko abin salla ya shimfiɗa tare da ɗauko kur’aninsa ya fara karatu cikin suratul lukman, sai da ya kammala tas yayi adduoin da ake yi bayan kammala karatun kur’ani sannan ya kalli agogo, uku saura minti biyu ya gani, don haka ba tare da ɓata lokaci ba ya tashi ya ta da sallar nafilar da yake yi duk qarshen dare, ni ko nace Allah ka bamu albarkacin bayinka na qwarai
*******
Shiru alhaji nasiru yayi yana sauraron kukar ‘yar tasa da yake ji da ita kamar rai, Allah ya sani duk wani abu da zai sanya zainab hawaye baya qaunarsa, shiyasa lokacin da yaji tana son fawwaz ya mata alqawarin aurensa domin cikar farincikinta, sai gashi mummunan labari ya iskesu na auren fawwaz, bayan ya san ‘yarsa ta ɗaura rai sosai a kansa saboda alqawarin da ya mata na aurenshi
“kin tabbatar kuwa ummie, amma abin da matuqar mamaki ace mutum kamar fawwaz a qasar nan yayi aure ba tare da kafafen yaɗa labarai sun yi ta sanarwa ba, ina ga impossible”
Cewar hajiya maimuna kenan da ita ma duk abin duniya ya dameta saboda kukan da zainab ɗin takeyi ba ji ba gani
Alhaji nasir ne ya numfasa yace
“bi ki san waye fawwaz ba, zai iya yin auren ba tare da kafafen yaɗa labarai sun ji ba tunda ba addinine hakan ba, kin san tarbiyar da fawwaz ya samo na ra’ayi a gurin mahaifinsa, hmm amma koma dai menene bari in kira hajiya hafsat ɗin in ji sahihancin maganar”
“wallahi momy friend ɗita safna tana da alaqa da su, a gurinta na ji aurensa, yanzu ma ta kira ni a waya ta sake tabbatar min saboda nima da ta kirani da safe ta faɗa min ban yarda ba”
“ki kwantar da hankalinki uwata, ba dai fawwaz ba, toh zaki aureshi, bari dai muyi magana da hajiyar”
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/13, 3:22 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*29*
Wayar ba ta daɗe tana kaɗawa ba hajiyar fawwaz ta ɗaga
“assalamu alaikum”
Cewar hajiya cikin salihar muryarta
A can ɓangaren alhaji nasir ya amsa
“wa alaikissalam hajiya, mun wuni lafiya”?
“lafiya lau alhaji, yaya iyalan”?
“iyalai alhamdulillahi”
“toh mashaa Allah, mashaa Allah”
Jim yayi na two minutes kafin ya numfasa yace
“hajiya nace ya maganarmu ne, ina ta kwana?”
Ita ma a can sai da ta ɗan yi gyaran murya tace
“eh maganarmu tana nan, babu abin da ya canza ta alhaji, ni na ɗauka ma kun yi waya da fawwaz ɗin”
“alhamdulillah, na ji daɗin jin haka daga gareki, kin san na ce miki nayi ta kiranshi ban sameshi ba, to tun daga lokacin ban sake kiranshi ba, domin na san ke ma idan ya dawo zaki masa maganar”
“ok toh yanzu ka sa mana ranar da zamu zo da shi gidan sai mu tsai da magana kafin iyayensa maza su shigo ciki”
Cikin washe baki alhaji nasir yace
“ni duk lokacin da zaki zo ki sanar da ni kawai hajjaju, zan yi zaman jiranku”
“toh shike nan, bari ya zo sai in ji ranar da yake da rarar lokaci, duk yadda muka yi zan nemeka in sanar maka”
“yawwa hajjaju, ina godiya da wannan karamci sosai sosai, sai na jiki”
“um um ba komai alhaji, an zama ɗaya ai”
“toh na gode, a gaishe min da amaryata me jan kunne”
Dariya hajiyar tayi tace
“lallai fa kana fama da amarya, gata nan sai surutu”
Dariyar shima yayi yace
“ai haka ake so, lafiyace”
“lallai fa, toh sai anjima”
“mu jima da yawa hajiya”
Kashe wayoyin sukayi duka a tare yayin da hajiya take shan tambayoyin amrat, wai hajiya ta faɗa mata da wa tayi waya, wanene me surutu??
Toh kina yi sai a qi faɗa amrat?😂, surutu kamar beauty na
Kallon zeey yayi bayan ya ajiye wayar yana murmushi
“uwata duk kin bi kin ɗaga min hankali akan shirmen banza, toh dai kin ji a gabanki muka yi waya da hajiyarsa, ta ce za su zo da shi ayi maganar auren, yanzu shikenan ko?, sai a share hawaye a tashi a ban guri”
Sai a lokacin kunyar abin da tayi ya rufeta, sunkuyar da kai tayi tana murmushi kuma ta kasa tashi, abokin karawarta hisham ne ya juyo ya kallo gurin da suke ya sama mata hanyar fecewa
“ban da rashin kunya ma irinta wannan yarinyar akan saurayi ki zo ki hana mu zaman lafiya, kiyi ta kuka a gaban iyayenki, hutu nake buqata tun da na dawo daga school amma kin hanani hutawa da sautin kukanki maras daɗin sauraro”
Ai kuwa nan ta ɗago fuskarta da sauri tayi kansa tana nuna shi
“kai wallahi hisham ka kiyayeni, ni ba sa’arka bace, banza kawai wawa”
Dariyar shaqiyanci ya mata yana cewa
“hey malama, a tashi min a kai domin na san ba dakuwa zan yi ba”
Dama neman hanyar barin gurin take yi, saboda haka sai tayi qwafa tare da jan wani shaiɗanin tsaki ta wuce ɗakinta, shiko hisham sai wuuu taji kunya yake cewa
“kai kai kai, ka shiga hankalinka, ka san dai yayarka ce ko?, ka ji min yaro da rashin kunya, bar ganin ka fara ajiye qasumba har yanzu dai ba a canza wa tuwo suna”
Cewar alhaji kenan yana zare idanu wa hisham
Tashi hajiya tayi tana tafiya tana cewa
“kai kake biyewa waɗannan yaran, anjima kaɗan zaka ga suna qusqus, wa ya sani ma ko gulmarmu sukeyi”
Daga alhajin har hisham binta da kallo sukayi suna dariyar maganarta
*********
“shegiya safna, kin so ki kasheni lokacina bai yi ba, da yanzu fa na dawo marigayiya”?
“me kuma nayi zeey baby”?
“ai zan shigo gidanku gobe, dole sai kin biya tsoratarwar da kika min, ai ke banzace wallahi”
Katseta safna tayi da cewa
“qawar banza ba, shirme kawai, ki fito ki faɗi matsalarki kin tsaya nuna min ke ‘yar fari ce”
“toh hasidin iza hasada, keh na fahimci baqin cikin kasancewata ‘yar farin nan kike yi, kin san dai ɗan fari shi ne ɗan so ko?, ba irinku ba, ku ba auta ba kuma ba ‘yan fari ba”
“in miki baqin cikin kalar haukan?, da ɗan fari da auta wannene me kan gado da wayo”?
Dariya suka kwashe da shi duka sannan zee tace
“to ‘yar rainin hankali na ji, yanzu dai abin da nake so ki sani shine har yanzu komata tana riqe da wannan babban kifin”
“wanne kifi kenan”?
“gee fawwaz mana yarinya, keh dai ki shirya shan shagalin da ba ki taɓa sha ba, wallahi har yanzu gee fawwaz na zee babyne ita kaɗai ɗinta”
Dariya safna tayi sosai sannan tace
“toh ban qi miki cewar zaki auri gee fawwaz ba, amma wlh sai dai ki je a ta biyu, domin ina da tabbacin yayi aure jiya, kin san yadda muke da raudat kuwa?, toh tun yarintarmu tare mukayi har yanzu bamu rabu ba, jiya na kirata a waya saboda ina son kai mata wasu kayan da muke so mu yi anko sai take ce min ta je biki gidansu antynta, auren gee fawwaz suke yi”
“keh bar min mugun fata zama da kishiya ba dai a gidan fawwaz ba, sam sam, sai anjima”
Tana gama faɗin hakan ta kashe wayar tayi jifa da ita tare da faɗuwa a kan gadon tana jan tsaki
*********
Saboda yanayin jikin yasa tayi nauyin barci bata farka da wuri ba har gee fawwaz yayi sallah yayi karatun kur’ani tana naɗe cikin bargo abinta, sai sheqa barcinta take yi cikin ni’imar da take jinta ciki, musamman sassanyar qamshin da yake ratsata ta ko ina, ga jikinta da yaji lafiyayyen sabulun wanka sau uku a rayuwarta, hakan ya taimaka sosai wajen nitsawarta duniyar barci
Tsaye yake a kanta yana nazarin yadda take shaqar numfashinta, tun bai taɓa jikinta ba ya gano sauqi sosai da ta samu ta yadda numfashintan yake fita, hankalinsa ya mayar kan agogo yaga idan bai tasheta ba za ta iya rasa sallar asuba domin rana tana gab da fara fitowa
Sunanta ya kira tare da bubbuga fulon da ta ɗora kanta a kai, a karon farko ba ta ji ba sai da ya sake bubbugawa tare da kiran sunanta
Buɗe idanunta tayi a hankali bayan tayi miqa ta saukesu a kansa, kunya ko qauyanci oho sai kawai ta ɗauke idanunta tare da jan bargo ya rufe mata fuska
Girgiza kai yayi yana murmushi yace
“ki tashi kiyi sallah, ko za a sake wani daren ne maryam”?
Toh tace a ranta tana cewa
“shi kuma wannan ba a ganin zuwanshi saidai mutum ya ganshi a kansa”
Ganin bata tashi ba yasa shi ficewa daga ɗakin yana cewa
“ki tabbatar kin tashi kin yi sallah kafin in dawo”
Tana gani ya fice ta sauko daman ta qi tashine saboda yanayin kayan jikinta
Tana zaune kan abin sallah ya shigo, kan kujera ya je ya zauna ya mai da hankalinsa a kanta, kanta ta ɗago ta kalleshi cikin jin nauyi tace
“ina kwana”?
“lafiya lau maryam, kin tashi lafiya”?
“lafiya qalau”
“da kyau, toh ya baqunta”?
“lafiya”
Shiru yayi na wasu mintoti sannan yace
“kin san me za kiyi yanzu”?
Kai ta kaɗa masa tana kallonsa
“ki tashi ki yi wanka, ki canza kaya kafin lokacin break”
Toh tace daga nan ta ja bakinta tayi shiru tana jan yatsunta
“idan kin shirya feenat tana so ta gaisheki, zaki iya fita falon ku gaisa amma ita bana so ta shigo nan”
Nan ma dai to ɗin tace
Wucewa yayi saitin labulen ya yaye, bin bayansa tayi da kallo tana tunanin me zai yi a gurin, ba ta qarqare tunanin ba taga ya dannan wani abu bangon gurin yayi qasa, waro idanunta tayi kamar za su zazzago tare da rufe bakinta da hannu, ji tayi kamar za ta saki fitsari ganin ya shige ciki tare da ɗaga bangon sama
Salati ta fara yi har da fifita saboda baqon abin da ta gani, mamaki da al’ajabi da tsoronta a wannan lokacin faɗinsu qauyencine, tana so tayi tambaya saidai babu wanda za ta tambaya a gurin, a taqaice ko akwai wanda zai ba ta amsar toh ita ba ta shirya tambayar da za ta yi cikin tsari ba,
******
Ita kaɗai take zaune tana amfani da wayarta, sai tiqar dariya takeyi, daga gani chatting take yi saboda yadda take sarrafa yatsunta
A cikin nutsuwarta ta fito daga ɗakin tana tafiya cikin sanyi ta nufo gurin feenat, jin motsi yasa feenat ta juyo, ganin mairo yasa ta saki fuska da fara’a tace
“oyoyo antyna kin fito”
A ɗarare ta zauna a kan kujerar tana murmushi tace
“ina kwana”?
“waiwai antyna ai nine da miqa gaisuwa gurin amaryarmu, gashi har qamshin amarci ya fara bulbule min hanci antyna”
Cikin jin kunya tace
“qamshin amarci kuma”?
“sosai antyna, ai kuɗin manyane, kin san amare gimbiyoyine sai ana muku biyayya don kar mutum ya kasa ganewa”
Murmushi kawai mairo tayi don taga surutun yarinyar ya fi qarfinta, ita ko feenat sai janta da hira take yi saboda ta sake da ita, suna haka suka ji ana kaɗa doorbell
Kallon juna sukayi sannan mairo tace
“kamar kun yi baqi ko”?
“kin yi baqi dai, ke ceh matar gidan ai amaryarmu, bari in je in dubo”
Qofar ta je ta buɗe
“oyoyo cwt amrat, oyoyo nanie”
Abin da feenat tace kenan tare da rungumo kyakkyawar yarinyar da take ta washe baki
hankalinta ta mayar kan yarinyar da feenat ta rungumo, yarinyar ta mata kyau sosai gashi ta sha ado na mamaki, ba ta taɓa ganin yarinya kyakkyawa kamar wannan ba tsawon rayuwarta,
Riqe da kwandon abinci nanie ta shigo ta nemi guri ta ajiye sannan ta zauna ta mai da hankalinta kan feenat tana cewa
“mun tashi lafiya feenat”
Feenat da hankalinta yake kan amrat tana ta tayata rawar kai da surutun da take yi tace
“lafiya lau nanie, ya su hajiya”?
“lafiya qalau, ya amaryar baban amrat”?
Waigawa tayi gefen da mairo take zaune take kallonsu tace
“ga amaryar nan, lafiyarta lau”
Nanie dai ta kusan kwafsawa domin har ta buɗe baki tace
“wann…”
Sai amarat ta katseta da cewa
“oyoyo my father”
Da gudu ta qarasa gurinsa yayin da yake tsaye cikin khakheensa a jikin qofa, hannu ya buɗe mata cikin farincikin da ba zai iya qiyascewa ba yace
“oyoyo cwthrt”
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/14, 7:04 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*30*
Juyi yayi tayi da ita sannan ya dakata tare da manna mata kiss a kumatunta duka biyu yana cewa
“nayi kewarki ‘yar kyakkyawar babyna”
Dariya takeyi tace
“dady ka tafi ka barni ni kuma nayi ta kuka wa hajiya”
“haba babyna?, kai amma kuwa dady baka kyauta ba, ka tafi ka bar amrat ɗinka tana kuka”
Cike da shagwaɓa tace “iyeh dady, yanzu ma sai da nayi kuka sannan hajiya ta yarda na biyo nanie muka zo gurinka, wai zan zo in dameku da surutu”
Jan hancinta yayi yana murmushi yace
“toh ba zan sake ba ‘yar gidan dady, kiyi hakuri kin ji,? kin yi?”
Murmushi tayi tare da gyaɗa kai sannan tace
“yawwa dady wai hajiya tace akwai amaryarka a nan”?
“ohhh amrat!, kin san me za a yi?, mu je ki gaishe da antynki”
Ana tare ta tana qin taruwa, amrat manya sai cewa tayi
“dady wacece antyna”?
Sauketa qasa yayi ya kama hannunta yana cewa
“muje ki ganta”
Gurin da mairo take ya je ya zauna, tuni ya haske mairon domin ko kusa da man ba haɗi, sunkuyar da kai mairo tayi tana jan yatsunta
Cikin ladabi nanie tace
“barka da safiya yallaɓai”
“yauwa nanie, mun tashi lafiya”?
“lafiya qalau, hajiya ce ta turo mu da abinci”
“ayyah mun gode, sannu da ɗawainiya”
“Allah na tuba wacce ɗawainiya kuma yallaɓai”
Bai amsa ba sai murmushi da yayi ya kalli mairo sannan yace
“cwthrt ga antynki ki gaisheta”
Gurin da mairo take ta mai da hankalinta, dukkansu qura wa amrat idanu sukayi saboda kallon qurillar da suka ga take wa mairo ba tare da tace komai ba sai da fawwaz yace
“amrat”
Sannan ta kalleshi tace “dady ban santa ba”
Hannunta ya kamo ya zaunar da ita a tsakiyarsu da mairo ya juya yana fuskantarsu yace
“kin manta kika ce min ina momynki?, ke ma kina son momy irin na fudel ɗin ajinku kullum yana ce miki momynsa momynsa”?
Da sauri tace
“eh dady, yace min momynsa ce take masa wanka da brush ba nanie ba, kuma tana koya masa karatu, ina son momy dady”
Ta qarasa maganar da kwantar da wuya
Cikin rauni ya ce
“kwantar da hankalinki cwthrt, ke ma ga momynki”
Ya faɗa yana nuna mata mairo da hannunsa, wayyo yara kuna sha’aninku, cikin murna tace
“da gaske dady”?
Murmushi yayi yace
“dady yana qaryane amrat”?
Kaɗa kai tayi tana cewa a a
“yawwa toh maza gaishe da momynki”
Rungumo mairo tayi cikin farinciki da murna tace
“wai keh ce momyna”
Mairo da take ganin abubuwan banbaraqwai wai namiji da sunan kakata kallon fawwaz tayi cikin rashin sanin me ya dace tayi wa yarinyar ko tsorone oho
Kai ya kaɗa mata sannan ta mai da kallonta kan amrat tana murmushi tace
“eh, ni ce momynki”
Sake qanqame mairo tayi tana cewa
“wayyo daɗi, nima nayi momy fudel, ina zuwa makaranta zan faɗa masa”
Dukkansu mutanen gurin sai da ta basu tausayi, nanienta kuwa har da share qwalla da bakin hijab ɗinta
Ita kanta mairo duk da ba ta san komai akan yarinyar ba amma sai taji wani irin tausayi da qaunarta ya shiga ranta, ita ma qanqame amrat ɗin tayi sosai a jikinta tana kallon fuskar fawwaz da idanunsa suka kaɗa yana kallon wani gurin
Tashi yayi ya wuce ɗaki bayan ya kira maryam
Kasa tashi tayi daga gurin saboda ganin idanunsu nanie ya saka mata nauyi sosai
“kiranki fa yayi antynmu”
Cewar feenat
Cikin jin nauyin ta tashi bayan ta ɗago amrat sannan ta ruqo mata hannu da nufin su je tare
“je ki dai ki dawo, ita amrat ta zauna”
Nanie ce ke faɗin haka sannan ta kamo hannun amrat
Sake hannun amrat ɗin tayi ta wuce, a hankali ta tura qofar ta shiga da sallama
Sallamar ya amsa mata yayin da yake zaune a kan kujera, a qasa ta zauna tace “gani”
“tashi ki zauna a nan”
Ya nuna mata gefensa
A ɗarare ta zauna ta sunkuyar da kai, hanunsa ya kai gefen wuyanta,
“ya kike jin jikinki yanzu”?
“da sauqi sosai”
“ok ki tabbatar kin sha magungunanki, bari in nuna miki yadda zaki sha, anjima likita zata zo ta sake duba jikin naki”
Magungunan ya ɗebo ya nuna mata yadda za ta sha sannan yace
“ni zan wuce gurin aiki, ina fata baki da wata matsala”?
“babu”
Saidai a ranta so take ta tambayeshi amma bata san me za ta ce ba
“toh sai na dawo”
Yace tare da juyawa, murya qasa qasa tace “Allah ya tsare”
Ba tare da ya juyo ba yace ameen sannan ya buɗe qofar ya fice
Ganin fitowarshi yasa amrat sake tashi ta rungumoshi, hannunta ya ruqo ya qaraso gurin su nanie yace
“nanie ku gaishe da hajiya, kar ki bar amrat domin gobe akwai schl ba kuma lallai ne mu je can yau ba, ni zan wuce”
“toh yallaɓai Allah ya tsare”
Ameen yace ya kama hanyar fita hannunsa cikin na amrat, sai da ya buɗe qofa sannan ya juyo yace
“yauwa feenat Dr Ngozi za ta zo duba maryam, ki kula min da ita plss, har yanzu jikin ba wai ya gama qarfi bane”
“toh yah fawwaz”
“ayya ya jikintan yallaɓai,? kayi hakuri hajiya ta ce min ba ta ji daɗi ba”
Cewar nanie
“da sauqi sosai”
Yace sannan ya sumbaci amrat yace ta koma ciki, juyawa take yi da baya tana ɗaga masa hannu shima ya ɗaga mata sannan ya ja qofar ya rufe
*******
ɗaya baya ɗaya yake bin fuskarsu da kallo yana zagayesu kasancewar an haɗesu guri guda sannan ya fara magana yace
“gani da kaina cikin wannan ɗaki a gabanku, bance ku faɗi wanda ya turoku dole ba amma ga wani albishir me daɗi, daga yau bana da tabbacin ɗayanku zai sake samun damar shaqar iskar da take wanzuwa cikin duniyar nan, bindiga da duk wani makami ba za a yi amfani da shi a kanku ba, amma abin da zai fara gudana yanzu shi zai tabbatar da albishir ɗin da na muku”
Umurni yayi wa masu azabtarwar nan suka fara gana musu azaba cikin wani irin ruwa mai tiririn sanyin qanqara, ai ko minti biyar ba ayi ba aka samu biyar daga ciki suna ihun za su faɗa, duk da haka fawwaz bai ba da umurnin a qyalesu ba har sai da ya tabbatar sun fice a hayyacinsu sannan ya sa aka dakata, tsabar azaba ukune kawai ba su suma ba, amma su ma saura qiris ya rage
Su ukun gaba ɗaya aka jera tare da ɗaura musu camera
Aka fara jero musu tambayoyi
******
Hajiya kuwa bayan ta gama amsa surutu da tambayoyin amrat game da wayar da suka yi da alhaji nasir sai ta ɗaga waya ta kirashi, saidai kiran ya je ne a lokacin da yake sauraren amsoshin da ake samu daga bakin ‘yan ta’addan nan, bai ma ji kiran ba saboda yadda ya mai da hankalinsa gurin sauraro
Hakuri miliyan masoyana, maryam ɗin ce sai a hankali, ni kaina nayi wuya wa kaina, masu kira su ji ba a ɗaga ba da masu saqo ba amsa don Allah ku min uziri, ba yin kaina bane, ku min addua kawai, zan dawo maryam ɗinku ta baya inshaa Allah
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/15, 3:12 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*31*
“wa ya turoku”?
ɗaya daga cikin su yace
“jagus ne ogan mu, shi yake mana umurni mu aikata komai”
“wanene jagus”?
“shine shugabanmu gaba ɗaya, yana karɓar umurnin ayyuka irin waɗannan mu kuma yana tura mu gudanar da aikin”
“waɗanne irin ayyuka yake saka ku”?
“muna garkuwa da mutane, muna kashe mutum idan ya mana umurni sai a biyashi, mu ma kuma sai ya zo ya biyamu cikin abin da ya samu akan aikin”
“za ka iya tuna waɗan da kuka kashe ko yin garkuwa da su”
Wannan tambayar ta firgitashi amma ya zaɓi ya faɗi gaskiya ko za a nemo jagus ɗin shima a ɗanɗana masa uqubar da suka ji
Cikin rawar murya yace
“mu muka kashe D.P.O na rundunar ‘yan sanda me suna muhammad musa fanti, mu muka kashe ɗan alhaji yusuf dala bayan ya ce kar a bamu kuɗin fansansa, mu muka….”
Sai kuma yayi shiru yana zazzare ido tare da sauke numfarfashin wahala
“muna sauraronka sai wa?, wa kuka kashe?”
Wata zuciyarce tace “ka faɗi gaskiya kawai hakan zai sa a nemo jagus duk inda suke”
Da wannan tunanin yace “mu muka……, umm ummm, ayi hakuri yallaɓai mu ka je muka kai hari wa matar……”
“matar wa”?
Suka ji muryar gee fawwaz cikin tsawa yana faɗin haka
A kiɗime yace
“ranka ya daɗe wallahi jagus ne ya turamu, kuma har da haɗin bakin ɗaya daga cikinku shi ya bamu labarin tafiyar da za ta yi zuwa missau da nambar motar da suke ciki har lokacin da suka fita daga gida shi ya faɗa mana”
Wani irin kallo da fawwaz ya tsareshi da shi sai ga fitsari yana sauka daga wandonsa, a tsorace yace
“yallaɓai don Allah ku barni in huta, ku tambayi wannan”
Ya qarasa maganar yana me nuna na kusa da shi
madakan fawwaz ya kalla cikin wani irin yanayi me ban tsoro, kusan ma ban taɓa ganin yanayin a fuskarshi ba yace
“idan ba zai yi magana ba ku mai da shi cikin glass ɗin qanqarar can, kar ku kuskura ku ciroshi har sai ya daina numfashi”
Ihu yayi ganin an damqeshi yace
“wlh zan yi magana ku dakata”
Wancakalar da shi sukayi sannan aka qara sai tashi wa camera
“kai muke sauraro”
Jiki da murya duk na rawa yace
“matar gee…. fawwaz ce!, ranka ya daɗe wallahi muma saka mu akayi”
Wayyo Allah zaki me tsorata namun dawa, cikin wani irin zafi fawwaz ya kai masa naushi a baki da hanci yana cewa cikin ɗaga murya
“wa ya turoku?, wa ya turoku nace !”
Qaramar bindiga ya ɗauka ya ɗora a goshinsa yana zaro ido, ba za ki ce fawwaz ɗin da kika sani bane saboda yadda fuskarshi ya rikiɗe da tsananin ɓacin rai
“wa ya turoku kuka kashe min mata?, zan kasheka matuqar baka sanar da ni sojan da yake sanar da ku sirrin gidana ba, waye shi, wanene??!!!!
“ban sanshi ba wallahi ….yall…aɓai, ni jagus kawai na sani, ban san wa yake masa umurni da aikin ba, wallahi ban sanshi ba, ko waya ba mu taɓa yi da su ba, duka jagus suke kira…..hinhinnmh wayyo, wayyo Allah na”
Kunamar bindigar ya ja yace
“dama ta qarshe da za ka rayu, a ina jagus yake, ina za a sameshi”??
Kamar numfashinshi zai fita yace
“a cikin garin nan yake a mafakarmu amma ba lallai a sameshi a gurin ba”
Kafin fawwaz yayi magana cikin madakan wani yace
“sai a ina za a sameshi”?
“lagos, idan irin haka ta faru can yake tafiya da sauran yaran da suka saura masa”
“ka san gurin da za a sameshi a lagos”?
“eh mun taɓa zama da shi a ɗaya daga cikin gidajensa na can amma ban san sauran ba”
Zaga ye ɗakin fawwaz ya fara yi bayan ya sauke bindigar daga kan mai jawabin cikin tsananin ɓacin rai da damuwa sannan ya juyo da sauri ya zo gabanshi yace
“zaka ba da address ɗin gidan domin duk inda ya shiga a cikin qasar nan sai na nemoshi, sai kun faɗa min wanda ya turo ku kashe min mata idan ba haka ba babu wanda zai rayu a cikinku”
Yadda yake maganar kawai za ku san baya cikin hankalinshi sosai, Allah ne ya kiyaye da ya harbesu duka a gurin, domin yanayine mai tafiya da tunanin zan rasa ko zan samu
Ficewa yayi daga gurin kamar kububuwa bayan yayi umurni da a ba wa waɗanda suka sume taimako ciki har da mai gadi kuwa da bai san laifin ma da ake tuhumarsu a kai ba, shi dai ya san yana gadi a gidan kuma ya san akwai maigidan amma ba zai taɓa cewa ga sahihiyar fiskar maigidan ba saidai sautin murya
Hmmmmm, manzon Allah yayi gaskiya domin yace qarshen duniya zai zama wanda yayi kisa bai san saboda me yayi kisan ba haka wanda aka kashe bai san me yayi aka kasheshi ba, yanzu dai ku duba irin abin da ya faru tsakanin matar fawwaz da ‘yan ta’addan nan, ba ta san me tayi suka kasheta ba, haka su ma ba su san me ta musu suka kasheta ba, infact ba su ma san wanda yayi umurni da a kasheta ba, wanne irin rayuwane wannan bayin Allah, anya muna tuna mutuwa kuwa?, anya muna tuna ranar da za mu tsaya a gaban mahaliccinmu domin amsa tambayoyi kuwa,?
‘yar uwa me kishiyarki ta miki kika kasheta,? me ɗan kishiyarki ya miki kika kasheshi?, me qawarki ta miki kika kasheta?, me abokinka ya maka ka kasheshi?, me ɗanki ko ɗanka ya miki ko ya maka kuka kashe shi?, yanzu kin yarda ku tsaya da su a gaban ubangiji yana shaqe ko tana shaqe da wuyarki tana cewa ko yana cewa ubangiji tambayeta me nayi ya kasheni?, yanzu ‘yar uwa kin yarda akan kishiya ki shiga wuta?, yanzu kin yarda ubangiji ya yi fushi da ke akan kin kashe ko azabtar da ɗan kishiyarki?, ‘yar uwa me kike wa kishin ne?, idan mijin kike kishi toh kin yi da kishiyarki saboda tana kwana ɗaki ɗaya da mijinki, to ita ‘yar ko ɗan me suka miki?, su ma suna kwana miki da mijinne?, me yasa kika mai da kanki dabba duk da kina da hankali?, ‘yar uwa ki yi wa kanki gata, ki gyara tun kafin lokaci ya qure miki, kar ki kashe wani ko wata ba wai don tsoron kar a kasheki ba, a a ki bari don Allah ne yace a bari ba ya so, nasihace ‘yar uwa, idan kin ji ya miki amfani, idan kin qi kuma hakan ba zai cutar da maryam da komai ba amma ki sani wata rana zaki tuna a lokacin da tunawar ba zai miki amfani ba, Allah ba ya canza kowa har sai ya canza da kansa
A kwance yake idanunsa na kallon sama, tsawon lokaci yana haka sannan ya tashi zaune, kallon agogo yayi tare da faɗin
“subhanallah”
Da sauri ya nemo gurin da ya watsar da wayoyinsa ya ɗauko wanda yake kiran familynsa da shi, missed call biyu ya gani na hajiyarsa, nambarta yayi dialing sai da ya ga an ɗauka sannan ya kara wayar a kunnensa ya mata sallama, amsa sallamar tayi sannan ya fara gaisheta tare da ba ta hakuri kan rashin zuwan da ba su yi ba da cewar wani uzirine ya ɗaukeshi
“ba wannan ba tukunna, ya me jikin”?
“jikinta da sauqi sosai hajiya, na barsu da feenat ta dinga ɗebe mata kewa”
“ka kyauta sosai Allah ya ba ta lafiya”
Ameen yace sannan hajiyar ta cigaba da cewa
“yanzu ma amrat ta gama min surutun wai tayi momy ita ma”
Hmmm yace daga nan yayi shiru
“ai ni kaina na ji daɗin yadda na ga yarinyar take ta farinciki, Allah ya albarkaci wannan aure”
Ameen cewar fawwaz a hankali
“toh ban san ta yadda za a fara ba dai fawwaz, ina ga fa dole ka zo a san me ake ciki tsakaninka da ‘yar honourable, ya sake kirana yanzu, me yuwuwa sun ji labarin aurenka a jiya”
A qufule fawwaz yace
“wai ni hajiya dole sai nine zan auri ‘yarsa, haba don Allah hajiya, ni fa bana son zafin kai da damuwa, a barni kawai in ji da wacce nake ciki ma”
“toh…. yanzu dai da ni kake yi kenan”
“a a ba haka bane hajiya amma ni ma..
“
katseshi tayi da cewa
“haka ne mana, idan ba da ni ba da wa kake yi tun da ni nace maka na yarda ka aurosu duka”
“shikenan kiyi hakuri hajiya, zan zo muyi maganar amma don Allah a barni in huta tukunna”
Albarka ta saka masa sannan ta kashe wayar
Jikinsa a mace ya kira nambar feenat domin ya ji labarin jikin maironsa
Wayar bata daɗe tana ringin ba feenat ta ɗaga, a ladabce ta gaisheshi sannan ya mata umurni ta ba wa maryam wayar
Wayyo mairo da infinix ita da ko tecno ba ta taɓa riqewa ba, ba ta ma taɓa yin waya ba a rayuwarta 😂🤣😳
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/17, 3:30 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*32*
Tsorone ya bayyana a fuskar mairo tare da diriricewa na rashin sanin yadda za ta yi da wayar, ba tare da ta karɓa ba ta tsura wa feenat idanu
“ki karɓa mana antynmu, yah fawwaz ne yake son magana dake”
Miqa hanunta tayi yana rawa ta karɓi wayar saidai maimakon ta manna wayar yadda ake yi a kunnenta daidai kan speaker sai ta juya qasan wayar za ta manna a kunnenta, dariya feenat ta gimtse tayi murmushi ta miqa hannunta ta karɓi wayar ta matso kusa da ita ta rufe kan speaker da hannunta tace
“zan buɗe miki muryar a fili, ki nutsu ki amsa wayar da kyau kin ji antynmu”?
Kai ta gyaɗa mata tabbacin za ta yi yadda tace sannan feenat ta ɗauke hannunta akan speaker ta buɗe muryar ta ce “hello yah fawwaz ga antyn”
Sallama ya mata tana jin muryarsa raɗau duk da akan cinyarta ta saka mata wayar, sallamar ta amsa cikin rashin sabo da wayar tana ta zare idanu, qauyanci dai sosai
“maryam ya jikinki”?
Fawwaz yace cikin sanyin murya
“da sauqi”
“sosai”?
“eh”
“mashaa Allah, likitar ta zo”?
“eh ta zo”
“ta miki alluranki”?
“tayi” tace tana kallon feenat da take mata dariyar yadda take amsa wayar
“toh yanzu akwai abin da kike buqatane”?
A a tace cikin gajarta zance, “ina feenat take”?
“ga ta nan”
“toh ba ta wayar”
Feenat da take saurarensu da sauri ta matso tace
“ga ni yah fawwaz”
“yarinyar nan ta ci abinci”
Duk da ta san abinda yake nufi sai tace
“wacce yarinyar”?
Murmushi yayi domin ya san halin feenat sarai da gangan tayi masa wannan tambayar
“maryam” ya ba ta amsa
ɗage gira tayi kamar yana kallonta tace
“oh… Maryam?, eh ta ci saidai ba sosai ba”
“ba ta ci ba dai kenan”
“a a taci saidai kamar yadda na faɗa maka kaɗan taci, ka san amarya wataqil tafi so ta ganta ga ta ga ka sai ta fi jin daɗin ci sosai”
Mairo da take saurarensu waro idanu tayi ta buɗe baki za ta yi magana feenat ta ɗora mata hannu akan libs ɗinta
Shi ko yallaɓai daga can yace cikin ɗaure fuska da murya kasancewar ‘yan rahar sun yi nisa
“keh ina wasa da ke ne?”
ɗaga gira tayi wa maryam tana murmushi tace
“yi hakuri yah fawwaz”
Hmmm yace sannan ya ɗora da faɗin
“toh ki tabbatar ta ci ta qoshi kafin in dawo, kin ji ko”?
“eh yaya, amma ga ta nan ka lallaɓata da kanka za ta fi sakewa ta ci”
“toh ba ta wayar”
Kallonta ta mayar kan mairo ta ɗaga mata gira tana murmushi, cike da mamakin feenat mairo ta masa sallama, amsa sallamar yayi sannan ya ɗora da cewa
“maryam me yasa kika qi cin abinci”
Tana cigaba da kallon mamaki wa feenat cikin rawar murya ta fara faɗin
“a..a…am…na…..”
“no kin gane ne, ki daure ki qara wani abincin kin ji, hakan ne kawai zai sa ki qara samun qarfin jikinki”
Toh tace duk da feenat tana ta kaɗa mata kai amma ba ta gane abin da take nufi ba
“toh sai na dawo ko”
“Allah ya dawo da kai lafiya”
Ameen yace sannan ya kashe wayar, hankalinta ta mayar kan feenar da ta sanya hannu ta ɗauki wayarta tana so ta tambayeta dalilin da yasa take kaɗa mata kai, saidai ba ta samu damar tambayar ba feenat sake motsowa kusa da ita tace
“gaskiya kin kwafsa antynmu, in ni ce ke da ba haka zan yi ba”
Tana murmushi tace
“me nayi kuma da na kwafsa”?
Cike da rigima tace
“ke da kike amarya ai kamata yayi ace kin ɗan kaɗa yayanmu tunda ciwo kike yi”
Sai da ta sunkuyar da kai saboda kunya sannan ta ɗago tace
“saboda bani da lafiya sai kawai in kaɗa shi”?
Lumshe ido tayi tana jijjiga kai yayin da ta mai da maryam tamkar wawiya gurin kallonta tace
“sosai ma kuwa, ba gashi har na yi miki hanyar da za ki rikirkitashi da shi kin kasa yin amfani da damar da kika samu ba”
“wani irin rikirkitashi kuma?, akan me”?
A ran feenat tace wannan kina da matsala amma a fili sai tace
“no ki gane ba rikitawar tashin hankali ba, kin ga kamar yadda na sanar da shi ba ki ci abinci sosai ba kin ga ya damu ko, sai ni kuma nace ya lallaɓaki da kanshi ko za ki ci, toh ke abinda ya dace kiyi a lokacin da yace ki ci abincin sai ki shagwaɓe murya kamar haka ki ce”
“ni fa gaskiya cwthrt bakina baya min daɗi ba zan iya cin komai ba, idan yace ki daure ki ci sai ki sake narke murya ki ce ba za ki iya ba ke kam, ki ce keh ba kya jin yunwa ma kwata kwata, da haka zakiyi ta rikitashi yana lallaɓaki, daga nan idan ya nace sai ki fara kukan shagwaɓa kamar haka kina cewa, toh ni dai gaskiya kaɗan zanci, zai sake cigaba da lallaɓaki domin ki cin ko kuma ya yarje miki ki ci kaɗan ɗin da za ki iya, keh kuma a lokacin sai ki sake cikin murya kamar haka ki kwantar masa da hankali da cewa ya kwantar da hankalinsa zaki ci ɗin, wannan ɗan jayayyar da kuka yi shaquwa zata qara a tsakaninku, ana iya wuni cikin begenki idan kin iya salon hira, ba komai ake amincewa da shi kai tsaye ba a wani lokacin kamar yadda ba komai ake qin amincewa da shi kai tsaye ba a wani lokacin, kin ga ke kika rikita kayanki kuma ke kika samar masa da nutsuwa, shi kawai abin da zai tuna shine ya rikice ke kuma kin kwantar masa da hankali, amma kina amsa wayar miji kamar kina amsa tambayoyi gurin interview”
Toh har gwara wawa akan yadda mairon fawwaz tayi gurin kallon feenat tana mamakinta da kalamanta musamman yadda take rangwaɗa murya cikin salo da iyayi, gaba ɗaya ta gama mutuwar zaune ko qyafta ido ba ta yi
Hannu feenat ta sanya ta jijjigata tana cewa “antynmu”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi yaqe tace hmmm
“mene ne kuma hmmm”? Cewar feenat
“a a ni bance komai ba”
Murmushi feenat ɗin tayi tace
“antynmu kenan, na san yanzu ba za ki fahimceni ba sai nan gaba kaɗan, yanzu kin san me”?
da idanu ta bita alamar tana saurarenta hakan yasa tace
“mu je muyi wanka, kafin mu dawo mu cigaba da hirar, yawwa ki zo ɗakina idan kin yi wankan ki ga wani abu”
Toh tace tare da miqewa ta wuce ɗakinta tana ta mamakim feenat
Sai da feenat ta ga ta shige ɗaki tace
“na gode da damar da kike bani mairoro, gaskiyar ya fawwaz ne kina da sauqin kai duk da a gefe guda kina da ɗaurarren kai”
Juyawa tayi tana murna ta shige ɗakinta ita ma
******
“yawwa antynmu, kin san me za ki gani da nace ki zo ki ga wani abu”?
“sai kin faɗa”
“sana’ar kwalya da ado na fara koya kuma a qa’idar sana’ar kullum sai ka samu fuskar da za ka mata kwalyar domin hannunka ya sake qwarewa”
Da mamaki mairo tace
“kwalyar?, yanzu kwalyar ce ake sana’arta, ko dai kayan kwalyar”
Murmushi tayi tace “kwalyar kuwa antynmu, sana’ace me zaman kanta, sai mutum ya zauna a canza masa kamanni da kwalya kawai, ya qara kyau, keh har hanci sai a ja miki”
Qara girmar idanunta tayi tace “da kwalyar”?
Hannunta ta rataye wuyarta da shi tace “qwarai ma kuwa, amma idan ba ki yarda ba ki ban fuskarki na wasu mintoti daga nan sai ki tabbatar”
“ni?, ba da ni ba” cewar maryam a tsorace
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/22, 12:44 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*33*
*kasancewarki fara, bak’a, koriya, shuɗiya, me kuɗi ko talaka, ba shine damuwata, abin alfaharina shine soyayyarki da na samu, ina qaunarku masoyana har ban san iya adadinta ba, kuna sakani farinciki, domin gano ɗanɗano da garɗin farinciki, kasance da masoyanka, kuna saka ni qara gudu masoyana amma a cikin tseren qaunarku, tare da haka nake sarrafo kalamai daga harshena, tsarawar zuciyata gurin jera muku kalaman barka da sallah, ubangiji ya maimaita mana, ubangiji ya karɓi ibadunmu, ya gafarta mana da iyayenmu da ‘yan uwan mu da ‘ya’yanmu da qawayenmu da abokan rayuwarmu baki ɗaya ameen summa ameen*
*fasaha online writers ina kallonku fa amma a zuciyata😂, hakan yasa kuke kwana cikin tunanina, ina son ku da qaunarku fisabilillah, toh ya take ne?, abin da nake so dai in ce shine barka da sallah, ubangiji ya karɓi ibadunmu ya yafe mana kurakurenmu ameen*
“haba antynmu, don Allah ki ban wannan damar, na miki alqawari babu abin da zai samu fuskarki na cutarwa daga kwalyar da zan gwada a kanki, don Allah antyna”
Feenat ta qarashe maganar har da lanqwashe kai, fuskar nan a marairaice
Roqon da feenat ta mata yasa ta amince duk da har wani harbawa zuciyarta take yi saboda tsoro, nan dai ta sallama wa feenat kanta cikin zuciyarta kuwa tana ta karanta bismillah🤣 meroro
Sai da feenat ta goge mata fuskar sosai da wani ruwan da nima ban sanshi ba, kun san nifa na fi mero qauyanci, saura kuma wata ta min dariya😏
Wayyo Allah, auduga ranar ta ci kakarta a fuskar mairo, haka feenat tayi ta goge damfararriyar dauɗa daga fuskar mairo duk da mairon tana ta yin shshhhsh saboda ɗan raunin da yake kan fuskarta duk da feenat ɗin tana ta kiyayewa saidai tana taɓa ciwon kaɗan saboda zafi shi yake fitar da zafi in ji hausa people😳, wayyo Allahna
Cikin qwarewa ta dinga fenfe fuskar mairo dan ni ban yarda feenat ‘yar koyo bace saboda yadda take tafiyar da tsarin kwalyar, ta dai feqe mairone kawai😂
Gaba ɗaya feenat ta canza wa mairo kamanni da wannan kwalya nata sai wani wal wal tare da dal dal fuskar mairo yake yi, hancinta da ba wani mai tsayi ba tuni ya taso yayi wani shirtaccen kyau, haka bakinta duk da ba girman bakin yake dashi sosai ba sai da feenat ta rageshi ta sake ba shi wani irin shape, yayi tsurut kamar da gaske, don Allah mata a rage yawan acuci, abin har baki ma😂, toh ban san ingancin haka a sharia ba dai, mu nemi ingancin hakan gurin malamai sisters, kar a zo ayi wasan da ba dariya
“waw my anty kin ga yadda al’amarin yake kuwa”
Feenat da take tsaye riqe da qugu a gaban mairo bayan ta kammala mata kwalyarce take faɗin haka
Murmushi mairo tayi tare da girgiza kai domin iya murmushin ta ga za ta iya saboda yadda take jin fuskarta
Juyata feenat tayi ta fuskantar da ita tana kallon mirrow, idanunta ta waro gaba ɗaya cikkn tsananin mamaki da al’ajabi tace “iyeh, feenat nice wannan kuwa”?
Qyalqyale mata da dariya feenat tayi sanna ta dafa kafaɗarta tace
“ke ce mana antynmu”
“gaskiya ni ban yarda ni bace, ki ga nayi haske nayi hanci bakina ma ba haka yake ba, ke dai har girana ma ba haka yake ba”
Cikin ganin qauyancinta ta kama hanunta ta ɗora mata a jikin kumatunta tana cewa “to wannan hanun kuma na waye”?
da sauri tace “nawane mana”
“toh haka fuskar ma take taki, amma idan ba ki yarda ba ki tambayi zuciyarki, idan kin ji yayana a cikinta toh kin tabbatar ke ɗin ce”
Feenat ta qarasa maganar da shaqiyanci irin na qannen miji amma ban da ni😳😏
Kunya ta ji, take ta sunkuyar da kai tana murmushi murmushi tsumewa tsumewa, murmushi feenat tayi tare da faɗin hmmm a ranta tace “qauyanci be yi ba, ko me yi abin jin kunyata ni kuma oho”?
Ni ko nace barta tayi feenat, ya fi a ce ba ta da kunya, domin kunyar yanki imanine, sayyidina usman shi kanshi yake jin kunya ma, ai na san ba kunyar da ta fi wannan ko readers?
A fili kuma tace “toh anty kin ga irin fasahar sana’ata, kuma dole kullum a dinga ban fuska ina qara qarfafa hannuna kan sana’ata saboda ku kuka ɗaukoni, idan ba haka ba ko?, hmm wlh kuka zan yi ta yi har sai kun mayar da ni gun hajiyata”
Yadda ta qarasa maganar cikin shagwaɓa da marairaice fuska yasa mairon darawa sannan tace
“amma ke auta ce ko”?
“ni ba auta bace amma hajiyata tana ji dani kuma tana tarairayata tare da lailayani kamar qwai, shi ma yah fawwaz ya sani ai”
Kallon yadda take rigima da rangwaɗi mairo ta tsayayi sannan tace
“caɓ amma kuwa, qatotuwa da ke kike wannan shagwaɓar kuma ke ba auta ba”?
Gira ta ɗaga mata tace “yes, sosai ma kuwa, ke ma zaki koyi wannan shagwaɓar tawa watarana, kin san a gaban masoyi kawai ake shagwaɓa”
“ba dai ni ba, caɓ”
Dariya feenat tayi sosai tace “yanzu dai jeki ki sanya wani kayan kafin nan nima na shirya sai muyi selfie”
“menene kuma salfi da har sai na canza kaya za mu yi duk da yanzu na saka waɗannan”??
“ke dai ki je ki dawo za ki ga selfie ɗin, abin da yasa nace ki canza kayanki wannan kwalyar ba ta dace da na jikinkin bane, cikin kayan da na kawo miki akwai wata baqar doguwar riga me kwalyar fararen stones a baya da gabanta, ki ɗauketa, za ta fi zama a jikinki, idan ba ta miki ba ki ɗauko multi colour ɗin nan za ta miki kyau ita ma”
Tashi tayi ta fice daga ɗakin zuwa ɗakinta, bincike kayan da feenat tazo mata da shi ta farayi, baqar rigar ta ɗauko ta sanya a ranta ta fi son ta sanya multi colour ɗin saboda sunanshi da ta ji daban saidai bata san wanne bane😂
Toh waini turancin dolene, ki ce rigar me kaloli da yawa mana a jikinta feenat, au kar dai nima na fi mero kwafsawa🤣
Yadda rigar ya zauna mata a jiki yasa na sake gaskata gudun qwaqwalwar feenat, na san lokaci ba zai ja da yawa ba za ta canza mana mairo, saidai fa yadda ta damqe kai da ɗan gyalen da aka haɗasu da kayan abin sai wanda ya gani, ko huhun goro dai aka yi wa wannan ɗauri auren da aka ɗaura da shi zai yi nisan kwana😂
Feenat da fitowarta falon kenan mairo ma ta fito tashi tayi cikin rigima tace
“wow antyna, kina wuta, wannan ruwan kyau haka, gaskiya Allah ya jiqan yayana yau”
Ba tare da mairo ta shirya ba ta qyalqyale da dariya ganin yadda feenat takeyi har da kaɗa hanu,
“feenat kenan” tace bayan ta tsagaita da dariya
“um mana, gaskiyata na faɗa ai, yanzu ma bari in sake gyara miki gyalen ki gani yadda za ki rikita tsohon amrat”
Ba ta musa ba ta barta ta janye gyalen daga kanta ta matso kusa da ita ta fara naɗa mata gyalen irin na ‘yan uwan ‘yan gayu
“bari in je ɗakina in zo antynmu”
Cewar feenat
Gyaɗa mata kai tayi tana murmushi, cikin qanqanin lokaci feenat ta dawo riqe da wani abu a hannunta mai ɗan banzan sheqi, sai da ta maqala wa mairo a jikin gyalen na fahimci fin ne irin me duwatsunnan, nan fa mairo ta qara haskawa tamkar tauraruwar nan surayya
Matsawa jikinta tayi ta zauna tana cewa
“duk abin da zance ba za ki gane ba sai daga bakin yayana, muyi selfien kawai, idan ya dawo zaki ji matsayin kwalyarki, oh kin ce ba ki san selfie ɗin ba ko”?
Ta qarasa maganar tana kallon cikin idanun mairo, kai ta gyaɗa mata tana murmushi
“ok toh bari ki gani” saita camerar wayarta tayi a kan fuskarsu tana murmushi ta umurci mairo da ta yi murmushin ita ma
Hotuna ta musu kala kala sannan ta tashi ta dunga nuna wa mairo style ɗin ɗaukar hoto tana ɗaukanta, har sai da ta gaji sannan suka zauna suna duba hotunan, mamakin kyau da tsarin da mairo ta ga tayi a hoto take tayi tare da santinsu
Ba tare da sun ji jiniyar motoci ba kawai sai ji sukayi an turo qofar falon, da sallama ya shigo cikin tafiyarsa mai kama da tsalle2 sauri sauri, feenat ce ta amsa masa tana murnar ganinsa yayin da ita kuwa mairo tana ganin shine ta sunkuyar da kai tana murmushi abinta
Har zai wuce ba tare da ya dubi inda suke ba sai kuma ya juyo da hankalinsa kansu, karaf idanunsa suka sauka akan fuskar mairo, girman idanunsa ya qara cikin aji daga gani ba sai ance ya sha ruwan mamaki da ganin fuskar maryam ba
A nutsattsen taku ya qarasa kusa da su ya nemi guri kan kujerar da yake fuskantar mairo ya zauna yana kallon fuskarta
A hankali ta ɗago fuskarta sakamakon matsa hannunta da ta ji feenat tayi, kaɗa mata kai tayi tare da qyafta ido
Ni dai nace akwai wata a qasa emmata, cikin jin kunya mairo ta rufe fuska ta tashi a gurin da sauri tayi cikin ɗakinta
Da kallo ya bita har ta qule ɗaki, bai san lokacin da yayi murmushi ba sannan ya dawo da kallonshi kan feenat yace “wannan aiki haka feenat da zafi zafi, ni na ɗauka zinariyace take sheqi a gefenki”
“kai yah fawwaz, gaskiya kana ji da antynmu, wannan koɗawa haka”
Jijjiga qafa yayi tare da miqewa tsaye yana cewa “toh ba dole ba feenat, amaryace fa”
Murmushi tayi tana faɗin hakane yah fawwaz, har zai murɗa qofar ɗakin ta ɗaga murya ta kirashi, juyowa yayi tare da amsawa, da sassarfa ta qarasa kusa da shi ta rage murya tace “yah fawwaz ka yaba don Allah, hakan zai taimaka sosai gurin samun cigaba”
Murmushi yayi yace “toh mama feenat zanyi, ko akwai wani umurnin”?
Da gudunta ta juya sai ɗakinta saboda kunyarsa da ta ji
Kai ya kaɗa tare da tura qofar
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/23, 3:49 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*34*
*wannan page kyakkyawan sadaukarwane zuwa ga taurarina, Aunties ɗina, Anty Ruky maman Abdjjl, Anty Hauwa S. Zaria, sai Anty Aisha garkuwa, Allah ya tsare min ku fulanin asali, daga kiran sunanku sai na ji qamshin nono, don haka a madadina da bakina da harshena da zuciyata muna me farincikin sanar da ku zuman sallata ba nama bane, abin da nake so kwasam da shobbel, ina nan zuwa jalingo da adamawa, wayyo Allah ya sa na faɗa daidai😳, domin karanbani na yi, miwala fulfulde ko saɗɗa😂🤣*
Tsaye ya sameta a tsakar ɗakin kamar tayi wa sarki qarya yayin da ta ɗago kanta ta kallon bakin qofar jin ya shigo
Yadda ya tsaya yake kallonta yasa tayi saurin sunkuyar da kai cike da kunya, ga wani irin nauyinshi da ta ji ya rinjayi zuciyarta, ji tayi ta tsargi kanta da kwalyar fuskarta
Fawwaz da yake tsaye yake kallonta ko mai ya tuna oho, da sauri ya juya tare da buɗe qofar ya fice, bai ɗau lokaci ba ya sake turo qofar ɗauke da sallama a bakinsa, kasancewar shigowar da yayi ta farko bai yi sallama ba hakan yasa ya zargi kansa ya koma ya sake shigowa
Hakan ya kamata maza su dinga yi a gidansu, rashin sallamar maigida a kan iyalensa matsalace da take taka muhimmiyar rawa gurin kawo matsala a cikin gida, idan ba a yi sa’a ba har aure ya kai ga mutuwa, sheɗanu suna amfani da wannan daman gurin wargaza rayuwar ma’aurata amma ba kowa yake ganewa ba, an taɓa yin wata ruqya a gabana da ya ɗaga min hankali, matar da mijinta auren soyayya suka yi, yana ji da ita tana ji da shi amma gagarumar matsala ta afka musu a dalilin rashin sallamar maigidan, idan ya tashi shigowa gidan zai shigo rai cunkushe wai shi boss, sannan ba a damu da wani adduoin neman tsari ba, aljanun suka ce hakan yasa suka shige jikin matar da mijin, gallazawar farko shine cututtuka da suka zuba a jikinta, sai gallazawa ta biyu zuciyar mijin da suke shiga duk lokacin da ya shigo gidan su sanya masa tsanar matar da jin haushinta, komai faɗa komai masifa, ba tausayi amma daga zarar sun bar gidan sabuwar soyayya zai tashi da tattali, karon farko abin da suka faɗa kenan a gurin ruqyar ba ya sallama shiyasa suke biyoshi su shiga zuciyarshi su ɓata ta a gurinshi, to ‘yan uwa me ya jawo haka?, a second biyu kawai fa ka gabatar da sallamar nan, kuma mace duk rashin kunyarta idan ka tsare iyakokin Allah wallahi bata isa ta taka ka ba, sallama ba zai zama janyo raini ba, ha ah to ban gane ba, sallamane zai janyo maka raini a gurinta ko kwanciya da kake yi da ita a matsayin matar aure, ko za ka iya haqura da ita a matsayinta ta matarkace saboda kar ta rainaka, ka dai tambayi kanka, yah Allah ka shiryar da mazaje da matayen musulmi ameen
Amsa masa sallamar tayi cikin sanyin murya sannan ta ɗan kalleshi tace masa sannu da dawowa
Bai amsa ba sai taku da ya fara yi ɗaya bayan ɗaya yana kusanta kansa zuwa gareta fuskar nan ɗauke da tsaro kamar zai kama me laifi, ita kuwa mairo da taga yanayin fuskarshi gashi yana kusantota sai ta fara ja da baya a hankali cikin dabara, ni ko nace yau ake yinta, bari dai in ga abin da zai kasance domin idan ba shirin duka ba toh wataqil shaqeta zaiyi😳
Cogewa tayi a jikin labulen windon ɗakin domin gudu dai ya qare, shiko fawwaz da ya ɗaura fuskar damisa wa fuskarsa tsayawa yayi a gabanta ya zuba hannu cikin aljihu ya cigaba da qureta da idanu ba tare da yace komai ba kusan minti biyu, hannunsa ya ɗaga ya kai fuskarta, ita ko maryam da ta saka tsoronsa a ranta sai tayi sauri ta ɗaga hannu za ta kare fuskarta, zuciyarta sai harbawa take, nan take ta fara zantuttuka da zuciyarta
“ashe da gaske sojoji suna dukan matansu?, toh ita me ta masa zai mareta?, ko gudowar da tayi ɗakine ya ji haushi toh”?
Ba ta qididdige tunaninta ba taji ya kira sunanta, a hankali ta fara ɗauke hannunta daga kan fuskarta tana ɗago fuskarta, idanunta a birkice take kallonsa cike da tsoro
Kai ya girgiza mata sannan ya sake ɗaga hanunsa bai dire a ko ina ba sai kan fin ɗin da aka maqale gyalen da shi, ɗayan hanunsa ya sake ɗagowa ya taimaka wa damanshi gurin zare fin ɗin
Mairo da take tsaye take sauraron abin da zai yi zuciyarta ce ta cigaba da bugawa da qarfi, shi ko gogan naku jujjuya abin yayi a hannunsa sannan sake matsawa kusa da ita ya gyara zaman gyalen sannan ya maqala mata fin ɗin qasa kaɗan daga gurin da feenat ta sanya mata, hannayensa ya sake zuba wa a aljihunsa ya qureta da idanu sannan yayi murmushi cikin ɗayar muryarsa yace
“maryam ba kyau kaɗai kika yi ba, har sheqi kike yi kamar adanannen zinare, gaskiya na yaba”
Wayyo qauyanci bai yi ba, wai dan ma sunanki maryam, diriricewa tayi cikin ɓacewar sahihiyar amsar da ta dace ta bashi daga qwaqwalwarta da zuciyarta
Ba tare da ya nuna damuwarshi da qauyancin da ta nuna ba ya ciro wayarshi ya saita camerar kan fuskarta zai ɗauketa a hoto, ita kuwa dillaliyar qauyanci sai ta rufe idanunta, maimakon hoton yayi muni sai ma ya fi kyau akan waɗanda feenat ta ɗauketa, guda uku kawai ya ɗauka ya mayar da wayar aljihu yana murmushi yace
“yanayinki ya nuna min cewa jikinki da sauqi sosai, tunda ga shi har kin yi ado wa angonki ko”?
Sai a lokacin ta sake fuskarta har tayi murmushi sannan ta rufe fuskar da tafukan hannayenta
“idan kin san akwai wata matsala toh ki sanar min kin ji, idan kuma babu to ki cigaba da shan magungunanki akan qa’ida”
toh tace ba tare da ta ɗago kai ta kalleshi ba, shima bai sake cewa komai ba ya wuce zuwa qofarsa ta jikin labule ya buɗe ya shige
Zaune suke a qasa su uku a falo suna cin abincin dare, fawwaz rabi cin abincine rabi amsa waya don haka kaɗan ya ci ya miqe ya bar gurin yayi cikin ɗaki
“antyna kin san me”?
Hankalinta kwacokam mairo ta miqa wa feenat tana girgiza kai alamar a a
“wannan irin kwalyar ta fuskarki ba a bacci da ita, dole kafin ki yi bacci kiyi wanka ki wanketa tas, ke kanki sai kin fi jin daɗin baccin, daga nan sai a yi kwalyar kayan barcin wa yayana”
Cikin jin kunya ta amsa da kai domin ba za ta iya da surutun feenat ba, amma yaushe za ta yi wani kwalyar kayan bacci wa yayanta, matuqar irin kayan jiyane ai har abada bazan masa kwalyarsa ba, tace a ranta 😳😂🤣
“yawwa antyna, yanzu ni dai barci nake ji kin ga tafiya, sai mun jone da safe”
Tashi feenat tayi ta barta a gurin ganin haka itama ta tashi tayi ɗakinsu, wanka ta shiga ta dirje fuskarta sosai sannan ta fito ta sanya kayan barci ta bi lafiyayyen gado ta fara lumshe idanu, tuni nutsattsen barci ya ɗauketa, duk abin da takeyi fawwaz na kallonta, damma mairon mairon qauyece da yayi kalle kalle da yawa amma iya ɗakin da yake iya kallonta a ciki, babu abin da tayi wanda bai gani ba, sai da ya tabbatar tayi barci sannan ya taso ya rufe na’urar tashi ya buɗe qofar ya fito, daidai kanta ya tsaya ya tofeta da adduoin neman tsari sannan ya juya ya koma gurin da ya fito
Baqar suit ce sanye a jikinsa yayin da mairo ta sanye da ɗinkin riga da zani, tayi kyau sosai cikin jan atamfar kamar ba mairo ba, gaba ɗaya feenat ta zazzage mata ilimin kwalyarta a kanta
Waya yake yi da antyn raudat yayin da idanunsa suke kan maryam
“na tura a ɗauko su muma yanzu zamu zo amma matuqar matar nan ko ‘yarta suka biyosu to tabbas a komawa zan sa a saukesu a jeji, ah toh motocina na ɗaukan mutanene kawai”
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/25, 12:53 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*35*
“wacce matar kenan”?
Kai tsaye yace
“haule mana”
“amma ina fata ba a gaban yarinyar kake faɗin wannan kalamai ba, ka dinga tuna cewa fa ita ma mahaifiyarta ce”
“Allah ya sauwaqe, ta je can ta nemi ‘yarta da ta haifa ba dai wannan ba”
“ai kuwa ko a addini ita ma mahaifiyarta ce domin irin seat ɗin da mahaifiyarta take da shi a gurin mahaifinta haka ita ma wannan take da shi, ka ga kuwa dole ka mutuntata a matsayinta ta mahaifiyar matarka”
Haɗe rai yayi kamar antyn raudat ɗun tana gabanshi yace
“addinin da kika zo da shi kenan, toh bari ki ji, maryam dai matatace, ni ke da iko mai qarfi a kanta kuma ina da damar cewa babu wanda zai ganta, kuma dole, tilas a hakura da abin da nace, kuma ita da nake shirin ɗaureta ma ne za ta zo yi a gidana”
Sai jin muryar hajiya yayi tana cewa
“toh sannu mai mata, ka ji nace sannu, kul ka kiyayeni na faɗa maka, ka rabani da wannan zafin zuciyar taka, ko da wasa kar na sake jin waɗannan maganganun a bakinka, idan ba a ce mahaifiyarta bace a ce wacece?, to ko ma dai menene idan ka tozartata ka tozarta mahaifin matar taka sirikinka kuma, ita kanta yarinyar sai ta ji ciwon hakan idan baka sani ba, ko da wasa ban yarda ka sake zaginta a gabanta ba, na faɗa maka”
Ran nan a ɓace yace “shikenan sai mun zo”
Wayar ya jefa a aljihunsa ya kalli maryam yace
“ki fito mu tafi”
Yana faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin, kujera ya nema cikin kujerun falon da yake kusa da feenat ya zauna ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana girgiza qafa
Yadda feenat taga fuskarsa a tamke yasa ta tashi cikin tsoro da dabara ta koma kujerar nesa da shi sai satar kallonshi take yi
Ita ko mairo da take tsaye cikin sanyin jiki ji tayi hankalinta ya tashi da irin yanayin da ta ga fuskarshi, musamman kiran sunanta da taji yayi a wayar tana da tabbacin fushinsa yana da alaqa da ita,
Cikin sanyi da mutuwar jikin ta ɗauko gyale ta yafa ta fito tana ta kici kici da gyalen tana yafashi yana zamewa, ko takalmi babu a qafarta
Yadda feenat taga tana yi yasa cikin tsautsayi da rabon ayi tace
“antynmu ba da wannan gyalen ya kamata ki haɗa wannan kayan ba, ki je ki canza”
Kallonta tayi cike da rauni sannan saci kallon fuskar gee fawwaz tace
“toh da wanne zan haɗa”
Ruɗewar da ta karanto a fuskarta yasa tace “mu je na zaɓa miki wanda zai fi kawo wuta”
Toh tace tana yi tana cigaba da satan kallonsa
Har sun juya za su shige ɗakin suka ji muryarshi cikin tsawa yana cewa
“keh wa ya baki izinin shiga min ɗaki”
Dukkansu sun firgice amma dukkan alamu sun nuna mairo ta fi tsorata saboda yadda ta qanqame jikinta, cikin rawar murya feenat tace
“babu”
“to ban son raini, kin ji ko ba ki ji ba”
Da sauri tace “naji”
Daga ita har mairon ya banka wa harara sannan ya tashi ya riqo hannun mairon yayi cikin ɗakinsu sannan ya saketa, da saurin ta matsa nesa da shi
Yadda ya qureta da idanu yasa ta sunkuyar da kai cikin tsinkewar zuciya
“baki ji abin da na ce ba ko”
Kai ta ɗago tana girgizawa idanuwanta taf qwallah
Qarasowa yayi gabanta cikin masifa yace
“toh me yasa kika kika mata izinin shigo min hurumina”?
Yadda yayi maganar yasa ta sunkuyar da kai hawaye har ya fara ambaliya, cikin muryar kuka tace
“ka yi hakuri”
Hawayen da ya gani yana tsiyaya daga cikin idanuwanta ya sanyaya masa jiki da zuciya, haɓarta ya tallafo cikin sanyin jikin
“kuka kike yi?, ki daina saurin kuka irin haka, kina tare da wanda zai amintar da ke ne ba wanda zai cutar dake ba, ni kawai na faɗi abin da bana so ne duk kuma a kanki nayi hakan amma ba za ki gane yanzu ba, ke dai ki kiyaye kin ji”
Kai ta kaɗa masa tana matsar qwalla, hankyn da ya ciro daga aljihunsa ya fara share mata fuska da shi yana murmushi yace
“kin ga har kin ɓata kwalyarki da hawaye, yanzu dai bari na zaɓo miki takalmi da gyalen sai mu je feenat ta sake gyara min amaryar tawa ko”?
Da sauri ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, abin mamaki su fawwaz har da dariya sannan ya wuce ya fara binciko mata takalmi da gyalen yana cewa “yau zamo taho da sauran kayayyakinki ma daga can, ni ban ga amfanin zamansu a can ba, ko kuwa”?
Shiru tayi ba tare da ta bashi amsa ba, shima bai sake magana ba ya zuba mata takalman a gabanta ya mata umurni da ta sanya sannan ya yafa mata gyalen, duk yadda ya so gyalen ya zauna ya qi har dai ya gaji yace
“anya maryam ba gurin feenat ɗin zamu tafi ba kuwa, kin san abinka da tsohon gwauro, har na manta yadda ake yi”
Murmushi tayi cikin jin kunya ba tare da ta ce komai ba, hannunta ya riqo suka fice daga ɗakin, ba su samu feenat a falon ba dan haka kai tsaye qofarta ya je ya tsaya yana qwanqwasawa, tana buɗe qofar ya wanketa da murmushi yace “qanwata ina neman afuwa kin ji, ga antynki idan kun gama sai ku fito mu tafi”
Yana gama faɗin haka ya juya tare da neman guri a falon ya zauna
Tsab suka fito ta qara gyare maryam tare da ɗora mata gyale ɗamas a kafaɗarta kamar gwanar abin
Basu tsaya ɓata lokaci ba suka wuce gidan hajiya cikin jerin motocin fawwaz ai kuwa sai baza jiniya suke yi a hanya har suka isa gidan
Hannunta cikin nasa suke takawa zuwa cikin gidan yayin da feenat take binsu a baya
Hajiya da tun jin shigowar motocinsa ta fara farinciki da murnar ganin matar ɗanta da za ta yi fitowa tayi daga can cikin ɗakinta ita da antyn raudat suka zo tarɓarta a babban falon gidan
Suna shigowa hajiya ta tashi ta rungumota tana cewa
“oyoyo da amaryar autana, oyoyo da maryamuna”
Ita ko maryam cikin jin kunya ta fara zamewa daga jikinta amma duk da haka hajiya bata saketa ba sai da ta zaunar da ita kan kujerar kusa da ita itama ta nemi guri ta zauna, qasa mairo ta zame tana gaisar da hajiya da antyn raudat, cike da farinciki suke amsa mata tare da yaba wa hankalinta domin sunyi sunyi ta hau kujerar ta qi yarda sai ma tukuikuye fuska da tayi da gyale
Gaisawa fawwaz sukayi da hajiya da yarsa sannan feenat ma ta gaishesu bayan ta nemi guri kusa da qafafun hajiya ta zauna tare da ɗaura kanta a kan cinyarta
“feenat baqin gidan gona, ya aka yi”?
Cewar hajiya tana shafa kan feenat
“lafiya lau hajiya, ina babyna”?
“babynki tana school feenat, tun jiya labarin sabuwar momynta yaqi qarewa”
Ta qarasa maganar tana mai da hankalinta kan mairo tana dariya
Kafin wani lokaci tuni ma’aikatan gidan sun shimfiɗe wani haɗaɗɗen carpet a qasa kore shar a tsakiyar falon sannan aka kewaye gurin da duk wani nau’in kayan marmari masu saurin fisgar hankali, abin burgewar kuma sai waɗansu qananan abubuwa kamar kofunan zinare da aka jerasu a kusa da carpet ɗin sai fitar da wani rin daddaɗan qamshi mabanbanta sukeyi,
Antyn raudat ce ta kamo hanunta ta je ta zaunar da ita kan wani abu na musamman me laushin gaske kalar jikin ɗawisu, bismillah ta mata tana mata umurni da ta fara cin kayan alfarmar da aka tanadar dominta
Duk yadda akayi da mairo ta ci taqi ci sai ma sunne kai da take tayi kamar mummunar amarya,
“haba antynmu, ko kaɗan ki ci mana, sai kin ci fa hajiya za ta ji daɗi, don Allah ki ci”
Feenat kenan me faɗin haka, miqewa fawwaz yayi daga kan kujerar da ya zauna yana cewa “wa yace miki ba za ta ci ba, ko san takurawa mutane kawai”
Zama yayi shima akan carpet ɗin yana fuskantar mairo, haɗa idanu suka yi da shi yana mata murmushi yace “maryam ki ci duk abin da ya miki kin ji, idan kuma kin qoshi toh zaki iya tashi, ko jikinne”?
Cikin rashin sanin amsar da zata bashi ta gyaɗa kai tana cewa eh
Cokalin fork ya ɗauka ya soka jikin wani gutsiren kankana sannan ya kalleta yace “ok ci wannan sai ki je ki huta” ta so yin gardama amma yadda ya tsareta da idanu yasa ta miqa hanu ta ɗauki wani gutsiren kankanar ta kai bakinta ta fara taunawa cikin nutsuwa bayan ta sunkuyar da kanta, cikin salonshi ya sa ta dinga cin abubuwa amma dai a kunyace take saidai tana tsoron masa musu kar ya ji haushi irin na ɗazu, shi kuwa goga na mairo sai murmushi yake mata abinshi
Hajiya kuwa suka ɗauke hankalinsu daga kansu suka yi ta hirarsu, ana haka suka ji wayar fawwaz tana zuba qara
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/28, 9:21 AM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*36*
“yallaɓai sun qaraso”
Abin da aka faɗa masa kenan bayan ya ɗaga wayar
“idan kun tabbatar da babu wata matsala ku shigo da su sai a musu jagoran zuwa cikin gidan”
“babu wata matsala yallaɓai, mun gama bincikenmu”
“yayi kyau, toh ku bar motocin su shigo”
“ok sir” aka ce a ɗayan ɓangaren sannan suka ajiye wayoyinsu, maimakon fawwaz yace baqin feli sun qaraso sai ya ja bakinsa yayi shiru yana zaune gaban maryam yana qara jan hankalinta akan cin fruit ɗin
Sallamar mutane suka jiyo da hayaniyarsu a bakin qofar, kafin su kammala tunaninsu akan cewa su ɗin su waye sai ganin mata sukayi suna shigowa cikin falon, ba tare da sun sha wata wuya ba suka gano cewa baqin feline suka qaddamo domin a tsarin ba lallai bane mutane irin na badiya su ɓoye kamanninsu wa me kallonsu
Wayyo qauyanci an qaiqayaka ba laifi a wannan lokaci, gabaɗayansu kallon gidan da tsaruwarsa ya rikirkitasu har ya ɗauke hankalinsu dags yin abin da ya dace a matsayinsu na baqi a gidan, sai can ragowar masu hankalin cikinsu suka nemo nutsuwarsu suka zube a qasa suka fara gaishe da su hajiyar fawwaz
Feenat kuwa ganin tayi tayi dariyar da take ji ta koma ta qi sai ta tashi ta bar gurin ta shiga ɗakinsu na ‘yammata a gidan hajiyar ta dinga kwasar dariya ita kaɗai
Hajiya ko cikin sakun fuska suke amsa gaisuwarsu tare da mutuntawa, abun haushi duk cikinsu babu wanda ya gano maryam da take tare da fawwaz akan shimfiɗar alfarmar nan sai ita da take ta kallonsu kamar wawiya, ita ɗinma ba dukkansu ta gane ba, ta dai san waɗanda ta sani, musamman baba uwandi da qawayenta na gidan malam sai Abula da indo da suka biyo ayarin, amma wasu kwata kwata bata sansu ba balle matsayinsu a gurinta yayin da wasu kuma ta sansu saidai ta mance ranar da ta ga waɗannan fuskokin
Kallonta ta mayar kan fawwaz ganin sun sarqe idanu yasa tayi saurin duqar da kanta qasa, so take ya mata izinin tashi daga gurin ta je ta gaishe da baqin amma tana tsoron faɗin hakan a gareshi saboda gudun yin laifi
Yanayinta yake nazari cikin kallonta da yake yi, shi dai yana da saurin fahimtar abubuwa daga cikin ɗabi’un mutane don haka ya harbo jirginta, tuno hirarsu da malam na farko a kanta yayi take ransa ya ɓaci, bin jama’ar gurin yake da kallo a ransa yana cewa
“yanzu duk waɗannan suna nan suka bar yarinyar nan ta shiga quncin rayuwa, amma yanzu kalli yadda suka yi zuga wai sun zo kallonta”
Tsaki ya ja qasa qasa amma mairo da take kusa da shi ta ji hakan yasa tayi saurin ɗagowa takalleshi, shima ita yake kallo cikin haɗe rai sannan ya ɗau wayarshi ya kira wata nan ba
Muryarsa sosai ya buɗe yana amsa wayar har da dariya yayin da ya ɗauko hankalin baqin da su hajiyar kansa, sai da ya tabbatar duk hankalinsu ya dawo kansa domin yanayi yana satar kallonsu sannan ya dakata da wayar ya kashe ya mai da hankalinsa sosai kan maryam ya fara zabga murmushi, ita ma kuwa an ci sa’a mamakin kalar murmushin nasa ya qamar mata da idanunta a kanshi
“maryam mu je mu gaishe da baqin ko, ko ba ki qoshi ba”?
Ya faɗa a hankali sosai still murmushin nan yana kan fuskarsa, ba ta yi magana ba sai kaɗa kai da tayi, duk da ya fahimci ta qoshi take nufi amma sai ya nuna bai fahimta ba ya ɗauko inabi ya kai bakinta yana cewa
“ci wannan toh sai mu je”
Kau da bakinta tayi gefe kunya duk ya dabaibayeta tace cikin muryar da ta wuce motsin leɓe da kaɗan
“na qoshi fa”
“da gaske”?
Kai ta kaɗa masa tana me tabbatar masa da abin da ta faɗa “ok maryam mu je toh, ko sai na ɗagaki”
Da sauri ta yunkura ta tashi tana faɗin a a, yayin da shima fawwaz ya miqe tsaye yana murmushi idanunsa na kanta
Suko qauyawiyuna idanuwansu kamar za su zazzago saboda abinda suke kallo, lamarin yayi tsauri ga waɗanda suka san maryam farin sani musamman ‘yammatan qawayenta da ‘yan gidansu, mamakin ganin mairo suke cikin sauyawar kamanni daga kwana biyu, a hakan ganinta suke kamar wata sarauniya, sai sheqi suka ga tana musu, ga wannan shimfiɗa kuma da ta taso daga kai kamar shimfiɗar sarauniya a fadarta
Har mairo ta qaraso cikinsu ta zauna kusa da jamilar malam ladan basu san ta qaraso ba, sai da ta fara gaishesu sannan suka dawo da hankalinsu jikinsu suka fara amsawa
Kaf ta gaishesu hanunta na cikin na jamila, ku zo ku ga qauyanci da gidadanci lokacin da mairo take gaishe da indo, haka ta dinga abu kamar wata haka-haka, Abula tun ba a zo kanta ba take ta gaishe da mairo, dole ta sa mairo raba hankalinta biyu tana amsa wa Abula gaisuwa kuma tana yin tata gaisuwar
Shima fawwaz haka yayi ta binsu da ɗaiɗai yana gaishesu, sai washe baki kuwa ake yi kamar gonar auduga, miqewa yayi ya shige cikin gidan abinshi bayan ya kalli mairo ita ma kuwa aka yi sa’a hankalinta na kanshi, murmushi ya mata kafin ya wuce
Wata daga cikin baqince ta ranqwafa daidai kunnen na kusa da ita tana cewa
“hama amma ba dai wannan bace ‘yar gurin Ibrahimu ba ko”?
“ita ce mana, wallahi ita ce wannan, kin san na je feli wata ɗaya da suka wuce”
“lallai hama wannan yarinyar Allah ya kawota aljannar duniya, ki ga arziqi hama kamar ana ruwansa a gidan nan, caɓ ina Ameena a wannan duniyar ta ga matsayin da Allah ya kai ‘yarta, ai ni hama ina ganin na samu abin alfahari duk da ba ‘yata bace”
“lallai tabai, to ni kuwa ai yanzu na ga abin alfahari tunda uwarmu ɗaya da ubanta, ke kuwa ai daman be dace ki zaqe ba tunda ba ɗakinku ɗaya da uban yarinya ba”
Haushi maganar hama ta bai wa tabai don haka ta harareta tace
“ke da kuke ɗaki ɗaya da ubantan me kika taɓa tsinana mata”?
Baqar maganar da hama ta mulmulo za ta faɗa wa tanbai ta haɗiye sakamakon daqwalen kaji da taga an sauke a gabansu da sauran abubuwan ci da sha, tuni suka yi tsit suka zubar da makaman yaqinsu suka fara hankaɗawa babban birnin tarayya😂
Ganin haka suma su hajiyar suka bar falon suka yi cikin gidan domin su basu damar sakewa
Kamar mairo za ta yi kuka tace wa baba uwandi
“baba uwandi idris”?
Sai da ta haɗiye madannin A da yake bakinta sannan tace
“idris yana gida mairo, yayi ta kuka wai zai biyo mu malam yace ba yau ba”
Abula ba a tambayeta ba tayi tsagal ko santin naman kaza ne oho tace
“baba haule kuwa tun jiya take ta dukanshi wai yayi mata shiru ko ta karyashi da duka”
Mairo tana jin haka ta fashe da kuka tare da kifa kanta
“ke Abula kina da hankali kuwa, wa yace miki ta dakeshi, shi da yake gurin malam, yi shiru ki rabu da ita mairo, babu wanda ya taɓa idris, kukan rashinki kawai yake yi, uwandi ta qarasa faɗa tana mai da hankalinta kan mairo
Maimakon mairo tayi shiru sai ma qara gudun kukanta da tayi domin ta tabbatar ba qarya Abula tayi ba saboda duk rashin kunyarta ba ta cika qarya ba
“subhanallahi, yanzu ke wannan yarinyar kina cikin irin wannan daular kike kuka?, me ya miki zafi haka”?
Yar baban maironce ke faɗin haka tana turmushe naman kaza a bakinta, zainaba yar ameena ce tace
“ba dole tayi kuka ba, yara su da gidan ubansu an mai da su bayi, sai yanzu da Allah yayi wa yarinyar walai shine ko wani matsiyaci zai ɗebo qafa ya nemi inda take”
Nan dai suka fara jefe jefen maganganu a tsakaninsu kowa so yake ya nuna mairo tashi ce, sai da baba uwandi ta dakatar da su ta hanyar nuna musu nan baqon gurine, ita kanta mairo sai a hayaniyarsu ta fahimci matsayin wasun a gurinta
Hhhh takwara kice dukkansu gayyar tsiyace gayyar…..
Jamilace ta fara rarrashin mairo tana bata hakuri, har da share mata hawaye
Duk abin da sukeyi fawwaz yana kallonsu, wayarsa ya ɗaga ya kira feenat yace ta zo ɗakinsa
Cikin nutsuwa ta turo qofar tare da sallama, tsaye ta sameshi a falonshi yana kallon hoton safiyya, hoton ita ma ta kalla sannan tace “yah fawwaz gani”
Ba tare da ya ɗauke kanshi daga kan hoton safiyyar ba yace
“ki je ki zo min da maryam”
“um….yah fawwaz”
Tarar numfashinta yayi da cewa
“bana son abin da zai ɗaga mata hankali balle wani zazzaɓin ya sake taso mata, ki je ki zo min da ita, gaisuwar ta isa haka, ai sun ganta”
Toh tace sannan ta juya ta fice
Sai da ta sake gaishesu sannan ta matsa kusa da maryam murya qasa qasa tace
“antynmu yaya fawwaz yana kiranki, taso mu je”
Share hawayen tayi ta ɗago ta kalli jama’ar gurin sannan ta miqe a kunyace tace wa jamila da take kusa da ita tana zuwa
Har ɗakin ta kaita sannan ta juya ta fice kuma har yanzu shima yana tsaye
Juyowa yayi yana kallonta hannayensa duka suna cikin aljihunsa
“maryam” cewar fawwaz, amsawa tayi tana kallonsa
“zo nan” kasancewar suna nesa sosai ta fara takowa zuwa kusa da shi, sai da tazo gab dashi sannan ta tsaya tace masa “gani”
Gefenta ya zo ya tsaya ya mai da hankalinsa kan hoton safiyya yana cigaba da kallo, gurin da yake kallo mairo ta kalla sai idanunta ya sauka kan hoton safiyya da take ta zabga murmushi cikin fararen qananan kaya, kyakkyawace fara tas, gurin da ta san me irin fuskar take son tunowa saidai kafin ta tuno taji muryar fawwaz yana cewa
“maryam ba zan tambayeki me yasa kike kuka ba, saboda nima ina da irin ciwon da yake ranki a raina, maryam….rashin wani muhimmi a rayuwa tashin hankaline, musamman mahaifiya”
Wani irin yanayi ta ji a jikinta sakamakon hannun fawwaz da taji akan kafaɗarta, da yatsarsa manuniya ya nuna mata hoton safiyya yace “maryam kin ganta, safiyya kenan, da hannuna na raineta da ta girma na aureta, har ta haifa min amrat sannan ta bar duniyar maryam” kallon cikin idanunta yayi hawaye taf idanunsa yace…..
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/29, 4:18 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*37*
“maryam zuciyata tana min wani irin ciwo a duk lokacin da na tuna da cewa na rasa safiyya a wannan duniyar, amma hakan ba yana nufin ban yi tawakkali bane, saidai ba zan iya dakatar da zuciyata ɗanɗanar wannan ciwo bane saboda bani da iko, alhamdulillah ina godiya wa ubangijina da ya ba wa idaniyata damar kwaranyar da hawaye domin sauqaqa wa zuciyata raɗaɗin da yake addabarta”
Sosai ya qoqarta gurin mai da qwallar da take shirin zubo masa saidai idanunsa sun rikiɗe sun koma ja kamar gaushi sannan jijiyoyin kansa sun yi ruɗu ruɗu
ɗaya hanunsa ya sake ɗorawa kan kafaɗar maryam bayan ya juyo da ita suna fuskantar juna ya cigaba da cewa
“maryam ana iya samun madadin mata amma ba a iya samun madadin uwa, hakan yasa nake girmama zafi da raɗaɗin da yake cikin ranki, duk da ba za ki samu kamar uwa ba maryam amma zaki iya samun mai rarrashin zuciyarki da tausasa mata har ma ki mance cewa akwai wata illah da rashin uwa ya miki a rayuwarki”
Ita dai maryam kallonshi kawai take yi amma idan har tace ta yarda da maganganunsa tayi qarya domin bata taɓa tunanin za ta mance illolin ranshin uwa a gareta saidai fa jikinta duk a mace yake da maganganunsa, ta matuqar tausaya masa akan rashin matarsa da yayi wacce yake so matuqa, zuciyarta kuma ta ɗarsu da son jin labarin safiyya kyakkyawa kamar yadda zuciyartata take faɗa mata
“maryam ina so ki sa a ranki kina tare da farincikine me kore baqin ciki a gareki, kiyi rayuwarki cikin farinciki domin kina tare da mai tausasa zuciyarki, ki sani duk wani qunci da kika taɓa shiga a rayuwarki waɗansu sun ɗanɗani irin wannan raɗaɗin da quncin, akwai kuma waɗanda suka fiki sannan kuma kin fi wasu haka tsarin rayuwa take, manzon Allah s.a.w yace cikin wani hadisai nasa guda biyu, hadisi na farko yace “idan Allah yana son bawa sai ya jarrabeshi” au kama qala rasulillahi s.a.w, a ɗayan hadisin kuma yace “idan Allah yana son wasu mutane sai ya jarrabesu”, ba za kiyi farinciki ba idan Allah ya jarrabeki domin ya nuna miki yana qaunarki? misali ace maryam da mijinta duk Allah yana sonsu domin ya jarabcesu ta hanyar ɗauke musu ababan qaunarsu a rayuwarsu, ita uwa kaɗai mijin kuma uba da qanwa kuma mata duka basa duniyar”
Ya qarasa maganar yana wani irin murmushin da ba sai an ce ɗacine cikin zuciyar me yi ba, maryam da take saurarenshi kuma waro idanu tayi da ta ji qarshen maganarsa, tsab ya gane abin da take nufi dan haka ya sake wani murmushin tare da kau da maganar da cewa
“kin sha maganinki kuwa yau”?
Da qyar ta samu bakin cewa “um”
Hanunsa ya kai jikin wuyanta ya shafa sannan ya jijjiga kai yace
“um yanayin jikinki ya nuna min”
Kallon da ta sake masa yasa shi faɗin
“kina mamakine?, toh bari ki ji, a baya ni a cikin sojojin ma likitane, likitan ma ɗan sa ido”
Yadda ya qarasa maganar da ‘yar guntuwar dariya ita ma sai ta ɗan dara, hakan kuwa ya masa daɗi domin daman abin da yake so kenan
Hannunta ya kama ya je ya zaunar da ita a kan kujera 2seater shima ya zauna a gefenta yace
“maryam kin ga hajiyata ko? wacce kuma kika gansu tare yayata ce hajiya na’eema amma ana ce mata antyn raudat, na san ba ki manta da fuskar ba ko”?
Eh tace masa sannan ya cigaba da ɗauke mata hankali da taqaitattun labarurrukan da ya shafi danginsa, har oganniyar kwalya feenat sai da ya faɗa mata matsayinta a gurinshi ta ‘yar qanwar mahaifiyarshi, da mahaifiyarsu hajiya dattijiwar da aka je ɗaukota da ita,
Duk hirarrakin da yake mata domin ya ɗauke mata hankali sai da maryam ta jefo masa tambaya ganin yadda ya sake da ita yake mata hira fiye da zatonta wanda shi a gurinshi baqin ne baya so ta koma gurinsu balle su sake ɗaga mata hankali
“ammm….umm…., nace…um”
Idanu ya qura mata yace
“kika ce me maryam”?
Qasa sosai ta sake yi da kanta tace
“kace mahaifinka ya rasu”?
“ya rasu maryam, menene”?
“Allah ya gafarta musu” tace a sanyaye “ameen”
Agogon hanunsa ya kalla yace
“muyi sallah maryam, ina so a mayar da jama’arki gida kar dare yayi ko”?
“um”
Wayarsa ya ɗaga ya sake kiran feenat yace
“ki je ki nuna wa baqi gurin sallah za a mayar da su yanzu”
**********
Shi ya jasu jam’i shi da maryam suka gabatar da salla sannan ya sake kiran feenat ta zo ta kawo musu abinci, sosai ya matsa wa maryam lamba sai da ta ci abincin da ɗan dama kafin ya qyaleta
“mu je ki sallami baqinki zasu tafi amma da sharaɗi, ba za ki yi kuka ba, idan kin san kuka za kiyi to ba za ki je ba, idan kuma kika ce min baza kiyi ba kika je kika yi raina zai ɓaci”
Tun ba a je gurin ba har ta cika idanunta da qwalla sannan tace “ba zan yi ba”
“tun yanzu ba gashi kin shirya kukan ba”
Girgiza masa kai tayi tana qoqarin mai da qwallar
********
Maryam tana ji tana gani suka fice daga gidan bayan sun mata sallama sai albarka suke suburbuɗa mata da fatan Allah ya kawo qazantar ɗaki, ba qaramin namijin qoqari tayi ba da suke bankwana da su jamila tana basu saqon gaisuwarta gun idris, hakan ma don fawwaz ya tsareta da idanune da babu abin da zai hanata kuka
Can ga su gada mutanen feli
Suna tafiya aka dawo da amrat daga school, ai kuwa tana ganin maryam ta buga tsalle da ihun murna na ganin mummynta
Nan fa surutu ya tashi, mummyna kaza, mummyna kaza, fir ta qi nanie ɗinta ta kula da ita kamar yadda take bata kulawa idan ta dawo daga makaranta, hatta cire unifoam ta qi yarda wai saidai mummynta ce zata cire mata
Ita kanta mairo tayi murna sosai na ganin yarinyar, kama sosai taga yarinyar take yi da uwarta, kyau da farin duk na uwartace duk da bata san uwar a zahiri ba
Lokacin da take shafa mata mai sai da tayi da gaske ta mayar da hawayen da suka ciko mata ido saboda tausaya wa amrat, yarinya qarama amma ba ta san uwarta ba, har gwara ita tana riqe da kamannin mahaifiyarta a qwaqwalwarta, ita kuwa amrat sai surutunta da dariyarta take yi bata da matsalar komai, bata ma san ana yi ba
Har dare suka kai a gidan hajiya cikin kulawa da tarairaya irinta nagartattun iyayen miji waɗanda suke aiki da hankali
Zuwa lokacin antyn raudat ta tsufa a gidanta, amrat ma har tayi barci kan cinyar mairo
Duk yadda hajiya taso ya bar mairo saboda amrat ya qi yarda wai ba yanzu za ta dawo gidan ba, amrat ɗin zata dinga zuwa can a week end, dole hajiya ta hakura aka tattara sauran kayan mairo aka fitar musu da shi
Ita kanta mairo bata so tafiya ta bar yarinyar ba amma ko da wasa bata saka musu baki cikin maganarsu ba, haka suka tafi tana kewar hajiya da kirkinta
**********
Satin mairo uku a gidan fawwaz amma zuwa lokacin ta samu cigaba sosai ta ɓangarori da yawa, yawan wanka dai har ta saba da shi, kwalya kuwa feenat tayi iya qoqarinta gurin koya mata wasu abubuwa duk da har yanzu ba ta sake mata kwalyar tana yi da kanta duka ba saidai an samu cigaba sosai, amfani da qamshi kuwa ta saba da shi ta yadda baza ta iya yin wanka bata bulbula ba, yanzu su suke yin abinci da feenat, kullum feenat tana mai da kanta busy gurin koya wa mairo girke girken da ta iya irin cimarsu ta ‘yan gayu domin fannin girkin gargajiya dai kam maryam tana ajin farkone, ba ta da matsala
Da kansa ya lura da kwamacalar da mairo take yi a sallah, ba tare da ya ce mata komai ba ya nemo mai zuwa ya koya musu karatun addini ita da feenat, kuma ya umurceshi da ya fara musu daga ɓangaren tsarki da sauran ibadodi wajibabbu, duk da feenat da iliminta amma tana samun qaruwa sosai ta fannin ibadunta, ba laifi maryam ma tana samun canji sosai ta fannin ingancin ibadodinta, domin ta fara gyara wa kurakurenta
Ta fara sakewa sosai da fawwaz domin yana janta a jiki da hirarraki, ranar da fara’ar suka motsa haka zai yi ta saka ta dariya, shi kanshi idan kanshi ya ɗau zafi bai cika dawowa gidan ba balle taga canzawar fuskarshi, domin a ɗaya ɓangaren ya kafe kai da fata gurin qoqarinsa na gano jagus amma har lagos ɗin suna ta bincike ba su ganoshi ba, shidai ya tsananta wa kansa sosai gurin nemo jagus, duk da a wani ɓangarenma yana ta bincike kan hoton mutumin da bai taɓa tsammani ba cikin gungun maɓarnatan, duk da bai fasa karɓar saqonnin gargaɗi daga ɓangarori da dama ba, ga kuma rundunoninsu da ake ta kashewa cikin dazuzzukan da suka tura, qoqari yake yaga an qara musu qarfi da kayan aiki ta yadda aikin zai qare cikin nasara, maganarsu da hajiya dai kullum cikin hakuri yake bata da cewar abubuwa sun masa yawa a masa uziri zuwa wani lokaci, kamar yadda ya faɗa mata haka take faɗa wa baban zee baby tare da bashi hakuri
********
Watansu biyu yanzu amma ko da wasa fawwaz be taɓa nuna wa maryam yana sha’awarta ba balle zancen neman hakkinsa a gurinta, duk da a yanzu ba lallai waɗanda suka santa su ganeta da wuri ba, fatarta ta goge tayi fresh tayi kyau, idanunta da haqoranta sun qara farare sai haskawa sukeyi, tayi ɓulɓul da ita gwanin sha’awa, gashin kanta yana samun gyara sosai amma na kitso, ba ta barin kanta ba kitso, har gida nanie take kai mata me kitso dan zuwa yanzu sun saba sosai da ita a silar amrat, sosai addini ya sake ratsa mairo, daɗin ibada take ji hakan yasa take yawan nafilfili, har fuskarta na fitar da annuri na musamman
Kamar yadda suka saba da feenat lokaci zuwa lokaci suna fita su zagaya bayan gidan da suke ciki a gidan gonar suna kalle kallen abubuwa masu ban sha’awa a gidan gonar, yau rigace ta cotton a jikinta ruwan sararin samaniya iya gwiwarta mai botira a gaban rigar, da farin wando ya kama jikinta sosai daga qasa yayi pencil, takalman qafafunta ma fararene flat, ta sha kitsonta ciku ta nannaɗe farin ɗan sirin gyalen kayan, sai haskawa take yi tare da fitar da qamshi
Hira suke tayi da feenat suna ta kallon yadda kifaye suke rayuwarsu da walawarsu a ruwa, wani lokacin har abinci suke watsa musu, wani irin firgitaccen qara maryam ta zunduma wanda ya ɗauko hankalin sojojin da suke kula da gidan, kamar abin haɗin baki fawwaz ya shigo cikin gidan daidai lokacin da wani daga cikin sojojin ya saki harbi a sama, da gudu ya fito daga cikin motarshi bayan ya ɗauko qaramar bindiga daga cikin motar yabi hanyar da yaga sun yi
Hankalinsa idan yayi million duk sun tashi saboda hango maryam da yayi kwance shame shame a qasa, hankaɗe wani soja yayi ya durqusa a gabanta ya ɗagota ya ɗorata a cinyarsa yana jijjigata tare da qwala mata kira amma ko motsi ba tayi ba, abin da ya bashi mamaki kuma babu wani alamar jin ciwo ko rauni a jikinta, feenat kuwa banda kuka babu abin da take yi domin ko za a yankata bata san abin da ya samu maryam ba
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/30, 3:37 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
~_*infacting valuable knowledge and entertaiment is our concern*_~👌🏻
*38*
Cikin ɗimuwa ya kalli feenat murya sama-sama yace
“me ya sameta feenat”?
Feenat tana kuka tace “wallahi yah fawwaz ban san me ya sameta ba, ni dai muna hira kawai na ji ihunta tare da faɗuwarta a qasa”
A masife yace “toh me kuka zo yi a nan ɗin”?
Tsuru tsuru feenat tayi saboda hango tashin hankali da tayi cikin idanun fawwaz, tsawar da ya buga mata yasa tayi saurin fara kame kame
Cikin sojojin wani yayi qundunbalan cewa “sorry yallaɓai a ji da marar lafiyar tukunna ina ga zai fi”
Kamar ya tasheshi daga barci, a zabure ya tashi tare da ɗorata a kafaɗarshi cikin gudu-gudu sauri-sauri yayi cikin gidan da ita sauran sojojin kuma suka kasu gida biyu, wasu suka dafa mishi baya wasu kuma suka fara zagaye gidan sona binciken dalilin faruwar lamarin
Tun daga qofa ya dakatar da su, tsabar ya gigice ita kanta feenat a waje ya barta ya rufe qofar, sa’ar da taci ɗaya bai saka key wa qofar ba, tana murɗawa ta buɗe ta shige ciki hankalinta a tashe saidai bata gansu a falon ba, haka ta zauna take ta zullumi ita kaɗai a falon tana sharar qwalla
Bai tsaya da ita a iya gurin kwananta ba, yaye labulen sirrinsa yayi ya buɗe qofar da take jikin bango ya shige ya rufe kirif,
Cikin gaggawa ya sauketa akan gadonshi ya ɗauko goran ruwa ya fara watsa mata a fuska, bai ɗauki tsawon lokaci ba mairo ta ja wani qaqqarfan ajiyar zuciya, tsabar ya ruɗe jefar da goran ruwan yayi ba tare da ya rufe bakin ba ya haura gadon ya ɗago kanta yana kiran sunanta
Ba tare da ta buɗe idanu ba ta sake zunduma ihu tana qanqame jikinta tana cewa
“wayyo Allah na zai kasheni, wayyo na shiga uku”
Da qarfi ya jijjigata yana cewa
“maryam ki buɗe idanunki, menene?, buɗe idanunki ki gani nine, wanene zai kasheki”
Jin muryar kawai take yi amma bata tantance me ita ba saboda firgici da take ciki, idanunta a rufen ta qanqameshi tana cewa
“wallahi gashi nan zai sareni, zai kasheni ne wallahi”
Yadda ta cukwikuyeshi take ihu abin ya ɗaure masa kai,gashi jikinta sai rawa yake yi, toh me yake faruwane?,
Duka hannayensa ya sanya ya rungumota jikinsa yana jijjigata yana cewa “maryam ki nutsu ki min bayani, me yake faruwa, mene ne? ki nutsu don Allah”
Sai a lokacin ta gane muryarshi da ya kira sunanta da sauri tace “macijine yah fawwaz, macijine mai kai biyu zai sareni”
Maciji kuma?, yace a cikin ransa, jim yayi na wani lokaci sannan yace “buɗe idanunki ki gani a ɗaki kike babu macijin maryam”
Ba ta musa ba dan ta san ba zai mata qarya ba, a hankali ta fara buɗe idanunta har ta waresu tas a ɗakin ba ta ga komai ba, wani wawan ajiyar zuciya ta sauke da ta duba bata ga komai ba sannan ta fara qoqarin miqewa daga jikinsa, mayar da ita yayi jikinsa ya ɗago haɓarta yana kallon fuskarta yace
“maryam me ya tsoratakine?, babu komai fa a gurin da kika faɗi”
Kamar za ta yi kuka tace
“Allah ƴyah fawwaz akwai maciji me kai biyu a gurin, daga cikin ruwan kifin nan fa ya taso ya fasa min kansa har biyu zai sareni”
“a a maryam, ba zan qaryataki ba amma cikin ruwan kifin nan kullum ana kula dashi yadda ya dace, maciji ba zai rayu a ciki ba, saidai idan wani abin kika gani daban”
Ita kanta bata san yadda akayi ta shagwaɓe muryar ba sai tsintar kanta tayi da yin magana cikin shagwaɓe murya
“da idanuna fa na ganshi yah fawwaz, har saitin fuskata fa ya zo ga shi dogo”
Shima binta yayi da idanu jin yadda tayi maganar cikin shagwaɓa har da gangarowar hawayenta, hannunsa ya sa yana goge mata hawayen yana girgiza kai,
“tashi muje mu duba”
Zaro idanu tayi tace “ina zamu je?”
Yadda tayin ta bashi dariya don ya fahimci a firgice take sosai, hannunsa yasa ya ɗagata daga jikinsa sannan ya tashi shima yana riqe da hannunta yace “ba gurin macijin zamu je ba sarkin tsoro, zo ki gani”
Gurin da na’urarsa take ya je ya tsaya ya sake hannunta ya buɗeta sannan ya kamo hannunta ya matso da ita kusa da shi yace “bari mu gani ko macijinne da gaske, kalli nan”
Ya qare maganar yana nuna mata kan screen ɗin
Da mamaki take kallon abin har ya zuqo hotunansu tun daga fitarsu har zuwansu gurin tafkin kifayen, tunda taga sun ɗau lokaci a gurin take tsorace saboda tana qiyasce lokacin da suka ɗauka a gurin kafin lokacin bayyanar macijin a gurinta, zuciyarta sai harba wa take saboda tsorin ganin macijin da zata sake yi a yanzu, amma ga mamakinsu ko ince mamakinta har ihun da tayi ta zube a gurin ba su ga komai ba a gurin, bai rufe ba har sai da ta ga lokacin da ya ɗaukota ya shigo da ita gida
rufe na’urar yayi sannan ya jiyo ya tsareta da idanu,
“ina macijin maryam”?
Qasa ta sunkuyar da kanta idanunta har sun kawo ruwa ta ɗago kan tace
“yah fawwaz ka yarda dani wallahi na ga macijin nan, ni ban san me yasa ba a ganshi a nan ba”
Yadda ya kafeta da idanu yasa tayi saurin sake sunkuyar da kanta,
“na ji kin ga macijin duk da ni ban ganshi ba amma wa yace ki fita ki je gurin”
Shiru ta masa still kanta a sunkuye
“ba ki ji abin da nace bane”?
Ya sake tambayarta, a hankali tace “kayi hakuri”
Tsaki ya ja sannan yace “ki kalli yadda kika fita fa, ko tunanin gardawan da suke gidan baki yi ba, toh ko ita feenat sai ta faɗa min dalilin fitanta a haka balle ke da aurenki, ki jini da kyau, duk ranar da kika sake fita ko qofar falon nan a haka sai ranki ya ɓaci, kin ji ko ba ki ji ba”
“na ji yah fawwaz, ba zan sake ba, kayi hakuri”
“nayi, ni bance ki min kuka ba, yanzu inane yake miki ciwo”?
Qwallar da suka fara gangarowa ta share da hannunta tace “babu”
“amma na san wannan faɗuwa da kika yi dole wani gurin ya miki ciwo, yanzu ki je kiyi wanka ki cire waɗannan kayan ki zo in baki wani magani ki sha”
“tsoro nake ji yah fawwaz, ni dai gaskiya ba zan iya shiga wanka yanzu ba”
“tsoron me kuma kike ji yanzu”
Kamar za tayi kuka tace “Allah na ga macijin nan yah fawwaz, Allah”
“toh yanzu ina macijin yake”?
“ni dai ba zan yi wanka ba, ka ban maganin kawai”
Murmushi yayi yace “maryam maryam…, toh mu je in rakaki ki ɗauko kayanki ki zo toilet ɗina kiyi wanka, ko nan ɗin ma macijin zai biyoki”?
Ita dai ba dan ta so ba ta yarda ya rakata ta ɗauko kayan, matsoraci da saurin tsorata ita da kanta ta buge kwalbar turare amma sai ta saki kayan hanunta a qasa ta je ta ɓuya a bayan fawwaz numfashinta kamar zai ɗauke, jikinta sai rawa yake yi kamar zata sume a karo na biyu
Ganin da gaske a tsoracen take fawwaz ya riqota ya rungumeta a jikinsa ya fara buga mata baya yana cewa
“maryam ki nutsu kin ji, babu wani macijin da zai iya shigowa nan saidai macijin tsafi”
“don Allah ya fawwaz ka qyaleni, ba sai na yi wankan nan ba”
Yadda muryarta yake rawa yasa shi saurin cewa “toh shikenan kwantar da hankalinki ba za kiyi wankan ba, mu je ki sha maganin kin ji”
Ai tana maqale da shi qamqam suka juya za su koma sai yaji wayarshi tana kiran sallah, dakatawa yayi da buɗe qofar ya ciro wayar ya ɗaga
“kana inane?, gamu a gidanku”
“toh gamu nan hajiya”
Feenat ce da ta rasa mai za tayi sai ta kira hajiyar fawwaz ta sanar mata, ita kuwa ba tai qasa a gwiwa ba ta fito ita da amrat da nanie aka kawosu kuma tun a hanya ta kira antyn raudat ta sanar mata, har ta manta da hajiya bilki sai kuma ta tuno tayi saurin kiranta ita ma ta sanar mata
ɗagota yayi daga jikinsa yace “maryam ki daure ki canza waɗannan kayan ko ba za ki yi wankan ba, kin ga anyi baqi gashi kayan jikinki kuma sun ɓaci”
Kai ta gyaɗa masa sannan ta sake shi ta ɗebi kayan da ta zubar tana sanɗa ta tura qofar toilet ɗinta a hankali
Zuwa yayi ya shiga cikin toilet ɗin ya dudduba ko ina yace mata ta zo ta gani ita ma, sai da ta tabbatar ba komai sannan ta shiga ciki tana waige
“ki kwantar da hankalinki ina tsaye a nan ina jiranki, ko zama ba zanyi ba saboda tsaro”
Cikin minti shabiyar har mairo ta jijjiqa wanka ta canza kaya ta fito, murmushi yayi ganin yadda ta fito da gudu daga toilet ɗin, hannunta ya riqo suka fice zuwa falon, har lokacin ba ta gama dawowa normal ba
har qasa ta durqusa tana gaishe da hajiya da nanie su kuma cikin jimantawa suke amsawa tare da tambayar abin da ya faru, duk da feenat ta faɗa musu wanda ta sani
Hankalin hajiya a tashe jin abin da ya faru daga bakin fawwaz tace maza maza ta haɗo kayanta su tafi can gidan, wai daman ban da fitina irin ta fawwaz yaushe me rai zai rayu cikin wannan jeji, wataqila ma sheɗanune suke tsoratata idan ba haka ba wani macijine ba a ganinsa
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/31, 1:15 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
~_*infacting valuable knowledge and entertaiment is our concern*_~👌🏻
*39*
“hajiya ni fa ina ganin kifine ya tsoratata amma ita da kanta ta gani babu maciji a gurin”
Cewar fawwaz, feenat ma cikin tabbatarwa tace
“nima dai ban ga maciji ba gaskiya, kuma duk muna tare da ita a guri ɗaya”
Cikin faɗa hajiya tace “yaya zaku dinga qaryatata, idan bata gani ba za ta ce ta ganine?, har da suma, duk yadda akayi akwai shaiɗanu a gurin waɗanda suke tsoratata, ta shirya kawai mu tafi ta zauna a side ɗinka na can, zaman nan ya qare daga yau”
Dariya fawwaz yayi yace “hajiya toh ko shaiɗanun ne akwai maganinsu da ya wuce adduane”?
“eh za tayi adduar ma amma za ta bar gidan nan, ai dama ba za mu zauna haka ba tunda sun fara bayyana mata kansu”
Nanie ma cikin jimami tace “sosai ma kuwa hajiya, daga haka fa ake cewa mutum yayi gamo”
“ai kuwa ko sun gamu za su rabu da izinin Allah”
Yadda tayi maganar duk gurin sai da suka dara, har da mairon ma
Jawota hajiya tayi jikinta tace “zo nan ‘yata, zaki bimu mu je can kiyi zamanki abinki kinji”
Kai maryam ta gyaɗa mata tana murmushi, ita kuwa amrat sai murna take yi tana farinciki momynta za ta koma gidansu, kusa da mairon ta koma ta kwanta a jikinta, hajiya ta ja kumatunta cikin wasa tace “ke tashi min daga cinyar ‘ya kar ki karyata”
Maqe kafaɗa tayi tace “oh oh mummyna ce, ke ba ki da mummy lol”
“ka ji ‘yar nema, hajiyar ke kika kashe min ita”
“taki ta tsufa ko amrat”?
Cewar nanie “amma dai tana nan ko”?
Miqewa fawwaz yayi yana dariyar hirar tasu yace “hajiya ina zuwa”
“ba kana zuwa ba, ta je ta haɗo kayanta mu tafi kar a kira magriba muna nan”
“kai hajiya, kin dai matsa sai ta biku, toh shikenan bari nima nayi wanka mu wuce, ko a nan zaku barni”
“zaka zo daga baya, amma mu yanzun nan zamu wuce”
“toh hajiya, maryam zo ki fara haɗa kayanki, kema feenat” yace yana tafiya
Nauyin tashi ta ji daga gurin har sai da hajiya ta sake mata magana sannan ta kamo hanun amrat suka tafi ɗakinta
Ta fara haɗa kayan amrat tana ta mata hira sai gashi ya shigo, kusa da ita ya zo ya tsaya yana murmushi yace
“matsoraciya kawai, gashi kin sa za a ɗaga mu daga guri me daɗi zuwa guri me hayaniya”
Murmushi ita ma tayi tace “yah fawwaz ba za ka gane bane amma ni na san me na gani”
“ba wani nan, ke dai matsoraciyace kawai”
Kallonsa tayi cikin ido sannan tayi murmushi tace “hmmm, shikenan na ji”
Kallon amrat yayi yace “je ki gurinsu hajiya muna zuwa”
Toh tace tare da rugawa da gudu ta fice daga ɗakin
Kusa da ita ya sake matsawa yace “maryam ki ɗau kaya kaɗan kawai”
“ba ka ji abin da hajiya tace ba”
“na ji mana amma ni nan ɗin yafi min, idan kika ɗibi kaɗan zan je in lallaɓata ki dawo nan, amma idan kika tafi da kayanki duka baza ta taɓa amincewa ba”
Juyowa tayi gaba ɗaya tana kallonshi tace “yah fawwaz ka yi hakuri ka taimakeni ka barni a gurin hajiya kawai, idan yaso kai sai kayi zamanka a nan ɗin”
Wani kallo ya mata wanda bai taɓa mata irinsa ba yace “saboda me zan zauna a nan ba tare da iyalina ba”
Shagwaɓewa tayi tace “yah fawwaz don Allah ka barni a can, idan yaso sai ka dinga zuwa duba mu idan ayyuka suka maka sauqi”
“haba” yace yana murmushi, “um” itama tace tana sake lanqwashe wuya
Buɗe baki yayi zai yi magana yaga ta zaro idanu waje tana ja da baya, gaba ɗaya daga kan fawwaz zuwa sama babu shi ya rikiɗe zuwa kan maciji har biyu duk sun fasa kai, ganin yadda ta rikice idanuwanta kamar za su juye, a kiɗime yayi kanta yana cewa “maryam menene?”
Wani irin firgitaccen qara ta zunduma ta zube a gurin
Wayyo tashin hankali ba a sa maka rana, cikin miliyoyin tashin hankali ya fara kiran sunanta amma ina babu alamar motsi
Su hajiya da suke falo jin ihunta da sukayi ba qaramin gigicewa suka yi ba, tasowa sukayi duka suka yo bakin qofar, hajiyace ta hau bugawa yayin da amrat take tayata tana kiran sunan fawwaz da ya rikice saboda sabon al’amarin da ya shigo rayuwarshi a yau
Hannayensa ya sanya ya ɗago mairo da take miqe a gurin ya zo ya buɗe qofar da hannu ɗaya yana cewa
“hajiya duba ki gani suman ta sake yi”
A matuqar razane hajiya da nanie suka karɓeta suna salati, da qyar hajiya ta haɗa yawun bakinta tace
“yanzu kuma mai ya faru fawwaz”?
“ni kaina ba zan ce ga abin da ya faru ba, muna magana kawai sai naga tana kallona tana ja da baya a firgice, ina yunqurin zuwa gurinta ta sake sumewa”
Cikin tashin hankali hajiya tace “kai min ita mota mu bar gidan nan fawwaz, ka biyota da kayan daga baya”
Cicciɓarta yayi ya wuce da ita suna binsa a baya nanie tana ta cewa “wannan wani irin masiface, wacce irin fitinace wannan”?
Yana fita sojojin nan suka taso wai za su taimaka masa su karɓeta, ai wani tsawa da ya buga musu da nice ruwa leda ashirin ba zan farfaɗo ba yace “matata zaku ɗauka ko me”?
Babu wanda ya amsa masa har ya ja tsaki ya wuce gurin motar su hajiya, shimfiɗeta yayi a bayan mota ya gyarata, su nanie suna fitowa ita ma ta shige baya ta ɗora kan mairo a kan cinyarta tana tofeta da adduoin da duk suka zo bakinta
Fennat ma bayan ta shiga ta ɗora qafafun mairon kan cinyarta tana sharar qwalla yayin da hajiya ta shiga gaba ita da amrat, amrat ɗin ma kuka take yi ganin feenat tana yi, hajiya dai tayi dauriya domin ba kuka sai tsabar tashin sense da zaku karanto cikin idanunta da fuskarta
Fawwaz yana tsaye a gurin kamar gunki har sai da ya tabbatar motarsu ta ɓace wa ganinsa sannan ya ja qafa ya koma cikin gida
Kai tsaye wani shahararren islamic center hajiya tayi umurni aka kai su lokacin har an fara kiraye kirayen magriba
*******
Zaune yake yana nazarin ta yadda zai yi ya kuɓutar da kansa daga tarkokin da yake da labarin fawwaz ya ɗana musu sai yaji wayarsa ta fara tsuwa, tsaki ya ja domin tun ɗazu ake kiransa baya ɗaga wa saboda wani kuɗaɗe da abokinsa yake nema a gurinsa shi kuma ba zai iya bayarwa ba, a wannan karon ma ya ɗauka shi ɗinne don haka ya sake yin biris, sai da wani kiran ya shigo sannan ya ɗaga da qyar ba tare da ya duba me kiran ba
“ga wata dama ta sake samuwa na ganin bayan gee fawwaz, mata, ‘ya da uwarsa duk suna cikin mota ɗaya, suna hanyarsu ta zuwa gamji islamic center, ka san me kake ciki, zai yi wuya ka sake samun dama irin haka”
ISLAM IS MY IDENTITY
[9/1, 5:19 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
~_*infacting valuable knowledge and entertaiment is our concern*_~👌🏻
*40*
Tsaye ya tashi yana zagaye ɗakin da wayar a kunnenshi amma ya kasa faɗin ko da kalma guda ɗaya ne, sai da na ɗayan ɓangaren ya sake mishi magana sannan ya numfasa yace
“lallaine na daɗe ina neman irin wannan damar akan gee fawwaz, na daɗe ina neman ranar da zan tarwatsa sauran farincikinsa da rayuwarsa, saidai kash, damar ta zo min ne a lokacin da nake cikin wani kangeggen keji mai tsananin matsi da qunci, ina so ka sani, duk wani motsi da zan yi a yanzu irin wannan motsin gee fwwaz yake nima daga gareni ya samu damar da zai tarwatsa rayuwata nima, ina me tabbatar maka da cewar babu wata hanya da za mu bi mu tsere matuqar muka afka ɗaya daga cikin tarakun da gee fawwaz ya ɗana mana, babu wani hasken ina tabbatar maka ko kaɗan”
Sai da ya sake numfasawa sannan ya cigaba da cewa
“ya zama dole mu bar wannan kyakkyawar damar da muka samu ta wuce mu domin tsira da rayuwarmu, ina buqatar lokaci zan nemeka mu haɗu a guri me sirri”
“hakan yayi, kayi tunani sosai wanda ni sai a yanzu na lura da hakan, sai mun yi waya kawai”
“toh madallah”
Daga haka suka ajiye wayoyinsu shiko babban shaiɗanin sai kewayawa yake yana zarya a guri kamar dillalin gudawa
**********
Fawwaz da ya koma gida gudu gudu yayi wanka ya canza kaya kamar kullum idan ba uniform a jikinsa to suit yake saka wa idan zai fita
Suit ɗin jikinsa na yau army colour ne sai baqin glass da baqar takalmi sau ciki, duk da yana cikin tashin sense amma yayi kyau sosai kamar maryam ta saceshi ta ɓoyeshi a zuciyarta
A mota ɗaya suka fita da drivernsa da yake soja sai kuma sunday
Hajiya ya kira ya tambayeta gurin da zasu sami gamji islamic center amma ba a ɗaga wayar ba, wayar antyn raudat ya kira ya tambayeta ta masa kwatancen gurin dan ita ma hajiya ta sake kiranta ta sanar mata abin da ya sake faruwa sallah kawai za ta yi ta ɗau hanya ita ma
Kwatancen gurin yayi wa drivern nasa ta waya saboda basa ganin juna, sai da ya tabbatar ya san gurin ya kuma gane sannan ya kashe kiran
munir ya kira ya sanar da shi abin da ya faru da maryam, shima lamarin ya ɗaure masa kai amma ya bashi shawarar su je asibiti shi da yake munir gidansu zallar boko ne ya kama jikinsu, godiya ya masa ya kashe wayarsa ya sake kiran nambar auncle A, wato arfat ɗan gidan hajiya bilki ya sanar masa da abin da ya faru, shima dai haka ya girgiza da jin lamarin sannan yace masa zai ɗauko haseenat su zo gurin idan aka fito daga magriba
*Auncle A shine amintaccen fawwaz a dangi, yanzu haka shi yake jan ragamar kamfanin fawwaz ɗin da ya gada daga babanshi na sarrafa fatu, kuma nasu yazo ɗaya sosai saidai yanayin aiki da ya rabasu*
Sun iso gurin gamjin islamic center har an shiga sallah don haka yana fitowa ya wuce shi da drivernsa da ya kasance musulmi masallaci suka bar sunday a motar
Da takalmarsa ya je ya jona sahu kasancewar yayi alola, shiki drivern sai da yayi gudu gudu yayi alola ya zo ya jona lokacin ana raka’ar qarshe, bayan an idar da sallar sai da suka ciko abin da ya tsere musu sannan suka yi adduoi suka fice daga masallacin, cikin adduoin fawwaz na magribar yau babu abin da ya fi roqa kamar waraka wa maryam ɗinsa da nema mata kariyar mahaliccinta daga sharrin dukkan wani abu me cutarwa
Kiciɓus sukayi da su hajiya da suka fito daga wani keɓaɓɓan gurin da suka yi sallarsu, da sauri ya qarasa ya riqo hannun hajiya bayan ya zare glass ɗin idanunsa yace
“hajiya ina maryam ɗin, ta farfaɗo”?
“ka kwantar da hankalinka fawwaz, mun zo lokacin ana ta kiran sallah, da muka musu bayanin abin da yake faruwa sai shi babbansu yace mu kwantar da ita kawai a gurin muje sallah mu dawo, da har na so qin amincewa gudin kar wani abin ya sameta ita kaɗai a cikin gurin sai yace mu kwantar da hankalinmu babu abin da zai sameta”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya mai da glass ɗinsa yace “toh tana ina ne yanzu hajiya”?
“tana cikin can”
Ta nuna masa da hannu, ai bai jira su ba ya fara tafiya ciki, kamar haɗin baki motar su arfat tana bayan ta antyn raudat, fitowa duka sukayi suka qaraso gurinsu hajiya, nan dai gaishe gaishe ya tashi da jajantawa juna a tsakaninsu, daga nan kuma suka ɗinguma suka yi cikin gurin
Maryam tana kwance a gurin da suka barta saidai yanzu kanta yana kan cinyar fawwaz, ya qura mata idanu ko qyaftawa baya yi, daga gani hankalinsa yayi nisan kiwo domin bai amsa sallamar da su hajiya suka masa ba
Neman guri suka yi suka zazzauna suka fara gaishe da fawwaz, sai a lokaci ya nisa ya ɗago da kanshi jikinsa a mace yake amsawa, idanunsan nan sun yi jajir
“ayyah wannan yarinya kina ganin ibtila’i a rayuwarki, Allah ya kawo miki qarshensa”
Cewar antyn raudat, kowa da yake gurin ameen yace suna masu tausaya mata
Kusan minti shida suka ɗauka shiru kowa da irin nazari da tunanin da yake yi a zuciyarsa, cikin ɓacin rai fawwaz ya fisge glass ɗin idanunsa yace
“wai ina masu gurinne, wani irin wulaqancine wannan, ko sai ita ma ta mutu kafin su zo su dinga wa mutane zancen banza, mu tashi mu tafi asibiti kawai hajiya”
Kowa saida ya tausaya masa dan sun san abin da yake tsoro, ayya fawwaz ba haka abin yake ba, komai yana faruwane a tsarin qaddara, saidai zancen nanne na hausawa da suke cewa “idan wuta ta qonaka idan ka ga toka sai ka tsere”🏃🏻♀
“yanzu za su zo fawwaz ka kwantar da hankalinka ka ji”
Cewar hajiya cikin sigar lallashi
Ya buɗe baki zai cigaba da masifar arfat yace “take it easy jarumi, ummm, komai zai zo da sauqi”
Qwafa yayi daidai lokacin da babban malamin ya shigo tare da sallama, sauran ne suka haɗa baki suka amsa amma banda fawwaz da yayi saurin kallon gurin da ya jiyo sallamar rai a ɓace
Zama malamin yayi akan kujera ya ɗago da niyar fara musu magana sai ya sauke idanunsa akan fawwaz
Da mamaki sosai akan fuskarsa yace “ranka ya daɗe kaine a nan,? ina ma laifinka ka turo mu tura har gida a duba maka me jikin”?
Shiru fawwaz yayi kamar ba zai yi magana ba domin haushi ma ya bashi da wannan dogon surutun, sai kuma yace
“mun wuni lafiya”? Lafiya lau malam ɗin yace masa nan dai suka gaisa sama sama sannan malam ɗin yace “iyalinka ce”? Eh yace a taqaice
Wani ruwa ya ɗauko a gefensa kan table cikin gora ya taso daga gurin da yake zaune ya zo gaban fawwaz ya tsuguna daidai kan maryam,
Murfin gorar ya buɗe ya tsiyayi ruwan a hannunsa ya watsa mata a fuska, ya sake ɗebowa ya watsa mata a fuska, tun kafin ya watsa na uku ta fara sauke ajiyar zuciya yana watsa na uku ta feso wani atishawa mai qarfin gaske tare da buɗe idanu tarwal
Tsuru tsuru ‘yan gurin sukayi da idanu suna kallon ikon Allah,
“wa sunanta” cewar malam Abdul aziz yana kallon fawwaz
“maryam” yace hankalinsa na kan fuskar maryam ɗin ganin yadda take ta motsa idanun bayan ta sake rufewa
A hankali yace “maryam”
Shiru tayi ta masa banza
“maryam kina jina,? kiyi magana idan kina jina”
Shiru nan ma tayi abinta tana cigaba da motsa idanu
Tashi yayi ya je ya ɗauko wata kwalba qaramar gaske ya dawo ya zauna ya buɗe murfinta ya sanya a qofar hancinta duka biyu
Idanuwanta ta buɗe ta fara farfarawa kamar ba idanun mutum ba, umurni malam ɗin yayi wa fawwaz da ya ɗagata zaune sannan yace a fitar da amrat daga gurin
Hajiya ce tayi umurni wa feenat da haseenat su fita da amrat su jirasu a mota
Neman abin zama yayi ya zauna saitin kunnenta bayan ya sa an rufe mata kanta da kyau sannan yayi ta’auwizi da bismillah sannan ya fara karatu
Hmmmmm, lallai duk inda wannan abu ya fito babu sa’a a lamarin, toh gani nayi da gaggawa haka har anyi ram?😂
********
A can qauyen feli kuwa tun bayan komawar dangin mairo sai labari ya bazu ciki kunnen kowa a qauyen cewa gidan maryam kaza gidan maryam kaza, har da masu kiransa aljannar duniya, ko ina dai zancen kenan yake tashi cikin qauyen har da qauyukan iyayen, mamaki ta al’ajabi dai ya kusa kashe wasu, wasu kuma tsoron Allahne ya sake shigarsu da girmama qarfin ikonsa da isarsa akan komai da kowa
A wani ɓangaren kuwa baqincikine yaso ya kai wasu lahira tun ba su shirya ba, ciki kuwa harda oganniya hamshaqiyar azzaluma haule, tayi baqin cikin wannan labari da take wasi wasin ba zai tabbata ba har sai da ɗiyoyinta suka je suka zo mata da baqin labari, tayi kuka sosai wiwi a ranar, sai da baqin ciki ya haddasa mata ciwon qirjin da yasa dole sai da ta ziyarci asibiti
Ayi hakuri, no time
ISLAM IS MY IDENTITY
[9/3, 10:33 AM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
~_*infacting valuable knowledge and entertaiment is our concern*_~👌🏻
*41*
Mahaifin mairo kuwa darajarsa da kimarsa sai ta qaru a idanun mutane, musamman masu kwaɗayi da son abin duniya, gani suke yanzu Allah ya bashi tamkini a doron qasa tunda ‘yarsa tana auren gee fawwaz
Abubuwan kunya dai iri iri anyi a dangin mairo, domin duk waɗanda sukayi buris da ita a baya sai gasu suna rushing zuwa gaishe da babanta da sanya wa yarinya albarka, wasu har da ɗan kayan hasafinsu wa idris da baban mairon, ni ko nace ikon Allah wai na kwance ya faɗi
Kakarta ta gurin uba tun da suke da mairon sai a wannan karon ta tako qafarta gidan domin gabatar da wani muhimmin magana a kanta, faɗa sosai tayi wa baban mairon akan aurar da ita da yayi ba tare da ya sanar wa kowa cikin danginta ba, wai ai ta ji labarin auren wulaqanci suka so yi wa mairon Allah ya kareta ya ɗaukaka darajarta, a ranar zagi dai da cin mutunci babu wanda haule bata gani ba, kakar mairon sai cewa take azzaluma, macuciya kin so a wulaqantar da yarinya sai Allah ya wulaqantaki, muguwa kawai kin saka marayu a gaba da zalunci, in Allah ya so sai kin girbe mummunar shukar da kika yi, ga ki ga duniyar ki cigaba da casawa ko zaki fitar da tsaba, zagi dai kala kala, shidai baban mairo daman tun zuwan da yayi ya sanar musu ta zageshi tas don haka yanzu maimaici yake ji, amma gwanar rashin mutunci kuwa sai da ta mai da martani cikin gatsali da cewa “ke me yasa da kika ga nake zaluntarsu ba ki zo kika ɗaukeshi kika riqesu a gurinki ba, sai yanzune kwaɗayi bar jana zaki ɗebo qafa ki zo kina wani surutun banza, kwaɗayi da son abun duniyane ya kawoki kema ba wai kin damu da su ba, don haka wallahi duk wanda ya k’ara sake linzamin harshensa ya zageni akan yaran nan sai na rama ehem, ban da rainin hankali me yasa da tun farko da kuka raina tsayuwar wata baku bita sama kuka gyara ba”
Nan dai aka casketa ba tsaba tsakanin haule da kakarsu mairo amma abin tausayi da tashin hankali baban mairon yana gurin bai iya cewa komai ba sai sunkuyar da kai da yayi qasa, haka babar tashi ta bar gidan tana kuka sharshar saboda zagi da cin mutuncin da take gani haule ta mata, sai bayan tafiyar kakarne Abula ta tashi tsaye cikin rashin kunya tace
“amma wallahi baba haule ba kya kyautawa, a gaban babanmu ki dinga zagin mahaifiyarsa, ai wannan ma wallahi ba yi bane”
Takalmi ta raruma ta jefeta da shi cikin tafasar zuciya don ita idan akwai abin da ta fi tsana bai wuce anbaton sunan mairo a gabanta ba,
“don ubanki idan kin ji haushin abin da nayi ki zo ki rufeni da duka”
Karkaɗe gurin da takalmin ya sauka Abula tayi tace “ko za a kasheni sai na faɗi gaskiya, kuma wallahi kema sai an miki abin da kika yi”
Kururuwa tayi tace “yaushe yaushe aka haifeki Abula, ni kike wa rashin kunya, ni kike wa baki”??
Abin mamaki ‘yar yarinyar nan Abula jan tsaki tayi ta bar gurin tana cewa “ke ba rashin kunyar kuka yi ba”
Mamaki kashe haule, haka tayi zaman ‘yan bori a qasa tana al’ajabin lamarin ganin tatsitsiya irin Abula wai ita take caɓa wa magana, shi dai babansu kamar baya gurin haka ya zama ko motsi.
Hmmmmmmm
********
“tani wallahi tallahi bana barci sosai tunda lamarin nan ya afku, abinci wannan bana ci ya sauka cikin cikina daidai, kullum cikin tunanin mafita nake, domin wallahi ko zan tafi tsirara sai mairo ta bar gidan gee fawwaz”
Tani da take sauraren haule gyara zamanta tayi tace
“lallai wannan al’amari dole ya girgizaki haule, nima dai da na ji zancen na yawo cikin ɗan qauyenmu na kurmi nace amma haule tayi babban kuskure, ashe ba haka lamarin yake ba, ta bayan gida aka fito miki, nima ina bayanki, duk yadda zakiyi kiyi ganin yarinyar nan ta bar gidan jin fahas yake ko wa”?
Duk da haule na dame sai da ta dara tace “oh su tani dai har an tsufa da baki duk tsami, gee fawwaz ake cewa”
Dariyar ita ma ta yi tace “toh ni ina zan iya faɗin wani jin fuhas”
Dariyar nan ma suka kwashe da ita sannan haule tace “yanzu matakin da zan ɗauka nake ta tunani tani”?
“mataki abu mai sauqine haule, a sauka ta gurin da aka hau shi ya fi dacewa”
“kamar yaya tani”?
“matso ki ji” kusa da ita ta matsa ta bata kunnenta tayi mata raɗa, wani uban shewa da suka yi bayan gama raɗan sai da na kusan zurawa da gudu, idiots😏
******
Zaune suke a gaban malamin da ya saba musu miyagun ayyukansu dake ɗam wani qauye qasa da kurmi kaɗan, tun kafin su faɗi komai ya fara jero musu abin da yake tafe da su, hakan yasa suka yi ta masa kirari da qarairayi, cikin kirarin har da mai gani har hanji mai tarin ilmummuka, niko nace tsinannu Allah yasa yaga naku hanjin ya lasheku dan uban….🤭😬
Alqawari ya musu na cewar mairo zata bar gidan haihata haihata kamar yadda ɗa idan ya bar cikin uwarsa ba zai koma ba, su dai su kawo daqwalen kaji jajaye biyar, baqaqen zakaru uku wai za a bawa rauhane, haka suka yarda suka yaɓi jiki yarkace yarkace tsinannu suka ɓala garinsu
A ranar da suka kawo kajin haule ko karyawar kirki bata tsaya yi ba, haka ta taho ciki duk yunwa, aiko malamin nasu ya ɗau alhakinta, domin lokacin da suka shiga gurinshi naman kaji suka samu cikin wata babbar samira a gabanshi yana dannawa amma ko tayi bai musu ba haka ya kira matarshi wai ta ɗauka taje ta sake soya masa wai ba su gama soyuwa ba, tsinanne Allah yasa ulcer ta kasheka al’ummar annabi su huta
Haule dai haka tayi ta haɗiyar yawu tana sakewa amma babu rabonta ko fuka fuki ne, Allah ya qara, ku kawo kaji ku gina arne mata kuma ba zai taɓa canza qaddara ba, sai akayi yaya?
Ga dai irinsu mairo nan suna rayuwarsu cikin aminci da ɗaukaka da jin daɗi, ba a mazan ba ba a matan ba, na rantse da Allah a yau idan nace zan buɗe link guda ashirin a yaɗa su kawai in ce waɗanda suka yi rayuwa irin ta mairone kawai zasu shiga maza da mata, zuwa gobe duk group ɗin za su cike tam, ko kaffara ba zan yi ba, toh don girman Allah mata wani irin ciwon haukane yake kamaku wanda har yau kuka kasa nemo maganinsa, idan kina da hankali ‘ya’yan kishiyarki, ko abokiyar zamanki ‘ya’yankine halak malak, me yasa mata kuka kasa gane hakan?, me yasa mata kuka kasa gane duk tsiron da kuke son dannewa shi Allah ya fi bashi kulawa da yayyafin ruwan albarka, me yasa mata ba kwa zama kuyi tunani, me yasa kika manta cewar baki san qarshenki ba, wa zai taimakeki a lokacin rauninki, kina da tabbacin zaki rayu da yaranki, kun yi da Allah cewar idan kun rayu da su za su yi albarkane?, me yasa ba za ki yi wa kanki faɗa ba?, kar ki bari lokaci ya qure miki ‘yar uwa, ki tuba tun kafin a rufe qofar tuban, irinsu maryam dai ko a shuwagabannin qasa da manya manyan ‘yan kasuwa su suka fi yawa, irinsu maryam zaki samu sune kan duk wani madafun iko cikin qasar nan da wasu qasashen, a mafi yawancin lokaci wahalallun ‘ya’ya suke riqe gida a gaba, ba za ki ji nauyi da kunya ba duk ranar da ɗan maqiyiyarkin ya ɗauki lomar tuwo ya sanya a bakinki ba?, me zaki ji a ranki idan ya kaiki makka watarana, me zaki ji a ranki idan ya ɗauki nauyin karatun yaranki tare da samar musu ingantacciyar rayuwa?, hmmm ba wannan ba ma, kin ga yaranki, wallahi watarana sai sun miki tawaye ko a bayan rankine akan ɗan uwansu, jini ya fi nono qarfi a cikin ko wani irin lamari, ki kula
*******
Toh su haule dai haka suka miqa daqwalen kaji suka juya da zummar idan aiki ya kammala zasu dawo da albishir ɗin goro farare a gareshi, hmmm to mu je zuwa wai mahaukaci ya hau hyena.
*****
Tun da malam ya fara karatu mairon fawwaz ta fara wani irin kuka da tsaki kamar na maciji dai tana kaɗa harshe, shi dai malam bai tsaya wani magana ba domin ya lura ba masu magana bane a kanta, wani irin miqewa da tayi da wani irin azababben qarfi tayi yunqurin watsar da su fawwaz, da qyar fawwaz ya saka mata qarfi kafin ya zaunar da ita, nan fa aka fara cakwakiya mairo tana shirin zillewa, su hajiya dai sai sharar qwalla ake yi, ganin yadda take wahalar da fawwaz yasa arfat kai masa ɗauki zai kamata amma tsabar kishi irin na fawwaz sai ya dakatar dashi ranshi a ɓace ya harareshi yace ya saketa, haka suka barshi yayi ta fama sai can Allah ya kawo musu tallafi mairon tabar haukan da take yi ta nutsu tare da qwace kanta a hannun malam ɗin ta musu sallama ba sai an tsaya cewa ba muryar mairo bane wannan domin akwai banbanci me tazarar gaske
Malam ɗin ne ya amsa sallamar tare da tambayar waye?
Cikin muryar gadara tace
“ku saka min hijabi kafin muyi magana”
Rai a ɓace fawwaz yace “ba za a saka hijab ɗin ba, uban waye ya kawoki jikin matata baqar azzaluma”?
Wani irin kallon banza tayi wa fawwaz sai kuma tayi murmushi tace
“ka ci sa’a kana da daraja a idanuna da sai na kwantsama maka mari irin na gargaɗi akan furucinka, ku ban haɗin kai ku sanya min hijabi in yi abin da ya kawoni in tafi ina da abubuwan yi”
Cike da masifa fawwaz ya daka mata tsawa zai fara magana malam ya dakatar da shi tare da faɗin
“ku bamu hijab ɗin”
Duk cikinsu banda hajiya babu me hijab, dole sai da aka karɓo gyalen feenat hajiya ta rataye a kanta sannan aka sanya wa mairo hijabin, malam yace ina saurarenki, kai tsaye ta fara cewa
“ban so haurowa kan goɗiya ba kamar yadda na alqawarta wa kaina saidai naga zaku sha wuya sosai da waɗannan miyagu shiyasa nayi tasowar da ba shiri, duk da bana kusa abin da ya farun ya faru, ba sai na ce muku ga abin da yake faruwa ba, ku bar komai a hanuna babu abin da zai faru da ita da izinin Allah”
“ke kuma a matsayinki na wa”? Cewar fawwaz cikin gatsali
Hmmm tace ba tare da ta kalleshi ba, malam ne ya girgiza masa kai da nufin hanashi magana, sai ji sukayi tace “barshi yayi tambayar raininsa a gareni, ba laifinsa bane, rashin sanin ko ni wacece shi ya kawo haka”
“ya zama dole sai kin faɗa min ke wacece, me ya kawoki jikin matata”? Cewar fawwaz a hasale donshi a ganinshi rainin wayo take musu
A hasalen ita ta harareshi tace “sunanmu ɗaya da matarka, rauni da yawan kukanta da yawan shiga damuwarta ya kawoni jikinta saboda ina tausaya mata kana da abinda za kayine”?
Tsabar zafin rai irin na fawwaz ɗaga hannu yayi zai kifeta da mari sai kuma ya tuna fuskar maryam zai mara sai ya fasa yace
“malam ta fita min daga jikin mata kawai bana son zancen banza da wofi, maqaryaciya kawai”
Ya qarashe shima yana harararta
“lokacin da na santa kai baka santa ba, don haka duk wani tsanani ina tare da mairo domin ni garkuwace a gareta, ba zan taɓa baka damar da zaka rabani da ita ba, ka ci sa’a ba dan kyawawan halinka ba da ni maryam sai na ɗaga maka hankali, na barku lafiya, kuce wa maryam lallai akwai takwararta a tare da ita, zata gane ina tare da ita lokaci zuwa lokaci, kai ma haka jarumi fawwaz, malam kayi qoqari mun gode”
Tana gama faɗin haka ta yi bismillah, sai ganin mairo sukayi ta shimfiɗe a gurin
ISLAM IS MY IDENTITY
[9/4, 5:30 PM] Dr. Gital💉: 🌸🥀🌼🌼🥀🌸
🌸🌼🌸
*ZAKKATAH*
BY
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
~_*infacting valuable knowledge and entertaiment is our concern*_~👌🏻
*42*
‘Dagota fawwaz yayi daga qasa ya rungumeta a jikinsa ya sanya hannunsa yana ɗan bubbuga gefen kumatunta yana kiran sunanta
Kasancewar maryam bata taɓa shiga irin wannan yanayi ba yasa ta tsinci kanta cikin wani mawuyacin hali, ji tayi duk wani gaɓa na jikinta na mata ciwo lokacin da hankalinta ya dawo jikinta kamar wacce aka yi wa dukan talauci dan bana ce na tsiya ba😂
Tana ji ɗagata da fawwaz yayi daga qasa amma bata buɗe idanunta ba saboda wuya, sai da ya fara kiran sunanta sannan ta qoqarta ta buɗe idanunta da qyar ta kallesa saidai bata amsa ba sai ma wani irin qureshi da idanu da tayi
“maryam” ya sake cewa cikin tattausan murya cike da tausayinta a ranshi
Nan ma bata amsa ba sai hawaye da idanunta suka fara kwaranyarwa
Hajiya da take kallonsu cike da tausayinta tace “sannu maryama, sannu kin ji”
Sai a lokacin maryam ta san suna gurin, waigowa tayi ta kallesu, take wani kunya ya rufeta, ji tayi kamar ta nutse cikin qasa, ɗan sauran qarfin da ya rage mata ta tattara ta yunqura zata bar jikin fawwaz, taimaka mata yayi ta tashi ta zauna saidai duk da haka ya jinginar da ita a jikinsa, sunkuyar da kanta tayi qasa tana tambayar zuciyarta dalilin kasancewarsu a nan saidai bakinta ya mata nauyi sosai, ji takeyi ba za ta iya magana ba
Antyn raudat ma cike da tausayawa tace “ayyah mairo, sannu kin ji”
Nan ma ba magana sai kallonta da tayi ta gyaɗa kai, haka da auncle A ya gaisheta shima kan ta gyaɗa masa
Kallon malam Abdul-aziz fawwaz yayi cikin damuwa yace
“malam me yasa bata magana”?
Murmushi malam yayi yace “wannan ba wata matsala bane, ba zai wuce baqon yanayin da ta tsinci kanta a ciki ba, amma ai ka ga tana jin maganar da ake mata”
Hankalinsa ya mayar kan maryam yace “maryam kina jina ko”? Kai ta gyaɗa masa alamar tana ji
“yauwa to idan kina ji kiyi mana magana, kin ga mai gidanki hankalinsa ya tashi da rashin maganarki”
Motsa bakinta ta fara yi da qyar cikin murya qasa qasa tace “ina ji”
“mashaa Allah toh, yanzu ina ne yake miki ciwo”?
Nan ma da qyar tace “jikina” tare da ɗora hannunta a kafaɗarta
“zai bari shima inshaa Allahu, sannu kin ji”
Kai ta sake kaɗa masa, ƴya juya ya kalli fawwaz yace
“zamu bata magungunan da za tayi amfani da su inshaa Allah zata samu lafiya, qarfin jikin ma duk zai dawo, saidai ta kula da magungunan da kyau, yawan sauraro karatun kur’ani da yawan yin alola ba sai lokacin sallah ba, idan zata kwanta ma tayi sannan ta shafe jikinta da adduoin neman tsari, ta guji yawan shagalta da duniya, kallace kallacen banza da wofi da kiɗe kiɗe, idan ta kiyaye inshaa Allahu za ta samu lafiya da izinin Allah”
Tun kafin fawwaz yayi magana hajiya tace “toh mun gode sosai malam Allah ya jiqan mahaifa”
Ameen yace yana me nuna jin daɗinsa ga adduar
“yanzu ita wannan matar fa malam, haka za ta yi ta zama a jikinta”?
“eh toh kasancewar itama jinnunce idan har tabi qa’idojin da aka gindaya mata babu jinnun da zai raɓeta balle shiga jikinta, duk da ma ita wannan ɗin tace tana tare da ita ne kawai ba a cikin jikinta take ba”
“su waɗannan malam ai maqaryatane, gaskiyarsu ɗaya suke cuɗanyata cikin qarya ɗari”
“gaskiyane wannan, amma ba a rasa masu gaskiya cikinsu, saidai ba za mu gaskatata ba, ita dai ta yawanta sadaka ma domin maganin masiface”
Ita dai maryam jinsu take yi tana jin kanta yana mata wani dummm
Godiya sosai suka yi wa malam sannan suka biyashi kuɗaɗen da ya cajesu bayan ya harhaɗa mata magunguna sosai yace kuma azo a karɓi ruwan zamzam ɗin da zai mata adduoi a ciki
suka fice yana musu rakiya da fatan sauqi a gareta
Fawwaz yana riqe da maironshi qam kamar jinnun zasu zo su ɗauketa ya kaita motarshi ya sanyata a baya, su feenat suna ta so su gaisa amma shi da yake ba a masa gwaninta cewa yayi kar su dameta ba ta son hayaniya, drivernsa yayi wa umurni da ya kaisu gidan hajiya, a lokacin su hajiyar ma kowa ya shiga motar da ya zo a ciki sun ɗau hanya
Kusa da ita ya shiga ya zauna ya rufo qofar ya juyo ya kalleta
Gani yayi ta jingina bayanta ajikin seat ta rufe idanunta, kusa da ita ya matsa ya sanya hannunsa shafa kumatunta cikin tausayawa yace “amaryar gee fawwaz me ake tunawane”?
Murmushi ta qirqiro cikin jin kunyarsa ta girgiza kai
“babu”? Eh tace cikin gajiyayyar muryarta
Hannunsa ya sanya duka ya janyota jikinsa ya fara mata magana a hankali bayan ya ɗago fuskarta tana kallonsa
“kiyi hakuri kinji mairon fawwaz, ban san al’amarin haka yake ba na qaryataki, ashe lamarin babbane”
Murmushi tayi cikin jin kunya dan banda yau bata taɓa kusanci da shi irin haka ba, haka yasa ta ji ba za ma ta iya qoqartawa tace komai ba, hannunta ya mammatsa yace
“jikinki yana ciwo ko”?
Nan ma dai sak, kan ta sake kaɗa masa
Sake matsa hannun yayi yace “bari mu je gida toh sai ki sake yin wanka da ruwan zafi, duk dai inda wannan abu ya fito Allah ya ɗaiɗaitashi, ya nemi can wani gurin ba mairona ba”
Ya qarashe da murmushi ɗauke kan fuskarsa yana mata wani irin kallo
Rufe idanu mairo tayi kirif tana murmushi a ranta tana cewa yau mutumin nan yana ban kunya🤦🏻♀
Dariya taji yayi sannan ya sake gyara mata kwanciya a jikinsa ya cigaba da matsa mata hannu
*****
Motocin suna fakawa su hajiya suka firfito suka shige cikin gidan yayin da fawwaz yake kame da maironsa a cikin mota sai da yaga shigewarsu duka sannan ya ɗaga mairo daga jikinsa yace “mu je ko”?
“um”
Bismillah yayi tare da buɗe qofar ya fita sannan ya fito da ita ma yana riqe da hanunta suka shige cikin gidan
A babban falo ya samesu suna ta maimaita abin da ya faru cikin jajanta wa juna
Sannu suka yi ta mata tana amsawa a hankali sannan fawwaz ya kama hannunta yana cewa “bari ta huta, hayaniyar nan tayi yawa”
“ai kuwa dai, wannan irin wahala sai da hutu, Allah dai ya kawo sauqi” cewar auntyn raudat, ameen duka suka ce yayin da shi kuma ya wuce da ita cikin side ɗinsa na gidan
“wai wannan mata ta baban amrat tana ganin tattali, sai kace safiyyace ta dawo”
Haseenat kenan take faɗa wa mijinta da suke zaune da shi kan two seater
“wallahi kiyi ya jiki, ko dariyarsa ba za ki sake gani ba, kin san shi baya shiga rayuwar mutane kuma shima baya so a shiga tashi”
Da sauri ta ɗora tafin hanunta akan bakinta tace “nayi shiru”
“da ya fi miki” cewar arfat
Fitowa yayi da sauri ya fice ba tare da yayi magana da kowa ba, qaramin akwati ya dawo da shi a hannunsa wanda ya taho wa maryam da shi ya wuce nan ma bai ce komai ba suma kuma ba su mishi magana ba
“ga kayanki, ki je ki yi wankan sai ki zo kiyi sallah, nima sallah zan je na yi sai in shigo miki da magungunanki ki fara amfani da su bayan kin ci abinci ko”?
toh tace tare da miqewa tsaye, har toilet ɗin ya rakata ya haɗa mata ruwan wankan sannan ya fice
*****
Jam’i sukayi da arfat kafin arfat ya ɗauki matarsa suka tafi suna masa fatan Allah ya kiyaye gaba, antyn raudat ma tafiya tayi bayan tayi sallah tana wa mairo fatan sauqi
Minti biyar ya ɗauka yana wasa da amrat kafin ya wuce yana musu sai da safe tare da ɗaukar ledar magungunan
Samunta yayi a kwance har ta saka kayan barcinta saidai ta buga dogon hijab ta duqunqune
Sai da yaga abincin da aka kawo mata sannan ya tuna da maganar abinci amma daga gani bata ci abincin ba
Zama yayi daidai saitin kanta ya kalli fuskarta yace
“har kin yi me kenan”?
Lumshe idanu tayi tace “shirin bacci”
“abincin fa, na ga yadda aka kawo baki taɓa ba”
Yatsina fuska tayi cikin rigimar da ta fara koya gurin feenat tace “ba zan iya cin komai ba”
“in ji wa”?
“bakina”
“sauko ba za ki rasa wanda bakinki zai so ba”
Shagwaɓe murya tayi kamar za ta yi kuka tace “yah fawwaz ni gaskiya…..”
Yadda ya qureta da idanu yasa ta canza maganar da cewa “toh ni duk jikina fa ciwo yake min”😢
Murmushi yayi yace “toh daure ki ci ko kaɗan ne sai in baki magungunanki ki zo kiyi kwanciyar, idan kin yi bacci kin farka zaki daina jin ciwon jikin”
Sai da ta yatsina fuska ta kalleshi sannan ta tashi da qyar, hannunta ya riqe ya taimaka mata ya kaita gurin da aka jera musu abincin
Dole dole dai haka yayi ta yi wa maryam ta ɗan taɓa abincin kafin tace ta qoshi, magungunan ya bata ta sha sannan ya miqa mata na shafawar yace ta shafasu
Da hijab ɗinta a jikinta take ta dabara tana shafawa shiko yana ta binta idanu cikin tausayi, a rayuwarshi bai taɓa ganin abin tausayi irin maryam ba, yana tausaya wa rayuwarta sosai ko safiyya be tausaya mata irin tausayin da yake ji akan maryam ba domin ita safiyya maraicinta da gata, burinshi ya ga rayuwar maryam ta inganta ta yadda za ta yi alfahari da rayuwarta da aurensa
******
Shiryawa yayi cikin kayan barcinsa ya fesa turarukansa sannan ya haura gadon da take kwance abin da basu taɓa yi ba wato haɗa makwanci
“maryam ba kiyi bacci ba har yanzu”?
Um tace tana jan yatsunta
“wai ni har yanzu jikin bai bar ciwo bane”?
Gyaɗa masa kai tayi tana cigaba da jan yatsunta
Matsowa yayi kusa da ita yace “toh bari in ɗan mammatsa miki jikin ko?, me yuwuwa ki yi bacci ma yanzu”
Bai jira amsarta ba ya fara matsa mata jiki a hankali har zuwa qafafunta da hannayenta
ISLAM IS MY IDENTITY