Mun Bude Shirin (Npower portal) N-Power Kashi Na Uku- Minister Sadiyya

Mun Bude Shirin (Npower portal) N-Power Kashi Na Uku- Minister Sadiyya

Npower batch 3 portal

Majiyar mu ta Dala FM radio Kano ce ta sanarda wannan bayanin inda ta ruwaito cewa:

 Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin N-power rukuni na 3 zubin farko na mutane dubu biyar da goma a fadin kasar nan. 

Ministar jin kai da kare abkuwar ibtila’i da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Faruk ce ta bayyana hakan, a wajen kaddamar da shirin a Abuja. 

Ministar ta bayyana murnar ta ga wadanda suka samu damar shiga shirin, sai dai ta ce, rukuni na ukun an raba shi zuwa kashi biyu, da ya hadar da rukunin na uku zubin farko mai mutane dubu biyar da goma, sai rukuni na uku zubi na biyu mai mutane dubu hudu da dari tara. 

Hajiya Sadiya ta kuma ce, rukuni na uku Zubin farkon an tsara bai wa wadanda basu da takardar karatu, su dubu hudu da hamsin, yayin da mutane dubu shida na rukunin za a dauki masu takardar karatu. 

Source: Dala FM radio Kano

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top