Muna rokon Allah ya yi mana maganin Buhari idan har ba zai iya kare rayukan al’umma ba – Sheikh Nuru Khalifa

 Muna rokon Allah ya yi mana maganin Buhari idan har ba zai iya kare rayukan al’umma ba – Sheikh Nuru Khalifa

You are currently viewing Muna rokon Allah ya yi mana maganin Buhari idan har ba zai iya kare rayukan al’umma ba – Sheikh Nuru Khalid

Sheikh Muhammad Nuru Khalid

AIKA ZUWA SHAFUKAN SADARWASHARE THIS CONTENT

Opens in a new window

Twitter

Opens in a new window

Facebook

Opens in a new window

Google+

Opens in a new window

WhatsApp

Babban Limamin Masallacin Apo Legislative, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kasa tabuka komai da yake wajen kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Da yake bayani a wajen hudubar ranar Juma’a, Limamin ya ce shugaban kasar ya iske Najeriya a hade kasa guda daya, amma ya kyale ‘yan bindiga suna rike da wani bangare na kasar a yanzu.

Ku je ku sanar da shugaban kasa cewa a karkashin gwamnatinsa akwai wasu tsirarun mutane da suka zama barazana ga mazauna wasu wurare, sun bukaci su hada kudi ko kuma su kai musu hari, kuma anyi haka a jihar Zamfara, cewar Sheikh Khalid.

Kuma sun hada kudin, har sun sanar da BBC cewar za su biya ‘yan bindigar wannan kudi a yau Juma’a.

Ku gayawa shugaban kasar akwai kasar da muke da ita Najeriya, da kuma wacce bamu sani ba wacce ‘yan bindiga suke da iko da ita yanzu.

Ko dai shugaban kasar ya dawo da kasar kamar yadda ya same ta, ko kuma muna yi masa addu’ar Allah yayi mana maganinsa.

Wannan budadden sako ne kowa ya gani a duniya. Na yadda da duk wani abu da za ayi mini, kuma na shirya fuskantar duk wani hukunci da za ayi mini kan kira ga hadin kan Najeriya.

Ya mai girma shugaban kasa bama so muji ana fitar da rahoton kashe mutane a karkashin mulkin ka. Ba mu son jin labarin abin kunya ga sojojin mu, kamar wanda aka fitar makon nan na cewa an kai musu hari har gidansu.

Muna da bidiyon ka, inda kake cewa suna da kwarewa wajen kawo karshen matsala kowacce iri ce a kasar nan. Ka ce idan aka zabeka zaka basu duka goyon bayan da za su kawo karshen ta’addanci cikin kankakin lokaci.

Ya shugaban kasa alkawari kaya ne. Idan har baka da masu baka shawara kan yadda zaka kawo karshen wannan lamari, mu mun shirya mu sanar da kai. Muna addu’ar Allah ya baka ikon cika wannan alkawari daka dauka idan kana so ka cika, idan kuma baka so ka cika muna rokon Allah ya raba mu da kai.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top