Yadda Ake Hada Bakar Humra

 BAKAR HUMRA

1. mahala.

2. hawi.

3. Garin farce.

4. turaren marakana.

5. turaren sandol na ruwa Dan awo.

6. turaren amarya.

7. madarar turare aba rai dadi.

8. madarar turare Sudan.

9. turare me sanyi ruwa kalar da kike so Mara maiko.

Inda Zaki dake mahala dinki, bayan kin soya sama-sama sai ki dake ta tayi taushi, shima hawi ki dake ki tankade, Shima haka garin farcen.

Yadda Zaki hadashi shine ki zuba ruwan turarenki na marakana kwalba daya, sannan ki zuba turare sandol na ruwa gwangwani daya, turare amarya, ma gwangwanin daya, turare me sanyi ruwa Mara maiko kalar da kike so gwangwanin daya, kisa madara turare aba rai dadi cikin kwalbar fiya-fiya, ki sa garin mahala cokali biyu na abinci garin hawi cokali biyu, garin farcen ma cokali biyu, ki juya sosai , bayan ki gama hadawa sai ki rufe humrar har zuwa sati daya ko biyu ko sama Inda ta tsumu sosai tayi kamshi.

Zaki iya yin humra da ruwan turare amarya wato ya fi yawa turare marakana kuwa sai ki sa gwangwanin daya yadda dai kike so, wannan dakakken su farcen Zaki ga in kin zuba kwalba suna yin kasa,Amma zai saka humra ta dinga Kara tsumu wa tana Kara kamshi.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top