turaren alajin na ruwa ko na marakana ko na matan arewa
1. jan ambur
2. farin ambur
3. misik
4. madarar turaren
kwamando
5. madarar turaren suzan
6. madarar turaren sarkin
turare
7. madarar turaren sandol
8. madarar turaren
ismiyaki
zaki daka farin ambar guda uku,
sannan ki daka jan guda uku.
sai ki zuba a kan ruwan turaren alajin ko marajana ko matan arewa Wanda Allah ya baki ikon siya roba daya, ki sami misik dinki guda hudu ki
zuba a tukunya ko wani abin silver dai Wanda bazai manne ajiki ba ki dora a kan garwashi zai narke.
idan ya narke sai ki juye a cikin ruwan turaren da kika zuba garin
abubuwan, sannan ki daka misik ki sa cokali uku sannan ki juya gaba daya ya juyu sosai sai ki sama kwalba ko roba kamar 3 liters ki zuba ki rufe ya tsumu, wannan garin misik dinda ambar din shi zai dinga kara tsuma humra ta
dinga kara kamshi za ki iya rufewa kwana bakwai ko zuwa sati biyu ta tsumu.