Yadda Akeyin kilishi

 

Kilishi

Kilishi dai nama ne da akasari ake yin shi a yankin da Hausawa suke a arewacin Najeriya, ko arewacin lardin Kamaru, ko a yankin jamhoriyar Nijar. Ana yin kilishi ne dai da naman shanu, ko rago, ko akuya, ko na rakumi. Ma’abota kilishi sun bayyana shi da zabebben nama wanda sai asalin mahauci dan gado ke yin shi. Mafi shaharar kilishi dai da naman shanu ake yin shi, saboda haka a sakamakon yawaitar shanu a yankin da Hausawa suke ya kai ga haifar da wasu kwararru a harkar gudanar da sana’ar yin kilishi.

Atakaice dai ba a yin kilishi da tsohowar dabba, (dangin shanu, awaki ko raguna); domin yi da tsohon dabba na sa kilishi rashin yin dadi da kuma tauri. Har ila yau ba a cika son yin kilishi da nama mai kitse dayawa ba. Dole ne sai an sami nama mai laushi wanda ba zai kuma ba da wahala ba yayin yanyanawa. Yanyana a nan dai na nufin fere ko tsele nama da za a yi kilishi da shi. Iya firar kuma ko shele naman da za a yi kilishi da shi na nuna kwarewar mai sana’ar, saboda hakan na daya daga cikin sharrudan iya yin kilishi.

Bayan mai Kilishi ya fere naman da za a yi kilishin da shi, sai kuma abu na gaba wanda shi ne shanya, wato shanya naman a rana don ya bushe, wanda akasari dai bushewar kan dauki kwanaki a kalla 5 in da rana in kuma babu rana to ya kan dauki kwanaki 10 kafin namar ta bushe yadda ake so.

Bayan an shanya naman sai kuma a yi kokarin kayan hadi; wanda suka hada da: maggi, gishiri, aya, soyeyyen gyada, barkono, shitta, kanamfari, masoro, albasa, da dai sauran su. Yayin da aka tabbatar nama ya bushe yadda ake so sai a yi hadi don sarrafa naman zuwa kilishi.

Bayan hada kayakin a kan dauko busheshen nama a gauraya ciki, sannan a mai da shi rana don sake bushewa a zango na biyu. Bayan naman ya bushe tare da kayakin hadin a tare da shi, sai kuma a gasa shi a wutan tukuba don samun kayakin hadin su shiga jikin naman yadda ake so

Atakaice dai waddannan su ne mata kai da ake bi don yin Kilishi a kasar Hausa.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top