Yadda ake spinach soup
![]() |
Spinach soup |
Barkanmu da sake saduwa a fanninmu na girke-girke. A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake spinach soup.
Abubuwan hadawa
1. Alaiyaho
2. Dafaffafiyar ganda
3. Dafaffafen kayan ciki
4. Dafaffafen kwai (ki bare bawon)
5. Dafaffafen kifi
6. Ganyen curry
7. Albasa
8. Dafaffen markadadden kayan miya
9. Tumatur na gwangwani
10. Kayan kamshi
11. Maggi
12. Man gyada
13. Lawashi
Yadda ake hadawa
1. Ki dauko alaiyahonki ki gyara shi ba sai kin yanka ba, sai ki wanke da gishiri ki zuba mishi tafasashshe ruwan zafi ki rufe nadan wani lokaci. Sai ki tace a colender. Ajiye a gefe.
2. Daura tukunyanki akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama. Sai ki kawo tumatur na gwangwani ki sa ki juya ki soya sama sama.
3. Sai ki kawo dafaffafen kayan miya ki zuba a ciki ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin.
4. Dauko ganda, kayan ciki, kifi, kayan kamshi, maggi (iya dandano da zai miki ki zuba a ciki ki juya ki rufe tukunya nadan wani lokaci sai ki kawo dafaffafen kwanki ki sa ki juya.
5. Dauko alaiyahonki ki sa a ciki ki juya ki kawo ganyen curry da lawashi ki sa ki juya kidan barshi ya turaru kadan sai ki sauke.
Ana iya cin wannann miyar da ko wani irin tuwo, kamar tuwon shinkafa da couscous da dai sauransu. A ci dadi Lafiya.