Yadda Akeyin Miyar Wake

MIYAR WAKE

Miyar Wake

1.Wake.

2.Manja.

3.kayan Miya.

4.Bushenshen kifi. 5.Albasa.

6.Maggi.

7.Kori.

8.Gishiri.

Yanda ake hadawa:

Da farko dai zaki surfe wakenki ki wanke ya fita sosai Sai ki dora ruwan ki a wuta ya tafasa, sai ki zuba wakenki ya yi ta dahuwa har sai ya nuna ya yi taushi ,Sai ki zuba jajjagaggen kayan miyanki, da albasa, da manja, da kifinki,(bacin kin gyara shi kin wanke shi da ruwan zafi, se ki zuba soyayyen manjan ki, sai ki jira miyanki har sai ya tatafasa.

Za ki ji yana kamshi Sai ki zuba maggi, da kori, da kayan qamshi, da gishiri, sai ki barshi kamar minti sha biyar za ki ji gida ya dau kamshi, Da zarar kin duba miyarki tayi shikenan sai ki sauke.

Zaki iya cin miyanki da tuwon shinkafa ko masara ko semonbita ko taiba.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top