Yadda Akeyin Turaren Wuta Na Daki

 TURAREN WUTA NA DAKI

1. Garin farce.

2. sukari.

3. lemon tsami.

4. jawur fari.

5. misik.

6. garin sandol.

7. madara turare Jamila.

8. wanis.

9. sabon yayi.

10. Binta Sudan.

11. kamfani.

12. naludu.

13. Dan duwala.

14. kafin kafi.

15. aba rai dadi.

16. turaren ruwa Mai maiko.

ma’ana madara turare

Yadda Zaki yi ki samu itacen al’ud dinki kilo daya, ko biyu, sai ki jika shi a madara turare Jamila da madarar turare wanis,da madara turare sabon yayi , sannan ki sa turarenki mai maiko na ruwa irin Wanda ake aunawa, a dogwayen kwalabe sai ki jika da wadannan turaruka ki rufe ki barshi ya jiku har yayi kwana bakwai, bayan sati daya sai ki bude itacen al’ud din da kika jika da turare, idan al’ud din kilo biyu ne sai ki sa gwangwanin daya, idan kuma kilo daya ne sai ki sa gwangwanin daya, idan sukarin gwangwanin biyu ne sai ki sa gwangwanin daya, idan sukarin gwangwanin biyu ne sai ki zuba ruwa cikin karamin roba, ki matsa lemon tsami, hudu a Kai, ruwan sukari sugar, idan kuma gwangwanin daya ne sai ki zuba ruwa Rabin karamin Kofi, ki matsa lemon tsami biyu a Kai, sannan ki saka garin jawur cokali daya, da ruwan lemon tsami, sukarin kisa miski kwaya uku a ciki, sannan ki Debi garin farce, da kika barza ki zuba, kadan a Kai, idan kin zuba sai ki barshi yayi ta dahuwa har sai ruwan sukarin ya Fara ja, sannan ki zuba garin sandol dinki, a Kai da garin dakakken miski , da garin dakakken jawul, da barzajjen farcen duk ki zuba a Kai, ki juya sosai, sannan ki zuba madara turare Binta Sudan, da madara turare Dan duwala, da madara turare kafin kafi, da madara turare sandol, da madara turare aba rai dadi, ki zuba a kan turare al’ud din da kika baza a faranti, madara Zaki Iya yadda kike so sannan ki juya sosai, sai ki zuba a kwalabe kuma Zaki kuma zuzzuba madara turare a Kai

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top