CABBAGE ROLLS
Cabbage rolls |
Cabbage
markadadden nama
attaruhu,albasa
magi,gishiri,
curry,tafarnuwa
mai,
Zaki jajjaga attaruhunki da albasa ki soyasu da garin tafarnuwa da curry da magi,gishiri ya soyu sai ki kawo markadadden namanki shima ki zuba a ciki ki cigaba da juyawa har ya hade jikinsa,
sai ki dauko cabbage dinki ki ciccireshi falle-falle ki wankeshi ki tafasashi yayi laushi sai ki sauke shi ki dauko wannan hadin ki dinga zubawa kina nadewa kamar haka,sai ki aje har ki gama sannan ki dauko jar miyarki dakika soya me dan ruwa ruwa sai ki sassaka sannan ki mayar ki dada dafashi kadan,ana ci da farar shinkafa,
Agajahub publishers