Da dumi-dumi: Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu

  Da dumi-dumi: Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu 

 

 niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin sabuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (NNPP) Barista Olusegun Bamgbose, ya mutu Bamgbose ya mutu ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, bayan gajeriyar rashin lafiya Babban daraktan FENRA, Kwamared Nelson Nnanna Nwafor ya tabbatar da mutuwar dan siyasan DUBA NAN: Danna “See First” karkashin karkashin “Following “ don samun labaran Legit.ng a shafinka na Facebook akai-akai Barista Olusegun Bamgbose, me niyyar takarar kujerar shugaban kasa na sabuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (NNPP) ya rasu.

 Bamgbose wanda ya kasance jagoran kungiyar masu fafutukar neman shugabanci nagari (CAGG) ya rasu a ranar Juma’a, 17 ga watan Satumba, bayan gajeriyar rashin lafiya, Daily Post da PM News sun ruwaito. 

Me niyyar takarar kujerar shugaban kasa a 2023 ya mutu Source: UGC Da take magana kan rasuwar dan siyasar, Gidauniyar FENRAD, ta bayyana shi a matsayin babban muryar lamuran shugabanci nagari da fafutukar kare haƙƙin ɗan adam. Babban daraktan FENRA, Kwamared Nelson Nnanna Nwafor, ya bayyana cewa Bamgbose a rayuwarsa bai taba yin kasa a gwiwa ba wajen kula da gwamnatoci yayin da ya ba da gudummawa ga muhimman batutuwan gina kasa. 

 Nwafor ya ce: “Ta hanyar sa bakinsa da ayyukansa, gwamnati ta sassauta manufofi da yawa da ba sani ba. Mutumin kirki ne, mai aiki tuƙuru, ƙaunataccen miji, uba da aboki ga kowa. Tawali’unsa, da yadda yake tafiyar da lamura ya sa mutane da yawa suka ƙaunace shi. A duk tsawon zaman sa a duniya, ya himmatu ga haɓakawa tare da kare muhalli, ɗan adam, da haƙƙin dimokiraɗiyya waɗanda suka yi daidai da manufofin FENRAD. “

Lallai mun yi baƙin ciki da wannan rashi kuma muna addu’a gaAllah, a cikin wannan mawuyacin lokaci, ya ba wa danginsa ƙarfin jure wannan babban rashi; Haka kuma muna yin addu’a ga abokansa, abokan aiki da waɗanda wannan rashi ya shafa.”

 A wani labari na daban, gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya ce duk wata jam’iyyar siyasa da ta tsayar da dan takarar arewa a matsayin shugaban kasa a 2023 na iya rasa goyon bayan mutanen kudu. 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top