Daraktoci sun daina sakani a Fim, Babu abin da zan zaba, Aure kawai zanyi na zauna a gidan mijina
![]() |
Officiall maryambooth |
Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Booth, wacce mahaifiyarta Allah ya yi mata rasuwa a kwanan nan Zainab Booth ta shaidawa kafafen yaɗa labarai dalilin da yasa masu shirya fina-finai (Producers) suka daina sakata a cikin fina-funan su. Jarumar ta alaƙanta hakan da bayyanar bidiyon tsiraicinta a shekarun baya kamar yadda Neptune Prime ta ruwaito
“Tun ina ƙarama na kasance ina fitowa a fina-finan Kannywood, saboda mahaifiyata Hajiya Zainab Booth(Allah ya saka mata da gidan Aljanna) ta daɗe a cikin masana’antar, don haka ban taba daina fitowa a fina-finai haka kawai ba. Amma tunda wani matashi da ake ƙira Dezeel wanda ya yi ikirarin cewa saurayina ne ya bayyana hotunan tsiraici na a kafafen sada zumunta, yanzu mutane na yi min kallon ƴar isaka mara tarbiyya”. In ji ta.
Maryam Booth wadda Hausa Daily Times ta gano a yanzu haka ta koma Babban Birnin Tarayya Abuja da zama tare da ƙaninta Amude Booth tun bayan rasuwan mahaifiyar su, ta ce a duk lokacin da mutane suka ganta yanzu a cikin gari sai su yi ta nuna ta suna ƙiranta da karuwa ko mace mara kunya.
Jarumar ta koka kan yadda alaƙa ta yi tsami tsakaninta da wasu abokan sana’arta da a da suke da matuƙar shaƙƙuwa, a yanzu babu abin da ya rage mata da za ta zaba da ya wuce yin aure a matsayin hanyar samun zaman lafiyar da za ta zauna a gidan mijinta.