Duk da tallafin gwamnatin tarayya, ‘Yan Najeriya na ci gaba da fama da bakin talauci
![]() |
Cbn anchor browers |
Gwamnatin tarayya ta samar da shirye-shiryen tallafawa mutane da dama ta hanyar bada jari ko bada kudi kyauta
A watan Nuwamba na shekarar 2020 ne Rahoton hukumar dake kula da Talaucin Duniya ta bayyana cewa, Najeriya ta zarta kasar India a yawan matalauta inda ta zamo ta daya a Duniya.
Endpoverty.org tace daga cikin mutanen Najeriya Miliyan 200, miliyan 90 na cikin bakin talauci.
Bankin Duniya ya bayyana talauci da cewa, mutanen da basa samun Dala 1.90 a rana.
Saidai ba matsalar gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari bane, kamar yanda Rahoton ya nunar. An samu matsalar ne tun bayan dawowar mulkin Dimokradiyya har yanzu.
Agajahub publishers