Jarumar Kannywood Fati Muhammad Na Neman Mijin Aure

 TANA NEMAN MIJIN AURE

Jarumar Kannywood Fati Muhammad

Kamar yadda kamfanin jaridar Dokin Karfe TV suka ruwaito labarin, tsohuwar tauraruwa a masana’antar Hausa film wanda aka fara da ita tun farko wato Fati Muhammad, ta fito tana shelantawa duniya cewa tana neman mijin aure

Fati tace: “Na shirya tsaf ina neman miji na gari domin nayi aure”

Wannan shine karshen kyawawan matan da suka sadaukar da kyawun surarsu a aikin banza, tun lokacin da suke da jini a jika ake musu nasiha su watsar da wannan sana’ar banza suyi aure amma basa yi, saboda duniya tana musu huduba

Wannan babban darasi ne ga duk wata yarinya mai gigiwa da taurin kai wacce taki yin aure ta kama sana’ar film, dama ance ba farkon ba karshen, ai ko ba mutuwa akwai tsufa, kamar yadda Fati ta tsufa ta dawo tana neman miji

Yaa Allah Ka bawa Fati irin mijin da ya dace da ita, Ka karemu daga sharrin ‘yan Hausa film Amin.

Daga Datti Assalafiy.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top