Kalli Hotunan Sabuwar Jaruma, Yaseerah Babangida da Kannywood Ta Gabatar
![]() |
Yaseera Babangida sabuwar Jarumar Kannywood |
Kannywood tayi matukar farin cikin gabatar da sabuwar Jarumar su, Yaseerah Babangida ga jama’a, masana’antar ta hau shafin su na Instagram don taya yaseerah murnar shigowa masana’antar.
![]() |
Yaseera kannywood |
Ta fara wasan ta na farko a cikin jerin fina finai film mai taken (Bugun Zuciyar Masoya) inda ta fito a fage daya kawai, a cewar daraktan fim din, Nura mustapha waye, ya ce jarumar tana da hazaka kuma tana bukatar tallafi don ta zama babbar Jaruma.
Nura mustapha ya bayyana cewa a shirye yake ya sake ba ta dama a film din sa mai zuwa.
Yaseerah ta fito daga jihar kaduna, Najeriya, tuni ta fara samun mabiya a shafukan sada zumunta yayin da take bude sabon shafin masoya a Instagram.
Masu ruwa da tsaki na Kannywood na kawo ƙarin ‘Yan wasan kwaikwayo don taimakawa masana’antar ta bunƙasa.