Kamfanin iPhone ya kera iPhone 13 Pro Max, wayar da ba a taba irinta ba a Girman Storage ( 1TB) Da Sauransu Duba Farashinta dasauransu Anan
![]() |
Kamfanin iPhone ya kera iPhone 13 Pro Max, wayar da ba a taba irinta ba a Girman Storage ( 1TB) Da Sauransu Duba Farashinta dasauransu Anan |
Babban kamfanin fasaha na Apple ya sake fitar sabuwar fasahar waya mai ban al’jabi A wannan karon, iPhone za ta fito da ma’ajiyar bayanai da baa taba yin wata mai irinsa ba Wannan ci gaba ya fito ne daga bakin wani shugaban na Apple a jiya Talata 14 ga Satumba DUBA NAN: Danna “See First” karkashin karkashin “Following “ don samun labaran Legit.ng a shafinka na Facebook akai-akai Babban kamfanin fasaha na Apple ya sanar da kirkirar sabuwar waya mai suna iPhone 13 Pro, irinta na farko wanda ke ba da ma’ajiyar bayanai Terabyte daya (1TB), yana bawa masu amfani da iPhone damar adana bayanai kwatankwacin na iPhone 13 sau biyu. An sanar da sabon samfurin yayin taron yanar gizo da kamfanin a ranar Talata 14 ga watan Satumba, in ji rahotom Peoples Gazette. Kodayake kamfanin fasahar a baya ya daura ma’ajiyar bayanai 1TB a kan iPad, samfuran iPhone suna da adadin ajiyar da a kai 512GB. READ ALSO Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin ‘yan bindiga a NDA Samfurin iPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max | Hoto: popsugar-assets.com Source: UGC Greg Joswiak, Babban Mataimakin Shugaban kamfanin Apple shashen tallace-tallace na duniya, a wurin taron ya bayyana cewa: “IPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max sune mafi kyawun samfuran iPhone na yau da kullum tare da mafi girman ci gaba a tsarin kyamarar mu, mafi kyawun kargin batir a cikin iPhone, da mafi kyawun wajen saurin aiki, saita sabon ma’auni na iPhone da ba da damar abubuwan ban mamaki da ba a taba yi ba.”
Apple kuma ya ba da sanarwar yana habaka ma’ajiyar iPhone akan daidaitattun samfuran sa.
Ya batun farashi? Farashin farko na iPhone a ranar fitar da ita zai fara a $999 kuma za a fara jigilar ta a ranar 24 ga Satumba.
Zabin 1TB akan iPhone 13 Pro zai sauki farashin $1,499 da $ 1,599 akan babban iPhone 13 Pro Max.
Ga Table na Farashin sabuwar Iphone 13 pro Max
![]() |
Table na Farashin iphone 13 pro Max |
Farashin iphone 13 128GB Storage in Nigerian Naira.
Farashin iphone 13 pro 256GB of storage
Farashin iphone 13 512GB of storage
Farashin iphone 13 1TB of storage
Sabuwar iPhone din na da jerin sabbin abubuwan ingantayya da sabuntawa wadanda suka hada da karamin kira, sabbin fasalolin kyamara wadanda ke ba masu amfani sigar bidiyo na yanayin hoto da zabin daukar bidiyo mai inganci da ake kira ProRes.
Za a iya samun iPhone 13 Pro da iPhone 13 Pro Max a cikin launuka hudu; ruwan toka, ruwan zinariya, ruwan azurfa, da shudi, kamar yadda CNET Tech ta ruwaito.
Sabbin abubuwa
Sabuwar iPhone din ta kunshi guntun karfe mai sauri na A15, da kuma fuska mafi haske, da karfin batirin da zai kai tsawon sa’oi biyu da rabi, kana ta zo da sabbin launuka da suka hada da ruwan hoda, da shudi, da ja, da baki da kuma fari.
iPhone13 colours
![]() |
Iphone 13 pro Max colour |
Sabuwar wayar ta iPhone na kuma da ma’ajiya mai daukar nauyin gigabait 500(500GB) wanda mafi karancin ma’ajiyarta ke kai wa har gigabait 128 (128GB) idan aka kwatanta da samfurin irinta na baya masu nauyin gigabait 64 (64GB) kawai.
Apple ya kuma bugi kirjin nuna goyon bayansa wajen kare muhalli, yana mai cewa an sarrafa wayar da kayyaki da dama da aka gama amfani da su – da suka hada da wayoyin eriyar da aka sarrafa daga robobin ruwan sha.
Kaddamarwar na zuwa ne a yayin da masu sayen ke cigaba da barin wayoyinsu na kai wa tsawon lokaci kafin su kara inganta su.
Kamfanin zuba jari na Wedbush Securities ya kididdige cewa masu amfani da wayoyin na iPhone kusan miliyan dari biyu da hamsin ne bas u inganta wayoyin na sub a har na tsawon shekara uku da rabi.
Paolo Pescatore, wani mai sharhi ne a hukumar PP Foresight da ya bayyana cewa da dama har yanzu ba su samu amfana da sabbin fasalin wayoyi na zamani ba.
“A yayin da da dama za su dauki inganta wayoyin a matsayin karuwa, akwai miliyoyin masu amfani da wayoyin da har yanzu ba su inganta su zuwa fasahar intanet ta 5G ba,” ya ce.
Ana iya amfani da fasahar intanet ta 5G ne kawai a kan samfurin wayar iPhone 12, wacce aka fitar cikin shekarar da ta gabata, da kuma sabbin samfurin da aka sanar.
A cikin watanni ukun tsakiyar wannan shekarar, kamfanin Apple ya sayar da kusan kasha uku bisa dari (25.9%) na duka wayoyinsa masu amfani da fasahar intanet ta 5G a fadin duniya, kamar yadda kamfanin IDC na ma sharhin ya bayyana.
Marta Pinto, babban manajan bincike a kamfanin na IDC ya ce: “Da wannan sabon matsayi, wadannan alkaluma za su karu tare da kara karfi wajen maye gurbin mamayar da kamfanin Apple ya yi a wancan gurbin.”
“Rashin kasancewa na farko wajen Not being the first [kaddamar da wayoyi masu amfani da fasahar 5G] ya yi amfani.”
Shi ma kamfanin Apple ya kaddamar da samfurin kananan wayoyi na iPhone 13 Mini, da Pro da kuma Pro Max.
Samufurin wayoyin iPhone 13, da Pro da kuma Pro Max na kunshe da kyamarori uku kuma wanda Apple din ke kira ” tsari n kyamara mafi inganci a yanzu”.