Mukoma kitchen- Yadda Akeyin Cincin a Gida

Yadda Akeyin Cincin a Gida

  Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka, da fatan iyali suna lafiya. Yau za muyi cin-cin

Abubuwan hadawa

Filawa mudu daya

Kwai 4

Suga

Baking powder

Gishiri

Man gyada

Kwakwa 1

Filebo (favour)

Butter

Yadda ake hadawa

Da farko za ki sami roba mai dan fadi sai ki tankade fulawarki ki fasa kwanki ki sa butter da gishiri kadan da baking powder da filebo.

Sai ki jika suganki da ruwa Idan ya narke sai ki kwaba fulawarki ya yi tauri ba canba yanda za ki iya murzashi a tire.

Sai ki dauko tirenki mai fadi ki shafa mai kadan, sai ki rika murzawa in ya yi fadi kamar kaurin tafin hannu ko kasa da haka, sai ki yanka kanana kamar yankan suga cube.

Idan kin gama sai ki dauko kaskonki ki dora a wuta ki sa manki idan ya yi zafi sai ki zuba ki soya har sai ya yi brown sannan ki kwashe. Haka za ki ta yi har yak are.

Ana iya ci da juice, ko shayi ko dai da duk wani drink da mutun ya ke so.

Taku a kullum, Rabiat Muhammad Babanyaya, mai fatan jin dadinku koda yaushe. Na gode.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top