Sadiya Kabala – Mutuwar auren da nayi a Jos shine abin takaicin da bazan taba mantawa da shi ba

 Sadiya Kabala – Mutuwar auren da nayi a Jos shine abin takaicin da bazan taba mantawa da shiba 

Sadiya Kabala – Mutuwar auren da nayi a Jos shine abin takaicin da bazan taba mantawa da shi ba

A wata hira da BBC Hausa ta yi da tsohuwar jarumar Kannywood Sadiya Kabala, a cikin shirin su na ‘Daga Bakin Mai Ita’, Sadiya ta amsa tambayoyi da dama bisa ga yadda shirin yake, an yiwa tsohuwar jarumar tambayoyi da suka shafi sana’arta, rayuwar ta, da dai sauran su.

Sadiya Kabala ta bayyana mutuwar auren da tayi a garin Jos, wanda a cewar ta akwai wani abin bakin ciki da ya faru wanda har ta koma ga Allah ba za ta taba mantawa da shi ba, inda hakan bai rasa nasaba da irin rabuwar da suka yi da mijin bayan wata biyu zuwa uku da yin auren.

Sadiyya kabala

Sadiya Kabala

Idan ba a manta ba, jim kadan bayan mutuwar auren ta, Mujallar Fim ta yi hira da tsohon mijin na ta, inda a cikin hirar ya bayyana cewa Sadiya maza take kawo masa gida shi yasa ya sake ta.

Sai dai wannan labari ya dauki hankulan mutane matuka, domin kuwa jarumar tayi ta jin maganganu daga bakin mutane kala-kala marasa dadi, yayin da wasu kuma ke ganin laifin mijin na yi mata bita da kulli bayan saki ya bita da bata suna.

Bayan haka a cikin hirar Sadiya Kabala ta bayyana cewa har ya zuwa yanzu ba ta yanke shawarar cigaba da harkar fim ba tukunna, inda kowa ya san cewa bayan mutuwar aurenta na baya-bayan nan da tayi a Abuja, wanda bai dore ba ta mayar da hankali a harkar kasuwanci.

Baya ga haka Sadiya Kabala ta bayyana cewa idan ta tuna iyayenta da ‘yan uwanta suna raye, tana kuma tare da su hakan yana faranta mata rai matuka, da dai sauran wasu amsoshin tambayoyi da aka yi mata, ga dai yadda hirar ta su ta kaya:

Har yanzu ban samu mijin da ya dace na aura ba – Adamar Kamaye

Fitacciyar jaruman nan kuma wacce ta yi suna a cikin shirin nan mai dogon zango na “Dadin Kowa”, Hajiya Zaahra’u Sale wacce aka fi sani da Adamar Kamaye.

Jarumar ta bayyana burin da take dashi na yin aure, a kowanne lokaci matukar ta samu irin mijin da take mafarkin samu a rayuwa.

Fitacciyar jarumar ta sanar da haka ne a wata hira da tayi da jaridar Dimukaradiyya, inda suke tambayar ta ko tana da sha’awar yin aure kuwa, ganin yadda shekarunta suka ja.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top