Wacce Ake Zaton Itace Mahaifiyar Ummi Rahab Ta Karyata Zancen Karanta Cikakken Bayanin Yadda Tattaunawar Takasance Anan

 Wacce Ake Zaton Itace Mahaifiyar Ummi Rahab Ta Karyata Zancen

Ummi Rahab

kwana biyu dai rikicin Ummi Rahab Da Mai gidanta Adam A Zango yayi sauki, wadda takai ga anfara binciken asalinta.

Yaseer Rahab daya kira kanshi da yayanta kuma mai rikonta ya bayyana wasu hotuna mai dauke da miji da mata, inda ya tabbatar da mutanen jikin hotunan nan a matsayin iyayen Jaruma Ummi Rahab.

sai dai wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuni wata mata da ta fito take ikirarin ba itace Mahaifiyar Jaruma Ummi Rahab ba hasalim ita bata da wata alaka ta kusa kota nesa da jarumar.

Ga dai abinda matar ta ce bayan wata mai suna fardous00 ta yi mata tambayar cewa ko ita ce Babar Ummi Rahab, sai ta ce:

To Firdausi zan baki amsar ki, da kika ce ko kece babar Ummi Rahab, ni ba Babar Ummi Rahab bace, ban taba ganinta ido da ido ba, amma ‘yar uwata ce a Musulunci, shine kawai iya abinda na sani. Mutane da dama suna tambayata ina da alaka da ita, bani da alaka da ita gaskiya.

Haka ita ma wata mai suna yarmama25 ta sake cewa ta ga an sanya hotonta da wani balarabe akan cewa sune iyayenta, sai ta ce:

Na gaji da amsa wannan tambayar, na riga da tun farko na bayyana cewa bani da alaka da ita, ban kuma san Ummi Rahab ba sai dai kawai alaka ta Musulunci, tiktok ku shaida na yi ‘ya daga yau nima na huta da amsa wannan tambayar.

Tashar Tsakar gida sun tambayi Yaseer yayan ummi rahab akan lamarin matar ya sanar da su cewa , wannan matar tayi kama ne da matar da ke jikin hoton daya saki amma ba itace mahaifiyarta ba, yace mahaifiyar Ummi Rahab tana nan kawai dai kama ne sukai da waccar matar

Ko me zaku ce?

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top