Abubuwan da zaki Nema
Yadda Akeyin Kunun Waken Suya
![]() |
Waken Suya |
1.Waken suya
2. Sugar
3. Flavor
Yanda ake yi
1 .Da farko zaki gyara waken ki ki cire tsakuwa da dauda, sai ki jika shi ya
kwana.
2. Da safe sai ki wanke ki rege, sai ki markada ko ki kai a markado miki
3. Idan kin gama sai ki tace ruwan ki cire dusar. Ki yi amfani da matacin koko
ba Rariya ba
4. Sai ki dora tacaccen ruwan a kan wuta ki barshi yayi ta dahuwa har sai gafin
sa ya fita
5. Ki sauke ki barshi ya sha iska, sai ki zuba flavor irin kanshin da
kike so da kuma sugar dai dai misali
6. Ki saka a fridge yayi sanyi
Ga sauki, ga dadi, ga bada lafiya
Agajahub publishers