Batun sauke manhajar E-Naira daga Playstore ya Sanya wasu sundauki Zafi akan Yan crypto- Nasir Nk
Nasan Daman duk abinda gwamnatin Nigeria zatayi indai zai hada da online zaka sameshi mara inganci .
Wai abin tambayar anan shine ?
Federal government dince Bata iya biyan kamfanin software ko portals din ne da har basa iya yin Mai inganci ko kuwa?
Ko Kuma kamfanin Basu da developers din da suka iya app ko website Mai inganci ne?
Wani abin bakin ciki zakaga da portal na gwabnati ya samu ziyarar mutane 1m zakaga ya fara makalewa idan ka bincika
bandwidth na portal din Sai kaga Bai wuce 2gb bandwidth ba.
A shekarar data gabata mukayi hasashe Akan kudin hada portal na empower din 2020 wih Bai wuce 200k Amma Wai Sai kaga Yana Hucking idan ana kokarin shiga domin submit na form.
Amma da aka Fadi adadin abinda aka ware na hada wannan portal din wlh Sai da masana akan website developers sukayi Allah wadai da wannan aikin domin wanna portal din ko unlimited bandwidth Bai samu ba.
A Nigeria ne kawai ake lunching abinda ba,a kammala hadashi ba .
Kuma ko kunya masana akan hanyar sadarwa basaji idan zasu kaddamar dashi kodan sunga majority mutanan kasar Basu San komai akan abinda ya shafi wannan bangaren ba.