Jaruma Saratu Daso ta janyowa kanta cece-kuce da zagi akan wata bidiyo data wallafa a shafinta na TikTok

Shahararriyar jarumar wasan kwaikwayo wanda fitowa a matsayin uwa a cikin fina-finan masana’antar kannywood wato, Saratu Daso, ta wallafa wata bidiyo wanda ta janyo mata cece-kuce a shafinta na TikTok.

A wata bidiyo da mukaci karo da ita wanda wata budurwa ta bayyana a cikin bidiyon tana Allah wadai da abubuwan da jaruma Saratu Daso take yi a shafinta TikTok.

Budurwar wanda ita ma jaruma ce a masana’antar kannywood ta bayyana tana korafi akan cewa, ya kamata ayiwa Saratu Daso magana akan abubuwan da take aikatawa wanda basu dace ba, ya kamata ta daina irin wadannan abubuwan domin idan tayi ma ba burge mutane take ba sai dai ma ta janyowa kanta magana sannan kuma mutuncinta ya zube.

Kamar yadda kowa yasan Rolle din da jaruma Saratu Daso take dauka a shirin fina-finan kannywood, tana fitowa ne a matsayin mahaifiya wanda take fada aji sannan kuma tana da zafi akan al’amuranta idan ta fito a matsayin mahaifiya ko kuma shugaba.

Amma duk wadannan abubuwan da take ba wai yana nufin a gaske ma haka take ba kawai dai tana nuna wannan izzar tata ne a cikin fim duba da Rolle din da ake bata.

Haka kuma wani lokacin mutane suna duba da wani abu duk wata mace da aka ce zata bayyana a cikin shirin fim to dan tayi wani abu ma a manhajar TikTok ko wani abu wanda zai janyo mata cece-kuce, inda hakan bai sa tsiraicin jarumar ya fita to babu wani laifi kuma ba abin magana bane.

Amma sai wannan budurwar ta bayyana a cikin wata bidiyo inda take korafi akan wata bidiyo da Saratu Daso ta wallafa, wanda ita budrwar take ganin wannan bidiyo da Saratu Daso ta wallafa zata ita janyowa masana’antar kannywood cece-kuce da maganganu, duba da ita ma babba ce a masana’antar ta kannywood.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top