Nigerian eNaira: Muhimmin Bayanin Hanya 10 ta soma amfani da tsarin kudin intanet na Najeriya

eNaira: Muhimmin Bayanin Hanya 10 ta soma amfani da tsarin kudin intanet na Najeriya 

BBC HAUSA, Legit ng, daily trust, Aminiya, CBN sune jigon hada wanan rahoton dangane da Hanyoyin da zakabi domin fara amfani da eNaira,

wBabban bankin Najeriya ya bayyana hanyoyin da za a yi amfani da sabon tsarinsa na kuɗin intanet da ake kira eNaira.

A ranar Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ƙaddamar da kuɗin na intanet.

e-Naira tsarin kuɗin Najeriya ne za a yi hada-hada ta intanet. Wannan ne karon farko da Najeriya ta rungumi amfani da kudin na intanet.

Buhari ya kaddamar da eNaira

CBN ne suka wallafa wannan bayanin a shafinsu

Bayanan hoto,

Yadda Buhari ya kaddamar da eNaira

A cewar CBN eNaira zai zama wata hanya mai inganci ta huldar cinikayya da kudin Naira da kasar ke amfani da ita.

Hakan na nufin a matsayin al’umma za su iya amfani da nairar ta intanet wurin sayen kaya a kasuwa kamar yadda suka saba yi da takardar kudin naira.

Kuma ma’aikatu da hukumomin gwamnati za su iya amfani da tsarin wajen karɓar kuɗaden shiga na gwamnati da kuma biyan haraji.

Mene ne matsayin addinin Musulunci kan amfani da kudin intanet?

Abin da ya kamata ku sani game da kuɗin intanet na Najeriya

Babban bankin Najeriya ne ke da alhakin kula da tsarin. Kuma CBN ya bayyana hanyoyin soma amfani da sabon tsarin kuɗin na intanet, kamar haka:

Za a fara sauke manhajar eNaira a kasuwar manhajar Google wato Google Play Store ga masu amfani da wayar Android

Za a nemi manhajar eNaira a sauke a waya

Bayan an sauke an buɗe manhajar za a fara yin rijista inda aka rubuta “Signup”

Za a zaɓi bankin da mutum yake mu’amula da shi

Za a saka lambar waya da kuma bayanan sirri

Wurin rijista za a rubuta cikakken suna da ranar haihuwa da asalin jihar mutum da kuma lambar bankin da ake mu’amula da shi da lambobin BVN

Idan an kammala rijista za a tura wa mutum saƙo a adireshin Imel da ya bayar domin tabbatarwa

Za a amince da tsarin eNaira idan an danna “Activate Wallet”

Domin fara aiki da eNaira za a saka suna da lambobin sirri wanda aka yi rijista

Idan ya buɗe mutum zai ga asusunsa na eNaira

Yadda za a saka da cire kuɗi a asusun eNaira

Wanda ya buɗe asusun eNaira zai iya saka kuɗi a ciki nan take daga asusunsa na banki.

Kamar yadda mutum zai buɗe asusun eNaira haka ma bankuna suna da tsari da CBN ya yi tanadi domin su.

Za a iya samun eNaira a manhajar bankin da mutum yake mu’amula da shi – akwai tsarin saka kuɗi da cire wa da za a zaba daga manhajar banki domin turawa da cire kuɗi daga asusun eNaira.

Mutum zai saka adireshinsa na Imel da aka yi masa rijista da lambobinsa na BVN – sai a saka lambobin sirri na asusun eNaira.

Za a turo wa mutum wasu lambobi a wayarsa da zai yi amfani da su domin tabbatar da cire wa ko saka kuɗi.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top