Siyasar 2023: Duba Jerin Sunayen fitattun ‘yan siyasa 11 na Najeriya da ke goyon bayan Tinubu

  2023: Sunayen fitattun ‘yan siyasa 11 na Najeriya da ke goyon bayan Tinubu 

 Fitattun jama’a a Najeriya sun fito tare da bayyana goyon bayansu kan Tinubu ya maye gurbin Buhari a 2023 Daga cikinsu kuwa akwai gwamnoni masu ci yanzu, ‘yan majalisu, sarakuna da sauran masu fadi a ji Ba kuwa a kudancin kasar nan, hatta ‘yan siyasan arewacin kasar nan sun bayyana cewa ya na da nagartar shugabanci 

Wasu fitattun ‘yan Najeriya sun yi ruwa da tsaki wurin tabbatar da goyon bayansu ga jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu kan ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari nan da 2023. Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, fitattun jama’ar da suke goyon bayan Tinubu sun hada da tsoffin ‘yan majalisa, ministoci da wasu fitattun ‘yan siyasa domin ya zama shugaban kasa na gaba. 

2023: Sunayen fitattun ‘yan siyasa 11 na Najeriya da ke goyon bayan Tinubu.

 Hoto daga elitethrive.com Source: UGC

 

Binciken da Legit ng ta yi ya bayyana yadda ake kara gangami saboda burin Tinubu na zama shugaban kasa. 

 Jaridar ta tattaro jerin sunayen fitattun ‘yan siyasa wadanda suka fito fili tare da bayyana goyon bayansu ga Tinubu. 

1. Hamisu Chidari Kakakin majalisar jihar Kano, Hamisu Chidari ya bayyana cewa jam’iyyarsa a jihar Kano za ta goyi bayan Tinubu a zaben shugabancin kasa mai zuwa. Chidari ya ce a jihar Kano, wacce ke da kuri’u masu yawa da kuma wakilan jam’iyyar a Najeriya, za su saka wa Tinubu taimakon da yayi wa shugaban kasa Buhari har ya hau kujerar shugabancin kasa. 

2. James Faleke Faleke wanda dan majalisar wakilai ne, ya bukaci Tinubu da ya fito takarar shugabancin kasa a 2023. Ya ce Tinubu ya bar ofis a 2007 amma har a yau ya na mulki saboda “ya mayar da hankali tare da jajircewa”. 

 3. Sanata Adesoji Akanbi Tsohon sanatan Oyo ta kudu, Adesoji Akanbi, sanatan da ya taba wakiltar mazabar Oyo ta kudu (2015-2019), ya tabbatar da cewa har gobe Tinubu ne madubin dubawa a siyasa kuma zai iya shawo kan matsalar kasar nan. 

4. Gwamna Babajide Sanwo-Olu Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana goyon bayansa kan bukatar Tinubu ta zama shugaban kasar Najeriya inda ya ce ya na da nagartar shugabantar kasar. 

5. Adeseye Ogunlewe Tsohon ministan ayyuka, Adeseye Ogunlewe ya yi kira ga Tinubu da ya bayyana bukatar son shugabantar kasar nan a 2023. 

6. Mudashiru Obasa Kakakin majalisar jihar Legas, Mudashiru Obasa a madadin kakakin majalisun kasar nan, ya ce dukkan kakakin majalisun kasar nan sun sha alwashin goyon bayan Tinubu a taron da suka yi a Kano. 

7. Abdulsalam Abdulkareem Zaura Dan takarar kujerar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a Kano, Abdulsalam Abdulkareem Zaura ya bayyana cewa ya na bayan Tinubu kuma ya na fatan zai fito takarar shugabancin kasa a 2023. 

 Zaura ya ce a shirya ya ke wurin “yaki da dukkan karfinsa da kudinsa” wurin tabbatar da cewa Tinubu ya zama

 shugaban kasar Najeriya na gaba. 

8. Joe Igbokwe Jigon jam’iyya mai mulki ta APC, Joe Igbokwe ya kwatanta tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin tubalin da ya assasa gini da cigaban jihar. Ya ce abubuwa za su daidaita matukar Tinubu ya zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

 9. Oluwo na Iwo a jihar Osun, Oba Abdulrasheed Akanbi Basaraken ya kwatanta Tinubu da mutumin da ya fi dacewa ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023. 10. Senator Abu Ibrahim Tsohon mataimakin bulaliyar majalisa kuma jigon jam’iyya mai mulki daga jihar Katsina, Sanata Abu Ibrahim, ya tabbatar da goyon bayansa ga Tinubu. Ya sanar da hakan ne yayin rantsar da kungiyar goyon bayan Tinubu a Abuja, inda ya ce zai iya tsaya wa tsohon gwamnan ganin yadda ya san shi sama da shekaru ashirin.

 11. Farfesa Mohammed Kuta Yahaya Tsohon sakataren gwamnatin jihar Neja, Farfesa Mohammed Kuta Yahaya ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su “samar da Bola Ahmed Tinubu a kowanne yanki na kasar nan.” 2023: Jihar Kano a shirye take ta goyi bayan burin Tinubu a shugabancin Najeriya, kakakin majalisa A wani labari na daban, biyo bayan jita-jitar burin takarar shugaban kasa na jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Hamisu Chidari, yayi babbar magana.

 Legit ng ta rahoto cewa ya ce APC a jihar Kano za ta goyi bayan Tinubu idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023. 

Chidari ya yi magana ne a wajen kaddamar da kungiyar goyon bayan Tinubu (TSG) da kwamitocin gudanarwa na kungiyar a Abuja ranar Asabar, 23 ga watan Oktoba. Source: Legit 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top