Sulaiman Fanshekara Tare da Amaryarsa Baturiya Sunsaki Sabbabin Hotunan Su Cikin Shiga irin ta hausawa
A jiya juma’a ne matashi nan mai suna Sulaiman Isah wanda ya auri Baturiya ‘yar kasar waje ya wallafa hotunan su shi da amaryar tasa inda yake yiwa masoya da abokan alziki barka da Juma’a.
Kamar yadda kuka sani labarin Sulaiman Isah dan garin panshekara ya karade kafafan sada zumunta da gidajen jaridu a lokacin da ake tsaka da labarin aure sa zasuyi da Baturiyar wanda ta masa fifikon shekaru masu yawa.
A duk ranar Juma’a al’ummar musulmai sukan wallafa sabbin hotunan su a shafukan sada zumunta domin yiwa ‘yan uwa da abokan arziki fatan alkairi da kuma nuna murna ga zagayowar wannan ranar ta Juma’a.
Sulaiman Isah yayiwa al’ummar musulmai barka da zagayowar wannan babbar rana ra Juma’a inda ya wallaha hotunan su shiga amaryar sa Baturiya suna cikin shiga ta kamala tare da bayyana farin ciki ga junan su.
A kwanakin nan al’umma sun yiwa Sulaiman Isah fatan alkairi duba da yadda ya rike amana wajan zama lafiya shi da amaryar tasa Baturiya, inda har ma yake jan ra’ayinta wajan sanya kaya irin na addinin musulinci.
A cikin hotunan nasu zakuga yadda sukayi shiga ta kamala tare da bayyana farin ciki a tsakanin su, inda zakuga itama amaryar tasa Baturiyar ta sanya kaya wanda yake nuna cewa tanabin umarnin mijinta wato Sulaiman din.
Ga hotunan nasu a kasa domin ku kalla.