AMANATACE HAUSA NOVELS

 Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
       Novels villa
     Duniyan novels 
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And 
Cool novel, makeup and cooking) 

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239

AMANA TA CE-Page-1-
to-end
OCTOBER 23, 2016 | RASHIDATKARDAM | 2
COMMENTS
[9:20PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rash Kardam
Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi,
kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji
Al-hassan ne ya fito daga dakinsa cikin
manyan kaya, yayi shiga ta alfarma,
dining yaje ya zauna hajiya fatima ne
zaune tana jiran mai gidanta, bayan ya
zauna ta masa sannu, ya amsa cikin
sakin fuska ya kalleta yace Fatima ina
Auta take, tace tana sana’arta har yanzu
inaga bata farka ba, cikin kulawa ya
kalli fatima yace hajiya ina fada miki
kulum ki ringa kula min da Auta, cikin
daure fuska tace Alhaji kulum haka
kacewa yarinya duk ta san garce sakalci
ya mata yawa ta girma aman kamar
wata jaririya, Alhaji ya nisa yace hmm
fatima akwai maganar dana ke so muyi
da Auta da Ammar, ana cikin haka sai ga
Ammar ya shigo cikin ladabi ya gaidasu,
suka amsa da sakin fiska, ya kalli Hajiya
yace Mum ina Auta tace tana daki tana
sana’ar ta na baccin sage barinje na
tasota, Ammar ya mike da nufin
komawa falon Abba yace aaa Ammar
bama haka ai kaima dana ne don ina
jinka ajikina kazauna mu karya tare,
ana haka sai ga Mum tafito Auta na biye
da ita, yau anyi sa’ah harta yiwanka da
wuri bata tsaya baccin gadonta ba, cikin
zazza kar muryanta ta gaida Dad dinta
da Mum san nan Ammar cikin kulawa ya
amsa, kusa da Dad ta zauna suka karya
bayan sun gama suka koma falo, dad ya
zauna mum na gefensa Ammar na kasa
tana zaune, Autar Hajiya na kusa da ita,
Abba ya dago cikin muryansa mai sa
sanyin jiki kalo daya zaka masa ka gane
yana cikin taradadadi, Zainab ya
ambata, Autar Hajiya sai da taji sunan
har cikin ranta tasan dad baya kiran
sunan ta haka kurum sai da dalili, ta
amsa da na’am dad, Dad ya kalle ta yace
Zainab ina son insanar dake wani abu,
sanana inaso ko bayan raina Auta
kikasance mai hakuri da biyya ga wanda
zakiyi tarayya dasu san nan ki rike
mutuncinki, karki sake kiyi watsi da
tarbiyan da muka miki, nasan ki amma
ina son ki kara rike mutun ciki, ki rike
Adu’ah a duk inda kike, Zainab idonta
duk ya ciko da kwala don tun da take da
dad bai taba mata zance makamancun
haka ba,maganar dad ne ya katse mata
tunani, Ammar ya kira ya amsa, dad
yaci gaba dacewa Ammar kai kadai na
yarda da kai acikin wayanda mukayi
tarayya, kaine ka rike min “AMANA” ta
don mutane yanzu ba yarda, san nan ko
bayan raina banyarda ka bar Zainab ba
ga “AMANARTA” na baka kai kadai
nasan zaka kula min da ita, cikin sanyi
jiki Ammar yace dad mai yasa kake irin
wan nan maganan Dad yayi murmushin
manya yace Ammar da Zainab atare,
yace kukadai zan sanar da maganan nan
kusani akwai wayanda suke min
barazanan kashe ni da iyali na akan
dukiyata, da nanema da gumi na,
nikuma naki amsamusu sabida mutuwa
da rayuwa tana hannun Allah, ba wanda
ya isa ya kashe wani face da izinin
Allah. Cikin damuwa Auta da Ammar
sukacewa suwaye dad murmushi yayi
yace ka kyalesu kawai zan sanar muku
amma bayanzu ba, hajiya ma tayi musu
nasiha sosai, dad ya mike ya fita hajiya
tayi daki Auta kuka takeyi Ammar ne ya
rarrasheta sai da tayi shiru kafin ya fito
harabar gidan nan sale suka fara masa
kallon bansa da kuma zaka sani yau,
musa kam dariya yayi sosai kafin yace
mun kusa ganin karshen wan nan
rigima taka da kafafa kamar gidan
ubanka, an samu gidin zama sai nuna
isa kamar dan gd ko ta kansu bai bi ba
ya wuce dakinsa shidai yana fatan Allah
ya tsaresa da sharrin masu sharri.
Dad bai dawo ba sai kusan 10 lokacolin
Auta tayi bacci hira sukayi sosai da
Hajiya kafin yace bari ya watsa ruwa
bayan yayi wanka hajiya fatima tafito
cikin kayan baccinta mai daukar hankali
ta nufi dakin Alhaji sun yi hira sosai
kafin suka kwanta, Misalin karfe 2 gari
yayi shiru sai sai hadirin daya hadu gari
yayi baki2 nan take ruwa ya tsinke sosai
kamar da bakin kwarya, kowani mutum
na gidansa yana bacci, wata bakar jeep
ce mai bakar glas na ga tanufo gaye din
gidan Alhaji Al-hassan sai da suka fito
duka kwan kwasa wa mai gadi ya bude
musu suka shiga, duk da ruwan da akeyi
bai dame musuba kalo daya zaka musu
kasan ba alkairi bane, atare dasu, sun
rufe fidkokinsu da marks bakinsu da
kwayan ido su da kofar hancinsu
ke waje, magana sukayi tsakaninsu
wanda sukazo a jeep dasu sale da
musa, da alaman dai sun san da
zuwansu, bayan sun gama ne, suka nufi
cikin gida ko da suka shiga dakin Alhaji
suka nufa suka samesi da hajiya suna
tare,
Ammar ko yatashi tun karfe daya
yasoma sallah nafilan da yasabayi duk
dare bayan ya idar duk da ruwanda da
akeyi yaji alamar shigowan mota da
sauri ya leka nan yaga wasu da bakaken
kaya sun rufe face dinsu duk abunda
sukayi na kallonsu nan yaga sun ciro bin
diga, yana kalon sun shiga ya bude kofar
dakinsa cikin sanda ya kwanta a kasa
yadoma tafiya da ciki kamar yanda soja
suleyi a fagen yaki cikin fulawas ya
soma bi ko da yaje ta kofar baya ya
shiga yayi sa’ar kofar abude take nan ya
tura a hankali, daman duk wanda
yashigo ta baya dakin Auta zai fara
samu don haka ya tura kofar a hankali.
yaganta tana bacci, a hankali ya soma
tashita, cikin ikon Allah ta mike ba gyan
gyadi, ihu zata sa ya toshe bakinta yace
Auta kina jina wasu mutane sun zo gidan
nan da kuma da alamar wayanda
dad yafa da.suna son kashesa ne, nan
cikinta ya fara rawa idonta ya ciko
da kwalla, yace dau hijab diki mu leka
muga don musan abinyi, kasa dauka tayi
shi ya daukar mata ko ta kalmi bata
tsaya dauka ba suka nufo falo a han kali
suka leka, nan suka ga abunda ya
razana su dad ne aka samasa bindiga
da Hajiya suna kara lekawa nan suka
ga fuskan Baba Sani da yayansa iyaka,
alokacin suka dana kuna mar bingigan
tass kake ji karan harbin bindiga,
nan take auta tasaki kara atake suka
juyo gurin da sukaji kara suna fadin
suwaye suka nufo gunsu.
Yan uwa amin afuwa za ku ga ban2
dana farkon dana soma sakewa, yanzu
na dawo da lbr daga tsakiya ne amin
afuwa inaga hakan watakil zaifi.
Shin su Autar Hajiya da Ammar suna
kubuta daga sharrin mutanen nan?
bacin gashi gate din gdn a kulle.
Suwaye wayan nan mitanen?
Mai nene alakarsu da Dad?
Waye Ammar?
Don son jin amsarnan kubiyo Yar Gidan
Kardamawa .
Taku akulum mai kaunarku
®WWA®
Rash .A. Kardam
[9:20PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rash Kardam
Tass kake ji karan harbin bindiga
nan take Auta tasaki razananen kara, da
sauri suka juyo girin da sukaji karan
suna fadin suwaye, suka nufo gun,
Ammar yana ganin haka yaja Auta tana
turjewa ita sai taje gun su Dad da
Hajiyarta, dakyar ya shigarda ita
dakinta yasaka key ya kullesu, ga ruwa
sai sauka yakeyi ana tsawa, nan
yarasa yanda zaiyi Adu’ah ya tuno na ne
man tsari daga abokan gaba ya fara
karantawa, autakan sai kuka take, ana
cikin haka su Kawu Sani suka iso kofar
nan suka fara jijjiga kofar, Auta ko kara
sautin kuka takeyi Ammar bai san
lokacin daya daka mata tsawa tayi shiru
don kukanta har cikin zuciyar shi
yake tabasa, nan ta damke bakinta ,
duk ya rue yarasa ya zaiyi gashi ba
hanya, kasu Baba Isiya da sani su jijjiga
kofa ga harbin suketayi, kiris
yarage su balla kofar nan take dabara
ta fado masa da sauri yayi gun Waldrop,
ya zazzagar da kayan ciki kasa da kyar
ya turo ya jawo ya kawo zuwa bakin
kofar ya tokare, nan ya janyo dress
miro shima ya tokare nan ya dafe kansa
sai ga wasu zafafan hawaye:'(:'( ke zuba
yana kiran sunan Allah ya kawo musu
mafita.
A bakin gate kuwa mai gadi da sale suka
leko ganin su Alhaji an sheka kiyama
suka sheke da dariya sukace yau ina
kudin ka ya dawo namu, gumus ne ya
fito yace kuba mu karfe ina tunanin
akwai wasu agidan nan zamu balle ko
fa, don yar Alhaji na tare da wani Sai a
lokaci idi yace kai:oops::oops:munyi
kuskure daya da muka bar dakin Ammar
bamu fara ta kanshi ba barinje na dubo
shi, ko da yaje dakin ba ammar nan yace
duk yanda akayi Auta tana tare da
Ammar amma bazasu gudu ba, don
gidan nan na rufe ba gurin tsira dariyan
mugunta suka farayi, wani
katon karfe suka samo wanda duka daya
zasuyi wa kofar su balle, nan suka nufo
cikin dakin da karfen.
Ammar kuwa adu’o’i yakeyi can ya tuna
windo dakin na glass da sauri ya mike
nan ya fara dube2 ba wani karfe a
dakin wanda zai fasa ga shi sukuma sun
kusa balle kofa duk ya kalli ko ina na
dakin ba wani abu, sai can ya kalli
Bedside drawer, da sauri ya dauko ya
zubar da kayan ciki, ya nufi windon da
karfin ya buga tare da bissmila bugu
biyu yayi mai kyau wundon ya balle
sosai yanda zasu wuce sai da ya leka ta
baya yaga ba kowa kafin ya dauko Auta
ya sanyota ta waje tasauka kenan yana
shirin fita wani kwanban da bai gama
balle ba ya yankeshi nan sai ga jini sosai
gashi kwalbar ya shiga sosai har sai da
yace washhhhh, lokacin su baba Sani
suka balle kofar suka nufoshi.
®WWA®
Rash Kardam
[9:20PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ya balle window din ya fara fitar da
Auta kafin ta zo fita wani kwalban glass
a jikin window din ya yanke shi ya shiga
sosai, ya ji zafi harsai da yace washhhh,
dai2 lokacin su baba sani suka balle kofa
suka nufo shi cikin zafin nama ya dirka
ga jini sai zuba ya keyi sosai, da sauri
Ammar ya yakwanta a kasa ta gefen
window, cikin hantsari ya fisgo Auta ta
fadi kasa wanda faduwar wata ya dai2
da wani dutsi nan ta buge bakinta sai ga
jini, kara tasa yayi sairin toshe mata
baki, su gumus da kawu isiya suna isowa
harbi suka fara amma bai kai ta inda su
Auta suke ba, baba sani ne ya ciza yatsa
don ya ji haushi ga window ya musu
kankanta baza su iya fita ba da sauri
yace ku zo mu zaga mu bisu da sauri
suka fita ga ruwa haryanzu zuba
yakeyi sosai.
Ammar na ganin sun bar window yayi
kokarin rashi ga jiri na debansa don
jininsa ya zuba sosai, ga Auta kuma jiki
ba kwari, ya mike yana tan gadi ya
dagata kasa tsayuwa tayijijjigata yayi da
kyar sai ta sauke ajiyar hrt kafin ya
mikar da ita suna mikewa suka hango
motar su baba sani sun nufosu, nan ya
fara janta da gudu tunda daga hayin
rigasa layin waya suke gudu sai da suka
wuce kantin yawo, kafin suka kara gudu
dai2 zasu fita a hayin rigasa, Auta ta
fadi da sauri ya dauketa ganin in yace
zai miki hanya zasu kamasa sai yayi
gurin wani sabon gini wanda dogayen
ciyawa sun bullo agun gabansa
kuma katon ruwa ne wanda ya taru, nan
ya kaisu gun ya tsuguna ya tare Auta da
numfashinta ke shirin daukewa
abunka da rashin sabo ga razana don
Auta in banda girki da take taya
hajiya bata wani wahala, tasaba da
rarrafen carpet tun tube da waya, baran
da ta rage ita daya ma Dad da Hajiya ba
irin gatan da basa mata.
Su baba sani da suka iso gurin nan suka
fita ga ruwa na sauka sosai duk dube2
da sukayi basu gansu ba,
Ammar kuwa suna gurin a tsugune da ke
Auta ce ta jikin garu, nan wata kuna ma
ta fito sabida ruwan da ya dameta a
gidanta tana fitowa kuwa kafar jidda ta
hau sai da tazo kusa da gwiwanta ta
danna mata cizo, har saubiyu duk da
zafin da taji tayi saurin damke bakinta
, Ammar na ganin haka ya kara matse
bakin nan kuwa kunamar ta
kara yanka mata cizo, sai murkususu
take tayi, gumus da duna sukace alhaji
ku tafi kawai mu zasu tsaya mu ne mesu
in baku mu kawo maka gawarsu ba to
zamu maka da lbr mutuwarsu, nan suka
tafi da motar suka bar su gumus a gurin,
sun dade suna dube2 sosai agun kafin
suka soma fita,
Autakuwa wuya yayi wuya bata san
lokacin da ta kwace bakinta ta saki kara
da sauri su gumus suka juyo nan suka
fara nufo gurin da sukaji karan,
Ammar na ganin haka ya mike yasoma
jan Auta suna kara gaba kawai suka ga
kato kogin ruwa ne a gabansu ga su
gumus sun nufosu.
Abun gwanin tausayi nikaina Rash
bansan lokacin da na fara zubar da
hawaye ba .
Allah sarki su Auta da Ammar Allah ya
kwace ku a hannu wayan nan Azzalumai
din Ameen.
Sai dare zakuji ni
Taku a kullum mai kaunar ku
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ammar ya ma rasa ya zaiyi ga Auta
numfashin ta na kokarin daukewa da
sauri ya suguna akasa ya ajiyeta acikin
tabo ga jini yana ta zuba daga
hannunsa,
Gumus suka nufo su da sauri nan ya
harba bindigan ya sake harba wa yaji
bullet ya kare cikin jin haushi yace oh ya
wurgar da bindigan akasa ya nufosu
ko da yazo daman Ammar na ankare
yana isowa suka fara kokuwa cikin ukon
Allah karfin yazo ma Ammar ya wurga
shi a wan nan ruwan, aiko dan uwan
gumus na ganin haka dake yana haskasu
da touch light, ga shi gumus nata fanjam
aruwa dake shi bai iya ruwa ba, kuma
ruwan da dan yawa, da sauri yayi gun
ruwan ko ta kan su Ammar baibiba ya je
gun dan uwansa don ceto rayuwansa,
Ammar na ganin haka ya dauki Auta
yasa gudu sai da yayi nisa ga ruwa ya
soma tsagaitawa, ya samu wani rumfa
ya ajiyeta ya huta, basu dade sosaiba ya
auta sai hawaye:'(:'(take tayi ko da ya
laluba kafarta yaji ta kubura suntum,
taba kafar dayayi har sai da tayi ihu
haka ya dauketa suka cigaba da tafiya.
Su gumus ansha wuya da kyar aka ciro
shi don har yasoma shan ruwa, yana
dawo wa hayyacinsa yake tambayar
mugum ina suke yace sungudu, mtssss
bahaka nasoba nan yace naga abunda ya
faru kar ka sheke zuwa lahira da wuri
shiyasa na ciroka kai kajimin
wayan nan sai kace mutuwar nima izini
takeyi, mikewa sukayi gumus ya karbi
wayar mugum don nasa ruwa ya bata,
baba sani ya kira ya tambayesu suna ina
yace yanzu zasu bar gidan Alhaji kenan
sukace gasu zuwa.
ko da suka isa nan suka samu baba isiya
da sani sun daure sale mai gadi da musa,
don daman sunyi akan zasu daure su
sabida ace barayi ne suka zo, hakan
sukayi, ko da su gumus suka iso nan
sukaga abunda ke faruwa dariya sukayi
sosai sukace Alhaji baku da dama,
Baba sani yace ya ina fatan kun sheke su
cikin sauri gumus yace ai har gawan ma
sai da muka yardasu inda ba mai gani,
nan kawu isiya yace aikin ku na kyau,
gumus yayi murmushi yace oga sai kudin
fa baba sani yace ina zuwa cikin gidan
suka shiga dakin dad suka duba drawer
nan suka ci karo da damin kudi sai
dasukayi dariya sosai kafin suka diba
nan suka fito falo, baba sani yazo cikin
izgilaci yace su Al-hassan yau an sheka
kiyama to ina naira kai dan taurin kai
yau zamu facaka da dukiyar da kake ta
kama dashi, yana zuwa kan hajiya sai da
ya shureta da kafa, ke kuma yar iyeye
yau munyi maganinki da yar da kuke so,
harda dauko bare wanda bakusan daga
ina yake ba ku fifita shi akan mu gashi
yau duka bakwa nan mun kuma samu
dukiyar cikin ruwan sanyi sai ya kece da
dariya sosai, nan suka fita suka
shiga mota suka tafi don suke su sallami
su gumus.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ko da sukaje gidan kawu isiya wanda
tutun nufawa, ba kowa aciki kuma ba
nisa sosai da gidan Alhaji marigayi, nan
suka shiga ko da suka zauna nan baba
sani yace yau burin mu yacika na gama
wa da Al-hasan da iyalansa, kamar
yanda mukayi Alkawari zamu ba ku
400k kowa zai dau 200k kenan gumus ne
yace oga mungo amma munaso aba mota
koda kwaya daya ne ehhh musamu na
yawo a gari, ko wani aiki kuke so zamu
muku cikin sauki kawu isiya yace aaa
bazai yuba abun yaso ya dawo musu
rikici baba sani yace ba matsala za a
duba in komai ya lafa abaku, nan ya
ciro 300k ya basu yace kurike wan nan
kafin komai in ya lafa zamu sallame ku,
gaba daya nan sukayi sallama kowa ya
kama gabansa.
Da safe yan unguwa suka fito don wasu
sunji karar tsayuwar don haka suka
yi cirko2 gashi jiya anyi ruwa sosa,
mukwabcin dad wani mai suna Alhaji
Abubakar yace yan uwa yau ban ga Al-
hassan a masallaci ba kuma duk rintsi in
ba jinya yayi tsanani yana zuwa sallah
amma yau shiru, ko lfy wani mai suna
Alhj kabir yace ni jiya fa kamar an shigo
unguwan nan don duk da karan ruwan
sama dake zuba naji ihu san nan
naji harbin bindiga sun dade suna
jimami kafin wani acikinsu yace kamata
yayi mu shiga gidan mugani, nan suka
dun guma suka shiga tun a kofa sukaga
masu gadi an daure su, da sauri suka isa
wajansu, bakinsu an toshe da tsumma,
kunce su sukayi nan Alhaji Abubakar ya
fara tambayan lfy, sun wahala yasa ba
wani amsa don dauri da aka musu mai
kyau ne hakan shi ya gala baitar dasu,
da sauri suka nufi cikin gidan bayan
sunshiga a falo suka tarar da gawan
Alhaji da hajiya nan suka soma jimami
masu kuka suka fara, alhaji
abubakar makocin dad police ne nan
take ya kira ja mi’an tsaro suka fara
binjike nan sukaje dakin Auta inda suka
ga yanda aka baza kaya da alamar kare
kansu da sukayi da kuma fasa window
da akayi gashi ba auta ko da suka zaga
nan sukaga jini da kuma alaman harbin
da akayi ta waje, Alhj Abubakar yace
cikin daya biyu ko sun kashe Zainab ko
sun dauketa ko da suka dawo gd sai
alokacin ya tuna da ammar nan ya nufi
dakin da ke tsammanin nasa ne sallaya
tagani a shin fide da alamar anyi sallah
akai ki da suka fito suka nufi kofar baya
nan sukaga an tura kofar anshiga duk
binciken da sukayi ba wani amsa nan
suka kira Alhaji sani da baba isiya suka
sai da musu, ko da suka iso gidan kuka
sukeyi sosai kai ka rantse basu da hannu
aciki har sani na ikirarin imyasan
wanda yayi kisan nan sai ya dau fansa,
kawu isiya kam ko mace iyakaci yanda
yake kuka. haka police suka tafi da
gawarwakin don kara bincike.
Ammar da auta kuwa tafiya yayi sosai,
sun shigo cikin gari kuma dare yayi
sosai don asuba ya kusa, nan yasamu
inda ba ayi ruwa ba ya kwantar da
Auta ya yagi zanin dake daure a saman
kayan baccinta ya kulle hannusa sai
runtse ido yakeyi alamar zafi, ya daure
hannuta ya dauketa suka cigaba da
tafiya sunyi nisa sosai, sai ga wani mai
mota yazo wucewa nan ya tsare shi sam
yaki tsaya haka ya cigaba da tafiya sai
ga wani da alamar wan nan irin yan
taxi masu zuwa gari zuwa gari har yaki
tsayawa komai ya tuna ya dawo
daukarsu, nan Ammar nace ina zan
kaiku Ammar yace ban sani ba mutumin
yace to ni saminaka zanje yanzu, yace
muje ka ajiye mu a hanya.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Motar suka shiga nan mutum min yace
subada 1500 kudin mota sai a lokacin
ya tuna basu da kokisi, innalinahi wa
inna ilaihi raji’un abunda ya furta gashi
sunyi nisa sosai, sun shiga jeji don sun
bar cikin garin kaduna sosai, jiki ba
kwari yace wa driver dan Allah ka tai
make mu wlh fitowar gaggawa ne ya
kama mu bakosisi ajikin mu, driver ya
narko ashar yayi, aefa baka isaba zan
dauko ku a bati ne ba ko sisi mai na
tsada kuma niman kudi na fito, waya
sani ko dan iska ne ma kai kasato musu
yarinya inazaka da wannan yar gashi
jikinta duk jini, kalala ta mata rayuwa,
ko sayarta zakayi, nan take ran Ammar
ya baci don tunda yake ba abundaya
tsana kaman zargi ko kazafi, shi da ya
tsani zina a rayuwansa mezaisa ya
aikata cikin bacin rai yace kaii Malam
ya isheka in har bazaka taimaka min ba
karka min wan nan zaton, nan mutumin
yace anyimaka kuma zata fita anan ba
wlh sai kabani kudina, nan ran Ammar
yakara baci wai shi dayake nima da
guminsa ga kuma Zainab yar gata
gabada baya wai yau sune a wulakance
ga shi an kashe su Alhaji shikenan Zee sa
ta dawo “MARAINIYA”nan take yaji
hawaye:'(:'(:'( wasu na bin wasu, sai a
lokacin ya kalli agogon hannusa mai
kyau yace ma
driver bani da kudi amma ga agogona in
zaka karba yafi karfin kudinka, driver
yace nagani ko da ya karba yagani yasan
zaiyi tsada dayawa nan yace to shikenan
yanzu in kaiku saminaka ne ko zaku
sauka anan tsabage bacin rai yace barin
musauka anan, ya dauki Auta suka fita,
gefen hanya ya kwantar da ita lokacin
gari ya waye sosai, sai alokacin yaga
kafarta ya kumbura sosai fa bakinta ma
ya kumbura sosai, gashi yayi ja abunka
da farar mace, gindin wata katuwar
bishiya yaje ya shinfida fallen zani ya
kwantar ta, ga yunwa yasoma damunsa
ga hannusa yana masa zafi sosai, bayan
ya kantarta, yasoma dube2 ko zaiga
ruwa don yasha yakuma ji alwala.
Acikin garin kaduna kuma Alhaji
Abubakar ko ince Inspector Abukar
shiyatsa akan gawan su dad har akayi
zana idarsu aka kaisu makwancinsu na
gsky, kafin kace me lbr ya baza gari, yan
uwan dad sun taru a gidan ko da Sadiya
yar Baba sani taji lbr ba karamin girgita
yayi ba baran da taji ance ba a ga Zee ba
tashiga tashin hankali don suna shishiri
sosai,
Inspector Abubakar daya koma gd ya
tausaya ma yarsa bulkisu don kawar
Autace sosai tayi kuka kuma nan ta
dauki aniyar saita dau fansa akan duk
wanda ya aikata abun, bayan kwana uku
da rasuwan su Dad yan uwansa sukace
su duk wanda yayi abun nam sun barshi
da Allah, sirutu kala2 su ka rinkayi har
saida Inspector Abubakar yaso ya
ganesu, bilkisu kuwa ranan kwana na
uku, tasami Abbanta akan ita ta canza
ra’ayi daga kan Science courses, yanzu
Law zata karanta don tazama barrister
don ta nimo ma Kawarta Ameeniyar ta,
hakkunta da cutar da ita da akayi, kuma
tace Abba ni ajikina inajin Zee bata
mutu ba ko ga yanayin statement din da
aka samu kuma kaga ba aga Ammar ba
nisan yana tare da ita kuma bazai
cutarta ba da yardan Allah don yana da
hali mai kyau, Inspector Abubakar yaji
dadin maganar yarsa Bilisu wanda ake
kita da futuhatul-khai, yamata Adu’an
Alkairi da fatan nasara.
Su baba sani nan suka fara kiciniyan
raba dukiyar dad har yaso su samu
sabani da baba isiya akan wanda zai
zauna a gidan dad da kyar Baba isiya ya
hakura akan shi za a bashi motar dad
babban ya rike.
Rayuwa kenan wai naka najikinka
shiyake son ganin bayanka basa tunanin
suma zasu mutu ba tsoron Allah wan
nan wani irin zamani ne burin wasu
mutanen su ci “Amana” yan uwa muji
tsoron Allah musani Amana tana gefen
siradi da Zumunci duk wanda ya karya
daya aciki to yasan makomarsa, don
ranan kiyama akwai wasu kugiyoyi a
kasan gadan siradi duk wanda yaci
amana ko ya bata zumunci ko da ya
kusa karshen haye gadanne haka
kugiyar zata finciko shi wasu
kafin su isa duk sun yaga naman jikinsu,
‘Yasalam’ yan uwa muji tsoron Allah mu
gyara rayuwar mu musan man zumunci
da Amana mu kiyayesu, ya Allah kasa
mudace da karshe mai kyau Ya Allah ka
daura mu akan hanya madaidaiciya
Ameen.
 Ammar sai da yayi tafiya mai nisa kafin
ya ga wani rafi nan ya rasa ya zaiyi ya
debi ruwa ya kaima Auta tasha ko zata ji
dama2 ga tausayinta shikam kasa sha
ma yayi in har Auta bata sha ba ba zai
iya sha ba, ya sanya hannumsa biyu ya
debi ruruwan yanufi gunta tun kan ya
isa ruwan ya zube nan yaji wasu
hawaye:'(:'( sun zomasa. Yana zuwa
kusa da ita ya ga sai wani irin nishin
azaba takeyi kamar wai shirin mutuwa
Ammar baisan lolacin da yasaki kuka
kamar karamin yaro yana cewa
Zainab dan Allah kar ki tafi ki barni ke
kadai kika ragemin bani da uwa ba uba,
gashi sun kashe mana Dad da Hajiya in
kintafi ina zansa kaina kuka yakeyi
sosai da sosai.
Nima Rash bansan lokacin da
nasaki kukan tausayi ba. Allah sarki
rayuwa juyi2 Allah ka kawo masu Auta
da Amar mafita Ameen.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Nan yasaki kuka mai ban tausayi,
jijigata ringayi sai yaga tasaki ba ko
alamar motsi atare da ita, da sauri ya
dauketa yayi gun rafin da ita yana isowa
yaga wani dan tsoho yazo diban ruwa a
gora, tsohon nan, ganin halin da Ammar
ke ciki yasa yace subhanallah bawan
Allah mai yasa meta Ammar kasa
magana yayi sai hawaye:'(:'(wani na bin
wani, tsohon na ganin halin da Ammar
ke ciki ya dibi ruwan goransa tare da
bisimillah ya watsamata sau 2 nan take
ta saki ajiyar zuciya mai karfi,
muryan ta ya dishe, ga jikint ba kwari
duk ya mutu, ahankali take magana sai
da Ammar ya sunkuyo dai2 bakinta
kafin yaji mai takecewa wayyo kafarta,
ammar da sauri ya riki kafar sai a
lokacin tsohon ya lura da kafan yace
yasalam mugani ya rike kafar wan nan
ae cizo kunama ne ya daneta,
yace yanzu ku biyo ni in taimaka mata,
ammar ya dauketa suka bi tsohon.
A cikin garin kaduna kuwa, su baba sani
sun shiga sabon rayuwa mai dadi da
dukiyar da suka dade suna mafarkin
samunsa, Sadiya sam nataji dadin yanda
Abbanta ke zakewa akan dukiyar dan
uwansa ba, tunda ba a ga Autaba kuma
hakan bai tabbatar da cewa ta mutuba,
abin duniya duk ya isheta, haka rayuwa
ta kasance musu cikin nishadi har sun
manta da wasu wai su Al-hassan da
fatima da wata diyarsu Zainab bare
Ammar dan kallo.
Ammar ko haka yabi tsoho nan sunyi
tafiya mai nisa sosao kafin suka shigo
wani karamin kauye wanda gidajen ciki
baifi a kirga ba, in kazo gida daya sai
kayi tafiya mai nisa kafin ka iske diga
daya, ko da suka isa kofar wani diga an
masa rufi da da ciyawa sai katangan
kara aka dan zagaya gidan naki biyu ne
a gidan sai dakunan kaji da baru
yan kanana da agwagi , suna sallama
wata yar tsohuwa ta fito daga dakin
danake zaton nan ne gurin kwanan su,
tace lale maraba baki mukayi, ganin
Ammar rike da joda ga jini ajinsu duka
yasa tace lfy kuwa, suwaye wayan nan,
tsohon nan yace bakine da sauri ta
dauko taburman sakar kaba ta shinfuda
musu, ammar ya kwantar da Auta tsoho
nan daki ya shiga ya dauko wani yar
jakar fata, ya dauko magani da nan ya
kama kafar ya matse gun cizon saiga
karin ya fito nan ya sake matsewa har
sai da Auta tayi kara ta kan kame
Ammar sai zufa tayi, saida yacire
yashafa mata magani, san nan yasa inna
laure ta dafa
Musu ruwan zafi ta kawo masa kadan a
kofi ya saka magani yabama Auta da
kyar ta iya shan maganin tana runtse
ido.
®WWA®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Bayan Auta tasha maganin, sai aka dawo
kan Ammar nan shima ya kunce daurin
da yayi ma ciwonsa, tsohon nan da naji
inna laure nakira da malam, ya dauko
wasu magun guna, ya wanke masa ciwon
da wani farin ruwa, nan ya haungo
karamin glass ya shiga hannun, sai da ya
dauko aska ya ciro glass din, duk da
Ammar na miji ne sai da na ga indonsa
yayi jajazur da alamar yana jin zafi
sosai, baran ciwon ya kwana shiyasa,
Auta kam kasa jure gani tayi sai kifa
kanta tayi tana kuka maras sauti…,
wai yau itace a kungurmin kauyen da ko
wuta babu bare ruwan fanfo, kafin
asauko gun kwanciya mai kyau, nan take
kalaman Dad dinta ya fado mata, inda
yake mata nasihan sa na karshe akan ta
yi hakuri a duk inda tasamu kanta,
sabida yanayin rayuwa.
Allah sarki duniya kenan wai ace su
baba sani su zasu kashe iyayenta akan
dukiya da son duniya, mai suka maida
zumunci ne ga cin “Amana” wan nan
wani irin rayuwa ne sam tausayi ya
kaurace a idon jama’a basa tunawa zasu
mutu su koma ga Allah, in har kayi mai
kyau zaka taras, kwanciyan kabari ma
akabar mutum dashi babban aiki ne
bare ace ka aikata mumunan abu har
akaika wutar yasalam!!… Innalilahi wa
inna ilaihi raji’un duniya tazo karshe
wayan nan abun duk alamun karshen
duniya ne Allah ya kyauta yasa mudace
da karshe mai kyau ameen.
Hawaye ke gan garimata daga idonta,
tayi nisa cikin tunani, sai ji tayi ana
share mata hawaye, tana daga ido taga
Ammar ne, shima hawayen yakeyi sai
alokacin tasamu tasaki kuka mai ban
tausayi, shima kukan yasaki, an rasa
mai rarrashin wani.
Malam da inna laure sun zuba musu ido
sai kallonsu sukeyi, tabbas ko basu fada
musuba suna cikin tsananin tashin
hankali, nan take ina kaure ta fara
hawayen tausayi, malam idonsa yayi ja
sosai, malam kenan akwai tausayi ga
taimako.
malam yace bawan Allah kai na mijine
ka kasance mai juriya a kowani hali duk
da bansan mai yasame ku ba aman da
alama kuna cikin tashin hankali, kuyi
hakuri, kusani duk tsanani yana tare da
sauki, kuyi hakuri ku bar ma Allah
komai, zai yi muku saukin Al’amarin,
haka rayuwa take kowa da irin jaraban
da ubangiji ke masa kuyi fatan Allah ya
baku ikon ci, Ammar ya amsa da ameen.
Inna ta mike ta debu ruwan wanka a yar
bahonta da tsage aka nane shi ta surka
kafin ta kaima auta bayi, sai da ta
taimaka mata kafin ta kaita bayi tafito
ta barta nan ta dauraye jikinta, don
ruwan da dumi sosai ya gasa mata jiki
kuma ta samu dan karfi, bayan ya fito
inna tasake sama Ammar ruwan ta
kaimishi shima wankan yayi, bayan
yafitoa wanka suka shafa mai dake
lokacin da mina ne, a kwai dan sanyi
kadan.
Malam ne ya hau kekensa yaje can
kauyen da gabansu anan ake samu
shago, yasayo musu suga, yadawo inna
laure ta musu surki mai dumi sosai, don
ya ware musu hanji, abinci ta dauko
musu dambu tayi daman, kuma ta danyi
da yawa, san nan Malam ya karamusu
da nashi, aiko sunci danbun sosai don
yunwa sukeji, sai da suka gama cin
abincin, san nan sukayi godiya ga Allah
da ya kubutar dasu, san nan Ammar ya
juyo ya gode ma Malam, cikin kulawa
malam yace karkada mu ni domin Allah
na muku, ita rayuwa bakan wa zai tai
make ka nan gaba, kuma dukiya da dan
mitum, da dabba ba a musu keta, ku
kara gode ma Allah ammar sai da yaji
kwalla, asai ana samun irin wayan nan
mutane a zamanin yanzu, Hamdalah
yasakeyi ga Allah da ya ciyar dasu.
Inna laure ta gyara daya dakin nan
dama da kyausa, in sunyi baki anan suke
kwana, ta kwantar da yar katifar bonun
da ke dakun tayi shinfidi akan gado,
inna laure kenan duk da acikin kauye
suke tsohuwar akwai tsabta, komai nata
tsab2 gwanin burgewa, ga kamala da
kyautawa.
Malam yace ga daki an gyara zamu
kwana da kai inna laure kuma sai su
kwana da kan warka, kafin in Allah ya
kaimu waye wan gari, sai kubamu
tarihin ku da abunda ya baroku da gida,
Ammar yace to, Malam ya kara cewa
meye suanan ka..? Amar ya nisa yace
sunana Ammar ita kuma kanwata
Zainab, Malam yace aaa babban suna
gareta, sunan Mahaifiya ta gareta, Allah
sarki Uwata zan kiraki da shi, har cikin
ran Auta taji sunan da irin kauna da
suka gwada musu, haka ta shiga dakin
inna laure ta kwanta don huce gajiya.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Bacci tayi sosai akan yar katifan inna,
sai magriba ta farka tayi sallah, bayan ta
idar inna ta kawo musu tuwon dawa mai
laushi miyar danyan kubiya yaji man
shanu, sai kamshi takeyi,nan suka ci
suka koshi, sai da sukayi isha’i kafin
Auta ta dingisa kafarta tashiga daki ta
kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa,
Ammar ma dakin suka shiga shida
malam suka kwana,
Auta bata farka ba dai asuba da inna ta
daga ta tayi sallah bayan sunyi sallah,
ta gaida inna ta din gisa zuwa dakinsu
malam ta gaidasu ta dawo ta zauna, don
ba halin taya inna girki,… Bata da lfy,
inna ta musu dumame da kunun
tsamiya, nan sukaci duk da damuwan da
suke sai da sukayi santi don inna
gwanar iya girki ce,…
sai bayan da suka karya kafin malam ya
umurci Ammar da ya basu tarihinsa
dana Auta, ammar ya gyara zama nan
take idonsa ya kawo hawaye, da bai
zubo ba ya fara dacewa,
Sunana Ammar Saad Saraki, ni haifafen
dan maiduguri ne iyayena yan mai
duguri ne, kenan su Barebari ne gaba da
baya, baba na ya kasance dan gidan
sarkin Gwaza ne, su biyar mahaifinsu ya
haife su, Uku mata biyu masa matan
akwai Ya fanna, da da hajja gana da
Yakura, sai wan babana sunasa hashim
sai babana mai suna Sa’ad, mahaifina
ya taso cikin kulawa da kaunar
mahaifinsa kasan cewar yana da
nutsuwa sabani yaya shi da suke uba
daya wato hashim,
hakan yasa suka tsani baba na da
mahaifiyarsa don shikadai ta haifa
sauran hudun duk yayan kishiyarta ce
Hajiya faima,…
duk tsanar da suka masa bai damesa ba
ya nimi ilimin boko da na addini bayan
ya kammala karatun degree dinsa ya
dawo gd,
sai mahaifin sa ya masa Auren gata da
mahaifiya ta, Hakimin liman kara, hajja
faty mahaifiya kenan ta kasance mace ce
mai kamala da kyautatawa ga hakuri da
juriya ga sanin darajan dan adam,
lokacin auren kudin da sarki Abdallah
Saraki ya kashe ba karamin tada
hankalin hajiya fatima yayi ba, nan tace
ita mai yasa baza ayi auren danta ba,
sarki yace a yanda bai nitsu ba shine
shaye2 yar wa za a hada shi da ita,
tun daga wan nan lokacin suka dau tsan
gwama suka daura ma kakata da da
mahaifiya ta, duk da hakan bai damesu
ba,
kwanaki sun ja yau wata 5 da auren
mahaifina da umma na nan ta fara
laulayin ciki, gashi yazo mata da laulayi,
bata son shan ruwan fanfo sai na rija
tunda suka lura da hakan, sukayi
makircinsu aka bata ruwan gdn gaba
daya don karta samu na sha, haka
kullum sai anje nimota ta a gari don in
bata sha ba tashin hankali ne, haka
rayuwa tayita tafiya.
Sarki Abdallah Saraki, ya yanke
shawaran sauka a mulki sai daura dana
Sa’ad Saraki akan mulkin gwaza, tun
daga randa sarki ya yanke hukunci,
hankali hajiya fatima ya tashi, nan suka
soma shiga bokaye, sai da suka san
makircin da sukayi mahaifina ya dau
mahaifiya suka bar garin bashi tun daga
lokacin ba asan inda mahaifina yake ba,
bayan tafiyan mahaifina bakin cikin
yasa yagamu da ciwon hawan jini, harya
makance da ganan kuma Allah ya karbi
abunsa,……
Mahaifina na barin gari bai zarce ko ina
ba sai kanon dabo tunbin giwa ko da
mai kazo anfika,….lol…. Amma basufi
yan Bauchi ba fa,
nan ya samu wani mutumin kirki ya
rikesa a unguwar Dakata, haka yayi ta
rayuwansa da umma na harta cikinta ya
kai na haihuwa, nan laraba ta tashi da
matsanacin ciwon mara nan sukayi
asibiti, ana kaita ta haifi danta,
tubarkala ko kalon dan batayi ba Allah
ya karbi abunsa, asai masalan da aka
samu lokacin tana mai duguri, maganin
da aka a rijiya ta sha don karta haihu
dake Allah yayi zanzo duniya sai da ta
haifen lokacin ya mata illa sosai, shine
sanadin mutuwarta.
®WHW®
Rash Kardam
[9:47PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Bayan anyi zana idarta matan da
babana ke gidan ta karbe ni haka ta
raineni har na girma na kai 15 yrs
lokacin ina secondary school, haka zamu
fita aiki mudan samo abunda zamuci
sam baba na yaki aure, ana cikin haka
malam suka shirya komawa garinsu, don
suma mazuwa ne, yan jalingo ne, tunda
suka shirya tafiya, mahaifi na yace na
shirya muje muga yan uwansa,
tunda ga ranan ya nimi kudin motan
tafiya muka shirya ranan asabar 12 /3/
2012 muka tafi mai duguri tun a hanya
mahaifina ya ke cemin gabansa na
faduwa, ko da muka isa mai duguri,
muka shiga motar gwaza, muna isa yaga
masarauta ya canza nan ya samu lbr
rasuwan iyayensa, mahaifiyar sa ma
bata dade da rasuwa ba, gidansu ya
watse nan mukayi kuka tare, daga nan
yace mu wuce cikin mai duguri,
washegari muna zuwa, cikin garin mun
sauka a tasha, kenan nace ma baba na
ina jin fitsari, nan yace inje bayan gidan
tashar na tafi kenan,
kafin in dawo naji karan wani abu
dammm, gurin ya dau hayaki asai bomb
ne ya tashi tare da mahaifina,
Innalilahi wa inna ilaihi raji’un, abunda
na furta kenan nan aka tattara wayanda
suka tarwa tse ki gawan mahaifina ban
samu gani ba tun daga nan na shig
gararin rayuwa, kwana na 2 a mai
duguri a tasha na dan samu taimakon
kudi na hada da nawa, nan ji a tasha
ana mitar Kaduna haka kurum naji
garin ya min,
nan nashiga motar,
Kiran sallah da akayi ne ya sasu mikewa
malam jikinsa yayi sanyi alamar tausayi,
inna kam harda hawaye Auta kam kuka
takeyi shabe2 don sai yau tasan tarihin
Ammar,
Bayan sun dawo daga sallah malam yace
su huta sai gobe yaji lbr Auta da zuwan
ammar kaduna, nan inna ta daura musu
abinci,..
 ta girka musu, dan waken dawa da wake
ba karamin, dadi yayi ba, don sunyi
santi inna ta iya daka yaji, don harda
yar bushahen namanta, takesawa acikin
yaji sai yayi zakwakwai, gwanin santi,
Da la’asar haka sukayi sallah sukazo
zauna malam yace zashi dibo ruwa nan
Ammar yace zan bishi, suka dau jarkuna
zuwa rafi, suna yar hiran duniya akan
abunda ke tafiya gar suka dawo saida
sukayi sawu 3 nan inna ta dafa musu
ruwan zafi sukayi wanka,…
Malam suka fita zuwa wajen gd,
suna fita suka hango yan matan kauyen
sun taru a dandali, tun daga nesa suka
fara gulman Ammar yau malam ya samo
santalelen saurayi, wan nan tafara naa
ne wancan na nawane, najaat tace kai
kustsaya kuga duk cikin ku kunga da
wanda ya dace sai ni, dake duk suna
tsoronta ba wanda ya tanka, nan malam
fa Ammar sukazo suka wuces7 zuwa
shagon kauyen, garin suka sayi taliya,
malam kenan akwai kokari.
®WWA®
Rash Kardam
[6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Suna hira da Malam har suka dawo gida,
….
da daddare basu wani hiraba sanadin
hadarin da ya hadu, daki suka shiga
suka kwanta ba a dade ba ruwa ya sauko
sosai, haka aka kwana ana ruwa, da
asuba malam sukaje sukayi sallah, inna
da zainab sukayi acikin gd, haka suka yi
koko da kosai shuka karya, bayan sun
karya sukayi wanka,..
Bayan sun kan mala komai lokacin gari
ya dan sha, kafin suka fito gidin biyar
kofar gdn kasancewar garin ba mutane
da yawa, don gida daya na da rata
tsakaninsa da wani gd,..
bayan sun zauna malam ya bukaci
ammar da ya cigaba da lbr sa…
Ammar ya cigaba da cewa bayan na mai
dugri mun dau hanyar kaduna, sai dare
muka iso kaduna don driver ma na gudu
sosai, ko da muka isa garin kaduna, mun
sauka a kawo, nan kowa ya fita don ya
tafi girin da yazo, ina ina tsaye ni da
wani a gefena sai ga mai taxi yazo, yana
fadin Abuja Road Magajin, nan mutumin
yace nan zaije, take nima na shiga taxi
din munyi tafiya mai nisa ina kale2 don
yanayin garin yayi kyau sosai, ahaka dai
muka iso magajin gari nan mutum ya
sauka nima na sauka, ko da na fito na
rasa inda zani, hakan yasa nazo
masallaci nayi sallah kafin na bar
masallaci don na fara jin bacci, kofar
wani shago na samu na kwanta don na
gaji sosai, kwanana 3 a gurin ganin kar
mutanen gurin su zargeni yasa na dau
ledata na fara tafiya, nayi nisa sosai
kafin naga wani guri mai gine2 na sama
ga jama a sosai, daga nesa naga an
rubuta “CHE CHENIA MARKET” da
manyan harufa, nan nasamu na kutsa,
kusa da shagon mai takalma na zauna.
na kwana biyu ina zama a gun har na
dawo dan aika a gun, abinda na lura a
kwai wani shagon takalma da less da
material, saman shagon an rubuta
“ZAINAB FASHION DESIGN” a bunda na
lura akwai wani alhajin da ke yawan
zuwa da yarsa wata kyakyawa na
karshe, suna sayan kaya ne ko mai
sukeyi ban sani ba, tun da na kalli
yarinya naji ta kwanta min a rai ina
sonta da kanwa, hakan yasa duk randa
zasu zo in sun sai kaya zanje in dauka
musu in gaida alhajin ko da babanta zai
bani kudi bana karba, sai yayi da gske
nake karba, hakan ya mana masa dadi,
har yasoma tambayata inane unguwan
mu, nan nasoma hawaye ganin haka
Alhaji ya kama hannuna muka nufi
motarsa, munyi tafiya mai nisan gske,
har na fara tsoro ko dan yankan kaine,
nan nakama adu’ah neman tsari, mun
isa wani unguwan da ba mutane sosai,
sai da mukazo kofar wani katon gd mai
kyau horn yayi aka bude kofar, gate din,
gd ba laifi kam yayi kyau sosai.
Munshiga cikin gd mata kyakyawan
mace ta fito da murnanta, tana sannu da
zuwa Alhaji, nan ta kalleni, tace Abban
Auta ina kasamo wan nan yaro mai kyau
haka, Alhaji yace bari mu zauna tukun.
®WHW®
Rash Kardam
[6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Muna isa gd wata mace kyakyawa ta
fito, tace sannu da dawowa Abban Auta
ya hanya, cikin sakin fuska ya amsa
lfylau Alhamdulilah, tace ina kasamo
kyakywan saurayi haka, dad yace
mushiga ciki tukun, Allah sarki dad
gwanin taimako, ko da suka shiga cikin
gd abinci ta kawo musu nan Ammar ya
faraci daman da dan yunwa ajikinsa,
har saida dad ya tausaya masa sosai,
bayan ya sun ci abinci ne dad yace suje
falo koda sukaje nan ya tambayi Ammar
mai yasa yake kuka da ya tambayesa,
san nan ina iyayensa, nan idon Ammar
yaciko da kwalla, dad ya rararshesa,
Ammar ya basu lbr iyayensa dad saida
yayi kwalla ya tausaya masa, kafin yace
ya kwantar da hankalinsa zai rikesa,
bisa “AMANA” nan Ammar yayi godiya
dad ya kaishi dakin da ke waje gefen na
masu gadi ya ce ya zauna anan.
Dad ya saya ma Ammar kaya bana
wasa ba haka ya cigaba da rayuwa
acikin gidansu Auta gashi sun shaku da
Auta sosai, a iya zamansa a gd yanda
yasamu lbr a gun dad wata rana suna
zaune ya soma bashi lbrsa dake sun saba
sosai2 dad ya ja shi ajiki,..
Ammar sai da ya kurbi surki mai zaki
yaji suga kafin ya ci gaba da cewa barin
baku lbr Auta a takaice
Wacece Auta Zee
Asalin Alhaji Al-hasan Kano haifefan
dan garin kano ne, zama ne ya kawo su
kaduna dake yayi karfi anan yake
kasuwancin sa, tun da ya dawo kaduna
bayan rasuwan iyayensa , sai ya dibo
yan uwansa ya sasu akan dukiyarsa,
mahaifiyarsh ita kadai ta haifa yayinda
yake da yayu yan uba wato Sani da
Isiyaka uwar su daya yayinda Sani shine
babba sai Baba isiya ka,
Baba sani yana da yaya 4 Sadiya itace
baba sai kabir san nan Anas sai Autarsu
Sa’dat sun kasance abin so gun iayensu
da kulawa Baban Auta shi ya dauki
nauyin karatun Sady ya hada su da Auta
gashi jininsu yazo daya baka rabasu ko
ina taresuke,.
Baba isiya kuma matarshi daya da yara
2 Fauziya ana kiranta da pinky sai kan
warta faima sina kiranta da faty, haka
rayuwa tayita tafiya.
Dad ya kasancr mai yawan taimako da
son talakawa sabanin yan uwasa da ko
kyauta yayi sun rinka mita kenan basa
son ganin wani ya rabe shi baran in
yana taimaka masa,
tun randa suka san dad ya kawo gdn
suka fara hada rai in ko mun gamu zagi
da hantara ba wanda ban sha duk in
kauda kaina sabida dad ya rikeni da
“AMANA” hakan nazamo mai aika a gd
kuma wani lokaci mina tare da auta da
Bilisu kawarta yar makwabtasu wato yar
inspector Abubakar bilki kasancean
sunan maman babanta ne shiyasa suka
boye sunan ana kiranta da futha wato
fatuhatul-khair, ba karamin shiri futha
da Zee Auta sukeyiba, haka Ammar yana
ji da ita.
Hajiya Aysha itace maman Auta ita
kadai dad ya aura tun aurens da yan
watanin Allah yabata cikin cikin ikon
Allah cikin baizo da wani laulayiba, nan
tayita kula cikin koda wata haihuwanta
yazo nan ranan nakuda ta kamata basu
jima da zuwa asibiti ba ta haifo yan
biyunta kyawawa mace da na miji
murna gun dad ba’a magana nan suka
dawo gd, tun kafin suna na mijin ya
rasu ya rage sai mace, mum tayi kuka
daga karshe ta hakura ranan suna yar
taci sunan zainab zainab wata ta 4 ta
kamu da rashin lby, asai bana tashiba
basuyi dogon jinya ba Allah ya karbi
abusa, tun bayan rasuwansu hajiya bata
sake ko bariba sai bayan shekara 5 ta
samu cikin Auta nan suka dau son
duniya suka daura akan cikin nan bayan
wata tara ta santalo yarta kyakyawa nan
taci sunan Zainab, haka sukayita rai non
xee harta girma.
Tun da na dawo gd Alhaji ya mai dani
makaranta nan nacigaba da karatuna
ina dawo inyita wasa da Zee da futha, ko
muyita karatu haka rayuwa tayita tafiya
Su baba sani basuda birin da
yawuce suga na bar gun dad don ba zan
manta ba akwai randa suka min sharrin
sata ranan nayi kuka kamar raina zai
fota.
®WISDOM HAUSA WRITERS.
Rash Kardam
[6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Duk wani abun da zasu min na kanyi,
hakuri in jure don ba dansu nake zama
ba,
haka rayua tayi ta tafiya har na gama
HND a gidan dad na karanta fanni
business, yayin da Zee Auta ta gama
secondary school dinta ita da Sadiya da
futha, ranan murna ba a magana don
sai da dad ya shirya mana kayatacen
liyafa, bayan mun gama mun dawo
zaman gida sai Auta da ke zuwa
islamiyya, ni kuma duk wa aiki ina yi
duk da cewan sun hana ni yi amma
nakan sa kaina wani lokacin.
samun shigan da nayi a gdn shi ya daga
wa maikatan gdn han kali har suke ga su
da suka dade ba a musu abunda ake
min, tun daga ranan suka fara kule2 na
hanyar da zan bar gdn.
Baba sani da kawu isiya burinsu yanzu
shine tayaya dukiyar dad zai dawo
hannun su don kulum samun cigaba ya
keyi, kuma ba abunda suka tsana irin
yawan sadaka da kyautata wa mutane,
acewar su baisan zafin dukiyar sa ba,
sun sha zuwa su samesa gameda ya
daina yawan rabar da dukiyan sa, yaki,
ya ce in dai akan wan nan ne kar su
sake tun karansa, tun daga lokacin suka
fara kule2 na makircin kawar da Dad.
Basu tashi razana ba sai ran da dad
yace musu zan fara aiki, a gurin kuma
yanzu zai bani manager a company nin,
ko kuma duk wani shiga da fuce kudi
yazama ta hannu nane, ko wani kayan
da za’a saya duk zai dawo hannu na,
ran da dad ya sanar min bakaramin
murna nayi ba har kuka nayi, asai
akwai irin su dad a duniya, asai bazan
yi maraicin iyayeba, dad yayi ta lalla
shina,.
Han kalin su baba sani ya tashi
matuka, nan suka fara shawar su jefa
dad acikin ruwa nan baba isiya yace
tayaya zamu jefasa, haka sukayita
shawar wari, har baba sani yace mufara
masa baraza ya daura mu a kan dukiyar
sa, ko ya bamu in yaki sai muje gd
mukashe shi da iyalansa da dan koran
da ya daura akan dukiyar, nan sukace
gakan za’ayi, tun daga wan nan rana
suka soma kiran dad suna masa bara
zana, akan dad ya basu dukiyar sa yaki,
don har nima a sha yimin barazana
akan na bar gdn dad amma naki don da
Allah na dogara nan da dad zai rasu ya
kiramu ya bani AMANA zee san nan
yasanar mana ana masa baraza, amma
yaki fadan ko suwaye, bayan da ya fita
ne na kirashi a waya na tambayesa da
farko ya ki fada min sai da na sanar
masa cewa nima ana min baraza na, na
basa lbr kafin ya ban lbr komai yace da
kar in sanar da xee hankalinta zai ta shi,
da daddare suka zo don kashe mu gaba
daya cikin ikon Allah ya kubutar da ni
da Auta kuma a lokacin taga wayan da
suka kashe mata iyaye, dali2 da yasa
yanzu na sanar mata kenan wannan
shine lbr mu, Malam da inna laure suka
dago fiskansu cike da kwalla ga tausayi
auta ma kukan take ni kuma hawaye ne,
wani na bin wani.
Malam yace Allah ya jikan iyayenku,
san nan a duniyar nan har ana samun
marasa imani irin wayan nan mutane
sun ci AMANA ga bata ZUMUNCI da
sukayi ba ko tausayi a ransu sai son
duniya, kuyi hakuri da rashi, da sannu
Allah zai toni asirin su ya kuma saka
muku, Allah ya jikan su muka amsa da
Ameen.
Yan uwa amin afuwa na rashin jina
kwana 2 waya tace ba charged, kuma
ban samu zama ba.
Luv u all my fanz
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Bayan sunyi sallah isha’i suka dan yi
hira kasancewar lokacin damina hadiri
ya hadu aka soma iska, dole yasa suka
shiga dakunan su don bacci, ruwa akayi
sosai washe gari da safe bayan sun
karya ne, Malam yayi shirin zuwa gona
nan Ammar yace zai bi shi suka tafi tare,
inna da Auta sukayi aikin gd.
Haka rayuwan su ya kasance acikin
kauyen cikin kwanciyan hankali, yau
kwanan su 10 kafar Auta har ya warke,
Ammar ma ciwonsa ya bushe har yayi
bawu, nan yasoma tunanin mafita don
zamansu kauyen kaduna sam baiyiba,
don marasa imanin nan suna sanin yana
cikin kauyen to zasu iya turowa a
kashesu baki daya, malam ya samu ya
masa baya ni yana so su kara gaba don
in mutu nen nan suka samu lbr zasu iya
turo wa a kashesu malam yace hakane
jiki ba kwari ya dau ko yan kudinsa da
ya tara na kayan gonan da ya sayar ya
basu yace suyi guziri inna kam da taji
zasu tafi har da yar kukanta don sun
shaku auta ma tayi hawaye, washe gari
alhamis suka fito da ga kauyen nan suka
shiga motar zuwa rigiyar malam wani
kauye da ke jahar bauchi, a cikin motar
suka zauna shiru ba mai magana sai yan
motan da suke hira duniya.
Haka har suka iso wani kauye wai
shi na bardo, nan yaga ana sauka kawai
sai yace bari su sauka gurin nan suka
sauka, koda suka sauka gefen rumfunan
garin dake bakin hanya ne ya sayo musu
fura da nono roba biyu ya ba ma zee ta
amsa, tafara sha kenan sai ga hawaye,
ammar na ganin haka yace Auta hakuri
zakiyi shi rayuwa haka take yau dadi
gobe ba dadi mukasance cikin gode ma
Allah, sai ya kara wada yar mu cikinta
yayi sanyi amma takasa shan nono, wai
ita ce yau a titi a kuma kasuwa take cin
abu, rayuw kenan Allah ya jikan su dad,
ganin taki sha yasa Ammar yakasa sha
shima, don baya kaunar ganin zee cikin
tashin han kali, nan2 sai yashiga
damuwa.
haka suka bar gurin suka dawo gindin
wata bishiya suka zauna, lokacin sallah
yayi ya nufi masallaci, yayi sallah dake a
gefensu yake bayan ya idar ya dawo
auta tayi alwala ta shinfuda dan kwalin
zanin da inna ta fata ta daura, tayi
sallah, haka har dare yayi koda aka
watse gashi basu san kowa ba, Ammar
ya duba musu gurin wani mai shayi da
benci a gun nan ya hada ma auta kwaya
biyu yace ta kwanta, haka ta kwanta
idonta na zubar da hawaye, tabbas tasan
ammar ne kadai ya rike iyayenta da
gsky, Allah ya saka masa da dawai niyar
da yakeyi da ita, Allah ya jikan iyayenta
da nasa Ameen, Ya Allah ka bani abunda
zan saka ma Ammar da shi, kuka ne
yazo mata marar sauti haka tayi mai
isarta daga baya tayi shiru, ammar ko
kasance wan benci biyu ne a gun mai
shayi ba wanda zai kwanta yasa ya dan
zauna ya jingina da jikin falangen gurin
shayi haka har bacci ya daukesu.
Cikin dare misalin karfe daya da
rabi, cikin bacci Ammar ya rika jin ihu
daga nesa tun abun na nesa har ya
matso kusa sai auta ma taji ta tashi, ihun
yayi yawa gashi gudu sukeyi sai a
lokacin yaji ana cewa barawo barawo,
yace ma auta ta tsaya kar ta fito jikinta
sai bari yakeyi nan ya fita itakuma tana
lekawa, aiko yana fitowa sai ga wani
tutum da gudu yabi bayan gurin shayi ya
gudu, ana haka sai ga mutanen sun yi
kansa suka nan suka fara dukansa suna
shine barawon, auta na ganin haka
tafito da gudu ta na ihu, wayyo Ammar
dina ba barawo bane, wayyo dad kuzo
ku kuga halin da muke ciki zasu kashe
shi kansu tayi gadan2 tana so ta kutsa,
da kyar ta samu tashiga dai2 wani ya
kai masa duka da dorina kenan ya sauka
akan Auta nan tasaki wani razanen
kara.
 ®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[6:40PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Wani kara tasaki, sai a lokacin suka kula
da ita, take suka haskata da toci sai
sukaga macece, wani daga cikinsu yace
mai ya kawo wan nan guri, sai da yace
tsaya in ga barawo nan tukun don
wancan gajeren wando ne ajikinsa, yana
haskawa ko ah… ah.. wan nan ba
barawon bane to ina yayi, sai dayan
yace wan can na da kirar gutun mutum,
auta ko sai ihu take, ammar ko motsi ba
yayi sanadin dukan da aka masa harda
bora, wasu ice haka akayita kwana
masa.
A kaduna kuwa sadiya Al’amari
abban ta ya daure mata kai don yasaka
dukiyar auta gaba sai ci sukeyi, a ko a
jikinsu, wata ran kam ma intasoma
masa zancen auta ya hauta da fada
kenan, haka yasa ta soma zargin wani
abu a tare da su,
Wani yammacin asabar sun fito
gidansu futha suna tattaunawa akan
batun auta da yanda zasu bi al’amarin
kenan sai suka hango abban sady, tun
daga nesa yasoma wurga mata wani
kallon tuhuma, ganin haka yasa tayi
sallama ma futha tashiga gd, aiko kamar
jira yake yazo ya fara zazzaga mata
bala’i akan tafita harkan futha ko ya
saba mata, shi baya son kawancen su,
ganin su tare ma baya so, sady tace kayi
hakuri abba ina tarayya da ita ba dan
komai ba sai tun auta ta nan muna tare
mun kuma shaku, abban sady yace
hungo nan uwaki da autan nace uwaki
da auta kar ki kara kira min sunan
wayan nan banza mutanen,
nan take idon sady ya kawo hawaye ita
kam bazata manta auta ba aminiyarta
jininta, anya baba na da imani kuwa ko
tausayinsu babu a zuciyarshi ko ya
manta dukiyar iyayenta yake wada
kansa shi, ya Allah kasanya mana
tausayi da imani a zukatan mu Ameen
ranan tayi kuka haka ta yini sukuku, sai
yamma tayi shirin issalamiyya ta tafi ko
da taje nan ta saida wa malaman su
akan sutayata adu’ah ta kuma musu
bayani ko mai ake ciki, tun daga ranan
ya zamana kulum a makaranta bayan an
gama karatu sai anyi ma auta da
iyayenta adu’ah.
Futha kuwa kwana 2 taji sady shiru
nan tashirya ta shiga gdnsu aiko nan
sukayi karo da abban sady, tun daga
nesa yasoma hararanta, tana isowa kusa
yace kee wajen wa kika zo cikin ladabi
tace baba kawar Auta ce nazo gun
sadiya ne, yace maza ki juya kar na kara
ganin lafarki a gdn nan yata batayi
kawance da ke ba don ban yarda da kee
ba.
ran futha in yayi dubu ya baci haka ta
juya gd jiki ba kwari kuma tana tunani
akan al’amarin nan,
anya ba hannu baban sady a kisan su
abban auta, to tabbas ko ma miye sai na
binciko ko da hakan yana nufin rasa
raina ne ya Allah ka bayya na gsky.
Muta ne da ke gun duk suka soma
watsewa ganin baya motsi gashi sun
dakesa ba akan wani laifi ba, gudun
shiga Case, auta ko in banda kuka da ihu
ba abinda take sai kiran sunan Allah ga
idonta har ya kubura yayi ja ga ammar
shi da matatce marabansu kadan ne,
wayyo Allah na ka taimaka min ka min
agaji in ammar ya tafi bani da wanda
zan kalla inji dadi, rayuwata zata zama
abar tausayi Allah kaine gata na ka tai
make ni ammar dina ya tashi, cikin
kuka take jijiga Ammar ga hawaye ga
majina duk sauka sukeyi, Ammar dan
Allah ka tashi kar ka barni ka manta
Dad ya baka “AMANA TA” ka tashi ka
kula da “YAR AMANA” ka kuka take
sosai mai ban tausayi tana ta surutai
amma shiri ganin haka yasa takara fasa
wani kuka mai ban tausayi wanda ni
kaina Rasheedah ban san lokacin da na
fara zubar da hawaye ba, gsky Auta da
Ammar kun ga jarabawar rayuwa ga wlh
Allah sarki auta abun tausayi, Allah yasa
ammar dinki ya tashi Ameen.
Jumma’at Mubarak 2 all my muslim
sisters n brothers.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:32PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Kuka take sosai ammar ko motsi baiyi ba
nan takara jin natsara su baba sani suka
jefasu cikin irin wan nan halin, wani
bawan Allah ne mai tausayi ya dawo
yace bai war Allah daga ina kuke, cikin
kuka tace ka taimaka min dan uwana ya
tashi shikadai ya rage min an kashe
iyayenmu, nan kukanta ya tsananta
cikin tausaya wa yace ki tsaya tai mako
daya zan miki yanzu ga gidan mai gari
can barin je na kirashi da gudu ya tafi
ko da yaje ya jima yana buga kofar kafin
aka bude, masa, mai gari ya fito suka
gaisa nan yasa sai damasa cikin damuwa
mai gari ya dauko garensa ko da suka zo
har lokacin ammar bai farfado ba,
hakan yasa suka daukesa zuwa asibitin
garin nan aka bashi agajin gaggawa,
bayan sun dan masa treatment ne suka
shin fidesa akan yar gadon asibiti, auta
ko in banda kuka ba abunda take, bayan
ansa masa ruwa mai gari ya musu
sallama akan da safe zaizo duba su, auta
kasa bacci tayi ga haddiri ya hadu nan
akara walkiya da sauri ta haye karamin
gadon duk tsoro ya ci kata baran data ga
wajen asibitin jeji ne, nan ta kan kame
ammar sosai hawayen ta na sauka a
akan kirjinshi cikin barci yaji an kan
kamesa, a han kali yasoma bude ido
yaga duhu da kyar ya iya daga hannunsa
yaji auta ne nan kuma yayi kokarin
mikewa kansa ne ya masa wani nauyi ga
sara masa da yakeyi, a hankali ya shafa
kan yaji bandeji ne an daure, sai a
lokacin ya tuna mai ya faru hawaye ne
yasoma zuba masa shima tabbas yasan
suna cikin wani yanayin da Allah ne
kadai zai fiddasu.
Auta jin alaman na motsa hannu
yasa da sauri ta shafi fiskansa nan taji
hawaye a hankali ta daga hannun ta
tasoma share masa hawaye tana cewa
kayi hakuri Allah zai saka mana kaji
kuma Allah yana tare damu yaga halin
da muke ciki ba zai bar mu haka ba, nan
ya karajin jikinsa ya mutu ga auta da ta
kwanta masa ajiki bai san lokacin da ya
sauke ajiyar zuciya ba, har azuciyansa
yana son auta ko da aure zatayi ba iya
bayar ta ga wani ba don bai son wani
yaci Amanar da dad ya basa ko in auta
tace bata sonsa to dole ya hakura don ba
zai takura ta ba, gwanda ya shiga ko
wani irin hali ne da ya sata a damuwa.
a hankali ya kara kan kameta a jikinsa
wanda sai da itama taji wani shock ya
ziyarci jikinta ajiyar zuciya tayi ahaka
suka kwana yau kam bacci mai dadi tayi
ajikin Ammar wanda rabonta da ta yi
tun iyayenta suna da rai, sai da asuba ta
mike da ta fiti kofar asibitin in da taga
randar ruwa ta diba tayi alwala ta shin
fida dan kwalinta tayi sallah,
bayan ta idar ne ta zo da ruwan ammar
da kyar ya iya tashi sabida jikinsa yayi
tsami tana zuba masa ruwan yayi alwala
yana kwance yayi sallah don kansa ya
masa nauyi.
 Sai da gari ya waye sosai gurin
karfe 9:00 mai gari yazo duba sa da yar
kununsa a kwanon sha da kosai nan
suka gaisa bayan sun gaisa ya ke
tambayan su mai ya kawo su gari da har
zasu kwana a kasuwa nan auta ta basa
lbr ya tausaya musu sosai, nan ya musu
sallama akan darana zai zo dubasu auta
haka take kula da ammar dan kudin da
malam ya basu shi suke yasan abun da
ya dan musu su ci, kwanan Ammar uku
a asibiti aka sallamesa jikinsa ya warke
sai tabo, ko da suka fito a asibiti gdan
mai gari ya nufa ya masa godiya san
nan yace yana so su kara gaba don yana
son cikin birni inda zai samu sana’a
yayi da karfinsa, nan mai gari ya ce
yanzi kana fita sai garin bauchi shine
babban gari, nan yaji yana son garin
don ya dade yana jin lbr garin bauchin
yakubu ga Addini ka mutunta mutum ga
iya karama baki, ga masa waina sai
wanda kazaba, nan yayi godiya mai gari
ya rakasu suka shiga motar bauchi.
®WISDOM HAUSA WRITER’S
Rash Kardam
[7:32PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Mota su ka shiga, a hankali suke tafiya,
haka kurum ya tsinci kansa da farin ciki,
tun a hanya yaji yana son garin ya
burge shi.
Auta ma haka abun yake tana gefen
Ammar ta dan jingina kanta a
kafadarsa, haka kurum take jin sanyi a
zuciyar ta, nan ta fara tuna irin
rayuwan da sukayi abaya lokacin
iyayenta suna raye, ku ina zataje a mota
suke tafiya mota mai AC ba hayaniya,
amma yau gata a motar kasuwa, Allah
sarki yarinyan da taso cikin gata da
kulawa ya daya tilo yau gata a cikin
gararin rayuwa Allah ya kawo masu
sauki Ameen.
Karfe goma da minti sha uku, suka iso
cikin garin bauchi, driver ya sauke su a
waje tashar mota na winti market, nan
suka sauka, kowa ya kama gabansa,
Ammar ya riko hannun Auta suka bar
gurin, titi suka tsallaka suka zo ta gefen
stadium akwai dan guri nan suka zauna,
kallo daya zakayi ka ga kamanin su auta
yanda ya canza sunyi baki ga rama da
sukayi sosai.
Sun dade a gurin sosai, amma sun
rasa inda zasuyi can yace bari yaje ya
nimo musu abinci, tace to gefen gun
masu sai da jarida da gyaran mashin ya
ga mai sai da shinkafa da wake nan ya
saya musu roba biyu da pure water
kwaya 2 ya kawo musu, haka suka ci
sukayi godiya ga Allah ya mayar wa
masu shinkafa ya karbi canji ya dawo,
haka suka zauna sai da aka kira sallah,
nan ya sake saya mata ruwa tayi alwala
shi kuma ya tafi masallacin da ke gefe
yayi sallah, bayan ya dawo suka zauna
hira ya rinka mata yana bata dariya don
ya debe mata kewa sabida yaga damuwa
a idonta sosai, haka suka yini har dare
agun suka kwanta.
Da gari ya waye sallah yayi yace
ta zauna a gun kartaje ko ina zaije ne
man abunyi ko da dako yasamu don su
rinka samun abunda za suci da in da
zasu zauna, haka ko akayi ya shiga cikin
kasuwar winti, haka yayi yawo sosai
amam shiru ba lbr aiki sai azahar ya
dawo yaje ya sayo musu shinkafa sukaci,
bayan sunci tace Yaya na anyi nasara
kuwa cikin mutuwar jiki yace ina Allah
baisa an dace ba, idonta yaciko da
kwalla tana shirin yin kuka ya girgiza
mata kai alamar aa, yace ko kin manta
Allah yana tare da mu bazai barmu haka
ba, kuma duk bakin da Allah ya tsaga
bazai hana shi abinci da zaici ba.
haka suka sake kai dare nan suka sake
kwana.
Washe gari ma haka yafita yayi
yawo har ya gaji gashi yan kudinsa sun
soma karewa saura dari biyar, yau sai
bayan la’asar ya dawo dake ya ba ma
Auta naira dari don tasayi abunda zataci
ko da yadawo yasamu tana bacci akan
yar fallen zanin da ta shimfida
tausayinta ya kama shi, Allah sarki auta
yau itace tamkar wata tsintaciyar mage
gwamma shima namiji ne, idonsa ne ya
ciko da kwalla a zuciyarsa yake adu’ah
Allah ya kawo musu dauki baisan
hawaye yana sauka da ga idonsa ba saiji
yayi auta na share masa hawaye itama
idonta yaciko da kwalla, tace Yaya na sai
dayaji sanyi har cikin ransa, mai yasa ka
kuka ban son ganin hawayen ka, in kai
kayi hawaye wazai rarrashe ni, kaine
mai sani farin ciki, Allah gatana kaine
gata na, yaya na waya taba ka karkasa
kanka cikin damuwa Allah zai kawo
mana mafita yana tare damu kaji,
kaman karamin yaro ya daga mata kai,
tace kayi min murmushi, ammar baisan
lokacin daya murmusa ba, itama
murmushin tayi ta rike hannunsa tace
Ya Allah kaja kwanan yaya na kabani
abunda zan saka masa dashi.
®WISDOM HAUSA WRITER’S
Rash Kardam
[7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Hancin ta ya lakace yace Ameen amma
kwanan mu gaba daya, haka suka zauna
cikin farin ciki har dare yayi suka
kwanta.
Da safe ammar ya sake fita nan
ma ya barmata kayan karin kumalo ya
fita, nan yayi ta yawon niman aiki da
kyar ya samu wani shago zasuna debo
kaya daga stored suna kaiwa cikin shago
amma ba kullum ba sai randa za a saka
kaya a shago ko sun dawo daga sari,
haka ya dawo da murna yake
sanarmata, nan ta tausaya masa tace
Yaya na zaka iya yin dako kuwa kai ya
daga mata yace eh kan wata, in dai
zamu samu abunda zamuci
Alhamdulilah.
Washe gari haka suka tashi kudin su ya
kare sai naira hamsin shinkafa ya sayo
ma auta ya zauna yasata a gaba taci,
tace aa sai dai su ci tare fir yaki don ba
zai ishesu dukansu ba, auta taki ci ganin
haka yasa ya dau cokalin roba ya fara
bata lbr abun dariya yana bata a baki
tana ci har ta cinye , ta kalli kwanon tace
kai yaya na gashi kasa na cinye kai ya
girgiza mata alamar kar ta damu, haka
sukayi ta hira har dare,
Futha ce ta fito sanye cikin shiga ta
alfarma ta shiga motarta ta nufi
makarantar da tafara zuwa, bayan sunyi
lectures kenan tafito tana zaune, kiran
sady ne ya shigo bayan sun gaisa ta
tambayeta kwana biyu tace lfy nan suka
taba hira ta hakuri gameda abunda
babanta ya mata nan sukayi sallama ta
dau ko hanyan gd tun daga nesa ta
hango wata sabuwar mota honda ta
hadu motar blue kalo daga gidan su Auta
tafito wanda yanzu su Sady ne acikin
gdn, sai da tazo kofar gidansu ta tsaya
don ta karbi lab top dinta da tabada ya
duba mata, bayan ta karba ta fito taga
wan nan Honda tatsaya dai2 ita nan aka
zuge glass wacce ta gani a motar bakara
min mamki tayiba da ace itace a
wannan motar, pinky ce yar kanini
baban Auta wato yar Baba Isiyaka, hy
tace mata sai a lokacin ta dawo daga
duniyar tunani gaisawa sukayi ya kwana
biyi tace lfylau ya school tace
Alhamdulilah, sun dayi hira kafin sukayi
sallama, futha ta tafi tana tsananin
mamaki sosai da sosai pinky ce haka
harda mota lalle sun samu duniya tabbas
dawata a kasa dole ma tabi didigi haka
taja motarta tashiga gida tan tunani
kala2.
Can cikin dare wani hadari ya
hadu ga iska daya taso sosai, Yaff yaff
yaff ruwa da iska yasoma zuba, kan kace
me sai ga ruwa ya barke baka dan ba,
nan Ammar suka farka kafin sunimi
matsuguni rua ya soma dukan su
bakadan ba duk inda zasu fake ankulle
nan suka dun kule a gindin shiya ruwa
nan dukansu Auta ta kan kame ammar
tana yar kuka ga ruwa sai dukar su
yakeyi wani tsawa aka sake sosai wanda
yasa Auta kara rugume ammar har sai
da yaji tsikar jikinsa ya tashi yaso ya
ture ta don yanda yasoma feelings, ga
wani murdawan da maranta keyi alamar
period ga ruwa na dukan su gaka ruwan
ya kare akansu tass barin sanyi auta
takeyi ga maranta na murda mata gashi
ba kayan canzawa haka suka tsuguna a
tsugune har gari ya waye jikinsu har ya
bushe auta kam mara ke ciwo gada2 ga
zazzabi na neman mata mumunan kamu
nan hawaye ya soma zuba don tabbas
period dinta ne gashi kudinsu ya kare ga
pant daya ke jikinta kayan da zata canza
ma baba gashi kwananta 2 ba wanka sai
yau da ruwa ya mata duka Yasalam!!!
Allahuma ajirni fi musibati wa aklifli
khairan minha, jikinta yayi zafi sai
barin dari takeyi Ammar ko da ya taba
jikinta nan take ya rikice ya shiga da
muwa gashi kudinsu ya kare ga auta
jikinta yayi zafin Innalilahi wa inna
ilaihi raji’un yake furtawa a bakinsa.
®WISDOM HAUSA WRITER
Rash Kardam
[7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Jikin auta yayi zafi sosai ga ciwon mara,
ammar duk ya rude yarasa me ke masa
dadi ga kudinsu ya kare gefen wani
shagon daya ga ba a budewa yaje ya
kwantarta lokacin gari yayi haske sosai
ya cire yar rigansa na janfa ya luluba
mata nan yace auta kiyi hakuri barin
fita neman kudi ko zan samu sai in saya
miki magani kai ta daga masa hannu sa
ta riko cikin muryan marasa lfy tace
Yaya na Allah ya ka fita sa’a ya amsa da
amin, ya fita
Shagon dako yaje yayi sa’a an kawo
kaya nan ya yasoma aikin kwasan kaya
tun bakwai yagara sai karfe shadaya ya
gama nan aka bashi kudin aiki 200 dake
kayan ba masu nauyi bane shiyasa,
hamdalla yayi yana shirin barin layin
masu kayan zai wuce yaji wasu suna
neman mai zubar da shara nan yayi
aikin ya gyara musu gurin tass suka
bashi 50 daya layin ma sun kitashi nan
ya fara musu aiki aka soma kiran sallah
ya bari da sauri ya ce zaije ya dawo
yana fita chemist yaje yasayo maganin
mura dana zazzabi yabi yasayo musu
shinkafa auta harda tea irin na masu
yawo suna hadawa yasa mata da murna
ya kama hanya zuwa gunta.
Futha bayan ta huta washe gari tacr
ma Sady tana so su hadu akwai abunda
takeson sani, nan sady tace zasu acikin
Kad poly haka ko akayi da yamma suka
hadu bayan sun gaisa futha take bata lbr
abunda ta gani Sady tace nima abun ya
daure min kai don pinky bakara min
busha take ba kuma Abba na nima yace
wai ya sai min mota ba a shigo da ita
bace ni kaina futha yanda suke bushasha
da dukiyar su Auta abun har na razana
ni kuma har yanzu sunki yarda ayi
binciken akan wayanda sukayi kisan
nan da kuma inda Auta take, futha tace
kar kidamu sannu a hankali komai zai
zama tarihi Allah ya toni asirin duk
wannda keda hannu a wannan
al’amarin Sady tace Ameen nan suka yi
hira gameda karatu har sai magrib suka
rabu.
Baba sani ganin Sady da futha suna
neman dinkrwa yasa ya baza mata kan
tsaro duk inda sady tayi ana biye da ita
don kar futha ta gano sirrinsu don bai
yarda da ita da mahaifinta ba suna masa
shigan sauri akan al’amarin, su baba
isiya yanzu abun nema ya samu
hankalinsa kwance ke cin kudin da bana
saba har in anzo neman taimako gunsa
yana ikirarin sunsan wahalar dayayi
yasamu dukiyar su asama kawai suka
gansa da kudi, kutaya ni ji wai har yana
cewa sun san wahalar dayayi, baba isiya
har wani yar tumbi yasaka yayi fresh ko
mai ya dai2 har ya manta da wani alhaji
Al-hassan.
A bauchi kuwa Ammar da
murnar sa ya nufo gun Zee Auta ya
musu samuwa don shi ko ta kansa
bayayi yafiso yaga ita taci kafin sai yaci,
yazo tsallaka titi har ya kusa tsallakawa
sai ga wani mai mashi ya yanko aguje ji
kake kiiiii mai mashin ya shiga da
Ammar da sam idonsa ya rufe baya
ganin hanya.
Yan gurin nan suka dau salati suna tafa
hannu wasu suka yanko da gudu suka zo
ba da taimakon gaggawa Allah sarki
kowa da irin jarabawar da Allah ke
masa a rayuwa kamar yanda Ammar da
Zee suka shiga haka wasu ke cikinta
kowa da kalar nasa ya Allah ka jarrabe
mu dai2 da karfin imanin.mu Ya Allah
kabamu Abin da zamu iya Ameen Ya
Allah.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:35PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Kiiiii kake ji karar mashin ta tashi sama
da ammar nan mutanen gurin duka dau
salati, wasu da gudu sukayi gurin, abinci
kam duk ya zube, nan mutane sukayi
kansa cikin ikon Allah bai ji ciwo ba sai
dai ya dan buge kafarsa gefen hanya aka
maidashi mutane sai sannu suke masa
Ammar na dawo hayya cinsa sai ya
hango robar abinci ta fashe maganin
kam bai san ida ya yarshi ba, nan take
wasu zafafan hawaye suka soma gangaro
masa a zuciyarsa yana gode ma Allah
daya sa yana da sauran rai in da Allah
yaso sai kafarsa ta cire ko hannu yana
da kyau a kowani hali ka tsinci kanka to
ka gode ma Allah sai ya kara maka, cikin
ikon Allah mai mashin ne ma ya dan
kurkurje nan ya ba ma ammar hakuri
don yanzu fitowarsa bai da ko sisi
ajikinsa Ammar yace ba komai haka ya
mike ya na din gisawa ya sake zuwa
chemist ya sayo paracetamol da da
maganin mura na ishirin ya sayo ma
auta shinkafa talatin ba ko ruwa nan ya
laluba aljuhunsa ya ga biyar hamdala
yayi ya sai mata pure water biyar da
sauri yana din gishi ya nufi gunta.
yasamu duk ta dawo wani iri dagata
yayi yana mata sannu abinci ya fara
bata da kyar ta iya ci kafin tasha magani
ya maida ta ya kwantar nan yaje yayi
alwala yayi sallah bayan ya idar yayi
nafila yana gaya ma Allah kukansa kafin
ya dawo gurin auta ga yunwa tasoma
damunsa sai da yaga bacci ya dan
dauketa kafin ya sake komawa cikin
kasuwa ya yi sharan yayi sa’ah mai
shagon mutumin kirki ne ya basa dari
buyu nan ya bashi sauran abinci ammar
yayi godia yaci kafin ya sake suwa wani
gu ya musu aiki nan ya.samo dari uku
nufo hanya.
Tun daga nesa ya hango auta rike
da cikinta tana juyi da sauri ya karasa
gunta,nan yasoma mata sannu yariketa
kuka tasoma masa duk ya rude ya
tambayeta mai ke da munta tace cikinta
ganin yanda take juyi yasa ya dauketa
da sauri ya nufi titi nan rake aka zuna
musu ido dake haka ya nufi chemist da
ita nan mai chemist ya soma dubata aiko
yace Malam period dinta ne zaizo nan
ammar ya zare ido yaya zaiyi ba pant ba
gun wanka mai chemist ya bata magani
tun agun tasha ya dan kwantar ta akan
benci sun dan dade don ciwon ya dan
ragu sai rashin karfi ajiki nan ya cemasa
kudin magani 200 haka ta bashi nan
suka mike zasu tafi kenan yaga shini ya
bata gun da ta zauna nan ta zare ido yau
yaga ta kansa ya zaiyi kenan Yasalam
Auta ko tsaban kunya kasa daga idonta
tayi sai hawaye nan ta fara Allah ya isa
masu baba sani duk sune ummul aba
isin sata cikin wan nan hali.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:38PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ammar gaba daya ya rasa mai ma zaiyi
ne sun dan dade agun mai chemist daya
ga basu tafi ba ya lura da matsala dake
ustaz ne yasha Sunnah ya koshi cikin
kulawa yace malam lfy dai ko ammar ya
dago idonsa da ya cika da kwalla ya ma
rasa mai zai ce, mai chemist yace ya
kamata ka kaita gd don tayi wanka ta
huta ammar cikin muryan sa na rawa
kamar zaiyi kuka yace mu baki ne a
garin nan bamu da kowa cikin
tausayawa yace ayya sai a lokacin ya
lura da yanda jikin auta ya baci nan ya
ce masu ammar zan muku taimako daya
ga gd na banisa kazo muje gun matana
ta taimaka mata da kaya ta gyara jikinta
ammar yaji dadi yacd ba matsala nan ya
riko hannun auta suka bi mutu min nan
gd sa na bayan stadium plat ne ciki da
falo sai stored sai kitchen nan ammar ya
tsaya daga waje shikuma sukayi sallama
suka shiga da auta nan wata mata baka
mai dan kyan jiki gata da sakin fuska ta
fito tana musu sannu dazuwa cikin
harshen fullanci ya mata bayani nan
naga fuskan Rahmat ya bayya na tausayi
tace yar uwa shigo dake bayinta na falon
ne nan ta hada mata ruwan wanka ta
kaita bayin shiko mai chemist ya kowa
waje gun ammar suka dan fara hira.
Rahmat ta ciro mata sabin pant guda 4
da Alway ko amfani da shi batayi ba ta
dauko mata riga da siket daya da dogon
riga dake da ka dan zata fi auta ki ba
nan ta samata a wata yar jakan biki mai
zip da hijab daya da sabulun wanka
sinki da na wanki biyu nan ta saka mata
riga da siket na eglish wears wanda tasa
da hijab mai hannu blue yadin plan
tuyobo bayan auta ta gama wanka nan
ta bata pant tasa ta bata mai da powder
tasha da lip stick kai kar kuso kuga auta
nan ta yi kyau abunka da farar mace ga
kyau azuciyar rahmat tana yaba kyau
irin na auta abinci tabata nan taci sosai
ta bata zobo yasha hadi kafin ta dauko
jakan ta bata lokacin har ta dauraye
mata kayanta sunsha ta nuke tasa mata
a hakar tace ki duba waje kice musu kin
gama nan auta ta leka tun da tafito
ammar ke kallonta sai murmushi yakeyi
ga idonsa ya ciko da kwalla rabonsa da
yaga auta fess haka tun suna gun su inna
laure a kauye yau har yar kyau tayi,
auta tazo da sauri tasa hannusa ta share
masa kwalla tace yaya na kabar kuka
nima zaka sani kuka murmushi yayi
yace babyn dad yau kinyi kyau sosai
tace ta gode duk abunda sukeyi mai
chemist na ganinsu duk sun bashi
tausayi nan ta sai dama su sakon rahmat
mai chemist yashiga gd ya fito masu
abinci sai da su kaci kafin Ammar ya
masa godiya auta tafito suka kara gaba.
Rayuwa kenan
* * * * * *
Sady abun duniya duk ya isheta yanzu
bata isa tafita ba babanta zai dameta
gashi yace matukar ta hadu da putha sai
ya yanka ta kuma motar da zai bata ma
ya fasa duk ita bai da meta ba sai
sauyawan babanta anya yana da gsky
yake haka yazama dole insan sirrin boye
tana cikin wan nan tunanin pinky tazo
cikin masu matsatsun kaya da kyar ta ke
motsi cab su pinky an samu duniya
yanda akeso rawan kai ya karu bare ga
mota a hanu….lol… Hira sosai sukeyi
anan sady take lbr ta ma pinky sauyin
iyayensu pinky kafada tada ga alamar ko
in kula cikin isa tace ni ba damuwata
bane tunda zanci mai kyau insha mai
kyau bani da matsala ga motar da zan
shiga ko ina ba sa’ar dazata min raini
kin ga ni ba damuwata bace kawai ke
ma ki share kizo ayi harka dake sis sady
tace ni kyale kyale baya gabana gasky
nakeso tafito kuma zanyi iya kokarina
pinky tace ae saikiyi ta kai nan tafice
tashiga motar ta tabar gdn.
Almarin futha kuwa jaratu tasa a
gaba don ta cimma burinta shiyasa ita
ko saurayi bata kulawa karatu takeyi ga
yawan adu’a Allah ya bayya na Auta ya
karesu a duk halin da suke.
Baba sani ko yanzu an waye daga zuwa
wan na hotel din sai gdn wacce
bazauran shida baba isiyaka holrwar su
suke acewarsu Allah ya basu kudi dole
suyi abunda ransu keso, Allah ta kyauta
ya Allah kar kabamu kudin da baza mu
kasheshi ta hanyar halal ba ameen.
* * * * *
Auta dun yitafiya kadan don su koma
inda suke zaune bayan sun isa gun
ammar yace zai sake komawa kasuwa ko
zai sami aiki nan auta ta bata rai tace ka
huta ai tau mun samu abunda zamuci
kuma gobe ba zamu rasa ba don duk
bakin da Allah ya tsaga ba zai hana shi
abinci ba nan sukayita hirasu gwanin
burgewa daga gani yau suna farinciki
ammar yace to kimin afuwa nima naje
cikin kasuwa a kwai bayan gidan wanka
da akeyi na kudi nima in samu nayi
wanka auta tace sai ka dawo Allah ya
kare nan ya mike yaje ya biya naira 20
yayi wanka ya fito ya dawo gun autarsa
suka cigaba da hiransu.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:38PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Haka suka yi ta hira kulum ammar sai
yaje dako ganin ba zai fiddasu ba ya
nimi gurin mai sai da kayan fruits da
kayan miya suka fara sayarwa yazana
yaro agun nan ya na dan samu har mutu
min ya kaisa gidansa da ke bayan winti
market daki biyi ne daya ciki da falo
shida matarsa sai daki daya karami ba
ko flasta su ammar ke ciki kulum
matarsa sai tasa auta aiki gata da
kazanta auta bata iya gani sai ta gyara
gurin wanki yaranta tace sai tayi tun
auta bata iya ba harta saba ko kadan
bata fada ma ammar ba don zai iya
cewa su bar gidan ita kuma bata so
suyita yawo a titi wataran tayi kuka ta
share hawayenta haka tayita hakuri
gashi abinci dan kadan take bata kamar
na dan yaro karami sai dare ammar ya
somata na ma da madara haka sukayita
rayuwa kwanaki sun wa watanni sun
tafi har sun kai shekara a bauchi ba
abunda ya canza sai baki da sukayi da
ramakam akwaisa duk da ammar na iya
kokarinsa akan auta duk abun da yasan
zai mata kyau sai ya sai mata har yasata
a wata islamiya dake bayan unguwan
tana zuwa, shiko riga mai kyau bai
damu da kansa ba wataran har mita take
masa kayansa kala uku rak itako ya
cikata da kayan ado duk iya samu kudi
ma ita yake kashewa hakan yasa sa’dat
shiga tashin hankali don mijinta baya
kashe mata kudi haka gashi yaron
hannunsa yana hidima wa kanwarsa
nan take lbr wa makwabciyar ta tace ke
sa’adat bazaki ganeba ne haka kurum
zai na kashe mata kudi batare da yana
latsata ba daki daya fa suke kwana in
baki shawara yau ki fito ki lekasi kigani
nan suka tafa sukayi shewa hakao akayi
daddare ta fito cikin rashin sa a taga
ammar a waje yake kwana auta tana ciki
sai datayi haka har sau uku awajr take
ganinsa sai randa akayi ruwa shine taga
ya kwana a daki ko da taleka taga shi
yana bakin kofa auta na karshen daki ba
haka taso ba amma tsabagen makirci
irin nata nan tafara habaici ma auta
akan ammar na aikata masha’a da ita
ranan tayi kuka amma ta danne bata
fada ma ammar ba
don tasan yana da zuciya sosai haka
sukayita rayiwa abunu tausayi.
Abangaren ammar kuwa kasuna tafiya
dai2 har yayi customer a kwai wata
hajiya datake yawan sayan kayan salad
da fruit agunsa da vegetables har sun
saba wataran kam yarta take turowa
tasaya agunsa hakan dai yaci gaba da
dana’arsa, auta ko sai rama take kulum
in yasata a gaba yana tambayanta tace
bakomai haka zai gaji ya kyaleta.
* * * * *
Zaune yake a gaban kayan fruits wata
bakar HONDA CRV TA cike da nuna isa
da gadara take taku tun daga nesa
mutane ke kallonta sabida ta tafi dasu ga
ta da kyau tafiya take kamar bazata taka
kasa ba kai daga ka ganta kasan naira
ya zauna ma iyayenta da fatarta sannu a
hankali ta tsaya tana kallon yar fruits
don ita bataga wanda mum tace tazo
gunsa ba har taxo zata juya ta hango
wani dogon saurayi fari mai kyau
tamkar sharukan kalo daya za kamasa
ya tafi da tunanin mace don daga ka
gansa kasan baragon namiji bane kuma
mijin nuna ma sa’a ne kasa kyafta
idonta tayi akansa shiko bai ma san
anayi ba wai kunu a wani gida, ko tan
tama babu shine Ammar din da mum
take sayan kaya a gunsa, woow amma
guy din ya hadu matsalar daya ne rashin
naira sai da taji wani mai saida fruit na
gefen ammar yana cewa hajiya kaya za
a baki kafin ta dawo tunaninta a
gadaran ce ta isa gun ammar tace aslm
ya kk tambaya nake wai wani shi
ammar fiska ba yabo ba fallasa yace eh
nine ammar din lfy cikin isa tana satan
kallonsa tace hajiya Maryam Alkali ne ta
aiko ni wacce take sayan kaya a gunka
yace ok ina jinki nan tace wai ka hada
mata kaya kamar yanda take saya nan
Ammar ya hada mata kaya masu kyau ta
bude jaka ta dauko kudi ta basa tsabagen
kallon da take masa ta yarda posd din ta
garin mayar wa jaka bata sani ba sai da
ta bar gurin zuciyarta cike da tunani
ammar har ta tada motarta ammar yaga
poss ya bita amma ina tayi nisa nan ya
budr sai yaga ID Card dinta da dunanta
Munayshat Alkali nan yaga complement
card dinta da address dinta da sauri ya
tsari mai mashin ya bi bayanta.
1 To masu karatu danso musan wacece
Munayshat? Kuma wacece Hajiya
Maryam Alkali?
2 Shin munayshat son Ammar takeyi zai
amsa kuwa to ya rayuwan auta zai
kasance
Kubiyo Yar gidan JARAWA don jin yanda
zata kaya taku a kulum mai kaunarku
Yar Mutanen Kardam.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:38PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ganin tayi nisa yasa ya bi bayanta da
gudu sukeyi da mai mashin amma ta
musu nisa sai da sukaje G R A adjacent
da government house naga naga sun
nufi wani katon kwalta ne a shimfede
kafin suka iso kofar wani hadadden gd
harda security a kofar ginan tun daga
kwanar shiga gidan zaka ga arubuta
Hajiya Maryam Alkali house, da manyan
zane, nan ya sallami mai mashin ya
basa N100 kudin mashi mai gadi suna
ganinsa suka tashi nam sukace wajen wa
yazo yace gurin wacce tashiga da mota
mai gadi yace ka bar gurin nan bazaka
shiga ba nan suka fara iskanci ma
ammar ransa har ya baci ya juya zai tafi
sai daya mai gadin yazo ya tambayesa
nan yace wacce ta wuce da mota yanzu
baka mai gadi yace ai gidan nan masu
tuka mota suna da yawa nan ya sake
duba sunan yace Munayshat ok lfy dai
ko yace lfy wa za a ce mata nan yace ace
Ammar mai kayan fruits nan security ya
shiga nan yayi karo da Aunty Mamu a
falo ga Kausar a gefenta nan yace Aunty
wani ne yazo gun munayshart wai
Ammar mai sayarda fruit nan hajiya
maryam ta fadada murmushinta ayya
ammar lfy daiko yace eh wai abu
yakawo ta nan aunty mamu tace kaje ka
shigo dashi, kausar mikewa tayi ta nufi
kitchen don dauko mult mai sanyi tasha,
Bayan ya koma ya shigo da ammar
gasky gdn ya tsaru a kwai naira a gdn
sosai don ya hadu iya haduwa da
sallama suka shiga cikin falon da yasha
blues da yellow da bakin labule ga
kujeru luntsuma luntsuma suma colours
din blue yasha gyara ga kamshin da yake
tashi ya duka ya gaida ta nan yace
shaidata mata yarta tazo sayan kaya
gashi ta yar da poss dinta nan tayi
godiya ta karba hauwa mai aiki ta kira
tace ta kawo masa abinci yace ya gode
hajiya ta bata rai ammar ae mun zama
daya ka dauken tamkar uwa a gunka
cikin jin dadi yayi godia hauwa ta kawo
masa zobo daman shi ma aboci zobo ne
ya sha kayan hadi nan ya dauka ya sha
gashi da sanyi nan ya wani lumshe ido
alamar jin dadi,
Kausar ta fito rike da malt a
hannunta tun da ta nufo falo ta hangi
wani hadadden saurayi ajin karshe ga
kyau sai da ta furta woow a zuciyarta
nan take taji ya tafi da ita amma jin kai
ta danne ta shigo da sallamarta dake ita
tana da hankali sosai ta gado halin
Aunty Mamu ne gefen mum dinta ta
zauna cikin isa tace masa sannu da zuwa
yauwa yace a takaice dai2 nan
munayshart ta shigo cikin wasu
matsatsun kaya riga da wando na
English wears tayi kyau sosai don suna
da kyau ba laifi sai dai matsalar rashin
gashi don sai da ta hada dana doki tun
da taga ammar tashiga wani yauki tana
karairaya wanda shi bai san tanayi ba
ma nan Mamu ta bata poss dinta nan
tace la ban lura ba ko da ta bude taga
kudinta ba a tabasu ba 80k ne a ciki don
harda zonen gwal dinta da yakai 60k
aciki kirar dubai sai daukar ido ya keyi
nan tace lah mum gsky na da AMANA
kiga ga kudi kusan 80k ga zobe na
nagode duk da nasan koda bata sukayi
banda wasu matsala amma gsky da
kanuna naji dadi nan ya mike da nufin
tafiya cikin sanyin murya yace hajiya
zan tafi tace angode kausar kam kasa
motsi tayi sabida zakin muryansa amma
dake ita tana da kamun kai ga jan aji
shiyasa take buyewa har ya kai kofa
Aunty Mamu tace Ammar in bazaka
damu ba ina son zan tambayeka cikin
ladabi yasoma takowa ya dawo in da ya
zauna ya sake zama kansa a kasa ammar
dan Allah ina son kafadan gsky waye kai
daga ina kake don daga alamar baka
dade da fara sayar da fruit ba don na
dade ina zuwa gun bana ganinka san
nan yanayinka baiyi kama da wahala ba
a kwai wani boyayen sirri atare da kai
cikin nutsuwa ya daga fuskansa nan
suka hada ido da munaysharr da ke
wurga masa shu’umin kallo Kausat ma
kallonsa ta keyi ajiyar zuciya yayi kafin
ya sake sukiyar da kansa cikin nutsuwa
ya fara magana.
Happy Jumma’at Mubarak 2 All My
Muslim Sisters n Brothers
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:39PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Cikin nutsuwa ya fara magana ni
Sunana Ammar Sa’ad Saraki iyayena
asalin yan mai duguri ne nan ya basu
lbr shi dana Auta ko da ya gama yana
dago kai yaga Hajiya Mamu harda
hawayenta Kausar ko kuka take mara
sauti don tana da tausayi lokaci daya taji
tana son auta ta tausaya mu bare
Ammar da shi ya ke mai rike AMANA
munayshart kam ko a jikinta ita dai
Ammar take so nan taji wani kishi auta
ma takeji sabida kulawar da yake nuna
mata, hajiya mamu ne ta katse musu
tunaninsu ta hanyan cewa Ammar lalle
kun ga jarabawar rayuwa Allah ya jikan
iyayenku san nan ina son in bazaka
damu ba zaka dawo gdn nan kana mana
aiki sai ina baka ko da 20k nasan a wata
sallaman da mai kaya yake maka bazai
wuce haka ba san nan zan rikeku tamkar
yayan dana haifa a cikina haka
kanwarka zamu bata kulawa godia yayi
sosai kafin tace yanzu ya tashi yaje ya
sallami mai kaya daga nan su hado
kayan su taho dashi ammar tsaban
murna kasa magana yayi sai hawayen
farin cikin gdy yayi sosai kafin ya mike
ya fita yana yam sharan kwalla Kausar
duk ya cikata da tausayi munayshart
kuma murna takeyi zata samu damar
wayar dashi daga nan sufara soyayya
haka ta mike ta nufi dakinta kausar ko
kitchen tanufa don taya hauwa mai aiki
girki don ita duk mulkin ta da jinkanta
bai hanata aikin gd sai dai bata son
raini gsky wan nan kena.
* * * * * * *
Ammar da murna sa ya koma cikin
kasuwa nan yayi bayani wa mai fruit ta
wani waje yana murna ta wani waje
yana bakin ciki don zuwan Ammar
bakara min alkairi ya samu ba ga
customers da ya samu ga kasuwa ta bun
kasa sai da ya dauki 5k ya basa kafin ya
hada masa kayan fruit nan sukayi
sallama ya nufi gd da farin cikinsa nan
ya shigo da sallama, auta na daki ta fito
ta amsa da murna ta amshi kayan da ke
hannu sa suka shiga daki kai in ka gansu
sai sun burge ka ka dauka Mata da miji
ne nan matar mai fruit ne ta fito da yar
kujeranta don taji mai yake wakana tayi
gulma nan taji shewar auta da sauri
tafara dogon wuya don taji meye amma
hakan bai yuwaba sai ta mike taje ta
tagar dakin tasa kunnen ta dai2 lokacin
tace barin hada kaya sai mu tafi ko mai
ta tuna sai tace tsaya nan tafito da sauri
abun da ta gani ne yasa ta turus don
matar mai fruit ta gani ta window ita
ala dole sai taji mai suke cewa sa’dat na
ganin auta ta ganta jikinta ya dau rawa
ta fara in ina dam….. Kwaro….na…ga…
Auta tayi murmushi tace dama sallama
zan miki don mun samu wani gun nan
zamu koma da zama cikin zare ido da
dafe kirji sa adat tace kenan kina nufin
gdn nan zaku bari kafin tabada amsa
sukaji sallama mai gdn ne da wata
matashiyar yarin ya wacce bazata wuce
21 yrs ba bakace kyakyawa ba laifi daga
ka ganta tasamu karatun boko da
gogewa kalon sama da kasa ta somayi
ma auta ko ba a fada mata ba tasan
wannane auta doguwar rigane ajikinta
baya da kauri sosai tayi rolling sai key
din motarta dake hannunta nan take
gaban auta ya buga,
Cikin isa take magana ina Ammar din
kice munayshart ne tazo tafiya dashi in
ji mum auta jiki ba kwari ta juya zuwa
dakin ta kira ammar da ke nike kaya
duk sunyi cirko2 a waje ya fito yana
ganin ta ya dan sake fuska bayabo ba
fallasa cikin in ina tace mum ne tace
inzo in taho daku murmushi yayi wanda
ya bayyana kyansa yace ba matsala mun
shirya nan auta da hijab dinta ki rataye
a kofa ta tsaya kamar gunki tana kallon
ikon Allah ammar hanin tayi kasake
yasa ya ajiye jakarsu yaje kofa ya dauko
hijab dinta ya sanya mata nan take
fiskan munayshat yaso ma canzawa don
tasan sai tayi da gsky akan auta nan
tukun yana samata ya riko hannuta daya
hannu ya dau jakarsu duka fito nan ya
ga motarta ta dazu ne nan ya bude baya
zasu shiga tace no ammar ka dawo gaba
ganin irin wan nan abunda munayshat
keyi yasa auta azuciyarta magana
wannan ko wacece haka tasan auta da
ammar ba mai rabasu sai Allah ko ina
tare muke ayya tasan ni YAR AMANA SA
CE kuwa amma barin fara gwada mata
nawa salon cikin shagwaba da bubbuga
kafa na zo gun ammar na riko hannun
ammar wanda har jikinsu yana gogan
juna nan ta kwantar da kai tasoma masa
magana cikin shagwaba Yaya na ni ni ni
ni ni ni.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:39PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Ya ni ni ni mu zauna a baya kar ka
barni ni daya wani gululun bakin ciki ne
ya tokari munay badan taso ba ta hada
fusaka tashi mazauni driver ta daura
belt ta fisgi motar da karfi sunyi tafiya
mai nisa kafin suka iso kofar wani katun
katafaren gd dake auta tasaba da naira
bata wani razana ba hakan suka kutsa
kai gd sai da sukayi packing sannan
suka fito munay a gaba tana wani karai
raya har suka shiga falo nan ba kowa
karararwa ta danna sai ga hajiya mamu
na saukowa daga matakalar benin gdn
cikin shiga ta alfarma fuskarta dauke da
fara’a tana ganin su tayi gun gun auta
tana fadin Zainab sannu da suwa hannu
ta tariko ta zaunar da ita kusa da ita
nan ta kira hauwa tazo ta kai auta dakin
da ke kusa da na munay bayan tayi
wanka kinzo kici abinci haka akayi
hauwa ta kaita daki ammar kuwa a
dakin dake wajen amma kofa biyu ne
daya zaja shiga ta falon gd san nan
akwai kofar da ke kallon harabar gd nan
aka masa masauki,
auta wanka tayi sosai ta wanke ko ina
na jikinta ga sabulu mai kamshi bayan
ta gama tazo ta shafa mai san nan tasa
dogon riganta da dan kara min hijab
tagama kenan hauwa tazo tace suje
dining taci abinci nan suka fita hajiya
mamu ne kadai a falon duk dari2 takeyi
don bata saba da suba amma haka
kurum take jin hajiya mamu a jikinta
don ta mata tarban mutunci wacce ta
dauko su ne kwai ke mata kalon
wulakanci kuma taga alaman zasu shafa
da ita sai dai auta ita sam bata iya
hayaniya ba haka ta rinka cin abinci
dari2 ana haka sai ga kausar tashigo da
sallamarta da alaman daga wani gu take
washh tace sannu mum na dawo hajiya
mami tace sannu da dawuwa mikewa
tayi ta haura sama sam bata lura da auta
tazo ba dakin mum dinsu ta nufa ta
ajiye mata aika kafin ta nufi dakinta
wanka tayi ta hau online tana duba
sakon da ka turo mata a whatsapp da
viber da fb nan ta yi ta reply.
auta bayan ta gama hauwa tazo ta
tattara kwananukan auta binta kitchen
tayi tare sukayi wanke2 bayan sun gama
ne suka dawo falo lokacin munay ta fito
cikin wash matsatsun kaya sai wani
kwarkwasa takeyi suna hada ido da auta
ta sakar mata harraa wanda saida auta
jikinta yayi sanyi nan ta sun kuyar da
kanta daki ta koma,
Munay tace hahaha yariya zaki gane
kurenki don sai kin gwammace kida da
karatu ammar ma yaci sa an ya min
shiyasa zan ragar nasa anma yanda yake
sonki ba zan lamunci ganin yana nuna
kulawa ga wata ba azuciyarta take
magana.
Ammar ko dakin da aka basa ba laifi
ya hadu sosai nan yasa tan kayansa
wanka tayi da man akoshe yake
kwanciya yayi yana tuna rayuwansa na
baya ga wani irin son auta da yake ji
ama yana tunanin hanyan da zai fada
mata in ya tuna yanda komai nata yake
sai yayi hamdala don tabbas yasan ba
zai iya bada auren auta ma wani ba har
sai in yaga yashi sonta da kaunart zai
iya hakura san nan kuma wanda zai
taya shi rikon AMANA TA haka yayi ta
tunani kala2 sai da aka kira magriba ya
mike ya nufi masallaci don gabatar da
sallah bai dawo ba sai da yayi isha’i nan
yasamu an kawo masa abinci zama yayi
yaci kafin yayi godiya ga Allah da ya
kawo musu sauyi a rayuwansu.
Hajiya mamu ne ta fito falon nan ta
tarar da kusar tana jiran su fito sai da
tasa hauwa ta kira wanda yanzu ake
kira da Zee nan ta fito kenan sai ga
munayshart sai wani cika takeyi tana
batsewa ita a dole yar gidan ganin auta
ta fito yasa tazo da sauri ta mangajeta
nan ta tafi luuuu…
®WISDOM HAUSA WRITER
Rash Kardam
[7:39PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Luuu ta tafi zata fadi cikin ikon Allah ta
rike karfe matakalan benin bata kai kasa
ba duk jikinta sai bari yakeyi amma ta
gode ma Allah da ya kareta yasa bata
fadi ba kasancewan ba wanda ya gansu
wani kalon warning munayshat ta mata
kafin ta wuce ta sauka ta karasa table
auta jikinta yayi sanyi sosai nan taji
wani sabon hawaye yana shirin zubo
mata kamar zata fasa sauka sai ta tuna
hajiya ce ta kirata in bataje ba ta kyauta
ba a hankali ta sauka ta hango su a
dinin cikin nutsuwa ta karasa sai da ta
gaida hajiya mamu sannan kausar da
fara a ta amsa munayshat kam wani
sako ta amsa mata ta gefen ido nan ta
sunkuyar da kai hajiya mamu tace yata
kisaki jikinki ki dauka kina gd ne ki
daukeni tamkar mum dinki ga aunty ku
kausar nan sai wan nan sis dinki
Munayashat muna hada ido ta sakar min
harara to na amsa ma hajiya na mata
godiya nan mukaci abinci bayan mun
gama munay ne tafara tashi ta nufi
dakinta kafin hajiya nan kausar tace ya
karin hakuri nace Alhamdulilah tace
bakomai mun zama daya ki dauke sis
dinki kai na daga mata nan tace da safe
zamu fita sai ki sai abun da baki dashi to
na amsa nace Aunty Kausar sai da safe
tace Allah ya kaimu a hankali na haura
sama gun dakina kamar munafuka ina
shiga na kwanta ina tuna irin tsanana
danake hango irin tsanar da munay take
min a idonta nan naji wasu sabin
hawaye suna zubo min kofar naji an
turo da sauri na daga kaina munay na
gani fuskanta ba ko alamar anuri nan
gabana ya fadi, kafarta daya ta daura
akan gadon daya kuma na kasa ya tsanta
ta nunani da shi kee duk randa naga kin
nuna shigewarki a cikin gd nan sai kin
raina kanki san nan ke zakina gyara
min dakina da wanki under wears dina
da nawa san nan kika kuskura kika fada
ma mum nasaki wayan nan aiki ko
Aunty Kausar sai kin raina kanki san
nan bana son kina shige ma Ammar don
ba tsaranki ba( jama’a kutayani jin
karfin hali anan harda kashe kamar ba
tare ta gansu da Ammar ba)
Kuma bana son in ina falo kina yawan
zuwa kinji ko idan kika kuskura kika
tsallake doka daya to zaki gamu dani
sannan kika fada ma Ammar wlh wlh
wlh kinji sau uku na rantse sai na kulla
miki sharrin da bazaki iya warware ba
sai kowa ya tsane ki kuna jina ko cikin
rawar murya mai shirin kuka na daga
kai wani harara ta sake min da baki na
miki magana ko da kai nan nace da baki
tace to da baki zaki amsa min nan nace
mata to ta rike kunne na in kunne yaji
jiki ya tsira kai na girgiza mata kafin ta
sakar min wani rankwashi wanda har
kwakwalwan kaina sai da naji shi.
Ammar ko ya na kwance sai juyi yakeyi
duk ya damu da kewar auta wanda in da
sabo to ya kamata ace ya saba don baya
ganin wata mace sai ita hakan yayita
sakawa da kwancewa ganin ba zai
fiddashi ba yasa ya dauro alwala ya
soma nafila daga nan yasoma rairo
karatun al-qur’ani mai girma da
muryansa mai dadin sauraro dake yana
da hadda akansa abun sai wanda yaji(ya
Allah ka azurta mu da ilimi mai albarka
da amfani amin) sai da yayi adu’o’i mai
yawa kafin ya shafa sannan ya kwanta
yana mai tunanin abunda ya aikata a
ranan na alkairi da istigifari har bacci
ya daukesa
Zee auta ko duk da AC dake dakin bai
hanata zufa ba sai gumi ke keto mata
tana kuka marar sauti wayyo Allah na
yau nayi rashin iyayena yau gani cikin
kunci kun tafi kun barni ina ma da
zanbiki yau na fada rayuwan da bansan
wata irin kunci zanulyi ba dad dina ka
tafi kabarni wayyo Allah na ka kawo
min agaji.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:44PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Washe gari Kausar ta dauko wasu
katanta masu kyau ta ba ma auta san
nan tace tayi wanka zasu shiga kasuwa
hajiya ta bada kudi ayi mata sayya
godiya tayi sosai daki tashiga tayi wanka
wani dogon riga tasaka dark blue da
gyalansa tayi rolling bakaramin kyau
tayi ba nan ta fito dai2 lokacin munay
tashigo hajiya da kausar suna ganinta
suka fara tafawa kausar tace Zee kinyi
kyau baka danba hajiya mamu tace
Masha’allah gsky kinyi kyau yata wani
bakin ciki ne ya daki zuciyar munay don
ta tsani ace ga wanda ya fita kyau ita
gani take tafi kowa kyau nan ta gode
musu ta karaso suka shiga motar kausar
suka nufi kasuwa sunyi sayya sosai kafin
suka dawo gd suna shi gowa ta hango
ammar a gate suna zaune da mai gadi
nan tayi gunsa da fara a suka gaisa
kausar ta karaso suka gaisa, ammar yaji
dadi ganin auta cikin farin ciki sosai nan
yayi godia ma kausar sosai don yaga
tana da nutsuwa ba kamar Munay da
rawan kai ya mata yawa ba nuna isa
haka suka nufi gd bayan sun huta auta
ta nufi kitchen ta taya hauwa aiki bayan
sun gama ta je dakin Munay ta gyara san
nan suka ci abinci rana.
* * * * * *
Hajiya Mamu ta bama ammar driver gd
tana so sai taga yanayisa kafin ta daura
sa akan dukiyarsa kafin Ahyan ya dawo
daga turai tun da yakusa zuwa ganin gd
kafin ya koma duk yanda sukayi to.
Haka rayuwa tayi ta tafiya auta na cikin
kunci amma ta boye sai dai tayi fari
sosai ga hutu amma fa ta rame sabida
damuwa haka take bautawa munay ko
tausayinta bata ji baran itaga ba mum da
kausar a gd tana mata ba dadi kam.
Haka rayuwa yayita tafiya yau sun dauki
shekara 2 a gidan yanzu hajiya tasa
ammar akan karamin shagon kayan ta
wanda yake cikin garin bauchi mall ne
babba duk abun da mutum kenema zai
samu hakan yasa ammar baya zaman gd
sai shago yanzu hajiya tana jiran Ahyan
in yazo zasu yi magan daga na Ammar
sai ya fara harkokin kasar wajen kawai
tunda taga yana da AMANA.
* * * * *
Yau gd an tashi da shiri don gobe bros
dinsu Ahyan zai dawo daga turai kausar
ne taja auta sukaje kasu nan suka suyo
kayan vegetables nan kausar ta umurci
auta da gobe zasu shiga kitchen tunda
taga auta gwanar girki ce kuma ta iya
sosai Munay wani haushin auta take ji
don bataso ta kusanci Ahyan don tasan
zai yi wuya yaga auta bai kyasa ba tunda
tana da kyau dai2 gwargwado.
Washe gari duk inda kaleka agidan
kamshi yakeyi Kausar da auta ne a
kitchen sai sarrafa girki sukeyi abun sai
wanda ya jiyo don ina daga nan yawuna
har ya tsinke bayan sun gama suka jera
komai a inda ya dace nan kausar tace
auta ta shirya da ita za aje dauko Ahyan
wanka tayi sosai kafi tayi kwalliya
Munay ko tace duk yanda zatayi sai ta
hanata zuwa don bazasu tafi da wan
nan mai kodaden fuskan ba, sai da
munay ta shirya kafin tazo dakinta ta
shigo ko sallma babu ta kali Zee Auta
tabbas kam tayi kyau amma sai tace ko
tsari bakiyi ba ina zakije da kodaden
fuskan ta ki mai kama da na biri wlh na
kuskura na ga kin saka kafa kin bimu
sai
Kinyi na dama da mata harara sama da
kasa tace sannan kuma kisani daga yau
bake ba kwaliya bake ba zaman falo
kinji ko auta da idonta ya kawo hawaye
ta daga kai da alamar eh kafin munay ta
gita a dakin falo ta fito tasamu kausar ta
fito nan tace ina Zee take Munay tace ai
bazata ba ko mai yasa oho kema kya
gayyaci wannan kofadiyar kausar kalon
tambaya ta mata duk da haka bata
daddara ta haura sama tasamu auta ta
kifa kanta tana kuka kausar da sauri ta
hau kan gado lfy zee auta tace kaina ke
ciwo bazan samu zuwa ba ba yanda
kausar ta iya dole ta hakura ta sauko ta
ja mata kofar suka nufi AVUBAKAR
TAFAWA/BALEWA AIRPORT BAUCHI,
kausar ke jan motar suka nufi airport
suna isa suka samu jirgin tasauka har
fasinja sun soma saukowa tun da suka
iso na zuba ma kofar sauka inga masu
fita tun daga nesa na hango wani guy
shidai ba fari bane amma ba laifi ya
hadu sosai yana da tsayi da fadin kirji
fuskansa dauke da murmushi hannu sa
rike da wata jaka yana sanye da jar riga
da yar bakar falmara yana sanye da
bakar wando jeans da takalminsa baka
da ratsin ja abun sai wanda ya ganin
tun daga nesa na hango kausar fara ary
ya karu da sauri ta mike tanufi wan nan
guy din mai kice da kyau don kalo daya
zaka masa kaga hutu da wayewa sun
masa yawa ga boko kunnesa makale da
yar manne kana gani kasan yana taba
rayuwa sosai amma fa ya hadu ba laifi.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:49PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Kunnensa makale da dan kunne manne
kana ganinsa kasan yana taba rayuwa
yahadu ba laifi sai dai bai kama kafar
Ammar ba don ammar na daban ne shi,
kausar na hango ta nufi guy din nan
tana fara’a tana isa kusa dashi dukayi
shaking din hannu tace ur wlc bros
fuskansa dau ke da murmushi yace tanks
my lovely sis munay ce ta iso da
mirmushinta amma sai wani kwar
kwasa take kai ka dauka gun sau rayinta
zata tana ziwa tace ur wlc tanks yace
mata Kausar ta karbi yar jakar
hannunsa kafin suka rankafa zuwa inda
motarsu take suka nufo gida cike da
murna.
Zee auta tun bayan fitarsu ta ci kuka har
tagode ma Allah ita yanda rayuwa ke
zuwa mata kenan tana fita a wannan
zata shiga wancan amma zata daure ko
kadan barata bari ammar ya sani ba don
ta ga yana cikin kwanciyan hankali.
Matsawan ya sani dole ne subar gidan ko
ya dau mata ki ni kuma bazan zamo
silan rugujewan farin cikinsa ba tunda
baya son ganina cikin damuwa hmmm a
hankali na sau ke wani ajiyar zuciya
tare da cewa ya Allah gani gareka ka
fiddani a cikin wan nan hali,
Alhamdulilah ala kuli hallin.
Saukowa nayi daga kan gado na nufi
dakin munay duk ta birkita kaya haka
na tattara na shiha toilet shima duk ta
bata sai da na gyara mata kafin na tafi
na Aunty kausar na ita ma na gyara
mata duk da yana gyare bayan na gama
ne na fito na nufi cikin na debi abinci
na ci na yi wanka na kwanta don
banson in ketare dokar Munay banson
abunda zaisa ta wula kanta ni bayan
nayi wanka Al-qur’ani na dauka nasoma
karatu
 har zuciyata, tayi min sanyi nan na
kwanta kan sallaya bacci ya dauke ni
ban farka ba sai karfe 2:30pm wanka
nayi ina son in fito falo ina tsoron karo
da su manay ga warning din da tamin
kar in sake inyi make up kuma kar na
hadu da Yayan su Ahyan ko mai yasa
oho ni ina ruwa na ma da shi gashi tasa
nayi nisa da Ammar dina dole wanda
kullum muna tare da shi ga kulawar da
yake b an na musamman nan take naji
wasu kwallan ta kaici yana zubo min na
goge hawayena na jingina da gado na
fara yan adu’ah dana saba ina mai
adu’ah ma iyayena da sauran musulmai.
Sannu a hankali suke tafiya yana kallon
yanayin garin kunnensa dauke da ear
peace yana bin wakokin Arjuli siyn
shararen mawakin da ke raira wakokin
India Ahyan yana son wakan sa sosai
don shi ya raira wakar Ashque ma, a
haka har suka iso G R A, a hankali
Kausar ke tukin har suka zo kofar gate
din su horn tayi cikin nutsuwa kafin
mai gadi ya bude musu kofar gate din
taje tasamu parking tayi parking da
murna ya fito yana kiran Mum yayi
cikin gd hajiya mamu ta fito da
murnanta ta tari danta nan ta kawo
masa ruwa mai sanyi sai kaga bakin
hajiya mamu har kuni danta namiji tilo
ya dawo yau kam murna ba a magana
sai da ya huta kafin suka nuna masa
dining kausar da munay suna gefensa
Mum dinsu da kanta tayi serving dina
sosai ya ke cin abincin yana santi bayan
ya gama ya nufi dakinsa ko ina a gyare
sai kamshi ya keyi wanka ya shiga
bayan ya fito ya yi sallah sannan ya sake
fitowa falo hira suka dan taba kafin H
Mamu tace yaje ya huta nan ya tafi
dakinsa kausar itama dakinta ta nufa.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Kausar tana shiga dakinta ta ganshi a
gyare ko ina murmushi tayi Allah sarki
baiwar Allah gsky auta tana da halin
kwarai ko jikinta barin dubota yanzu
haka halan ko abinci bata ciba dakin
auta ta leka ta ganta jingine da gado ta
lumshe idonta da alamar kamar bacci
take amma ba baccin take ba fridge taje
ta dauko mata kunun aya ta nufi kitchen
ta dauko mata abinci da plate ta dawo
dakin a hankali ta ke tada ta Zee ta bude
idonta taga Kausar ce murmushi tayi
tace Aunty Kausar kun dawo lfy ya
hanya kausar tace wato ko ki fito ku
gaisa da bros ko auta tace zanje in gaida
shi
Kausar tace to tashi kici abinci na san
yanzu haka ba abinda kika ci ba musu
auta ta mike taci abinci sukayita hira
harsai la’asar kausar ta nufi dakinta don
ganatar da sallah la’asar auta ma sallah
tayi bayan sun idar ne suka shiga
kitchen sukayi abincin dare bayan sun
fito ne auta ta koma daki don yanzu ta
hana kanta zaman falo bata son
hayaniya sam.
Ammar business ya zauna ga shago sai
kara habaka yakeyi abun sai son barka
burinshi kulum autarsa ya ganta cikin
farin ciki san nan komai ya samu ita
yake sayama wa haka account dinsa ma
da sunanta ya bude duk kudin da ake
basa nasa yana sawa a gun kamar kulum
da ya saba zuwa sari kano yaje yayi sari
nan ya ga wasu dogayen riguna masu
kyau haka ya saya musu su uku Zee Auta
maroon da ratsin golden colour na
kausar baki na munay ash da ratsin baki
sosai yayi sayya yana ta sauri ya dawo
don ya gana da dan hajiya mamu wato
Ahyan don shima ya nuna nasa farin
cikin dawowarsa.
* * * * *
Kaduna kuwa haka rayuwan futha da
sadiya ya kasance yanzu futha ta gama
diploma har tasamu Admission a degree
tana gamawa zata tafi school of law haka
tacigaba da gu danar da yan bincikenta
don ta dau ma kanta alkawari sai ta
gano wanda ya kashe ma auta iyayenta.
Sadiya ma haka abun yake karatunta
take cikin kwanciyan hankali amma sai
dai kulum tunaninta autar ta awani haki
take ga iyayenta ku su nuna damuwarsu
a kan magana gashi dukiyar sai habaka
take abinda ya daure mata kai yanda
taga wasu mutane tu da alamar ko bacun
ransu baba isiya da Abbanta basa son
gani gashi kuma mai gadin gidansu Auta
da sun dawo sun dinke da iyayenta
kuma wani abun daure kai yanda pinky
kewasa da naira ba mai kulata sai kara
daure mata gindi akeyi in yau ka ganta
awan nan motar gobe da wancan
kawaye kuwa sai yayan manya take
harka da su abun sai hmmm don yanzu
ji take da kanta tana kallon Big Girl ce
ita ga naira ga hutu.
Ammar ya dawo yayi murna da ganin
Ahyan sosai ya kawo tsara ba masu auta
da kausar san nan yanzu an yanke
shawarar zai fara fita waje nan yayi
murna da godia san nan ya ce ma auta
ya kamata suje kauye su gaida su Inna
larai da Malam don su musu karamci da
bazasu taba mantawa ba, hajiya mamu
ya samu ya mata bayani tayi murna san
nan ta basu goma na arziki sukai musu
nan kausar tace zata bisu tunda gobe
zasu dawo munay sai wani yatsina take
ita ala dole tana kyamar yan kauye,
Tunda Ahyan ya dawi ko da wasa basu
taba haduwa da auta ba yau kwanansa 4
ya ba masu kausar hakuri akan kayansa
ran Thursday sai iso sukace ba matsala,
Ammar wanka yayi sosai haka ma auta
sunyi kyau kausar ta dau Camera don
tana son zuwa kauye ran asabar da safe
suka dauko hanyan suwa kauyensu
Malam suna masu farin ciki.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:49PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
[10:47AM, 4/5/2016] Rash Kardam :
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Sai karfe 12:00 suka isa garin sun samu
su inna cikin lfy bakaramin murna
sukayi da ganinsu ba nan ina ta musu
tuwon geronta mai kaushi miyar danyen
kubiya ga man shanu sosai su kaci suna
zuba santi baran Kausar ma tafi kowa
santi don ta dade bata ci irin wan nan
abicinba ga surki yaji suga sosai koni
rash sai da na lashe baki don yawuna
yana tsilo tsabar kamshi ya ishen.
Sai da suka huta bayan sunyi sallah
asazahar tukun ammar ya basu
tsarabansu nan sukayita murna kafin
suka fara hiran yaushe gamo nan
ammar ke bama su inna lbr bayan barin
su garin sun tausaya musu sosai sai
yamma sukayi wanka suka fita zaga gari
dandali suka nufa tun daga nesa suka
hango yam matan garin sunyi wanka
masu sayar da abinci na sayarwa abun
dai sai kun gani.
Najaat ce da tawagar kawayenta tunda
ga nesa ta hango ammar da su auta
zunguro ummen da zulai kaii kalli
wancan kamar wanda suka taba zuwa
maciya da malam la shine dan birni kai
kali wancan auta ta nuna sina kama da
wan nan yar India mai gashinan ga
kawarta ma kamar yar india nan suka
saki baki sai kallinsu suleyi haka su auta
da kausar da ammar sukayita hotuna sai
magriba sukamar dandali suka dawo gd
bayan sunyi sallah ne suna zaune suna
hira sukaji surutun mutane da yawa
kuma mata sai azo a dan lekasu a koma
can dai abun yayi yawa sai malam ya
mike ya a hankali ya fake aiko lokacun
su najaat suka leko karaf malam ya rike
ta waye nan tafara inda2 daman tazo
gaida ina ne sai taga yan birni malam da
ya gane waye sai ya kyaleta yace su bar
labe ba kyau nan suka shiga cike da
murna suka gaida su inna sai satan
kallon ammar sai da suka dade sosai
kafin suka musu sallama suka nufi gd su
malam ma sukayi sallama wa su auta
suka shiga dayan dakin inna da kausar
da Zee suka kwana daki daya da safe
inna ta soya musu kosai da yar tsame ta
musu kunun tsamiya haka suka karya
cikin farin ciki daga nan suka fara
shirin dawuwa bauchi,
Su inna sun cika mu da tsaraban kauye
su daddawa ne wake gyada kuka harda
zuma,
Wanka sukayi sannan ammar ya ciri
10k ya bama malam inna ko 5k godia
sukayi sosai kafin suka rakosu gun
motarsu suka dau hanyan bauchi.
Tun bayan da su kausar suka tafi kauye
da yamma ahyan tazo cin abinci ya ga
ga abinci har abinci a ido yana sawa a
baki yaji ba test karshe haka ya hakura
tea ya hada ya sha mum ma da tana
sawa a baki ta ajiye gashi hauwa bata
nan ta shiga cikin gari yau munay ce
tayi abinci sai da ta sha tea kafin ta kira
munay tayi mata fada akan ta dage ta
koyi girki din girki shine mace kiga
kausar da Zee mana yanzu ina ne zasuje
baza suyi abinci wa mitum yaci har
yana santi Munay sai zun bura baki
takeyi ita a dole an mata fada ta tashi ta
nufi daki sai kunkuni takeyi haka dai a
daddafe suka kai washe gari Mum ke
musu abunci ahyan ma ya masu kausar
ta dawo don yafi gane cin abincinta sai
ko in mum ce ta musu yana ci sosai.
Ba mu iso cikin gari ba sai kusan 1:40
dake ba mu fito da wuri ba ko da muka
dawo wanka mukayi muka ci abinci
kafin mukasa aka shigo da tsaraba muka
nuna wa mum yau hauwa’u mai girki ta
dawo dan haka daki na nufa na fara
baccin gajiya.
Yau kwanan mu 3 da dawuwa daga
kauye kulum gidan mu cike yake da
wakar india daga gani nansan yayan su
kausar ke sawa kuma shima da alama
masoyin wakokin india ne kulum in ina
daki yasa wataran nayi rawa wataran in
zauna ina bin wakar baran wakikin
Arjuly Siyn ina son wakarsa yau tun da
safe munay tazo ta min warning in
gyara mata daki san nan in kade mata
cikin Waldrop dinta zata fita sai yamma
zata dawo tun da ta fita nasa ka wando
wizy da yar rigata mai dan tsayi ya
kama jikina nan nashiga na gyara ma
munay daki na fito zan sauka kasa
dauko dauko fresh milk insha don nayi
aiki sosai ina fitowa naji daga wani
dakin da ke kusa da down stairs naji
ansaka wakar Vear wai take Surili
akhiyon wale, daman mayar wakan ce
ko ada nan na fara tika rawa irin na
wakar don mutum2 ake wakar amma ni
daya nakeyi sai nan take na tsinci kaina
cikin ni shadi ina bin wakar ina
rausayawa.
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
A hankali ya ke saukowa sanye da
3quater da yar riga mai gajeren hannu,
ya jimma a tsaye yana kallonta wannan
wacece da bai taba ganinta ba ko ita ce
Zee din da mum ke fada gsky yarinyan
ta hadu ba laifi wani juyinda tayi a
rawan sai da yasa Ahyan hadiye yawu
don wannan tana daya daga cikin irun
matan da ya ke so ta hada koma2 gyara
tsayuwa yayi yana kallinta don baison ta
bar rawan,
Sam ita bata san da mutum ba
tsakaninta da Allah take tika rawa,
Dai2 nan Ammar ya shiga kallon ta
yakeyi cike da so da kauna dake yasan
ita mayyar wakokin india ne ganin auta
cikin farin ciki yasa shima ya tsinci
kansa cikin farin ciki sai a lokacin ya
lura da ahyan da yayi tsaye yana
kallonta nan take ransa ya baci kishin sa
ya motsa bai san lokacin da yaje ya mata
wata damka ba kee baki da han kaline
bakisan akwai wanda bai kamata su
kalleki haka ba tsaya wa nayi ina masa
kallon tuhuma sai a lokacin naga ahyan
ya karasa saukowa sai min wani kalo
yake wanda ni kaina sai da na tsargu,
Munay ce ta shigo ko sallama babu
ganin irin hallin da muke ciki yasa ta
nufo ni da sauri kee baki da han kali ne
zaki fito cikin irin wan nan shigan duk
ta rude kai ka rantse a kwai mijinta a
ciki na fito da wan nan shigan nan take
jikina ya hau rawa da gudu na haura
sama ammar kam dakinsa ya koma
ransa duk a jagule ahyan kuma bayana
yabi da kallo yaga duk yanda illahirin
jikina yake motsawa tabbas dole yasan
abinyi akan wan nan yarinyan.
Wacece Hajiya Mamu?,..
Asalin sunanta Maryam Alkali
haifafiyar garin katsina ce aure ne ya
kawota bauchi,
Hajiya mamu ta taso cikin kulawa da
tattalin iyayenta Alhaji Alkali mutum ne
mai karamci da sanin ya kamata yana
da mata daya mai sunan Xahra mace ne
mai mutumci da kamala shekaransu 2 da
aure basu sami haihuwa ba sai da suka
shiga shekara na 3 Allah ya basu
haihuwar diyarsu ta farko maryam inda
suke kiranta da Mamu sai bayanda suka
sanu shekara 4 Allah ya sake basu
haihuwar fatima haka suka taso cikin
kulawa da kaunar juna inda mamu tayi
aure ta auri wani shararen dan kasuwa
bayan tayi aure da wata 3 Allah ya bata
cikin ahyan haka sukayita tattalin cikin
har tazo ta haifeshi yaci sunan Ahyan
ma’ana Gift of Allah
Bayan shekara 2 akayi bikin fatima
itama bayan aurenta da sheka 4 ne ta
haifi Kausar kenan kausar yar kanwan
hajiya mamu ne tunda fatima ta haifi
kausar ta kamu da lalurin rashin lfy
bata dade tana jinya ba Allah ya karbi
abunsa nan H Mamu ta karbi kausar ta
dawi hannunta sai da kausar ta kusa 4
years hajiya mamu ta haifi munay haka
taci gaba da kula da yaranta tana basu
tarbiya mai kyau mijinta yana
kasuwancinsa ka Allah ya sanya musu
Albarka dukiya sai haba ka yakeyi
kwanaki sunja lokaci ya tafi har ahyan
yagama secondary nan Abbansa ya fara
shirye2 na fitansa karatu waje yayi
hatsari ya rasu tabbas sunji mutuwar
nan ba kadan ba bayan yanyi arba in ne
hajiya mamu tayi ciki ciku yatafi karatu
kasar waje nan ita kuma tani mi aiki
tana zuwa sam taki aure don tana kula
da yaranta Kausar dake tana kama da
mamarta in ka ganta baakace ba hajiya
mamu bane ta haifeta ba don suna kama
munay da dad dinsu tayi kama sam ita
halinta ya fita daban bata son kowa a
kusa da ita ga jinkai ga nuna isa kamar
yar President.. Lol…
Yawancin kawayenta yaran manya ne
bata harka da yaran masu kananan karfi
acewarta za a raina ta don kalin kanta
take kamar yar gidan dan gwate ….lol…
®WISDOM HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:54PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Hakan yasa munay bata son talaka
komai nata da yayan masu kudi take
harka ,
Tunda ahyan ya tafi sai sai suyita waya
da yan gida acan turai kuwa ya samu
abokai yan duniya bushashan su kawai
sukeyi duk da bai yi wasa da karatu ba
amma baka rasa shi gidan faty rawa duk
ya iya zuwa amma sam bai shan giya
hasali ya tsaneta sosai da sosai haka
rayuwansa ya kasance har zuwa yanzu
da ya rage masa 1 year ya hada masters
dinsa shiyasa komai nasa ya ban2ta da
sauran ga wata yar dan kunne manne
da ya makala a kunnensa,
wan shine lbr H mamu.
Jiki ba kwari na haura dakina tabbas
yau na san munay sai ta min ba dadi ga
ammar ransa ya baci anya na kyauta
masa kuwa duk yanda yake kokarin
kyautata min ace yau ni na bata masa
rai gsky banyi adalci ba bau kyauta ba
take naji wasu zafafan hawaye suna
gan2min kwanciya nayi nasoma kuka
maras sauti, kamar daga sama naji an
zuba min dundu har kirjina sai danaji
ya amsa munay na gani da bulala ido na
zaro nan na sauko na hada hannuna
biyu na fara bata hakuri.
kee yar iska mai kodadden fuska waya
baki daman saka wayan nan kayan bare
kiyi make up har ki sauko falo nan take
muryana tasoma rawa dan Allah kiyi
hakuri munay ta dago dorina kamar
zata zuba min na runtse ido sai hawaye
amma sai naji shiru a hankali na bude
idona sai naga tana harara na tace daga
yau ina kara ganinki a tsakar gida sai
kin gayama yan garinku, kinci sa’an yau
yan mutuncina suna kusa da kinji
ajikinki ban tankaba tace kuma ki
shirya kabar punishment na musamman.
Fuuuu ta fita nan na saki wani ajiyar hrt
nayi hamdala da bata bugeni ba.
Ahyan kuwa yana haurowa sama yana ta
bin dakunan da kallo don ya ga wanne
ne wan nan yarinya ta ke ciki har ya iso
dakinsa nan ya zauna a yar kujeran da
ke dakin ceke da tunani.
®WISDOM
HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:54PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Gsky wannan ta hadu komai nata
das2dashi nan ya kasa shan malt din da
ya dauko ya kwanta ko da ya rufe ido
Zee yake gani shi kadai sai wani smile
ya keyi wan nan tasa ce dole ya bi duk
yanda zaiyi ya mallaketa.
Ammar ko da kyar ya isa daki kirjinsa
ya masa nauyi yashiga tsananin damuwa
don karara ya hango tsananin sha’awa
auta a idon Ahyan kuma gashi da alamar
bayida kamun kai nan ya dau ruwa ya
sha ko zaiji sanyi a zuciyarsa amma ina
nan yakama zarya a daki yana tunanin
abunyi shin ko zai tun kari auta ya fada
mata yana son ta ne wata zuciya tace
kar tace bata sona ya zanyi gashi ina
tsananin kaunarta auta tamkar wata
bari na zuciyata ce matsawan ba ita ba
zan rayu dai2ba nan ya tuna komai yayi
zafi a kwai Allah take ya soma karanto
adu’ah kafin yaji sanyi a ransa.
H mamu ko sai yamma ta dawo gd
bayan ta huta ne ta leka dakin kausar
tasamu tana bacci ta wuce dakin munay
bata nan daga window ta hangota a
garden, nan ta fito ta nufi na Zee auta
tana kwance da sallama ta shiga jin
muryan H mamu yasa ta mike tana mata
sannu da dawuwa bayan sun gaisa tace
yana ganki haka auta ta kalo murmushi
tace bana jin dadi ne tace ayya sannu
kinsha magani kuwa tace eh tace to
Allah ya sauwake, ameen tace daman ina
son in fada maki gobe zani Sokoto akwai
abunda zanyi tace to Allah ya kare
ameen tace kafin ta mike ta nufi dakin
Ahyan kwance ya ke akan katuwar
katifar sa idonsa na kallo sai da ta taba
sa tukun ya mike tace mai kake tunani
haka kai ya sosa yace mum ba komai
tace fadamin dai tace ba kimai tace ok
daman so nake ka shirya gobe zamuje
sokoto da safe samu fita ido ya zaro nan
ya tuna da auta ga dama ta zoma sai
yayi saurin cewa mum gobe ina da
abokina zai zo daga abuja kinga in na
tafi ban kyauta ba tace ok zan tafi ni
kadai in yaso kafin ka koma sai kaje ka
gaidasu ya ce to,
tana fita ta tarar da kausar ta tashi ta
fito falo ga hauwa da munay nan nan ta
zauna sukayi hira nan take fada musu
tafiyanta kausar tace zan biki mum
munay tace nikam inaga sai bros zai tafi
sai mitafi tare mamu tace Allah ya
kaimu suka amsa da ameen tace ma
kausar sai ki shirya yanzu don mass
zamu bi ba flight ba tace to da sauri tayi
dakinta ta shirya su munay da mum
suka shiga hirarsu.
Washegari da sa ahyan da kansa ya
kaisu tashan mass suka shiga mota sai da
suka tashi kafin ya dawo gida, ya yi
wanka ya fita yau yana cikin farin ciki
yasan yau zai san yanda zaiyi samu ya
biya bukatarsa don tunda yazo 9ja bai
samu ya biya bukata ba gudun kar Mum
dinsa ta ganesa.
Auto ko sai kusan 10:am ta fito zata
gyara ma kausar daki don ta bata
sallahun ta gyara mata ta wargaza gashi
suna sauri tazo tasa shiga dakin dai2
munay ta hada tea zata sauka fafo
sukayi karo nan take tea ya zube ajikin
munay cikin bacin rai ta wanke auta da
kyakyawan mari har sai da ta rike
kuncinta sai da taji radadin ya ragu ta
daga hannu zata rama komai ta tuna sai
ta fasa auta ido ta zaro lalle yau da kin
gane kurenki wlh eyeh lalle kin samu
kanki a bakaken larabawa…lol.. Amma
zanyi maganinki fuuu ta koma daki don
dauraye jikinta auta na kuka ta gyara
gurin da tea ya zuba sannan ta shiga
dakin kausar ta gyara ta fesa room
freshener ta ja kofar ta koma dakinta
taci kuka ta gode ma Allah bata sake
fitowa ba sai rana lokacin hauwa ta
gama abinci ta debo ta koma dakinta,
Bayan sallan la’asar munay tayi shirinta
ta fito don zuwa gidansu kawarta fiddy
ta zo don ta sa auta ta gyara mata daki
ta taba taji ta kulle ta kwansa auta
najinta taki budewa dole yasa ta fita sai
da tayi nisa kafin auta ta bude taga
alamar bata nan ta koma ta kwanta ko
kofar bata rufe ba.
Ahyan yazo shigiwa anguwan yaga
motar munay tafita cikin murna da
zumudi yayi azamar zuwa gd don yaje
ya samu biyan bukatarsa gun auta ya
dan danata don yasan zai huta yanda
take ja gata da yalwar kirji komai nata
dabane wani murmushin mugunta yayi
yanufi gidan horn biyu yayi mai gadi ya
bude masa ya nufi parking space ya a
jiye motar da sauri ya nufi cikin gidan
har yana tuntube.
Nima Rash ina ganin haka na bisa da
sauri don in ga mai zai aikata nan take
faba yasoma dukan tara2 bakina yana
raa ina furta bai ra……..pp….. Din…Zee…
Aut…..zai…
Sai kun jini da daddare.
®WISDOM
HAUSA WRITERS
Rash Kardam
[7:54PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Da sauri ya shiga gidan, yayi hanyar
stairs a hankali ya ke tafiyar, sai da ya
taba kofar dakinta yaji a bude, kafin ya
nufi nasa ruwa ya watsa, ya sanya
kanan kaya maras nauyi, ya nufi fita
daga dakinsa kenan, wayar sa tayi kuka,
badan ya soba ya juyo ya dauki wayar,
sunan Jenifa ya gani a scream din
wayar, da sauri ya daga daga daya
bangaren akace hello my luv, ya kk? Ya
9ja? yau she zaka dawo ne?nayi missing
dinka da yawa, nan ta fara masa salonta
na janye hankali, “take ya manta da
abunda yayi niyya” suka shiga hirarsu ta
masoya, bai ankara ba, sai jin ana kiran
sallah mangariba, sai lokacin ya tuna
kudirinsa, da sairi ya ce mike yana fadin
oh!!! Shirt, ya tsa ya ciza, kafin ya kashe
wayar, ko sallama baiyi ma jenifa ba,
Yana fitowa daga dakinsa ya ga munay
tana haurowa, sam baiso ta dawo, batare
da ya cimma burinsa ba, sannu da gida
ta masa, ta wuce dakinta, haka ya
hakura yakoma daki, yana jin haushi
kansa da ya biye ma jinifa, (ni kuma
Rash nace bawan Allah ko ka manta duk
wanda ya rike Adu’ah Allah, ba zai kyale
mun gu ya cuce saba, sai bisa jarabta ko
kaddara).
Ammar ko duk hankalinsa bai kwanta
masa, da ahyan sam, ana sallah magriba
ya dawo gida, sai da yazo ya samu auta
tana sallah, bayan ta idar ya tabayi lfy
ta, ya ajiye mata abunda ya sayo, kafin
ya koma dakinsa, auta da wuri ta rufe
kofar ta, sanin halin munay, kartazo ta
cimata mutunci, aiko munay tana zuwa
ta kwan2sa kofar dakin taji akule ba
haka taso ba.
ba yanda ta iya taje ta kwanta.
gari na wayewa, bayan auta tayi sallah,
ta yi karatunta sannan ta mike taje ta
hada tea ta dawo tana breakfast, sai ga
munay tazo, fuskan nan ko alamar
murmushi babu, nan take gaban auta ya
fadi, kanta ta sunkuyar kasa, tana zuwa,
ta zauna a yar kujeran da ke daki, ta
daura daya kan daya, tana kada kafa.
Kee waya baki damar da har zakina
kulle daki?, ko kin manta da doka na
ne?, auta ta kada kai alamar àa, to maza
ki bar cin abincin nan, kije ki hadan
breakfast, cikin sanyi jiki, tace mai zan
hada miki?, wani mugun kallon da
tamata yasa ta yi shiru, idonta duk ya
kawo kwalla, munay na fita ta nufi
kitchen, haka soya mata Chief da
indomee sai tea da yaji kayan kamshi, ta
kawo mata daki, ta ajiye zata fita munay
tace inagama ki dawo kizo kittara
kwanukan kai ta kada mata, ta fita da
sauri, sabida kukan da ke shirin zuwa
mata.
“Allah sarki rayuwa nikuma haka Allah
ya tsara min, Ya Allah ka bani ikon
hakuri”, kuka tayi sosai kafin ta share
hawayenta, ta nufi dakin munay ta debi
kwanukan kenan, munay tace dan ajima
kimin girki da dan yawa, don ina
‘suspect” din a kwai bakin da zanyi in
sunzo, san nan ki tabbatar yayi dadi, in
ba hakaba, kin san saura ta fita, adakin
ta je ta jiye, falo ta gyara, bayan ta gama
ta nufi dakin ammar ta gaidashi, ciki2
ya amsa nan ta bashi hakurin abunda ya
faru, sam ba zai iya fushi da autarsa ba,
dole ya huce suka danyi hira, kafin ta
dawo cikin gd.
Ahyan kuwa tun daren jiya, ya gama
kwanton baunan sa, Allah bai bashi sa’a
ba yayi ta zarya amma ta rufe daki, dole
ya hakura ya kwanta cike da haushi.
auta da wuri ta daura girki, ko ina a gd
sai kamshi ke tashi, bata gama girkin
rana ba sai 3:40 tashiga tayi wanka, ta
dauko kayan da Ammar ya musu tsaraba
tasa, gata fara ga kayan maroon da baki,
bakaramin kyau ya mata ba, “(ko kai
mai karatu katsara irin wan nan kaya a
idonk ya kake ganin auta zata fito)”.
Munay manya bacci tasha, sai da ta tashi
wanka tashiga, tana fitowa ta bude sif
dinta tana zaban kaya can idonta ya kai
kan wani green sai lokacin ta tuna
Ammar ne ya sayo musu a dubai da yaje
sari, da sauri ta dauko, nasan yau un
yaganni da shi zaiyi farin ciki, tana sawa
tayi make up kamar zata bar kasan.
Misalin4:30 wayarta tayi kara, tana
dagawa taga bsty ta ce, da sauri tace ya
kun isone?, bsty tace eh, right!,….
gani zuwa da sauri ta nufi gate, tana
zuwa ta hango su, oyoyo ta musu, kafin
suka rankwafo zuwa falo.
bayan sun zauna ne munay tace kee
auta!!, auta!! auta!! cikin isa da gadara
take kiran, Ganin bata fito ba yasa tayi
hanyan stairs, fuskanta dauke da
kwandon bala’i.
  auta ko jin kira bana karau ba, yasa
tafito da sauri sam bata lura ba saiji tayi
garam!!….. Sunyi karo da mutum cikin
tsoro ta ja da baya kee yar iska dan
ubakin waya baki damar tafiya kwa2ra
agidan nan?, ta sadakar da duka kwai,
duk tsoro ya cikata amma jin ta zagi
ubanta yasa taji wani bacin rai da
karfin guwa yazomata.
®WISDOM
HAUSA WRITER’S
Rash Kardam
[7:56PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
Da karfin guwa, ta soma zazzaga ma
munay masifa wanda, wanda yasa
munay sake baki don bata taba
tsammanin ta iya masifa ba.
sai a lokacin taji muryan xarah na cewa
munay kika bar wan nan mai kama da
Aljanan, take miki rashin kunya, daga
hannun munay ta kai mata mari, auta
ko cikin zafin nama ta rike hannun, ido
munay ta zaro sai a lokacin ma ta lura
da kayan jikin ta, aiko take ranta ya
kara baci tayi kam ta da niyar duka aiko
auta ta damko ta, sai lokacin karfi ya zo
mata nan ta shake munay, sai ga idonta
ya fito alamar tafiya taji shaka, xahrah
da kaltum suna ganin haka, sukayi kan
auta zasu fara jibgarta sai ka ahyan ya
shigo ko sallama babu, yana yar
wakansa, ganin abunda ke faruwa, yayi
kansu kai!! meye haka? Mts ya fisgo
xahra da kaltum, kafin ya kwace munay,
sai haki takeyi, auta ko jin wuyanta ya
bushe ta wuce kitchen ta dauko faro mai
sanyi, tana takun isa, ta zo falo ta taras
yana fada wa munay, suna hada ido ta
yi mata gwalo, nan munay takara
harzuka sosai, kamar zata fasa ihu.
Auta bata gama gyara zama ba, taji
tsayuwar motar Ammar da sauri tayi
mike don bata son ahyan ya tafi ya
barsu, zasu iya mata rashin mutunci,
kitchen taje ta dibi rabin girki da tayi
wa munay, duk da tasan ya masa yawa,
amma don ta kularta, ta diba da yawa
sosai, tazo ta wuce su tayi dakin ammar
lokacin yana cire ta kalmi, da sallama ta
shiga, kalonta ya tsaya yi don tayi kyau
sosai, bai san har ta iso gefensa ba, sam
ya shagala da kalonta sai da ta hada
hannunta tana tafawa, kafin yayi firgit
ya sauke wani ajiyar hrt, sannu da zuwa
ta masa, ya amsa da sakin fuska, kalonta
yayi, ya ce my sis gsky na iya zabe, don
kayan nan ba karamin kyau suka miki
ba, murmushi tayi tace na gode Allah ya
kara budi, ameen ya ce barin watsa
ruwa, tana zaune ya shiga dakinsa, sai
da ya dau 10 minutes, kafin ya fito cikin
kaya maras nauyi, abincin ta zuba masa,
nan kamshi ya fara dukan hancinsa,
aiko bai tsaya wata2ba ya fara diban
abinci yana santi, sai da yaci yayi rabi
sanna ya sha ruwa, yace Alhamdulilah.
Hira suka rinkayi yana bata dariya sai
kyal2lewa takeyi, sai da aka kira sallah
magriba kafin ta masa sai da safe, ta
nufi cikin gd, sai da ta dan leka ta ga
basa nan, ta nufi kitchen da hanzari ta
ajiye cooler ta nufi dakinta, key ta saka
tayi sallah haka har akayi isha’i ta
kwanta.
 Da safe ta hada breakfast ta dibi nata ta
koma daki, bayan ta karya ta koma daki,
bata fito ba sai karfe daya ta daura na
rana lokacin munay na bacci, tana
gamawa ta diba ta koma daki, bayan taci
wanka tayi ta zauna tana duba littafin
adu’ah. Sai kusan uku taji tashin mota
tasan munay ce, tana tabbatar da ta bar
gidan ta fito ta nufi kitchen ta gyara ta
kama wasu ayukan.
Su mum sun isa sakoto lfy, tayi duk
abunda ya kaita, da taso su kwana 2
amma sai aka mata kiran gagawa dole
suka shirya don ta jirgi zasu dawo yau
din nan 5 jirginsu zai sauka.
Auta ko han kali kwance take aikin ta,
har da yar waka ta, ahyan ne ya shigo
gd ya leka daki munay yaga bata nan,
murna fal ransa ya nufi dakinsa ruwa
ya watsa kafin ya canza kaya zuwa
boxer da singlet ya nufi dakin auta, nan
yaga fata dawo dakin ba, buya yayi a
toilet.
Auta na gama aikinta ta shigo dakinta,
bata rufe kofa ba turawa tayi don zata
koma jimawa kadan ta dauko zobon da
taha kafin yayi sanyi, kan gado ta fada,
bata wani dade ba ta fara gyan2di, a
hankali ahyan ya bude kofar, lokacin
bacci barawo ya dauketa, kusa da ita
yazo nan ya fara mata wani irin salon,
“(ido na zaro ina rokon Allah ya kubutar
da wannan baiwa daga hannun wan nan
maras tausayin)”.
Auta kamar daga sama taji ana mata
wasu abun da ya basa tunaninta, a
hankali ta soma bude ido ganin ahyan
yasa tasoma kokawan kwace kanta,
amma ina yafi karfinta, sai kokarin
rabata da kayanta yakeyi, da kyar ya
samu ya yaga rigan jikinta, ganin daga
ita sai bra yasa ta ja da baya ga hawaye
da ke zuba, shiko sai wani dariyan
mugunta yakeyi, haka har suka iso
bangon dakin, ya nufota gadan2 tasaki
wani razanane kara,
Wanda yayi dai2da shiigowan Ammar
gidan, bai karasa parking ba sai ga su
hajia mamu sun iso, auta ganin ba
wanda ya jita yasa takara takarkarwa
iya karfinta tasaki ihu ta fadi kasa
sumamiya, shiko hakan baisa ya ci gaba
da abunda yayi niyar yi ba.
aiko dukansu da ammar da su hajiya
bansan wanda yafi wani gudun shiga ba,
nima ina ganin haka na bisu da mugun
dugu har sai da wayata ta fadi.
Mai karatu ban samu daman daukar
wayata ba, nabisu don inji gurmin da za
a toya, kar ya wuce ni, in na dauko
zakujini a next page….lol…
Taku a kulum mai kaunarku Yar
Mutan Kardam
®WISDOM
HAUSA WRITER’S
Rash Kardam
[7:56PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Da gudu suka nufi cikin gidan, duk a
rude suke, ammar garin hawa stairs ya
fuge kafarsa, nan take sai ga jini ya
soma fita, amma ko ta kansa bai bi ba,
yana isa yaga kofar arufe yayi zaton da
key ne ajiki, komawa yayi da baya yayi
wani duka ma dakin, sai yaga ko motsi
baiyi ba kafin yasake naushin, H Mamu
ta zo da sauri ta murda kofar sai gashi
ya budu, duka suka shiga dakin, abunda
suka gani ne yasa su suman tsaye,
ammar da gudu ya kaima ahyan damka
wanda shi gaba daya baya cikin
hayyacinsa yana kokarin kire ma auta
skirt yakeyi, ammar ya shake wiyarsa ya
makasa da garu take kansa yasoma
zubda jini, ran hajiya mamu ya baci
idonta ya rufe, ga hawaye zai zuba
yakeyi dai2 nan munay ta shigo ganin
abunda ammar yake ma bros dinta yasa
tafara dukansa wani naushin da ya mata
sai da ta fadi gebe dan azaba kasa kuka
tayi, hajiya mamu tazo tafara taya
ammar dukan ahyan, sai da suka ga
baya ko motsin, suka kulyalesa, kausar
kam kuka take kamar ranta zai fita,
ammar da gudu ya dauki auta yayi waje
da ita wanda marabanta da gawa
kadanne, kausar da H Mamu suka rufa
masa baya, akabar munay da bros sai
kuka take tayi.
Ni’IMA CLINIC, ya nufa gudu yakei
kamar zai tashi sama har sai da yan
hanjin cikin kausar suka kama disko,
suna isa emergency suka nufa, da sauri
nurses suka karfe ta suka shiga da ita, ba
a dade ba na hango Mrs Adul cikin
shigan kayan likita, tayi emergency,
ammar ko kasa zaune yayi sai zagaya
wa yakeyi, yana hawaye nan wani bakin
ciki ya tokaresa, bai san lokacin da ya
buga hannunsa a garu. Har sai da hannu
tayi kass, kausar duk ta tsure da
lamarinsa daman haka yake da zuciya,
(ni rash nace hmm).
Can Mrs Abdul ta fito fiskan nan baya
bo ba fallasa da sauri Ammar yayi gunta,
Dr ya jikintan? Ta tashi kuwa? Atare ya
jero mata wayan nan tambayan, ajiyar
zuciya tayi kafin tace Alhamdulilah, bata
tashiba amma zamu ce da sauki, amma
meye ya razana ta haka don tayi dogon
suma, amma muna sa ran farfadowanta
a kowani lokaci, aziyar hrt ammar yayi,
Mrs Abdul taci gaba da cewa, zamu kaita
dakin hutu ba kuma mai zuwa kusa da
ita don bata son hayaniya, suna tsaye
akazo aka wuce da ita special room,
hajiya mamu kam duk takasa cewa
komai wai ace ahyan ne ya aikata haka,
ina tarbiyan da tabasa duk yasa kafa
yayi watsi da shi, in sonta yakeyi, mai
yasa bazai fada mata, sai ayi musu aure
ba? Dole in gwada wa ahyan bacin raina
dole nasan abin yi, kausar kam kasa
hada ido tayi da ammar don tana jin
tsanar ahyan amma sun gode ma Allah
da Allah yasa bai kita mata haddi ba.
Munay kuwa ganin kar dan uwanta ya
mutu, yasa ta mike tana dingishi, ta nufi
harabar gidan isa mai wanki ta ganin
nan ta kwala masa kira, kazo ka
taimaken, sanin halinta yasa ya biyo ta
da sauki, sama suka haura nan tace ya
kamata ahyan ahaka suka fito, mai gadi
ke tambayan ta, maike faruwa? Wani
mugun kalo tamasa wanda yasa dole
yaja bakinsa yayi shiru, sabida sanin
halinta, da gudu suka nufi T.H, suna
zuwa emergency ta kaishi nan doctors
sulayi caaa akansa basu dau lokaci ba
suka gyara masa ciwon da yaji kuma ya
farfado amma sun masa aluran bacci,
sannan suka nufo munay suka fada mata
san’nan ta tanadi kayan tea, don in ya
farka ta fara bashi ruwa mai zafi ya sha,
nan tayi godiya ta nufi hanyan gd.
Ammar ko ganin an wuce da auta ga
kayan da ke cikinta duk ayage yake wani
sas’san jikinta na aje, yasa ya nufi gd
don ya dauko mata kayanta acanza
mata, bai ce kala wa H Mamu ba don
wani haushin su yakeji, fita yayi ya nufi
gd a mota don yana hanzari baya son
yin nisa da auta, gani yakeyi kamar za’a
sake mata abunda aka mata, yana isa gd,
dakita ya nufa ga mamakinsa bai ko ga
su munay ba amma dake ba damuwar sa
bane kuma baya son ganin su, nan ya
dau mata fallen zani da karamar riga,
sai hijab, yazo fita kafarsa ta gogu da
takalmin auta nan yaji wani azaban zafi
da sauri ya kali gun, sai alokacin yaga
ciwon da yaji, bai tsaya takan ciwon ba
yazo sauka daga stairs yaga munay tana
tahowa sai dingishi takeyi, wani mugun
kalo ya watsa mata, fuskansa sam ba ko
annuri, kamar baitaba dariya ba, nan
take wani tsoronsa ya dira mata azuciya.
Luv u all my fanz
Rash Kardam
[7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Wani mugun kalo yamata, yanzu tsoron
ammar ta ke baran da ta tuna nashin da
ya mata da sauri ta dawo da baya, ta
sauko sai da ta bashi hanya ya fita,
sannan ta haura ta debi duk abunda zata
diba ta dau poss dinta dake tana da kudi
aciki ta nufi asibiti, tana zuwa ta nimi
gu ta zauna ta zuba tagumi tana kalonsa,
tana fatan Allah yasa ya tashi.
Ammar ko yana fita ya nufi dakinsa
ajiye ki din mota, don shikam yabar
amfani da abun gidansu kuma yau zaisa
afara nima musu gd, don tabbas shine
silan ja ma auta wan’nan abun, in da bai
yarda yazo gidan nan ba da ahyan bai
mata haka ba, ko da ya fita abokinsa
auwal ya kira yace masa gd yake so mai
dan saukin kudi, amma ba wanda yake
da mutane da yawa ba, auwal yace an
gama zuwa gobe zakaji “feedback” nan
sukayi sallama ya nufi asibiti, yana
zuwa yasamu H mamu suna inda suke
sun zuba tagumi, nan yaji tausayinta,
gsky tayi masa karamci gashi tilon danta
na miji ta wasa abunda bata tana zaton
zatayi ba, bata so kanta ba ta bama dan
ta laifinsa, gaskiya hajiya mamu tacika
mutuniyar kirki uwa ta gari, wacce take
son yayan wasu ta kuma kula dasu
tsakaninta da Allah, Hajiya mamu Allah
yasaja miki ya biyaki da rikon gsky da
kika mana ameen, amma bazan iya
cigaba da zama’a cikin gidan ki ba, don
tunda yasoma kuskuranta, nan gaba
zaiyi abunda yafi haka ni daman
hankalina bai kwanta dashi ba, cikin
zuciyarsa yake magana, sai da yaji H
mamu tace ammar sannu da dawowa,
firgigit ya dawo hayyacinsa, Murmushi
ya kakalo wanda yafi kuka ciwo yayi,
ammar duk yaba ma hajiya tausayi
lokaci daya duk ya canza kamar bashi
ba, kausar tamasa sannu, ya amsa ya
tambayesu ya mai jiki sukace haryanzu
dai ba lbr, kayan ya mika musu yace ya
kamata su je gd su huta, h mamu tace ina
ae ba inda zata zata kwana da auta, tace
kausar taje gd, ido ta zaro don auta bata
tsira itama tanaga intaje abunda zai
mata kenan bare uwansu badaya bare
uba, don da aure a tsakaninsu, ajiyar hrt
tayi kafin tace mum kata kafarki, h
mamu dake babbace ta gano kausar
kuma sai taji badadi azuciyarta danta
yau ake gudu,(umm tsakanin uwa da
danta sai Allah duk da taga laifinsa
amma sai da taji wani iri, yan’uwa ya
kamata mu na tausaya wa iyaye mu
kyautata musu, don sun sha wahala ba
kadan ba akan mu ya Allah kaba mu
ikon tausaya musu da jin kansu, kaman
yanda suka mana muna kanana Ameen).
Su hajiya mamu da kausar suka kwana a
dakin masu jinya, shiko zama yayi a
kofar dakin akwai chair azaune ya
kwana da safe bayan sunyi sallah yaje
ya sayo musu abinci, suka karya sai ga
Dr ta zo nan suka gaidata, suka
tambayeta ya mai jikin tace musu da
sauki nan ta wuce office dinta, wayarsa
ce tayi kara yana daga wa yaga auwal da
sauri ya dauka, bayan sun gaisa yace my
man an samu gida ku biyu ne aciki
amma yace min daki2 ne in kana da tym
sai kazo muje a nan dutsin tanshi ne,
yace ba matsala na gode sukayi sallama
ya kashe wayarsa, sai kusan 10 ya bar
asibiti direct gun auwal yaje, sun duba
gd ba laifi yayi gashi daki dadai ne, ko
wan’ne da bayi aciki san’nan akwai kofa
a tsakiya, sai ta waje ma akwai kofa
kamar na falo ta wajen gidan sai yar
karamar gate dake gun, kuma gidan na
da kyau sai na dayan yana tsam’manin
ciki da falo ne da bayi, sai kitchen da
wani karamin daki na saka kaya, dake
bauchi muna da arahan haya kudin ba
masu yawa bane, 60k ne kawai nan yaga
arahansa don inda a kaduna ne abun sai
a slow, nan yace zaibada kudin zuwa
jimawa san’an yasa aka kira masa
almajirai ya biyasu yasa su wanke masa
dakin don yau zai kwaso musu kayansu
ko gobe.
Yana fita bank yaje ya zaro kudi a
account dinsa don duk wata hajiya
mamu na sallamansa da 30k kudin da
take basa gashi yau kusan shekaran su 2
da wani abu, a gidan kunga ya dan samu
wani abu, duk abunda ya kamata ayi
anyi, yaje gida dakin auta ya kwaso
mata kayan ta dake sif dinta wanda
yasan’nata ne, shima ya dibi nasa, ya
ajiye, kasuwa ya shiga ya sayo musu
katifa manya guda 2, yazo ya ajiye, ya
gaji likis gashi yanzu magriba ta kusa
duk da yana lekasu ya tambayi lfy auta,
yanzun ma asibitin ya nufa.
Munay tana zaune ta zuba tagumi,
ahyan yasoma bude idonsa, yana kalon
dakin da kyau, sannu a hankali ya
komai yasoma dawo masa, kara yasaki
yana kiran no! no! no!, ( nikam nace to
no! Din na me nene ko yaso sai ya gama
biyan bukatar sa ne? oho, ko haushin da
mum dinsa ta gansa ne? Oho zamuji
koma miye nan gaba).
Taku a kulum mai kaunar ku
Rash Kardam
[7:57PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Ahyan bakaramin damuwa ya shigaba,
yau yasan mum dinsa tayi fishi dashi bai
kuma kyauta ba, dole yaje ya bata
hakuri, da kyar ya iya shan tea ya sha
magani ya koma ya huta.
Yana isa asibiti ya gaida su H
mamu, san’nan yanufi gun Dr yake
tambayart cikin Zee tace d sauki, dakin
ya dawo ya zauna a gefe, ya zuba ma
auta ido ko kyaftawa baya yi,wayar H
Mamu yayi ringin tana dagawa taga
munay ce, da kamar bazata daga ba,
amma sai ta dauka daga daya bangare
akace, “hello mum ya kk? Mum duk
abunda bros ya miki ya kamata kiyi
hakuri ki tausaya masa, kizo ki ga
jikinsa, a kan wan”nan yar da ba’a san
asalinta ba, sai wai2 amma ki kyale dan
ki wanda kikeso” wani tsawa ta daka
mata nikaina sai dana tsorata, wato
munay kema bayansa zakibi ko? Kuma
kar in kuskura inji kin kara zaginta ni
baruwana da shi, har sai ya gyara
halinsa tukun mtss ta kashe, ammar har
rashi saida yaji taisayinta don tacika
uwa ta gari ba mai son kanta ba, sai yau
yaji kara sonta a matsayin uwa, “Allah
ya biyaki mum”, kausar ma jikinta duk
yayi sanyi ammar yayi karfin hali yace
mum kije ki dubasa da jiki, duk abunda
zaiyi bazaki taba kankare alakar kuba,
“hannuka baya ruba ka yanke ka yar”
dan kine dan haka adu’ah shine mafita,
taji dadi amma bata nuna ba sai kawar
da kan ta tayi kamar bata jishiba.
Zee ce ta fara motsi kada2 sai tasaki
wani kara take sukayi kanta dukansu,
ihu take tana kiran sunan Allah, sai
kuma ta soma cewa Ammar…. ammar…..
Ammar kazo ka kwace ni zai kashe
wayyo Allah na, wayyo mum kun tafi
kun barni, ammar da sauri ya je ya kira
Mrs Abdul da sauri sukazo allura ta mata
take bacci ya sake daukarta, Mrs Abdul
tace karku damu zata farka cikin
hankalinta, ajiyar hrt ammar yayi godia
ma Allah dr tafita ta basu gu.
Sai can dare ta farka, taga mum nan
ta soma tuna mai ya faru kuka tayi
sosai, mum na lalashinta, tea ta hada
mata tasha ta kai mata ruwan wanka
tayi taji dadin jikinta kafin tayi sallah.
Ahyan kuwa an sallamesa cike da
tsoro da zullumi ya shiga gd, da farko
kam yaki shiga sai da munay tashiga ta
duba masa ko mum na’nan, taga
batanan tukun ya shiga gidan.
Kausar jin munay na gd yasa
tadawo kuma hauwa mai aiki ta dawo
yau, tukun ta koma gd, ya rage h mamu
ke ajikinta, gsky ta gwada musu kulawa.
Sai can yamma ammar yazo yana gun
cuku-cuku neman shagon da zai dan sari
kaya yazuba aciki, ya fara business da
yan kudin da ya tara na albashin da
yake samu.
Sai da ya gaida h mamu tukun ya yima
auta ya jiki? ta amsa da sauki, sun dan
taba hira kafin yace ma mum yana so
zai roki gafaranta don ya mata laifi sai
da ya bata hakuri kafin yasanar mata da
hukunci da ya yanke, da farki taso taki
akan sai dai ahyan ya bargidan, ammar
ya nuna mata ilan hakan san’nan ta
amince, sun na cikin hira Mrs Abdul
tazo ta basu sallama, kaya suka tattara
san’nan ya tsara musu napep suka je
gudan sai da h mamu ta gyara ma auta
daki duk da a gyare yake kafin ta musu
salama akan gobe zata dawo.
Ko da ta koma gd tasamu ahyan ko
kalon inda yake batayi ba, da gudu yazo
ya rike kafarta yana bata hakuri tureshi
tayi ta wuce idonta cike da kwalla, “a
zuciyarta tausaya masa amma sai ta
gwada masa kurensa”.
Washe gari sukaje da kausar suka duba
auta tare da kayayaki bayan sun dade
suka musu sallama suka dawo, washe
gari ammar ya tattara yan kudin h
mamu da ya sani da wasu ta kardunta
ya kaimata yabata hakuri sam bata so ya
bar yi mata business ba don yaron yana
da “AMANA” amma ba yanda ta iya
haka ta hakura nan ta dibi kudi mai
yawa tabasa yayi godiya ya fito kenan
suka tsaya da mai gadi sunyi hira sosai
sai kusan 9:00 ya nufo gida ya sai musu
nama da yan kayan motsabaki abakin
titi mai mashin ya ajiye shi yazo shiga
lugun gd da suka koma wasu yan’isa
suka tsaresa harda wukakensu suka
nuna kudi suke nema baiyi musu ba ya
basu kudin da aka bashi, har sunce ya
tafi dayan yace kai tsaya ban…..
Taku mai kaunar ku a kulum
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Wani daga cikinsu ya ce tsaya, baiyi
musu ba ya tsaya, daya daga cikinsu
yace haka zamu kyaleshi baiji a jikinsa
ba,ammar adu’ah ya ke tayi na neman
tsari, gani basa kusa da shi kuma yana
yin kwana zai shiga gidan da suka kama,
fakar idonsu yayi yasa gudu don ya
sadakar ko ya tsira ko su mishi illa, iya
karfinsa yake gudu yazo dai2 shiga
gidan kafin ya bude kofar gdn, wani
daga cikin yan saran ya kai masa sara
cikin ikon Allah bai same sa sosai ba, ya
shiga gidan sakata.
Auta jin haya niya ta fito ita da matar gd
sun tsaya cirko2, nan matan gd take bata
lbr yan sara garin nan take auta ido ya
ciko da kwala, yayanta ta tuna ko a wani
hali yake oho nan ta fara masa adu’a
kariya daga uban giji, suna tsaye agun
sukaji an rufo kofa matar rayi daki da
gudu sabida tsoro, auta kam ko motsi
kasawa tayi da sauri tayi zaure tsaban
dakiyar zuciya tana haska wa taga
ammar da sauri tazo ta rike hannusa
tana hawaye shiko ido ya runtse sabida
safin ciwo sai mai da numfashi yake yi
kama hannunsa da auta tayi yasa ya
bude idonsa, han’nu da ba ciwo yasa
yana goge mata hawaye suka nufi daki,
dan kwalinta ta yanka biyu ta daure
masa han’nu tana masa san’nu ya amsa.
3yrs leter
Garin kaduna wata kyakyawan yarinya
na hango cikin farin ciki ta nufi gidan
inspector Abubakar ko dana kare mata
kalo naga futha ce ta kara girma sosai
tadawo cikakiyar mace abun sai mai
karatu ya ganta, cikin murna iyayenta
suka tareta bayan yar kwarya-kwaryan
malimar da aka shirya mata, sadiya ma
ta hallara inda yanzu tagama karatunta
ta dawo cikakiyar yar’jarida walima ya
gudana cikin kayatarwa.
Baku tambayeni ya labarin pinky
yar’rawan kai, hmm ku biyo ni
kuji.duniya ta juya don yanzu pinky ko
yar motar da take ja babu don yanzu
dukiyar baba isiya ta kare ba abunda ya
rage masa yanzu sai diabetes da tasa sa
agaba har an yanke kafa daya gasa rai
kwa-kwai mutuwa kwa-kwai, don shi
tun daga duniya yafa ganin nasa saka
makon bai ko ina ba matansa sun gujesa
don tanzu ba abun duniya.
Baba sani kuwa ba laifi komai yana
tafiya yanda ya kamata don har ya
manta da wasu yan’uwansa da kuma
yar’auta rayuwansa ya ke ci son ransa.
Garin bauchi kuwa ammar da auta ci
gaba ya samu cikin she kara biyu Allah
ya buda wa ammar ya albarkaci
dukiyarsa da ya nema da guminsa yanzu
shaguna 2 garesa na atamfa da shadda
less masu kyau sai na takalma da
jakukuna, wani abun dadi sunan auta
yasake mayarwa, haka rayuwansu ya
kasance cikin jin dadi da farinciki,
watara na ammar suna zaune da auta
take cemai tana son suje kaduna ko da
ba dade wa zasuyi ba, ina son inga futha
da sadiya don nasan bayan tafiyata suna
cikin damuwa ina son inga wasu
yan’uwa, ammar yace ina sane da haka
don ba yanzu nake son zuwa ba akwai
lokaci in muna raye don na dau wa
kaina alkawarin matsawan ina raye sai
na dau fansa masu Dad da mum kuma
sai an yanke masu baba sani hukunci
dai2 da laifinsu, auta har cikin zuciyarta
taji dadi ta kuma kara masa fatan na
sara.
5 weeks leter
Ammar ne a shago yana ta fama da
jama’a cikinsa ya fara murda masa tun
na daurewa abun har yasoma da munsa
kafin kace me ammar ya fadi akasa
cikin firgici yaron shaginsa ya dauwaya
yana son ya kira auwal abokinsa ya kira
auta cikin rudewa yake mata bayani
akan zasu kaishi asibiti, sai da tayi
magana ya ga ba auwal ya kira ba, da
sauri ya kira na auwal akwai yace gani a
kofar Central market din yanzu zan
shigo da gudu yazo suka daukesa sai
“NI’IMA CLINIC” auta cikin rudewa ta
kira wayansa nan auwal ya daga tana
kuka tace kuna wani asibiti ne yace suna
ni’ima tace to gata zuwa, duk da bawani
yawo take a gari ba mai napep tatsara
ya kaita tana zuwa ta samu auwal sai
safa da marwa yake a kofar emergency,
nan yasoma lallabinta don kuka take
sosai, ana cikin haka nurses tafito ta ba
ma auwal ta kardan magani yace bari
yaje ya sayo.
Dr tace tafito auta na ganinta ta nufeta
tana hawaye Dr ya jikinsa, ta ce da
sauki, ke ce matarsa, auta kamar ta ce aa
ta dauka ba wani abu bane kawai sai
tace eh nice ok!! Ki biyo ni office to tace
Dr tayi gaba tana binta a baya sai da
sukaje wani office ta nuna mata kujera
ta zauna, sai da Dr ta cire glass din
idonta, tace ya sunan ki madam tace
Zainab, Dr tace zainab daga ganin ki
kamar wayyayiya amma kina abu kamar
baki san komai ba, ae yanzu kai ya
waye, duk auta na cikin duhu sai da Dr
tace mai yasa baki ba wa mijinki
hakkinsa kinsan laifin ki kuwa Allah na
fushi dake haka mala’iku suna tsine
miki, ga shi kinsa mijinki cikin wani hali
yanzu in ya fara bin matan banza fa
hakki na kanki, don a yanzu haka sperm
ya masa yawa don in bai samu ya biya
bukatarsa ba zai iya shiga ko wani irin
hali, auta sai da taji gananta ya fadi,
dake Dr macece nasiha ta mata sosai,
tukun tace ta je ta duba mijinta, sai a
lokacin suka ga sun dade sosai kusan
1hrs tana mata nasiha kwatance dakin
da aka kaisa tamata, auta jiki ba kwari
ta fito ta nufi dakin.
Ammar ko bayan da aka masa
allura ciwon cikin bai dade ba ya lafa,
auwal a gefensa kusan 40 minutes yayi
ya farka dake jinisa da karfi ko alluran
bacci aka masa bai cika dadewa ba, nan
auwal ya fara masa nasiha akan tunda
auta yakeso ya fito ya fada mata ko
yanimi wata ya aura, sai da yagama
maganarsa kafin ammar ya fara magana
da ni bana son takura ma zainab don
banga alamar tana sona ba, abunda ya
hanani sanar mata kenan kawai
shakuwar da mukayi ne, ni kuma banjin
zan zauna da wata mace kamar bazan
iya mata adalci ba, zuciyata zainab take
so, sai hawaye ya fara zuba masa amma
zan bama zuciyata hakuri matsawan
zainab taki amincewa na auri wata ko
don gudun fadawa halaka.
Auta da ta dade da isowa tana shirin
shiga taji anakiran sunanta, nan taji duk
abunda suke fada kuka takeyi tana fadi
bazan iya ba Ammar .
Hmmm karkuso ku gani alokaci idi na
zaro don tsananin mamakin auta duk
halaci da ammar ya miki cab… Ko dai
mai take nufi zamuji nan gaba.
Taku a kulum mai kaunar ku
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Ammar abu duniya ya ishe sa,
zaune yak’e a shago, ya zabga tagumi,
wayar sa ce tayi kara ya duba yaga
Auwal ne, ya dauka da sallama sa, daga
ban garen Auwal yace” kana jina
Ammar ta fiya ce ta kamani ta gaggawa
zan fita zuwa waje,” kana leka min gun
business dina komai ake ciki kana sanar
da ni.
Ammar ya ce “ba matsala Allah ya
k’are,” sai ka jini.
Hajiya Mamu ce zaune tak’e na zarin
hukunci da yakamata ta yanke ma
Ahyan, ta dad’e ta na tunani, kafin naga
ta saki wani lallausan murmushi, wanda
hakan yak’e tabbatar min da ta samu
amsa ta.
Munay ce ta shigo gdn, H Mamu ta mata
kalon tsaf tana na zarinta, sunan ta kira
Munay zo nan, tazo ta zauna, a nats’e ta
ke kalonta, Munay ina kike yawan zuwa
kw’ana b’iyu?, ba kya yawan zaman
gida, fada min?, “cikin zafin rai tayi
maganar.”
Munay duk ta tsorata da yanayin
Mum dinsu, kame-kame ta far’a yi,
tsawa ta sake daka mat’a, Mum da…
Ma..umm..um.. Wani mari ta sakar
mat’a, kin bar fit’a. “sam ni ban yarda
da tarbiya kawarki sholly ba.
Fada ta mata sosai, ta tashi ta bar
Munay a gun.
Ahayn karatun sa yak’e ba wasa,
duk randa zasuyi waya da “Munay sai
ya mata nasiha sosai mai shiga jiki. Don
shi yanzu ya fita harkan yan’matan
b’ariki, ya kima ga Allah.
Auta z’aune tana nazarin abunda
take ma Ammar sam wani sa’in bata
ky’autawa amma ta rasa mai yasa
zuciyarta ke sata hakan, abun na da
munta, ga wasu muna’nan makarkan da
rakeyi, wani sa’in ma ko ta f’arka,
bakinta kasa furta addu’a ya keyi.
Haka rayuwan su ya kasance, ba d’adi,
don yanzu “Ammar ya bar shiga
harkanta,” tun daya gane bata son ganin
sa bare farin cikinsa.
Sam ba zai iya mata wulakanci ba in ya
tuna “Dad da Mun da AMANATA da suka
bashi, sai yaji ba zai iya wulakanta ta
ba.
Munay ke shirin ta na zuwa gun
“Malam don yau’ne zai gama mat’a
hadin mafani ta,da in ta tun kari
“Ammar bazai iya mata musu ba.
Da kyar ta samu ta fito a gida ba tare da
Mum ta ganta ba, ta dau hanyan Firo
nane garin da bokan yake. Tayi tafiya
mai nisa har ta kusa g’arin, tun daga
nesa ta hango wasu mutane sun taru
amma basa da yawa, basu fi su b’iyar
zuwa shida ba, sai da ta iso kusa ne taga
wata motar da tana yawan zuwa gidan
Malam, kamar zata wuce ganin hatsari
ne yasa ta d’awo da baya ta tsaya. Matar
da tak’e zuwa a motar ne ta yi hatsari,
ga wasu muna’nan magan-ganun da
tak’e fada, ba dad’i ji. ” ni Jimma’i na
kashe Farida, ni nayi asiri ma Sadiq ya
bata, ni na haukata zainabu” da
sau’ransu, abun ba dad’i ji.
“Munay jikinta yayi sanyi, tasoma
nadamar a’bunda tak’e aikata wa. Kafin
su bar guri “Matar nan ta cika tana ihu
tana birgima a cikin dati.( Mata muji
tsoron Allah kar ku d’auki zuwa gun
boka a’ bu ne mai kyau, tun daga ranar
da zaki sa ka f’arki sallah bazata karbu
ba, ga azaban lahira ga haduwa da
karshe maras ky’au, muji tsoron Allah
mu gy’ara).
Munay ta shiga motarta, ta dawo gida
cik’e da nadama, kuma yau zata fasa
kwalban da “Malam yace asirin ciki
kwalban, zai raba Ammar da Auta. Kuma
zan nimi gafaran su, kar nima nayi irin
wan’nan mutuwar.
Garin kaduna kuwa yau sun tashi
da jimami don yau sunyi rashin “Baba
Isiya, Allah ya karbi abunsa.( tabbas
duniya ba gurin zama ban’e, ko kai ko
ka so sai ka bart’a. Yan’uwa mubi
duniya, a san’nu in ka d’auka da zafi,
zaka ga da z’afi, rayuwa bata da
guarantee).
Su “Pinky an shiga damuwa,” yanzu sai
Mum dinta k’adai ta rage mata. “Ya
Allah ka jarrabe mu, jarabawar da zamu
iya Ameen”.
Auta ce zaune tana sauraron wa’zin
Malam ja’afar Mahamud Adam, sosai
wa’azin ke shigarta, gashi yana baya ni
game da yawan Addu’a da amfanin
zama da al’awala, duk sai taji kamar ta
ita yakeyi, tunani ta far’a ” Yaushe
rabon da na zauna da al’awa?, Yau she
rabon da na yawaita yim azkhar?.
Tabbas ko tantama b’abu shiyasa nak’e
yawan ma farkai.
“Yaro ne yayi sallama, ana kiran Zainab
a waje,” wai tazo yana jiranta. Wani
gaushi ne ya tur’nuketa, mts tayi tsuka.
Taku a kulum mai kaunarku
Happy birthday to you Maman Abideen,
i wish you long life n prosperity.
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Auta ta d’ade a bakin k’ofar
“Room”, duk “maganar da su k’ayi taji”.
Kuka ta k’eyi sosai tana fadin no!!
B’azan iya ba, Ammar.
Ta d’ade a gun tana k’uka, sai da
taji ‘Auwal na shirin fit’owa’, kafin ta
share hawayen ta, nufi d’akin.
San’nu tayi ma Auwal, ta b’aye shi,
ya’ya mai jikin? “Da s’auki’ ya bata
amsa, a takaice”, jikin ta ba kw’ari, ta
isa gun g’adon, idon sa a lumshe”tamkar
mai bacci” kan “white chair” da ke gefen
g’ado ta z’auna, sai da aka kira sallah
la’sar kafin ya m’ike ta basa “pure
water”, yayi al’wala.
Dake ” jikin sa da s’auki,
“Alhamdulilah”, b’ayan ya d’awo daga
sallah, ta basa abinci da aka k’awo musu
yaci.
“Kw’anan uku, aka sallame su, duk w’ani
hidima, “Auwal shi ya yi musu, har aka
sallame su”.*****Kw’ana ki sun tafi,
“Ammar ya daina gani fuska a gun Auta”
ta d’aina shiga har kansa, duk ” Ammar
ya fita a hayyacin sa, ya rame ga
damuwa ta masa y’awa,” Auta ko bata
ma san yana yi ba”.
Yau take “friday” ta fito gidan”
Aunty Mamu ta kai musu ziyara” tun
tana napep ta lura da “wani mai jar
m’ota, yana binsu a b’aya, har suka iso
k’ofar gidan su, tana sallaman mai
napep, zata shiga g’ida, sallama ya
mata”Assalamu’alaikum c’ikin murya
mai d’adi” k’amar ana busa sarewa ya
mata sallama”, Auta kamar zata shiga
g’ida amma s’anin muhimanci “sallama”
yasa ta amsa ba t’are da ta juya ba, cikin
salo da hikima, ya ke mata magana,
wanda sai dayasa ta juyo, hira ya soma
yi m’ata, tana yar dariya, sun d’ade
agun sosai, sai da yama sallama zai tafi
tana juyowa, “Ammar ta g’ani ido sa
c’ike da kw’alla ” abun gw’ani tausayi,”
Auta ko kalo sa bata yi ba, tabi g’efen sa
ta wuce, hmmm nikam n’ace “Auta kar
ki mana haka”.
Soyayya ce mai k’arfi ta kulu
tsakani Auta da Adam’s abun ba’a cewa
k’omai, “Ammar ko ya d’awo “so silent”
komai ya cakude masa, ga son Auta da
ke barazana ga rayuwan sa”, abun sai
Addu’a.
Munay ko duniya tayi d’adi, yanzu
ta samu wata kawa mai suna Sholly ita
ta k’ara bude mata ido, har kan gaban su
kawai suka sani sune gun malamai, don
su samu samari masu k’udi.
Ahyan k’uwa duniya ta masa kunci,
sam mum ta fita a har kansa, gashi yau
saura “3 days” ya koma “school” duk
b’aya cikin hankalin sa, “ya’yi nadamar
abun da ya aikata, yanzu a shirye yake
da duk w’ani hukuncin da “Mum” ta
yanke zai d’auka.
“Alhamdulilah, lfy uwar jiki b’abu mai
fushi d’ake.
Nagode da kulawar ku gare ni, Allah ya
bar zumunci” Ameen.
Rash Kardam
[8:00PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Yaro ne yayi sallama, aka amsa
masa,yace”wai ana sallama da Zainab a
waje”. Mts taja tsaki cike da takaici Auta
tace”kaje kace waye ne?, yana fita
takama guna-guni ita kadai, ni wan’nan
Adam din ya wani takura wa mutum,
mts haushi ma yake ban yanzu. Yaro ne
ya sake daw’owa yace”wai inji Adam.
Tace kace masa bata’nan, Yaro ya tafi
bai kuma dawo’wa ba.
Auta tayi kw’anciyar ta, tana mai tuna
abunda tayi ma Ammar, kw’alane ya
cika idon ta, tabbas ban ky’auta masa
ba, na dawo butulu, ta yaya ma hakan ta
faru dani?, har na aika ta masa hakan
ya zama dole in basa hakuri, don
Ammar shine jigon rayuwa ta da farin
ciki na. Kuka ne ya kw’ace mata, tana
mai tuna iya’yenta, addu’a ta musu da
fatan samun Rahman Allah.
Munay tana isa gida d’akin ta, ta
shiga ta kw’anta a bakin gad’o, kuka taci
mai isarta, tana danasani abunda ta
ai’kata. Tace “Ya zama dole in’nimi
gafar su Auta, matsa’wan in basu yafe
min ba, bazan samu Rahman Allah ba,
don na shuga gakki su. Kw’albar asirin
ta da’uko, ta b’oye a hijab d’inta, ta nufi
gurden, tana zuwa ta d’au katon dutsi,
tayi bismilla ta kw’ad’a ma kw’albar,
nan take wani bak’in hayak’i ya soma
fita, gurin ya fara jujjuya mata, duk
addu’a da tazo bakin ta yi take yi, sai da
ta tsuguna kafin zuwa jimawa ta daina
ji, da sa’uri ta mike ta nufi d’akin ta,
al’wala tayi, ta fara sallah tana mai
neman gafara gurin Allah.
Hajiya mamu duk shirin take yi ta
na jiran dawo’war Ahyan zan iya masa
hakuri matsawan zai bi umu’rnina da
sharud’an da zan gindaya masa to zan
iya hucewa.
Kausar ce ta i’so falon tace “Mum na
gama duk aiki da kika sani. Ok!. Wayar
ta ne ta yi ringing Ahyan ke kiranta, ba
kaifi da fara’arta ta d’au sallamansa.
Cikin ladabi yace “Mum ayini lfy?.
lfyklau ya karatu?. Alhamdulilah!! “Mun
ma gama yanzu results muke jira nan da
5days zan dawo, Alhamdulilah!! Allah
yasa a ga saka mako mai ky’au, Ameen
Ya Allah.
Cike da murna ya kashe wayar, yana
mai tam’bayar kansa anya kuwa yau
Mum dina ne ta amsa min magana?,
kuma Batare da ta nuna fushinta ba.
Hmm!! “Ya zama dole in yi amfani da
wan’nan lokacin don in wanke laifina.
Da wayan nan tunanin yayi bacci.
Ammar ne ke shago duk ya rame
ya fita hayyacin sa, waya yakeyi da
Auwal, sun jima suna tat’tau’nawa
sukeyi sun d’anyi hira sosai, Auwal ya
ce”ina dawo’owa gobe fa, don akw’ai
abun da zanyi ran friday. Cikin farin
ciki Ammar ya ce haba? Eh! ya bashi
amsa, to Allah ya kawo ka lfy Ameen. Ya
kashe wayar.
Auta zaune take ta gama yan aiki
da zatayi, wanka tayi tasaka riga da skirt
English wears, sun mata ky’au. Tana
zaune taji gaban ta na yawan fad’uwa
addu’a ta tsanata yi.
Ammar ne ya sh’igo kai da ka ga
yanayinsa baya cikin hayyacinsa, tun
daga sha’ago maransa ya soma murd’a
masa, da ky’ar ya’iya k’arasowa cikin
gd, yana shiga dai-dai k’ofar d’akin ya
zube yana fidda wani-irin numfashi, da
sauri Auta tayi kansa, ta rike shi tana
kuka, tana cewa”Yaya na dan Allah ka
tashi ban son irin wan’nan wasan,
nasan na maka laifi wlh na tuba bazan
sake ba. Ina sai wani rikon da yamata
numfash’insh’i ya kara sama-sama, kai
in ka ganshi bazaka d’au zaka dawo ka
gansa da rai ba. Wani kara ta saki dai-
dai lokacin su Hajiya Mamu da Kausar
da Munay suka shigo gidan, da gudu
sukayi dakin ganin halin da yake ciki
Hajiya Mamu tace “Munay yi sauri ki
juya motar nan zamu nufi asibiti da sh’i.
Matan da ke gidan ita da mijinta suka
sh’igo, mijin shiya taimaka a ka sash’i a
mota suka nufi asibiti. Dr ranan da suka
kawo sh’i ita suka samu. Emergency aka
nufa da sh”i sun dad’e a kansa kafin Dr
ta fito ba alamar dariya a fuskan ta tace
“ma Auta da H Mamu su biyo ta office.
Sai da ta zauna ta nuna musu kujera
suka zauna ta kalli Auta ta banko mata
wata harara, “ke Zainab wato ba ky’ajin
nasiha ko.
“Anya kina tsoron kamun Allah kuwa?.
Sh’in kin san hakki aure a kanki kuwa?.
Cikin fada-fada take mata maganan.
Zainab ina tausaya miki, Auta kam in
banda kuka marar sauti ba abinda
takeyi. Cikin rud’u Hajiya Mamu tace”
Dr ni ban fahimci mai kike nufi ba?, Ina
son ki min karin baya ni.
“Dr bata boye ma H Mamu komai duk ta
sanarma ta, “salati Hajiya Mamu ta saki
ta kalli Auta, Zainab yaushe Ammar ya
sama mijinki?. Cikin kuka tace”Mum
nifa lokacin da muka kawosh’i Dr ne
tace ni matarsa ce?, shine nace mata eh!
ban d’auka abin da zata fada ba kenan.
Ajiyar zuciya Hajiya Mamu ta
saki,san’nan tayi baya ni ma Dr yanda
zata gamsu.
 Dr tace”na fahimce ku amma gsky
Hajiya d’anki nacikin wani irin yanayi
yana bukatar Aure don Sperm ya masa
yawa. Baran yau abun yayi worse, kuyi
iya k’oka kafin nan da 10days ku masa
Aure, in ba haka ba zai iya fadawa
halaka gash’i haisai da ya sumar da sh’i.
Hajiya mamu tace”Dr in Allah ya yarda
zamuyi iya k’okarin mu ayi Auren kafin
10days din. Right!! Allah ya taimaka
ameen suka amsa.fitowa sukayi daga
office d’in H Mamu tana ta nazarin
wan’nan Al’amarin tanaga hadin dazata
yi zai’zo dai-dai lokacin Ahyan ma ya
dawo Allah yasa su bi umurni na, Ya
Allah ka taimake ni akan had’in Auren
yaran nan da zanyi Amern.
Taku a kulum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:01PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Munay da Kausar kulum suna hanyan
Asibiti a d’an kw’anak’in da sukayi suna
zuwa Asibiti Munay tana sh’ish’ige ma
Auta ta kuma bata hak’uri akan abunda
ya faru baya.
Kw’anan Ammar biyu a Asibiti aka
sallame sa, tunda suka dawo Auwal ke
dawainiya da su, sam bai nuna
gazawarsa.
Yau Ahyan zai dawo H Mamu ta kira
Kausar tace”ina son kiyi girki ma
yayanki yau zai dawo, ta da’uko wasu
k’aya masu ky’au tace kisa wannan
zakije ki da’uko sa daga Airport. Cike da
ladabi ta amsa tace”nagode Mum Allah
ya k’ara bud’i yasa afi haka. Ameen!
Sai da ta gama girki kafin tayi wanka
tasa goduwar rigace bakaramin ky’au ya
mata ba. Key d’in motarta ta d’auko ta
nufi d’akin Mum da sallamarta ta tura
k’ofar ta shiga, tace “Mum nagama
girkin na jera su a inda ya dace, kuma
bros ya kirani yace nan da 40minutes
jirginsu zai sauk’a, ina son inje da wuri
k’ar yayita jirana.H Mamu tace”to sai
kin dawo Allah ya kare, banda tuk’in
gan-ganci. Ta amsa mata da to ta fito
cikin nutsuwa take tafiya harta isa
ABUBAKAR TAFAWA/BALEWA AIRPORT.
Bata dad’e da zuwa aka sanar nan da
5minutes Jirgin UK zai sa’uka. Jirgin na
sa’uka fasinja suka suma fitowa mik’ewa
nayi naje gurin, sai da mutane suka fir-
fito can na hango Yaya Ahyan cikin wata
bakar Suite yayi masifar ky’au ya kara
haske da k’iba,sai ya dawo min tamkar
wani bako ciiin zuciyata nake cewa”gsky
Yaya Ahyan na karshe ne duk macen da
ta same shi taji dad’i,” Ya Ahyan yana
matuk’ar burgeni amma kash zai yi
wuya na saye zuciyarsa. Ahyan kuwa
tunda yake sau’kowa ya ky’alla idonsa a
kan kausar sai da ya kusa suman tsaye,
d’an shek’ara biyu zuwa uk’u da yayi
baya gari, Kausar ta k’ara cika da ky’au
tamkar ba ita bace. Hmmm yace”Kausar
ina matuk’ar sonki tun kina yar yarinya
amma nasan Mum da wuya ta bani ke.
Dai-dai lokacin ya iso kusa da ita. Sam
bata san ya iso ba saida ya hura mata
iska a idonta wani sas-sanyan ajiyar
zuciya ta saki, sai alokacin ta farga ya
iso kusata ita, watsowa yayi dab da ita
har tana jiyo fitar numfash’insh’i, ga shi
duk ya cikata da kamsh’in turarensa
Ayhan yace”Kausar mai kike tunani
haka?. In ka ji yanda ya ke maganar
tamkar rad’a zai mata a’cikin kunnenta.
Cikin jin kunya tace maba babu ok!
Trolley da ke hannu sa ta karb’a suka
sh’iga mota, tun a hanya Ahyan ke satar
kalonta har suka iso gida. Munay tana
jin tsatuwar mota ta fito da gudu tana
oyoyo my bros, tana i’sowa sukayi
sharking din hannu, suka nufi cikin
gd.sai da Ahyan ya huta Kausar ce tayi
serving d’insa bayan yaci abinci ne ya
shiga gaida Mum.
Bayan sun gaita H Mamu take
tambayarsa Yaya karatu? Alhamdulilah!
Yanzu kam mun kammala result yayi
ky’au duka suka amsa da Alhamdulilah!
Allah ya sanya Al’k’airi Ameen.
Mum tace”Ahyan kaje ka huta zuwa dare
ina son ganin ka zamuyi magana, ya
amsa da to ya tashi ya nufi d’akinsa da
Kausar ta gyara masa sh’i.
Ammar kam jiki Alhamdulilah ya war-
ware har ya fara fita, abunka da mai
zafin nama. Yana zaune wayars tayi
kara Hajiya Mamu yagani cikin
girmamawa ya d’aga wayar bayan sun
gaisa Hajiya tace”Ammar ya karfin
jikinka?, yace da sauki, tace
Alhamdulilah! Yau in ka taso daga
kasuwa ina son ganinka da magriba, to
Mum zan’zo in Allah ya kaimu, yauwa
nagode sai’anjima.
Ammar na sallah magriba ya zo gun
Hajiya sai da ya gaisa da mai gadi kafin
ya sh’iga ciki.
Munay ya fara gani a falo yaukam cikin
nutsuwa ta gai dash’i ya amsa ta je
kitchen ta kawo masa drink da abinci,
tace”barin k’ira maka Mum din, bata
jira amsan sh’i ba ta nufi sama, tana
zuwa ta sanar da Mum Ammar ya zo H
Mamu tace”ki kaisa falon baki can
zamuyi magana, sannan ki bi kice ma
Yayanku ya same ni acan to ta amsa. Sai
da ta fad’a ma Ahyan tukun ta sanar da
sak’on Mun wa Ammar, dake ba bak’oba
ne falon ya sh’iga ya zauna, sai ga
Ahyan ma ya sh’igo hannu ya mika masa
suka gaisa, Mum ne tash’igo itama da
sallama suka amsa ta nimi gu ta zauna,
nasiha ta musu sosai mai sh’iga jiki,
sunansu tak’ira d’aya bayan d’aya suka
amsa ta d’anyi sh’iru kafin tace”na
yanke hukunci had’aku aure da k’anne
ku. Cikin razana suka d’ago a tare suna
kallonta, sake mai-maita abunda ta fad’a
tayi, Ahyan ta kanka zan fara, kasani
tun lokacin da yar’uwa ta take raye
muka yi al’k’awarin zamu had’a
ya’yanmu Aure, ina son in cika wannan
burinmu, kuma bin umarni na sh’i zai
sa na yafe maka abunda kayi min, don
haka na yanke hukunci had’aka aure da
yar’uwan ka Kausar har na sanar da yan
Sokoto. Ba shawara nake baka ba
umarni na baka, ta kai dubanta ga
Ammar ta kira sunansa, ya amsa jiki ba
kw’ari,tace”Ammar kaima ina ga zaka
auri Zainab don tafi sabawa da kai ta
sh’ak’u da kai sosai, Ammar a cikin
zuciyansa yafurta Alhamdulilah!.a fili
kuma sunkuyar da kansa yayi yace to
Mum Allah yasa hakan shine mafi
al’kairi!, Ta amsa da ameen. Tace”don
haka kuje ku fara sh’iri wata sati ne
d’aurin Aure da tarewa. Sannan bace sai
kunyi kayan karya ba a’a mu al’kairin
abu mukeso suka amsa da to sh’ikenan
ku tash’i kuje Allah ya muku albarka
ameen. Amm Ammar ina so ka zo min
da Auta da kayanta zata dawo gdn nan
harsai anyi biki sai ka d’auketa to ya
amsa suka fita.
Ammar na isa gida wata zuciya tace
karkayi sauri sanarda Auta kai zata Aura
halama bata sonka kawai ka gwadata ka
gani.
Da sallama ya sh’iga gidan amam ya
d’aure fuska Auta da fara ta masa sannu
da zuwa, ganin yanayin sa ya sa
tace”Yaya na mai ya sameka? Kona
maka laifi ne? Kai ya gir-giza mata
alamar a’a to mai yasame ka? Dan Allah
ka sanar min.
Cikin al’hini ya soma yimata bayani
kam hahiya zata hadasu Aure kuma
wata sati duk Auta ta k’agu taji da waye
yace ni da Kausar da ke da Ahyan
what?? Tace “ina sam bazaiyuba ni wlh
bana sonsh’i. Ina da wanda nake so,
cikin damuwa Ammar yace” wa kike
so?.shiru tayi tana kallonsa don bata san
lokacin da ta furta maganan ba, Ammar
yayita bata kalamai akan ta d’au
k’addara da abunda Allah ya zab’a mata,
Auta kam kuka ta somayi mara sauti,
daren ranan bata rintsa ba.
Da safe kuwa idonta duk ya kumbura
Ammar na ganin ta sai duk ta bashi
tausayi kamar zai fad’a mata ko zata
samu sauki, don yana hango tsagw’aron
Sinsa acikin kw’ayar idinta amma ya
share.
Yace”Auta ki sh’irya zuwa dare ina
dawo zan kaiki, cikin fush’i tace”ni ba
inda zanje kai naga alamr ma baka
damuba daman baka damu dani ba,
kuka ta saki mai tsuma zuciya har
k’asan zuciyansa yake jun kukanta, fita
kawai yayi a d’akin don bazai iya saura-
ronta ba. Yinin ranan bata ci abimci mai
ky’au ba sai da azahar ta samu bacci ya
d’auketa ko da ta tash’i bayan la’asar
idonta ya washe wanka tayi takiyin
kw’aliya tace”ni ba ida zani daman son
da Ammar ke min bana gsky bane, hmm
ko ajikinsa bai damuba mts ni haushin
Kausar din ma na fara ji. Ni rash
nace”kw’aji min Autan nan harta na da
bakun iya fush’i Ammar kuma fa da ya
ganta da saurayi yayi yaya?.
Da yamma da Ammar ya dawo sunsha
rikici don fir tace ita ba inda zata je, sai
data ga ya bata rai kafin ta fito tana
kuka ta dan debi kayanta kad’an suka
tafi.
A gd basu same su ba don sun fita
sayayya tana zuwa dakinta ta wuce, sai
magriba suka dawo ganin karsu fahimci
halin da take ciki yaa ta d’an biye
damuwarta ta sake kad’an, sukayi hira
har zuwa 8:40 Mum ta haura sama
Munay ma haka Kausar da Auta kad’ai a
falo.
Ammar ya sh’igo zai musu sallama ya
wuce yatarab ba Mum ya musu sai da
safe ya fita.
Biyo sa tayi da ta sha gabansa
kasancewar ida suke ba haske kafin ka
isa harabar gdn ne, kuma tasoma masa
tace”ni wlh bana son auren inada
wanda nake so kuma shiya yace yana
sona ai, ganin Ammar yayi sh’iru baice
mata komai ba tasa ta fada jikinsa ta
sake kuka nan take Ammar taji lbr
yasoma sauyawa, kara rungume Auta
yayi yace”Zainab sai da taji sunan har
cikin kw”anyanta, bata iya amsawa ba
sai binsa da tayi da ido yace wa kike so?,
jin tambayar tayi tazomata a BAZATA,
shiru tayi ta kafe sa da ido ganin
yanayin da take kuma ya fahimci
sh’itake so, sai yamata dabara sunanta
yasake kira akaro na biyu kasa amsawa
tayi yace”Zainab kina Sona?.da sauri ta
daga kai alamar eh! Lallausar murmushi
ya saki ya kara rungumeta fuskansa ya
duko zuwa dai-dai kunne ta yace Zainab
nine mijin da zaki aura, nayi hakane
don in ga kina qauna ko ba ky’a qauna
ta. Dukan wasa ta kai masa a kirji
yace”wash ashh kika dake sai na rama
zata gudu ya cabkota ya kara mannata
da jukinsa tana kiciniyar kw’acewa ta
kasa sai da ya bata lafiyayan kiss tukun
ya saketa don kar ya wuce gona da iri.
Da gudu tayi cikin gd tana yar dariya.
H Mamu ta sanar da kausar ita ma ba a
samu matsala da ita ba. Don haka suka
ci gaba da sh’iri.
Ammar akw’ati Uku da kit ya yi ma auta
bai wani yi kayan karya ba turmi
ish’irin ya mata sai English wears da ya
samata. Ban garen Ahyan shima turmi
talatin yayi da akw’ati hud’u da kit
komai sai son barka a talakance ba
karya aciki.
H Mamu ta had’a yan Amareta tana ta
tsumasu su Munay sai shirin biki akeyi.
Ammar gida ya kama musu plat su kadai
ba mai tsadan daga hankaliba 80k ya
samu.
Ya sh’irya shida Auwal sukaje k’auyen su
Malam ya sanar musu da Inna laure
yace”Malam ina son kazama waliyin
Auren mu, yaji dad’i sosai basu bar
kauyen ba sai tare da su Malam gd da
suke ya kaisu d’aki Auta.
Amare liyafa suka sh’irya sai angwaye
da suka sh’irya Dinner.
Yau take laraba duk gidan acike yake da
yan biki yan sokoto sun zo, Amare ko
Mum ta hana su fita anata gyara su
Ammar da Ahyan sun had’a kai tare
suke komai da Auwal Munay ko da
Auwal tunda aka fara hidimar biki naga
abunsu sai a slow.
Yau Al’hamis takama yau za’ayi liyafa
Mum ne ta kawo musu wani sari mai
ky’au sosai, masu kw’aliya suka gyara
Amare lokacin da suka fito gun liyafar
dake acikin gd za’ayi hmmm masu
karatu lokacin da suka fito karkuso ku
gansu ohoho abun bacewa komai don
sun sha ky’au kamar ba gibe, liyafa
akayi na gani na fada malama Khadija
da Malam Juwairiya suka gabatar da
nasiha game da rayuwan aure.
Bayan an tash’i a gunne suka nufo gida
suna d’aki munay ke zi-zita irin ky’an
da sukayi tace”Allah yasa wankar
Dinner tafi na yau murmushi sukayi
dukansu gabaki d’aya.
Ran jumma’ah tun da safe suke aiki dafa
abinci yan d’aurin Aure sai da suka
kammala komai H Mamu tazo tasa
Amare sukayi wanka cikin atafa sun sha
turare had’in yar mai duguri, bayan
Sallah Jumma’ah aka saida Aure Ahyan
da Kausar, Ammar da Zainab daga guri
yan d’aurin aure suka wuce zaranda
holel don gudanar da walima.
Da dad’dare Amare sunsha ky’au cikin
gown kowacce kala d’aya da angonta
Ammar yasha shadda fari da ratsin
marun yayinda Auta tasha gown fari da
ratsin maroon colour aciki ta sha make-
up sosai tayi ky’au.
Ahyan kuma daga nesa na hango shi da
farin shadda yasha aiki da zare blue
colour, Kausar ma gown ta sha fari da
ratsin blue colour bakaramin ky’au tayi
ba.
Mutar d’aukan ya biki ne ta tsaya duk
suka debi wayanda suka dace, Munay da
Auwal ya d’auketa a motarsa yayinda
aka tafi da Kausar da Ahyan a motar
abokinsa, sai da aka gama kw’ashe su
kafi naga wata k’atuwar Jeep baka mai
bak’ak’en glass perker ba a dad’e ba
naga wata mata tafito da Auta tun daga
nesa take zuba ky’ali. Ammar kam sake
baki yakeyi yana kallonta baita ba
d’aukar ky’an Auta ya kai haka ba, bud’e
murfin motar aka sata aciki, sai da ta
zauna tukum taji k’amshin da tasaba ji,
da sauri ta kalli gefenta Ammar ta gani
yana mata murmushi. Lokacin aka jasu a
motar hannusa ya sanya cikin nata
yafara murzawa dake cikin motar ba
haske matsowa yayi kusa da ita ya janyo
ta jikinsa ya sanya haske wayarsa yana
haska fuskanta sai da yagama kalon
fuskanta ya gan-garo zuwa bakinta da
ya sha jan baki a gankali ya soma. Oh!!
Na gaji masu karatu sai zuwa page d’in
gaba zaku jini.
Taku a kulum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:01PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Wayar sa ya haska ta da ita tayi ky’au
kamar ba Auta da ya sani ba, a hankali
ya soma bin fuskan da kalo har yazo dan
k’aramin bakin ta da yasha janbaki
maroon, idonta ya haska yaga ta lumshe
su wani kyau na musamman ta kara
masa a hakan, take yaji wani farin ciki
ya lulubesa yau Autarsa ta dawo
mallakinsa YAR’AMANA sa, a zuciyara
yace”ina ma da su dad suna yare suga
wannan rana nasan zasu fi kowa
farinciki. Ya Allah kajikansu kamusu
Rahma Ameen.
Kashe wayar yayi ya kara matso da
fuskansa har Auta na jiyo numfash’insa,
nan take yasoma jin wani abu na tsirga
masa, bakinsa yasa cikin nata yafara
mata wasu salon, dai-dai lokacin suka
iso, a hankali ya matsa gefe jiki ba
kw’ari.
Duk yan dinner sun shuga su Ammar
kadai ake jira, sai da su Ammar suka
d’au lokaci kafin suka fito Ahyan na rike
da hannu Kausar gsky sunyi ky’au.
Ammar yace”amana afuwa mun bata
muku lokaci. Murmush’i Ahyan yayi yace
“mush’iga kawai don lokaci na kara
tafiya. Ahayan da Kausar sune a gaba sai
Ammar da Zainab, tunda suka saka kafa
acikin hall d’in na saki baki ina k’alon
Amaren nan, gsky Allah yayi halita a gun
baran na bayannan wato Ammar da
Auta. Amrah ce ta zungureni kai Rash
wannan wani irin kalo ne kamar zaki
cimyesu, hmmm nace”My Amrah ke dai
bari kawai Amaren ne sun tafi dani sun
had’u sosai gsky sun dace da junansu.
High table din nake bi da kallo gefen
Ammar Auwal ne da Munay sai kujeran
kusa da su Jidda da Ghali(Haughal) na
gani, ko da na kali gefen Kausar
Raheenat da MY na gano sai wata kawar
kausar da saurayinta.
Kid’a ne ke tashi a gun ko ina ka duba
jama’a ne suke zaune kowa da
masoyinsa ga Mrs Umar ma da Sojanta
sai luv suke sha. ‘Daya daga cikin
abokan Angwaye ya bud’e taro da
addu’a, kafin aka soma gudanar ta
dinner sai da suka danci abun motsa
baki, aka umurci Amarya Kausar da
Angonta suka fara sauka kid’a aka sake
musu nan fa yan liki suka taso bayan
sun taka ne, aka umurci Zainab da
Ammar su fito, tunda aka kira sunasu
Auta ta lafe ajikin Ammar bata son
sauk’a, Ammar ya janyota jikinsa kai ka
dauka wani zai kw’aceta ita ko ta lafe
ajikinsa, cikim nutsuwa suke sauk’owa
abun gwanin burgewa ohoho masu
karatu naso ace kunje gun dinner nan
don duk lbr da zan baku na Ammar da
Auta zai d’auke mu lokaci mai tsawo.
Waka aka sake musu kan kace me yan
likin Ammar da Auta sum taso suka fara
musu har suka zo tsakiyar hall din, a
hankali Ammar ke ta kawa amma Auta
taki rawa ganin haka yasa ya kara
matsowa kusa da ita ya mata cakulkuli
aiko ta kw’ato jikinsa nan yafara ju-juya
ta, in ka gansu kw’a d’auka salon
soyyansu suke zubawa.
Haka tarin dinner ta kare cike da farin
ciki suka dawo gida, kyar Ammar ya bar
Zee tash’iga gd.
Taku a kullum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:01PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Hajiya Mamu taso akai amare yau Amma
dare yayi, haka ta hakura.
Da safe bayan sun karya ta zo d’akin
Amaren da kayan fruit ta basu da wani
abu kowacce cikin kofi d’aya, ni Rash
nace “ko miye wannan oho!?.
Haka suka yini Mum sai d’irka musu
abubuwa takeyi tun daya yamma ta
hada su a daki d’aya ta soma musu
nasiha gami da basu sirrikan saye
zuciyar miji.
Da dad’dare aka zo d’aukan Amare
sunsha kuka kam da ky’ar aka fita dasu,
kowacce akayi kaita gidanta.
Abokan Ahyan ne suka raka sh’i saida
suka dan tsokani Amarya, da yan
barkw’acin su kafin suka masu sallama
da fatan samun zuri’a na gari suka tafi,
nima fatan alkairi namusu nafito tare da
jan musu gate d’in gdn. Na nufi gidansu
Auta don inga wainar da ake toyawa ta.
Ina isa na tarar da Auwal ne da Saeed
suka rakash’i, nasiha sosai suka musu da
yan shawarwari kafin suka musu
sallama suka fito, Ammar ya musu
rakiya bai wani dad’e ba ya dawo gefen
Auta ya Auna tare da furta Alhamdulila!.
Agogon dake hannusa ya cire yace
Zainab kije kiyi alwala muyi nafila mu
gode ma Allah da wannan babban
ni’ima daya mana. Mikewa tayi ta nufi
toilet ta d’aro alwala bata dad’e da
fitowa ba shima ya fito suka suka tada
kabbara. Raka’a 2sukayi kafin ya dafa
kanta yasoma karanto addu’ar da in
mutum yayi Amarya ko sabon abu zaiyi
kafin yafara amfani da abun. Ga addu’ar
kamar haka”Allahummah inni as’aluka
khairi ha wa khaira ma jabaltaha alai,
wa ‘a’ uzubika min sharri ha wa sharri
majabalta ha alai”. Ma’anarsa sh’ine Ya
Allah ina rokonka Alkairinta da
d’abi’anta akansa, kuma ina neman tsari
da sharrinta da sharrin da ka
d’abi’antar ta akansa.( yan’uwa yana da
kyau mu runka yawaita yin wannan
addu’a yayin da mukayi sabon abu,
Addu’ar tana da matuakan amfani, Allah
yasa mudace Ameen).
Sai da ya gama karantawa tana amsawa
da Ameen har ya kai karshe, kitchen
yaje ya d’auko musu plate ya saka musu
kazan da fresh milk mai sanyi yasa musu
a kofi, Auta ta kasa sakin jikinta da sh’i,
naman ya d’auko yazo dai-dai bakin ta
ta kawar da fuska tana yar murmushi
kasa-kasa, cikin zolaya ya dawo ta gefen
da ta mayar fa fuskanta cike da tsokana
yace” Amarya yau kunyata kike ji?.
Uhmm ta fada tare da sake mayar da
guskanta ta d’aya barin mikewa yayi
cikin shauk’in so da kauna yace”baringa
ta ina zamu fara, ita ko sai zi-zilewa
takeyi.
Rash Kardam
[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Haka sukayi ta hiransu cikin
barkw’anci, Ammar ne ya mik’e ya yace
barin watsa ruwa d’akinsa ya nufa, Auta
ma ta mike taje tayi wanka mai ta shafa
sai man baki ta kw’anta ta lumshe
idonta tamkar mai bacci, Ammar ya
sh’igo cikin sh’irin kwanciya yayi ky’au,
ya tsaya k’are ma Auta kallo tayi ky’au
cikin kayan baccin, wani lalalusan
murmushi ya saki ya kashe musu wuta.
Ni Rash nace”oh! Wanan mirmush’in
kam yau na sam Auta sai ta gane
kurenta agun Ammar, bare mai nema ya
samu.
Da safe na leka gidan Zee Auta na tarar
tayi wanka Ammar ma ya shirya cikin
sh’iga mai ky’au, yazo dab da ita yace
my swt muje mu yi breakfast, cikin
shagwaba tace” ni ni sai tayi sh’iru, bai
tsaya kara sauraronta ba d’auketa kamar
wata baby sai dinning ya direta abaki
ya rinka bata abinci har sai da ya
tabbatar ta kosh’i tukun ya ky’aleta
sh’ima ya karya. Ammar da Zee soyayya
suke gudanarwa mai tsabta, basa son
ganin d’ayansu cikin damuwa komai
tare sukeyi in Ammar na gd.
Kw’aki sun ja, watani sun tafi, shekaru
da yawa sun shud’e, wani make-ken gida
na hango wanda ya tafi da hankali na,
ina tsaye ina kale-kale na hango wata
mota k’iran Toyota Camry 2016 blue
colour, ta sh’iga wannan gidan, da sauri
na da gudu yanda komai gadi ba zai iya
rik’eni ba bare ya hanani sh’iga gd, cikin
flowers na lab’e, motar ne ta karasa
sh’igowa ina kallo tayi parking a wajen
ajiye mota, duk na kagu in ga wacece
zata fito ta dad’e kafin ta bud’e k’ofar
motar, k’afarta ta fara sauko da su
Yasalam na furta, masu karatu sai kunga
kafar tamkar na Zee hrt tsaban kyau…
lol… A hankali ta k’arasa fitowa sai naga
wasu yara su biyu mata sun fito d’ayar
zata kai 10 yrs karamar kuma zata kai
7yrs yaran sun had’u kama, mai gadi ne
ya musu sannu da dawowa ta amsa da
sakin fuska, ta nufi cikin gd. Zarah ce
tayi nufi stairs tana kw’ala kira ma
nanny su k’ira, khairat kuwa dake suka
zube a falo ita da Mum d’inta.
Wani had’ad’en guy fa ba zai wuce 40yrs
ba ya sauko rike da hannun wani yaro
kamar su d’aya da sh’i sai a lokacin na
gane ko suwaye AMMAR da ZEE AUATA
da yaransu, duk ta canza ta k’ara ky’au
ta da girma.
Yazo kusa da ita ya zauna yace”Madam
kin dawo ya hanya? Alhamdulilah! Ya
kalleta kafin yace “My Luv ina son yau
zanje na taho da su Malam da Inna, don
an gama gyara gidan ansa komai aciki,
cikin jin dad’i tace” Abban zarah ka
ky’auta Allah ya kara bud’i Ameen,
Zainab Malam sun can-canci haka don
sun mana abunda bazamu manta ba,
tace” hakane kam ALKAIRI DANKO NE
book by Ummu Aisha, Baya tab’a
fad’uwa kasa bamza.
A ranar ya je ya taho dasu Malam da
Inna gd ya musu mai ky’au sunyi murna
sosai.
Taku a kullum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Alhaji Ammar Sa’ad Saraki ya dawo
hamshakin d’an kasuwa mai cike da
naira ya sanu ciki da wajen kasannan,
yana da company a yawancin State d’in
dake 9ja.
Jerin gwanon motoci na hango
sunyi com boys abun gwanin burgewa
number motar kuwa duk iri d’aya ne
ansa A S Saraki1 har zuwa 10 ya nufi
gdn sa, ko da ya shiga matarsa ceta taso
cikin shiga ta alfarma ta yi welcoming
d’insa, sai da ya huta yaci abinci ya
kaleta yace Madam kinyi ky’au kuma
kulum kara ky’au kikeyi, cikin salon da
ta saba rikita sh’i ta juya ido tace”kaima
haka sh’iyasa kulum nake k’ara sonka. A
natse ya kalleta yace”Zainab ku shirya
ke da yara tunda suna hutu nagama yi
mana booking din jirgi ran friday zamu
kaduna. Da sauri tazo ta run gumesa ko
mai ta tuna sai tafara zubar da hawaye
janyota yayi jikinsa yasoma lalash’inta
yace”nasan me kike ma kuka ki share
hawayenki yanzu ne lokacin da zamu
dau fansa.
A yanzu dum wani moving din Baba
Sani ina da lbr akansa kuma Baba Isya
ya rasu a razane ta d’ago amma tuna
abunda sukayi ma iyayenta cikim kasa-
kasa da murya tace”to yau ina Baba
Isiya yake gash’i ya tara da su Dad,
rayuwa ke nan duniya ba gurin
matabbata ba ne.
Tun ran Alhamis suka je gidan H
Mamu suka mata sallama tare da musu
fatan nasara daga gidan kuma suka nufi
gidansu Malam suma Addu’a suka musu.
Ran friday tun karfe 1:00pm aka
kaisu Airport basu dad’e ba jirginsu ya
d’aga sai KD, 1hrs ya kaisu cikin garin
KD, wani katafaren gd da Ammar ya
gina acikin garin kaduna suka sauk’a,
garin duk ya fawo ma Auta wani iri basu
fita ko ina ba sai washe gari suka sh’irya
cikin sh’iga ta alfarma da yan yarasu
uku Zarah ce baba sai mai bi mata
Kairat sai Al-hasan mai sunan Dad suna
kiransa da junior, yaran ky’awawa da su
gwanin burgewa. Motocin Ammar ne
suka jero zuwa k’ofar gdn. Ammar rik’e
da hannu junior sai Auta rik’e da hannu
Kairat suka sh’iga mota suka nufi Hayin
Rigasa.
Taku a kulum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Motoci ne a jere suka sh’iga layin duk
jama’ar dake unguwan sai lek’e sukeyi
don basu taba ganin motoci sun jero irin
haka ba, wasu kamma cewa suke yau
gwamna ya zo umguwansu, dai-dai
k’ofar gidan su Auta motar ta perker
body gurad d’insa ne suka fito sai da
suka rarrabu a gun kafin aka bude ma
Ammar k’ofar motan ya fito, zagawa
yayi ya bud’e ma Zee sai yara suka fito
daga motarsu, duk yan gurin ba wanda
ya shaidasu sai dai sunga ansa AS Saraki
a jikin motar kuma suna jin lbrsa. Baba
sani dake sh’irin fitowa yaga mota a
k’ofar gd sa tabbas yana jin lbr AS
Saraki k’odai mafarki yakeyi ne kam ya
san ba abunda zai kawosa gidan.
Ammar ya mika masa hannu suka gaisa
yace ka sai dani kuwa Baba Sani da yayi
mutuwar tsaye yace”Eh! A S Saraki da
nake jin lbrsa ne ko? Ammar yayi
murmushin kasaita yace”kw’arai kuwa
nine, mush’iga daga ciki falo su Auta aka
sh’iga da su sai da aka kawo musu kayan
shaye-shaye sam Baba Sani bai ganesu
ba, sabida shekaru sun tafi da yawa ga
naira ya zauna musu, Ammar ganin bai
ganesa ba yace wata kasuwanci ne nake
so muyi da kai, na samu lbrka gurin
wani yaron ka mai suna Gumus, ya yaba
da kai sh’iyasa naji ka kwantamin a rai
da mu had’a business, sun d’anyi hira
kafin yamasa sallama ya rako su har
bakin mota saida suka sh’iga ya kima gd
cike da murna tabbas tsun-tsu daga sama
gashashe, nikam Rash nace”wato mai
hali baya fasa halinsa a ko ina yake”.
Sun d’ansoma tafiya kenan sai ga motar
Futha ya danno kai dake glass gin ta fari
ne Ammar yasa aka dakatar da ita sam
Auta bata lura da itaba sai da yace
mata”Sweet kali can aiko ta kalo futa
zata fita da gudu ya riketa yace zaki
wargaza mana plan d’in mu Short note
yayi ya bama body gurad d’inda ya bata,
ko da ta karanta ta bud’e murfin mota
da sauri ta fito Ammar ya rage glass d’in
motar sa tabbas sune ba gizo suke mata
ba. Ammar yace kin gane a kw’ai Adress
din mu so kizo ki same mu anan plan
d’in mu zai iya wargajewa ok! Motar ta
takoma cike da murna tana gode ma
Allah da ya bayya na mata su Zee dinta
Da yamma Barrister Futha ta nufi gd su
Ammar ko da taje sunyi murna ita da
Zee sannan suka bama juna lbr bayan
rabo Futha cikin mamaki tace”no
wonder biri yayi kama da mutum dom
na dad’e ina zarginsa kam nan ta ce bari
na sanar da Sadiya don baza a rasa
wani evidence a gunta ba, ringing biyi
yayi ta d’auka sun gaisa futha ta bata lbr
komai cikin murna tace”Futha suna ina
nan ta bata Address d’in gidan bata
dad’e bakuwa ta iso sun gaisa itama aka
bata lbr taci kuka jin Babanta ke da
hannu kuma ta d’au alwansh’i basu
goyon baya don a kamash’i, Futha
tace”yau weekend ne bazaiyu ayi
karansa ba amma zuwa Monday sai ayi
yanzu dai Ammar duk abun zai zama a
hannuka ne duk yanda za’ayi kar kabari
ya bar gari ko ya ganeka ok! Haka suka
watse.
Yau monday duk wani ma’aikaci ya
fita aiki, yau ne su Ammar suka kai
karan Baba Sani, police har gd sa suka je
aka kamasa C.I.D aka kaisa, ba irin
wahalar da ba’a masa ba ama fir yak’i
fad’ar gsky harranan sh’iga kotu, kowa
ya hallara a koto, mai gabatar da kara
ya tashi ya koro bayani ba alkali,
barrister Futha ta fito ta gaida alkali
kafin ta soma yan tambayoyi ma Baba
Sani amma fir yak’i yarda da sh’i yayi,
rashin wata kw’akw’aran shaida aka
d’aga karan har sai 5/3/2016 haka aka
watse amma kotu ta hana belin Baba
Sani har sai ansamu gsky.
Taku a kullum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Yau takama ranar da za’a koma kotu,tun
da wuri su Futha suka hallara don su
had’a shaidar da Ammar yace ya samu
amma shiru bash’i ba lbr sa, sai dab da
za’a sh’iga ya k’araso gunsu jiki ba
kw’ari ya iso Futha cikin damuwa ta
ce”ya dai ina fatan ansamu nasara.
Ammar yace”wa yanda zasu taho da su
gumus da Duna da su baba mai gadi na
kira wayarsu a kashe kuma bawani lbr,
wani iska mai zafi ta furzar tace”ga
Sady sh’iru itama bata iso ba, dai-dai
lokacin aka sh’iga kotu mai gabatar da
kara ya karanto kara da akeyi, lauyan
mai kara ta fito bayan ta gabatar da
sunan ta ta zauna, lauyan mai kariya
sh’ima ya gabatar da sunansa, nan aka
nemi mai kara ta gabatar da shai du, sh’i
alkali ya ce”rash’in wata gamsash’iyar
shaida kotu zata… Bai karaba Sady
tash’igo cikin hanzari tace ranka
sh’idade akw’ai shaida a tare da ni,
gabad’aya aka juya ana kalonta, a
hankali ta zo gaban mutane d’auke da
wata envelope ta mika wa Alkali ta sake
bash’i wasu kaya tace”ranka sh’i dad’e
ni d’iyar wacce ake kara ne, sanan bin
ciken danayi, na samo wad’anan kayan
da su akayi amfani gurin kashe Alhaji
Al-hassan da Matarsa sanan hatta
bindigar da akayi kisar akw’ai sanna
akw’ai ta kardan da sukayi tsakani
mahaifina da Marigayi Baba Isiya akan
zasu raba dukiyar Mahaifin Auta. Wayar
Ammar ne yayi k’ara yana dubawa yaga
number Kabir ne da sauri ya d’agawa
yace kana ina? “Gani a k’ofar kotu muna
tare da su gaba d’aya, right! Sai da ya
nimi permission ya sai dama Futha ga
sunan azo dasu, batare da bata likaci ba
ta sanar da alkali ga wasu saidan ma an
taho dasu, nan ta bukaci a had’a ta da
police suka fita aka sh’igo dasu, Baba
sani ya cika da tsanani mamakin gani su
Gumus Da Duna da Masu aikin gdn, nan
aka gatar da su, alkali ya ce”bisa ga
kw’araran shaidar da aka samu na Sani
da laifin kashe d’anuwansa da Matarsa,
kotu ta yanke masa hukun d’aurin rai da
rai, alkali ya mike kafin sauran mutane
suka fito, Auta rungume Sady tayi tana
kuka irin wanna jahadin da tayi, suna
fitowa daga kotu gidansu Futha suka
nufa sai da suka ci abinci tukun Auta
suka koma gdsu.
Auta bata bar garin kaduna ba saida ta
raba ma Matar Baba isiya da Su Sady
sauran duk’iyarta ta mallaka musu don
su samu abun rayuwa, cike da farin ciki
suka dawo Bauchi Ammar ya kalli Auta
yace”Alhamdulilah! Yau na sauke nauyi
da nayi ma kaina alkawari shekara da
shekaru.
Taku a kullum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam:
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Zaune suke a falo Zee Auta sai zuba
shagwaba take wa Ammar ko sai biye
mata yakeyi, junior ne ya biyo Khaira ta
d’aukar masa yar babynsa da gudu, suka
sauko falo, ya kasa kamata sai yaje gun
Ammar da yar kukan shagwaba
yace”Dad kaga Khairat ta d’aukan YAR
AMANA TA Ammar yayi dariya kafin ya
karbi Teddy ya basa, yace” kema zan
sanyo miki naki, da murna tace” thanks
u My Sweet Dad luv u too, junior ya kalli
Ammar yace” Dad kaifa ina YAR AMAN
KA?. Cike da fara’a ya nuno musu
Mummy su, da gudu suka haura sama,
sh’ikuma yazo ya d’auki Auta kamar
yarinya yana ju-juyata yace” ina kara
sonki ko da yaushe yarinya kike k’ara
dawowa, kw’ayar idonta ya kalla yace”
sh’iya sa nake kara tattala AMANA TA
CE.
Alhamdulilah!! Tsarki da mulki iko su
tabbata ga Ubangijin Talikai,
Ina mika godia ta ga Allah(S.W.T.A) da
yabani damar na kawo k’arshen littafina
mai sunan AMANA TA CE.
Yan’uwa ina fatan zaku d’au darasin da
ke cikin wannan littafin, ko da yaushe
mukasance masu kula da zumunci,
hadisi ne guda ankarbo daga (musulum
ya karbo daga manzon Allah tsira da
aminci Allah su tabbata a garesh’i
yace”la yadakulul jannati khad’i’u
rahimi, mai yanke zumunta bazai shiga
Aljannah ba” ya Yan’uwa kusani
Zumunci da Amana suna gefen siradi
duk wanda ya yanke daya acikinsu
kugiyace zata jash’i zuwa wuta). Sanna
kuma duk wanda yayi riko da Zumunci
da Amana to zaiga sakamako mai ky’au,
yana da ky’au muna tarayya da mutanen
kw’arai sanna nu neman tsari da
shaid’an don harda sh’i yake in gizamu
zuwa aikata ba dai-dai ba.
Gareku mata masu zuwa gurin boka ko
Malam tsubbu hakan baida amfani sai
tarin zunubi, ku sani duk wanda yaje
gun boka Allah bazai karbi Sallah sa ba
na kw’ana 40 sanan Mala’iku suna tsine
mata, Ya Allah kasa mu fi k’arfin
zuciyan mu Ameen.
IYAYENA ABIN ALFARINA
Iyayena abun alfarina jin-jina da godia
ta musamman gareku
Alhaji Abdullahi Garba Kardam da
Hajiya Khadija Aliyu Abdullahi.
SADAUKARWA
na sadaukar da wannan littafin gareku
Zainab Al-hassan(Autar Hajiya)
Maryam Alkali(Mermu)
Kausar Luv
Zee hrt
 Nucceyluff
Bilkisu Sildibe(Futha)
Fatima(Falmi)
Fulani Cerdiya
Munay
Sadiya A Dahiru
Maman Abideen
K’AWAYE NA KUNA RAINA
Aunty Zainab,Dijah Tahir,Afrah Luu,
Queen Memie,Hauwa A Shehu
(jiddah),Maman Safwan,Nana Fiddausu,
Indiana Fidy, Maman Khairat, Maman
Abideen,Amrah,Mrs Ak,Myer,
Najaat,Haugal,Cutie, Swt Fauxie,Zeenur,
Xarah BB,Bebaloo, Zahra,Maman
Fawaz,Nana Dizo, Hasna Idris.
Da duk sauran wanda ban samu rubuto
sunansu ba.
KUNFI KOWA SON LITTAFINA
Mrs Abdul, Farhat B Haske, Aliyu
Haiydar Hajiya Jamila, Khadijat
Khadijat, Bilkisu lame, Rahma S Musa,
da sauran wanda ban samu damar jero
suba.
GODIYA MAI TARIN YAWA GA YAN
GROUPS DINa
ZAUJIN NUHR
RASH KARDAM HAUSA NOVELS
1&2
MURMUE HOME OF NOVELS
EXTREME HAUSA WRITTERS
WISDOM HAUSA WRITER’S
BEST HAUSA WRITERS GROUP
DUNIYAR LITTAFIN HAUSA
HAUSA NOVEL GROUPS
KHALEESAT HAIYDAR NOVEL GROUP
FB.
Godiya ta musamman ga masoyan
littafina, sai mun had’u a sabon littafina.
Taku a kullum mai k’aunar ku
Rash Kardam
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
        (admin
       Novels villa
     Duniyan novels 
   Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
          And 
Cool novel, makeup and cooking) 

      WHATSAPP NO:
    +2347039625239
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top