Malala Yousafzai: “Ban fahimci aure ba sai da na shiga ɗakin miji”
Malala ta kira ranar aurenta da mai muhimmanci a rayuwar ta
ASALIN HOTON,MALIN FEHEZAI
Bayanan hoto, Malala da angonta Asser |
Kasa da mako guda da yin aurenta, fitacciyar mai fafutika kan ilimin ‘ya’ya mata kuma wadda ta dauki kyautar Nobel ta zaman lafiya, Malala Yousafzai, ta bayyana cewa a baya ta yi wa aure mummunan fahimta, kamar yadda ta shaidawa mujallar Vogue ta Birtaniya.
A wata hira da shirin Andrew Marr na BBC, matashiyar mai shekara 24, ‘yar asalin Pakistan, ta ce da gaske ne ta damu matuka, kan halin da ‘yan mata ke fuskanta a sassa daban-daban na duniya na auren wuri.
Mai gabatar da shirin ya fara ne da taya Malala murnar auren da ta yi a makon da ya wuce, daga nan ya jefo mata tambayar abin da ya sauya tunanin ta akan aure, alhalin a baya tana adawa da shi?
Sai Malala ta kada baki ta ce; ”Ba na adawa da aure, na dai damu ne da yadda ake yin auren, da abin da yara mata da aka yi wa aure cikin kankantar shekaru ke gani, da auren dole, da halin da suke fuskanta bayan mutuwar auren, da kuma rashin daidaito tsakanin miji da mata na matukar daga min hankali.
Sannan rawar da al’ada ke takawa kan matan da suka samu kansu a irin wannan halin ita ma abin dubawa ce.”
Malala Yousafzai ta zama amarya
An zabi Malala sakatariyar jin dadin dalibai a jami’ar Oxford
Sai dai Malala ta ce a gare ta lamarin ba haka ya ke ba, kamar yadda ta ce ”ta yi matukar sa’a”, ta samu abokin rayuwa (mijinta) da ya fahimce ta da amincewa ta ci gaba da gwagwarmayar da ta ke yi kan ‘yancin ‘ya’ya mata.
A baya dai Malala ta bayyana karara ba ta goyon bayan aure. A wata hira da mujallar Vogue a watan Yuli Malala ta jaddada cewa; “Har yanzu, na kasa gane dalilin da ya sa mutane ke yin aure.”
“Idan kana son rayuwa tare da wani mutum, me ye dalilin da dole sai an yi a rubutu, me ya sa ba za ku yi zamanku a matsayin abokan rayuwa ba? Mahaifiyata ta taba daka min tsawa, tare da cewa; kada ki sake fadar haka! Dole ne ki yi aure, aure abu ne mai ban sha’awa”.
Samun labarain aurenta ya yi matukar kada wata guguwa a shafukn sada zumunta musamman Tiwita, inda dubban mutane suka dinga ta aiko da sakon taya murna ga sabbin ma’auratan.
Cikin wadanda suka taya Malala murnar auren har da Firaministan Canada Justin Trudeau, da Jemima Goldsmith da Sajid Javid.
Mijinta Asser Mlik fitaccen dan wasan Kurket ne, wanda yake rike da mukamin babban Manajan hukumar Kurket ta Pakistan (PCB).
Matashiyar mai shekara 24, ta sanar da auren nata a shafinta na Tuwita, inda ta ce ita da iyalanta sun gudanar da dan karamin bikin auren a gidansu da ke birnin Birmingham a Birtaniya.
Ta shaida wa kusan masu bibiyarta a shafin kusan miliyan biyu cewa ”wannan rana ce mai cike da farin ciki a rayuwata,” inda ta bayyana sunan mijin nata Asser.
A shekarar 2012 ne Malala ta samu mafaka a Birtaniya, bayan harbin da mayakan Taliban suka yi mata akan hanyar su ta zuwa makaranta.
Source bbchausa