Buri Na Idan Na Kammala Karatu, In Zama Matuƙiyar Jirgin Sama, Cewar Khadijatul Iman Sani Danja

Buri Na Idan Na Kammala Karatu, In Zama Matuƙiyar Jirgin Sama, Cewar Khadijatul Iman Sani Danja

Masu magana sun ce Kyan da ya gaji uban sa, to lallai za a iya cewa Hakan ta kasance a farkon rayuwar Khadijatul Iman Sani Danja, wadda take ‘ya ce ga fitaccen Jarumi Sani Danja da Kuma Mansurah Isah.

Domin kuwa tun tana shekaru biyu a duniya ta fara yin fim wanda mahafinta ya shirya Mata fim Mai sunan ta Khadijatul Iman, Kuma tun daga lokacin a ke saka ta a fim lokaci zuwa lokaci. Kuma finafinan da ta yi na baya bayan nan su ne Akhila, Sai Kuma sabon fim din da ya fito a wannan lokacin wato Fanan, wanda ta taka muhimmiyar rawa a cikin fim din.

 

 

Majiyar Blueink News Hausa Ta Jaridar Dimukaradiyya ta nemi jin ta bakin ta a game da yadda ta dauki harkar fim, in da ta ke cewa.

“To ai ni harkar fim a jina na take tun da uwata da uba na duk ‘Yan fim ne don haka Ina alfahari da fim, Kuma na taso a cikin sa tun Ina karama na ke yin fim.

 

Kuma Alhamdulillahi da ya ke iyayena su na kula da ni wajen karatu Hakan bai sa na yi wasa da karatu ba, don haka na fi mayar da hankali na wajen karatu Don haka ma ba a gani na sosai a cikin fim din, a yanzu ne dai da mahafiya ta ta shirya fim din Akhila da Fanan, to sai ya zama Ina ciki Amma dai fim din da na ke yi ba ya taba karatun da na ke yi, don su ma ba sa son duk wata harka da za ta taba mini karatun”.

Ko da muka tambaye ta wanne buri take da shi idan ta kammala karatun?

Sai ta ce “Ina son idan na kammala karatu na yi aikin tukin jirgin sama Don shi na ke Sha’awa, don haka babban burina kenan, Ina fatan Allah ya ba ni nasara a Kan karatuna da na ke yi a yanzu.”

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top