Fuskantar damuwa; Bambancin da ke tsakanin Mace da Namiji
A yayin da dan adam ya shiga cikin wata damuwa wacce ta dunguzuma tunaninsa, yakan bi hanyar da yake ganin ita ce mafita a gare shi domin domin samun mafita. Mace akwai salon da take bi domin tunkarar damuwarta, haka ma namiji shi ma akwai hanyar da yake bi domin tunkarar damuwarsa.
Ita mace a duk sadda aka bata mata rai, to babban abunda take buqata daga wajen mijinta, Danta, saurayinta, Dan uwanta, shi ne ya zauna ya saurare ta ta bashi labarin wanda ya bata mata rai, bayan ya saurare ta qila ma ba sai ya ba ta hakuri ba, da kan ta ma za ta ce, “na amayar na huta.”😃😃Da zaran an qi saurararta, sai ta shiga damuwar cewa wai ba a son ta ne ko ba a ba ta kulawa hakan ya sa aka ki yin zaman dirshan domin ta bayyana wadanda suka bata mata rai.
Shi kuma namiji a duk sadda ya shiga damuwa to fa a Duniyar halittarsa ya fi son kadaici, da qaranta magana. A duk sadda Mamarsa, Matarsa, ‘yar uwarsa za ta nemi jin damuwarsa, amsar daya ce,”Babu komai”.A lokacin sai a ga ya kunna Talabijin ko Rediyo,ko ya dauko Jarida,ko ya dauko littafin karatu,ko ya bar gidan,ko ya tafi Filin qwallo domin kallo,a nan ne damuwarsa yakan sami saukin damuwarsa
Wannan hikimar Allah ce da ya halicci mace da namiji sannan ya hada su rayuwa a muhalli guda, kuma rayuwar daya ba ta kammaluwa sai da dayan.
Allah ya sa mu dace, Ameen ya Rabbi.