Fuskar Dan sandar da yake bin Y’an kasuwa a Kano yana amshe masu kudi

 Fuskar Dan sandar da yake bin Y’an kasuwa a Kano yana amshe masu kudi

Dan sanda a kano mai suna Friday, da yake bin yan kasuwa yana amshe masu makudan kudade kamar yadda rahotonni suka tabbatar da hakan. 

Ta hanyar zuwa da wani informer na yan sanda a matsayin wai barawo ne, idan Suka shigo kasuwa kawai sai ya nuna mai tsautsayi a tafi dashi sashen binciken yan fashi na tsohuwar SARS a rufe sai yan uwansa sun biya  a kalla #100,000,#200,000 harma #400,000 kafin a sake shi.

Ranar litinin da ta gabata Dan jaridar nan na freedom rediyo mai yin Shirin Inda ranka yayi batun tare da tattaunawa da victims din, abin mamaki washe gari talata mutane su kayi ta tururuwa zuwa freedom domin shigar da rahoto akan shi wannan the same Friday din.

A halin da ake ciki wannan babbar matsalace, domin duka abinda ke faruwa a North West yana da alaka da zaluncin hukuma.

Maganar da nake daku yanzu haka Friday yana yawansa cikin garin kano kuma harma yana neman Nasiru Salisu Zango domin ya kashe shi sabida ya ambata da bakinsa cewa Nasiru yayi programme din karshe kuma harma an nadi muryarsa yayin da yake furucin.

Shin wai Ina gwamnatin Kano Ina malamai da sarakuna ko kuma kawai su kwacen zabe Suka iya.

Maganar da nake a yanzu hakan akwai matasan dake shirin yin zanga-zanga a jihar kuma fa ba wai yan jagaliya bane utane ne na gari nutsatstsu kuma masu ilimi zamani da addini.

Muna fata gwamnati zata duba ta tabbatar an hukunta Friday domin zaman lafiyar kowa. 

Source: Alfijir Hausa 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top