Gaskyiyar Magana Dangane da komawar Tsohuwar Jarumar Kannywood a Masana’antar Ta Kannywood

 Gaskyiyar Magana Dangane da komawar Tsohuwar Jarumar Kannywood a Masana’antar Ta Kannywood 

Bayan bayyanar hotunan jaruma Rahama Sadau sanye da kayan Fulani tare da sauran manyan jarumai kamar Sani Musa Danja, Magaji Mijinyawa da Rabiu Daushe, da dama sun dinga sa alamar tambaya akai.

Tashar tsakar gida ta bayyana yadda ganin hotunan jarumar yayin da ake daukar finafinan barkwanci, Gambo da Sambo a garin Gombe ya janyo surutai.

Ganin jarumar yayin da ake daukar wannan shirin ya sa idanu su ka koma kan Kannywood inda ake ta tambayar shin Rahama Sadau ta dawo Kannywood ne?

Ganin ana daukar shirin a wata jiha daga cikin jihohin arewa kuma tare da manyan jaruman ya sa mutane su ka dinga cece-kuce da gutsiri tsoma inda wasu ke tambayar ko ta koma Kannywood ne?

Kowa ya san abinda ya faru da jarumar a shekarar da ta gabata inda ta wallafa wani kaya da su ka bayyana tsiraicin ta.

Lamarin ya janyo surutai har wani makiyin Allah ya yi suka ga ma’aiki a karkashin wallafar da ta yi wanda jama’a su ka yi ca akan ta.

Jarumar ta amsa laifinta inda ta ce ita ce sanadi har ta yi bidiyo cike da nadama ta na neman yafiya daga daukacin musulmai.

Hakan ya kai ga kungiyar mashirya fina-finai ta kasa ta MOPPAN sun bayar da sanarwar dakatar da ita a karo na biyu.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a rubuce da ta bayyana an janye dakatar da jarumar ko kuma makamancin hakan ita ma jarumar ba a sake ganinta a wani shirin Kannywood ba tun bayan nan.

Har wani shiri da ta ke yi mai dogon zango na ‘yar minista ma ta dakatar da shi gabadaya. Amma bayan nan jarumar ta ci gaba da fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood inda ta fito a wani shiri mai dogon zango na The Plan.

Sannan jarumar ta samu ketarawa kasar Indiya inda aka dauki shirin Khuda Hafeez. Sai dai a wannan karon an gan ta a garin Gombe.

Bayan bincike an gano cewa shirin ba na ‘yan Kannywood bane, shirin wani mai shirya fina-finai ne a kudancin Najeriya Dimbo Atiya wanda ya shirya shirin Sons of the Caliphate.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top