Jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsen-ma, a jihar Katsina, ta Amince da maki 130 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga Jami’ar a wannan shekarar

 FEDERAL UNIVERSITY DUTSIN-MA, KATSINA STATE

  Jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsen-ma, a jihar Katsina, ta Amince da maki 130 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga Jami’ar a wannan shekarar, Ga Ɗaliban da suka sanya Jami’ar a matsayin zaɓinsu na farko (First Choice), inda ta buƙaci ɗaukacin ɗaliban da suka nemi jami’ar ta tsarin UTME da su yi rijistar Post-UTME ɗin makarantar, wacce za’a fara daga ranar 15 ga watan Nuwamba mai kamawa, yayin da za’a rufe a ranar 19 ga watan, Haka zalika su ma ɗaliban da suka nemi jami’ar ta tsarin shiga kaitsaye wato DE, ana buƙatar suyi rijistar Online Screening a cikin wannan wa’adin.

  Bayan haka, ga ɗaliban da suka nemi makarantar  ta tsarin jarrabawar UTME, akwai wasu kwasa-kwasai da makarantar ta ware cewar sai ɗalibi ya samu maki 150 zuwa sama kafin ya cike su, waɗannan courses ɗin kuwa su ne :

•Microbiology

•Dukkannin kwasa-kwasan da suke tsangayar Kimiyyar kula da lafiya (Health Science)

•Kimiyyar Siyasa (Political Science)

•Sociology

•Accounting

•Economics & Development Studies

•Biochemistry & Molecular Biology

•Library and Information Science

•Law

•Sai kuma dukkannin kwasa-kwasan da suke tsangayar Injiniyanci (Engineering).

  Sannan ga Ɗaliban DE wajibi ne ya kasance ɗalibi yana da aƙalla Lower Credit a sakamakonsa na Diploma, ko kuma mafi ƙaranci Point 9 ga waɗanda suka yi NCE, Sannan akwai dama ga ɗaliban da suke da Point 6 a sakamakon su na IJMB.

    Allah ya bada Nasara

Daga : Miftahu Ahmad Panda (PRO ASOF ONLINE JAMB ORIENTATION COMMITTEE).

 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top