Jaruma Maryam Wazeery Wacce Akafi Sani Da Laila A Cikin Shirin LABARINA Ta Amarce A Ranar
Inda Jarumar Tayi Auren Bazata, Ba Wanda Ya Sani Sai Lokaci Guda.
An Sami Sanarwar Auren Nata Ne Bayan Da Shugaban Kamfanin Saira Movies Yayi Sanarwa A Shafinsa Na Sada Zumunta Inda Yayi Sanarwa Kamar Haka
A madadina da Kamfanin @sairamoviestv Muna taya “Yar uwa @maryamwazeery Murnar Auren da tayi a yau. Allah ya basu zaman Lafiya, Allah kuma ya basu zuriya dayyiba 🙏 congratulations 🍾🎉🎊🎈 muna missing din ki LAILA 🙌 #LABARINA
Ba Yau Jaruman KannyWood Su Fara Irin Wannan Auren Ba Na Lokaci Daya. Ko A Baya Bayan Nan Jaruma Zahra Diamond Itama Tayi Irin Wannan Auren Na Lokaci Guda. Sai Kuma Rahama MK. Wacce Akafi Sani Da Hajiya Rabi Bawa Mai Kada Itama Ta Amarce Na Sirri.
Muma Muna Fatan Allah Ya Bata Zanan Lafiya Ya Kuma Albarkace Auren Nata Da Tayi. Amin