Jarumar shirin Labarina Nafisa Abdullahi ta bayyana abin daya haddasa rigimar su da abokiyar ta Hadiza gabon
Ficacciyar jarumar masana’antar kannywood wanda take taka rawar gani a cikin shirin nan mai dogon zango wato Labarin, ta bayyana dalilin da yasa a kwanakin bayan sukayi rigima da abokiyar sana’ar ta Hadiza gabon.
kamar yadda kowa ya sani Nafisa Abdullahi jaruma ce wacce tayi fice a masana’antar shirya fina-finai ta kannywood tun shekarun baya har kawo yanzu, wanda ya yanzu tauraruwar jarumar take kara haskakawa.
A lokacin da ake tattaunawa da jaruma Nafisa Abdullahi a shirar da aka yi da ita ta bayyana cewa, dama tun asali babu wata alaka mai karfi tsakanin ta da abokiyar sana’ar ta wato jaruma Hadiza gabon, sannan kuma tace ko sada zumunci basa yi ta hanyar yin chating.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta kara da cewa: Akwai jarumai da dama a masana’antar kannywood wanda suke zaman lafiya da su, amma duk a haka basa sada zumunci kamar yadda basa yi da Hadiza gabon.
Nafisa Abdullahi tayi cikekken bayani sosai a lokacin da ake tattaunawa da ita akan abinda ya haddasa rigimar su da abokiyar sana’ar tata jaruma Hadiza gabon.