Kotu Ta Tura Shararren Dan Wasan Barkwanci Shagiri Girbau Kidan Kaso

Kotu Ta Tura Shararren Dan Wasan Barkwanci Shagiri Girbau Kidan Kaso 

 Wata kotu a Kano ta Bada Umanrnin tsare mai yin barkwancin nan a kafafan sada zumunta na soshiyal mediya wanda ake wa lakabi da Shagirigirbau. 

Kutun ta Bada umarnin a tsare shi a gidan gyara halinka har zuwa ranar 8 ga watan da muke ciki inda za ta yi zama don sauraron kararsa da gwamnatin jihar Kano tayi. 

‘Yan sanda sun kama Shagirigirbau ne aka kuma kai shi kotu bayan wani bidiyo da yayi wanda gwamnatin tace yayi shi ne akan Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da wasu mukarabban gwamnatinsa su biyu. 

Bidiyon da Shagirigirbau yayi ya karade kafafan sada zumunta na soshiyar midiya inda yake cewa a dai na kiransa ‘Mista Man’. 

Shagiri Girbau dai ya kasance Aminin Ali Artwork wanda yake siyasar madugu Kwankwaso, wanda anasaran Wannan abun nada alaka da siyasa.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top