Maganar Gaskiya Muna Bukatar Aure – Rashida Mai Sa’a shugaban Zawarawan kannywood

 Maganar Gaskiya Muna Bukatar Aure – Rashida Mai Sa’a shugaban Zawarawan kannywood

Tsohuwar jaruma a Masana’antar fina-finai ta kannywwod, Rashida Adamu Abdullahi, wadda aka fi Sani da Rashida Mai Sa’a, ta yi yekuwar neman mijin aure ga duk wanda ya shirya auren su ya zo sun shirya.

Jarumar ta Kara jaddada maganar ta ne bayan wadda ta yi a shafukan ta a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, in da ta ke cewa.

“Jama’a su Sani ni Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a da kawaye na su Hadiza Kabara da Teemah Yola da Jamila Nagudu, duk cikakkun Zaurawa ne idan akwai Mai son wata a cikin mu to ya fito mun shirya, Kuma zan tsaya Wa mashi, a matsayina ta shugabar su, don haka idan har da mai bukatar auren mu, to ya fito mun shirya”.

Ganin cewar a na yi wa maganar ta kallon kamar da wasa take yi don haka ba Lallai ba ne a samu wanda zai Taya din, Sai ta ce:

“Babu maganar wasa in dai mutum ya shirya to ya same ni duk wadda ya ke so a cikin mu idan an daidaita abin ba zai zo da wahala ba, don haka maza kada su dauka da wasa mu ke yi, mun shirya auren ga duk wanda ya shirya zai auren mu, in dai da gaske ya ke yi. “

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top