Miji ɗaya zamu aura nida ƙawata duk wanda ba zai haɗamu ba sai ya haƙura—Zainab da Ummie

 Mata Adon GariMiji ɗaya zamu aura nida ƙawata duk wanda ba zai haɗamu ba sai ya haƙura—Zainab da Ummie

Wasu ƴan mata guda biyu masu suns Ummie da Zainab waɗanda aminan juna ne sun taso tun yarinta kuma sun rayu a tare, sun bayyana cewa miji ɗaya zasu aura a shafukan su na sada zumunta.

Karancin mazajen aure na daga cikin manyan kalubale da yanmata ke fuskanta a wannan zamanin.

Idan zamu waiwaya watan Ramadan daya gabata, yawancin addu’a da yanmata suka gabatar kuma suka nema ayi musu shine samun abokin zama na aure.

Hakan kuma zai sanya zukatanmu tunanin lokacin iyayenmu shin akwai irin wannan qarancin mazajen auren? Ko kuma lokacin nasu akwai yawaitan mazaje sama da mata ne? Ko kuma yawaitan mazajen da matan suna kunnen doki? Kada muyi tunanin hakan. Wataqila wancaan lokacin mata sunada qima da kuma daraja yadda aka tarbiyan tar dasu domin a gina gida dasu bawai a shiga ginanne gida dasu ba.

 

A wancaan lokacin, da zarar matashi ya kai aure kuma zai iya ciyarda kanshi da matar shi, sai yafara neman aure, kuma tabbass macen dayake aura takan taimaka mishi gaya wajen gina future dinshi.

Abinda nake qoqarin isarwa anan shine: yanmata da kansu suka kirkiri “KARANCIN MAZAJEN AURE”.

Yau abun ya canja zani ya rikide yazama wani abun daban. Kasamu yarinya matashiya 13-16 years ka tambayeta wani irin Miji takeso ta aura? Zakaji abubuwa kamar haka: “Dole yazama dogo ne mai fadin kirgi, kyakkyawa mai kudi kalan zuwa unguwa, yanada motar hawa da kuma gida, wanda zai iya nuna shi a ko ina nace shine mijina. Sannan daga bisani kaje ta hada da: “Kuma mai tsoron Allah” wai don kada ace tanason duniya.

 

Idan kayi wannan bincike ka samu wannan amsar, saika duba unguwarku kaga samari nawa ne suka cika wadannan sharuda, anan zakaga matsalar.

Zakaji yanmata suna cewa: “bazai yiyu nasha wahala a gidan Ubana ba kuma naje gidan wani gardi inashan wahala”. Hankali irin na tinkiya kenan.

Yake Yar’uwa! Idan daga farko kinyi auren komai na tafiya daidai sannan daga bisani kuma duniya tawa Mijin naki daurin tomtom? guduwa zakiyi kenan?.

Babu wanda ke fatan shan wahala, ammana zaifi dadi a fara da wuya daga bisani aji dadi, sai yazamana anyi karshe mai kyau.

Matsalar kuma shine: irin yadda yara mata ke kwatanta irin mazajen da zasu aura kusan duk daya ne.

Idan yanmata 50 suna muradin auren irin wannan miji daya cika sharuda, sannan kuma namijin daya cika wadannan sharuda nasu 1 ne kacaal, kuma namijin mace 1 zai dauka a cikinsu, toh sauran yanmata 49 din yaya kenan?

Nanfa zakaji sunfara lamenting: “KARANCIN MAZAJEN AURE”.

Wani abun dubawa kuma a wannan zamanin namu shine: zaiyi matuqar wahala saboda yanayin tattalin arzikin kasarmu kasamu matashi mai matsakaitan shekaru da baiyi aure ba da wadannan sharudan da yanmatan yanxu ke so..

Idan zaka lura, yawancin yanmata masu niyyar aure sunyi aure domin basuda buri illa miji nagari dazasu aura su gina gida tare dashi.

Hanya daya da zakibi kisamu mijin aure shine cikin wassu sharuda dakika gindaya na irin Mijin dakike so.

Shifa Mijin aure, mutum ne da Allah Ya halitta kuma aka halicci mace daga gareshi domin tallafa mishi da cikamar martabar shi.

Yakamata Yanmatan zamani su gane cewa: “AURE BAWANI SHIRI BANE NA RAGE RADADIN FATARA”.

Aure ibada ce, hanyace ta bautar Ubangiji. Wadanda suka dauki aure a matsayin wata hanyar ficewa daga talauci, suke shiga damuwa.

Mata sune masu gina gidaje, bawai masu duma gidaje ba.

Yar’uwa kada ki rude ki dauka hanyar da namiji ke kai yanxu yatace qaddararsa, a’a wannan hanyar dakika ganshi a kai yau wataqila hanyace da Ubangiji Ya nufa zaibi kafin ya kai ga qaddararshi.

Wani abun kuma shine baki san ko cewa qaddar tashi tare zaku isa wajen ba, meye zai hana duk wanda kika aminta dashi da dabi’unsa da addininshi ki dauke shi a matsayin mijin auren ki?

Ya Ubangiji Ka ganar da yanmata sune ke janyowa kansu karancin mazajen aure ba wassu ba, Ka kuma hada maso buqatar auren da mazajen nagartattu.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top