Shahararriyar mawakiya Di’ja ta bawa Mansurah Isah gudunmawar naira N75,000 akan sabon fim din ta mai suna Fanan

 Shahararriyar mawakiya Di’ja ta bawa Mansurah Isah gudunmawar naira N75,000 akan sabon fim din ta mai suna Fanan

Kamar yadda kuka sani tsohuwar jarumar masana’antar kannywood Mansurah Isah ta fitar da wani sabon shirin fim din ta mai suna, Fanan, wanda fim din ya sami daukaka a wajan al’umma masu kallo.

sai a yau kuma jarumar ta wallafa wani labari a shafinta na sada zumunta Instagram akan wata babbar kyauta da abokiyar ta ta mata mai suna, Hadiza Bello Salma Olo, wacce aka fi sani da Di’ja.

jarumar ta bayyana wata abokiyar ta mai suna, Hadiza Salma Bello Olo, wacce aka fi sani da Di’ja, wanda ta bata gudunmawar katin shiga kallon wannan fim din nata mai suna, Fanan.

Inda Di’ja ta bada gudunmawar katin “Free Tickets” na zunzurutun kudade har naira dubu saba’in da biyar N75,000, a matsayin gudunmawar ta.

Inda Mansurah Isah ta bayyana cewa, dama sun dade da Di’ja domin su aminan juna ne wanda abotar su tayi kyau sosai domin Di’ja tana da kirki.

Sannan kuma ta fadi yadda suke mu’amala da aminiyar tata Di’ja wanda ta kasance mace mai son jama’a da kuma sanin darajar zaman tare.

Ga hoton kudaden da Di’ja ta bawa Mansurah Isah a matsayin gudunmawar ta. 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top